Showing 6001 words to 9000 words out of 12964 words
Chapter 3 - TSATSUBA BOOK 8&9 By Abdulaziz Sani .pdf
kafafunta biyu, saboda
karfin dukan sai da shima sadauki darkus yayi sama yaje ya gwara bayansa a jikin katangar filin
gasar ya fado kasa a kan fuskarsa fuskar tasa ta dauje jini ya rufe masa idanu kafin a goge jinin
dake kan idanun nasa tuni siyama ta daka sufa a sama izuwa inda takobinsa take ta zarota
daga cikin kasa ta luma masa ita a ciki take takobin ta faso gadon bayansa sadauki darkus yayi
mutuwar tsaye ya sandare kawai sai jaruma siyama tasa kafarta ta sake dukan kirjinsa sannan
gawar tasa ta fadi kasa rikica kamar giwa ta fadi nan fa filin gasar ya rude da shewa gami da
tafi ana yiwa jaruma siyama kirari bisa wannan gasa bayan ta kashe sadauki darkus a wannan
lokaci ne kuma kwatsam sai aka ga jaruma siyama ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya.
.
A guje likitan sarki hulbasu da masu taimaka masa suka ruga zuwa filin gasar kan jaruma
siyama don bata taimakon gaggawa
a dai dai wannan lokaci ne hailur yazo daf da kunnen sarki hulbasu yayi masa rada yace ya
shugabana gada daya fa dakarun sarki shardas da suka rako shadila duk sun sulale sun gudu
ga dukkan alamu sun gano shirinmu da jin wannan batu sai sarki hulbasu yayi murmushi yace
ai nima tun dazu na lura da hakan amma ko kadan ban damu ba saboda na san cewa duk
shirin da zasu yi a yanzu ba zai kai namu ba maza kaje ka karasa shirin komai ni da dakaru
zamu fara yin gaba saika taho da sauran iyalansu gama fadin hakan keda wuya sai aka ga wani
karamin tsuntsu ya shigo filin gasar a sama bai dira a ko ina ba sai akan jaruma siyama wacce
ke kwance magashiyan likita na yi mata magani tsuntsun na dira akanta sai aka ga ta bude
idanunta ta rmike tsaye zumbur tamkar babu abinda ya sameta ta kurawa bakin kofar fita daga
filin gasar idanu.
.
A dai dai wannan lokaci ne aka jiyo sukuwar doki ya nufo cikin filin gasar tashin kurane ya hana
ganin dokin amma kurar na lafawa sai aka ga ashe wani farin ingarman doki ne dauke da
mutum biyu na gaban dokin yarima hulkas ne na bayansa kuwa wani jarumi ne a cikin shigar
bakake tufafi goye da tagwayen masu. .
Koda jaruma siyama ta hango dan uwanta yarima hulkas bisa doki ya tunkarota sai fuskarta ta
fadada da murmushi ta ruga gareshi da gudu. Nan take shima yarima hulkas ya duro daga kan
dokin ya karasa gareta a guje suka rungume juna cikin tsananin farin ciki yana ma tayata
murnar lashe wannan gasa a dai dai wannan lokaci ne yarima hulkas yaji an dafa kafadarsa ta
baya yana waigawa yaga ashe sarki hulbasu ne shima ya rungumeshi cikin farin ciki sarki
hulbasu yayi masa rada a kunne yace bamu da isashshen lokacin.
.
Lokacin yin wani bayani ga juna yanzu domin yin hakan zai sa mu bata lokaci yanzu mun gama
shirin komai dama kai kadai muke jira maza ka dauko yar uwarka akan wannan doki naku duk
da cewa ku uku ne ku sameni a bayan gari mahaifinka ma zai riskemu a can nan take aka
kawowa sarki hulbasu dokinsa ya hau dakarunsa suka take masa baya a lokacin da ya zaburi
dokin nasa da gudu ya fice daga filin gasar.
.
Al amarin da ya daurewa yan kallo kai ke nan suka cika da tsananin mamakin dalilin da ya hana
a tsaya a bayar da kyauta ga jarumar da ta lashe wannan jarumtakar da akayi wato jaruma
siyama nan dai filin gasar ya waste mutane suka tafi suna hasashe da zargin cewa lallai babu
lafiya yau. .
Al amarin dakarun sarki shardas kuwa ashe gaba dayan suka sulale daga cikin filin gasar suka
ruga izuwa cikin daji inda suka sake haduwa suka tattauna akan yadda za su sace gimbiya
shadila cikin ruwan sanyi domin su mayar da ita gida kada fishin sarki shardas ya hau kansu
nan take shugabansu sadauki Murzanu ya dubesu yace na yarda da jarumtakarku da nacinku
gami da iya yakinku saboda haka yanzu zamu koma izuwa cikin wannan birni na askandariyya
daya bayan daya kamar yadda muka hadu a nan yanzu kuma sai dare ya raba sannan zamu
shiga har cikin gidan sarautar sarki hulbasu mu aiwatar da nufinmu.
.
A halin yanzu sarki hulbasu ya gaya mini cewa yanzu zai mana rakiya tare da gimbiya shadila
da dakarunsa domin mu isa gida lafiya na nuna masa cewa na amince da hakan amma na san
karya yake yi so yake ya shirya mana wani tuggun ya cutar damu
shi yasa nace mu rarrabu mu buya a cikin birnin nasa ba tare da ya sani ba tuni na aika da
dakarun yan leken asiri domin su kai labarin abinda yake faruwa ga can birninmu saboda a
sanar da sarki halin da muke ciki ta hanyar karfin sihiri a duk inda yake.
