Showing 12001 words to 12964 words out of 12964 words
Chapter 5 - TSATSUBA BOOK 8&9 By Abdulaziz Sani .pdf
gane cewa azababben yaki ne aka kaure dashi tsakanin
boka labarusa da jaruma rulaiya, cikin alamun fishi
hailur ya dubi yarima hulkas yace yakai dana ka tafi
izuwa ga jaruma rulaiya wacce ta ceci rayuwarka kuma kayi
mata halarci ka ceci rayuwarta ka bar mu da wannan
tsohon azzalumin abokin gabarmu mu dauki fansa a kansa
koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya ruga da gudu izuwa jikin tsaunin
nan ya kamashi ya fara hawa shi dai wannan tsauni
saboda tsananin tsawonsa duk abin dake kansa daga
kasa ana hangoshi dan mitsitsi tamkar kuda ne
Abinda su yarima hulkas basu sani ba shine ashe can karshen
wannan tsauni wutace take dafa dutse yana narkewa saura
kadan dutsen yayi bindiga ya fara aman ruwan wutar
lokacin da yarima hulkas ya shafe dakiku masu yawa yana hawa
kan wannan tsauni yaga ko rabin tsawon tsaunin bai
kai ba sai hankalinsa ya dugunzuma ya fara
tunanin cewa anya kuwa ma zai iya kaiwa can saman tsaunin
har ya taimaka wa jaruma rulaiya ba tare da ya gaji ba ya
subuto kasa ya hallaka.
++ ++ ++
ACAN kasan tsaunin kuwa sai su sarki hulbasu suka taru
su uku akan sarki shardas suka rinka yankar naman sassan jikinsa da kadan kadan yana ihu
da kururuwa saboda tsananin zafi da zogi da azabar da yake ji
hatta kunnuwan sarki su hulbasau daban -daban suka
yankesu sannan suka kwakule idanuwansa daya bayan
daya
A haka dai suka yi tayi masa azaba kala iri iri har rai yayi
halinsa cikin mummunan kisan gilla wato sarki shardas
ya zama Gawa !
A dai dai lokacin da su hailur suka kashe sarki shardas ne
shi kuma yarima hulkas ya isa can saman wannan dogon
tsauni da kyar da sidin goshi bayan duk jikinsa ya
kukkuje sau tara yana zamewa a saman kamar zai fado kasa amma cikin sa a sai ya sake
chafe tsaunin
hakika yarima hulkas yasha
bakar wuya wajen hawa kan wannan dogon tsauni
domin kaiwa jaruma rulaiya dauki, yana isa saman tsaunin sai yayi arba da jaruma rulaiya
da boka labarusa kwance a kasa jina jina sun yiwa junansu mugayen raunika
suna jan ciki sun nufi inda hular lamsara take wacce
ke sakale a jikin wata karamar bishiya a can karshen gabar tsaunin
A wannan lokaci ne kuma tsaunin ya fara girgiza alamar
cewa wutar da ke ci a karkashinsa na yin bindiga
a sannan ne kuma hailur da sarki hulbasu da siyama suka
hau kan tsaunin da karfin sihirin tsafi kawai sai suka hango
boka labarusa da jaruma rulaiya sun durfafi taba
hular lamsara da hannayansu shi kuwa yarima hulkas ya ruga
garesu da gudu ai kuwa sai saman tsaunin ya dare gida
biyu jaruma rulaiya da boka labarusa suka gangara
zasu fada can kasa inda dafaffen dutsen ke ambaliya
ga wuta a cikinsa muraran
cikin tsananin sa a jaruma rulaiya ta ruko wani dutse bata
fada can kasan tsaunin cikin wutar ba amma sai taji caraf
shima boka labarusa ya cafko kafarta nan fa nauyin boka
labarusa ya fara rinjayar jaruma rulaiya koda ganin haka
sai yarima hulkas ya samu da kyar ya daka tsalle sama ya dira
a karshen tsaunin shima ya cafo hannun jaruma rulaiya ya zamana
cewa nauyinta
dana boka labarusa ya dawo hannunsa, hailur da jaruma siyama da sarki hulbasu
kuwa
sai suka rasa yadda zasu yi su kai wa su yarima hulkas dauki
saboda tsaunin cigaba yake da daddarewa ko taku
daya suka kara hallaka zasuyi , hular lamsara dake sakale
a jikin karamar bishiya itama rawa take yi wanda ke nuna
alamar a koda yaushe itama zata iya fadawa cikin
ruwan wutar nan ta kasan tsaunin ta narke
koda hailur yaga halin da ake ciki sai ya kwallawa yarima
hulkas kira yace yakai dana ka saki hannun jaruma rulaiya
domin ka ceci rayuwarka, kuma kaje ka dauko hular lamsara
kafin ka rasata har abada
Koda jin wannan batu sai yarima hulkas ya juyo da fuskarsa
ya dubi hailur a lokacin da hawaye ya zubo masa yace
yakai abbana ka gafarceni ba zan iya zabar hular lamsara
ba na bar masoyiyata rulaiya ta hallaka saboda
tana bina bashin ceton rayuwata da tayi, nikam na zabi
soyayya akan duniya ku dauki danganar rashina
itama wancan hular ta lamsara gwara a barta ta fada
cikin wutar can ta narke hakan ne kadai zai haifar da zaman
lafiya a duniya
gama fadin haka keda wuya sai nauyin boka labarusa da
na jaruma rulaiya ya rinjayi yarima hulkas su duka
ukun suka rikito daga saman tsaunin suka
fada cikin wutar dutsen dake kasan tsaunin suka hallaka
gaba dayansu !!
Koda ganin abinda ya faru sai hailur da sarki hulbasu
da kuma siyama suka kurma uban ihu suka fashe da
matsanancin kuka na bakin ciki, yayinda nima kaina Al amin
na tayasu.
ALHAMDULILLAH!!!
A nan ne wannan labarin hikayar yazo karshe Inda marubucin
yace domin jin cigaban labarin mu hadu a littafin DARUL DAULAT, domin jin cigaban LABARIN
SARAUNIYA LARBISA,
karfa ku manta cikin labarinta muke sannan muka
tsunduma cikin kuma labarin sadauki Hulkas
wanda sai yanzu aka kammala, idan Allah ya sa littafin
darul Daulat ya fito zan siyo na zo na karas muku domin
kuji yadda wasan zai kasance, kafinnan kuma zanso
kowa da kowa ya baje kwakwalwarsa ayi muhawara akan wannan hikaya
shin Da gaske ne kai/ ke zaku iya shekawa ta sanadin masoyi ?
Nidai... Baridai naji daga gareku
Amma kafinnan nidinne Abubakar Saleh AlQuyramey nake cewa Sai Allah ya kaimu gobe zaku
jini da wani Sabon Littafi wanda nasan cewa zai kayatar daku Matuka
Up Up Up Up Up
comments da likes dinku yana matukar kara mana kwarin guiwa saboda haka aci gaba da
suburbudowa ehem