.
Koda sadauki murzanu yazo nan a zancensa sai ya sallami gaba dayan dakarun nasa suka
rarrabu a cikin shiga ta bad da kama suka bi hanyoyi daban daban shi dai sadauki marzanu tare
da wadansu dakarun nasa mutum dari biyu sai suka bi wata barauniyar hanya ta bayan wani
katon tsauni sai da suka yi yar doguwar tafiya ta kusan tsawon dakika dari bakwai da arba in sai
suka yi kicibis da sadauki Ruhaisu babban yaron hailur shima dakarunsa mutum dari biyu da
goma na take masa baya, cikin tsananin kaduwa da mamaki sai sadauki marzanu suka tsaya
cak suka dora hannayansu akan kufen takubbansu domin basu taba zaton cewa za a tarfasu ba
haka, suma su sadauki ruhaisu sai suka dora hannayansu akan kufen takubban aka fara kallan
- kallo, Take sadauki marzanu ya tuno da sadauki ruhaisu sa adda suka fafata kazamin yaki a
can shekarun baya sa adda sarki shardas ya kaiwa kabilar su hailur hari suka karkashe su har
sarki shardas yaje fa hailur kasan wannan tsauni mai tsawon gaske kuma ya dauke matarsa
shadila ya tafi da ita shima ruhaisu ya gene sadauki marzanu sai zuciyarsa ta kama tafarfasa
kamar zata kone saboda tsananin kiyayyar dake taso masa cikin tsananin fishi ya dubi sadauki
marzanu yace yakai tsohon abokin gaba kayi sani cewa jama arku da sarkinku sun dasa mana
bakin cikin da har abada ba zamu taba mantawa dashi ba amma na dade ina jiran wannan rana
da takobina zata dau fansar jinin kabilata akanku na rantse da darajar shugaba hailur
tsakaninmu daku dole ne wasu su zama gawa anan kafin
mu rabu.
.
Koda jin wannan batu sai sadauki marzanu ya bushe da dariyar mugunta yace kai samari
hakika tsautsayi ne ya sa kuka yi wannan babban ganganci na tunanin taremu da yaki da kuma
kokarin kwacewa sarki matarsa, ina mai tabbatar maka da cewa a wannan karon sai mun karar
da ku gaba dayanku ta yadda har abada ba za a kara ganin irin zuri arku ba a doron kasa, koda
sadauki marzanu yazo nan a zancensa sai sadauki ruhaisu ya tari numfashinsa yana mai daka
masa tsawa yace kai wawa mara hankali da tunani shin ka manta ne cewa sarkin naku ne ya
fara kwatar matar mu ?? Yanzu ne zamu dawo da abarmu garemu kuma mu dauki fansar jinin
yan uwanmu da kuka salwantar ka sani cewa ku azzalumai ne masu cin zarafin talakawa sata
kwace da danne hakki tsawon shekaru to ku sani cewa shi ramin karya kurarre ne kuma
gaskiya.dokin karfe ce wanda baya taba mutuwa.
.
Koda gama fadin hakan sai sadauki ruhaisu ya zare takobinsa ya yiwa dakarunsa nuni da a
afkawa abokan gaba, ai kuwa ba su tsawa jiran komai ba sai suka zare takubbansu cikin
hanzari suma su sadauki marzanu suka zare nasu takubban aka ruguntsume da azababben
yaki nan fa wuri ya hargitse kura ta tashi karar karafa da kururuwar mazaje ta fara cika
kunnuwa.
-- -- --
Ragowarrdakarun murzanu kuwa su dubu daya da dari takwas sun sake rarrabuwa izuwa
mutum dari hurhudu wannan shine babban kuskuren da suka tafka domin inda a cure suke
gaba daya sai an kai ruwa rana kuma an kai gwauro an kai mari kafin a ci galaba a kansu.
++ ++ ++
Mutum dari hudu da suka nufi gabashin birnin askandariyya sai suka yi kicibis da tawagar sarki
hulbasu nan ma sai aka kacame da Yaki amma da yake su sarki hulbasu sun ninkasu sau goma
a yawa nan suka karkashesu a cikin kankanin lokaci basu bar daya ya tsira da rayuwarsa ba.
++ ++ ++
Dakarun da suka nufi yammacin birnin kuwa sai sukayi kicibis da yarima hulkas jaruma siyama
da jaruma rulaiya bisa doki guda su uku, koda ganinsu sai yarima hulkas da siyama suka zare
takubbansu da nufin su afka musu amma sai jaruma rulaiya ta dakatar dasu tana mai daga
musu hannu har izuwa wannan lokaci rulaiya bata yarda koda jaruma siyama taga fuskarta ba
domin a rufe take cikin bakin kyalle, take jaruma rulaiya ta duro kasa daga kan dokinta ta dubi
dakarun nasu sadauki murzanu taga basu fi su dari hudu ba kawai sai tayi tsaki sannan ta juya
ta dubi yarima hulkas tace ai abin kunya ne ace mu ukun nan ne zamu yaki wadannan kananan
kwari kawai ku barni dasu rabin sa'a tayi min yawa na gama dasu.
.
Koda gama jin wannan batu sai dakarun sadauki marzanu suka fusata ainun suka zare
takubbansu suka afkawa jaruma rulaiya gaba dayansu Wohoho Hakika mai karfi sai Allah ya
isa kuma duk wanda ya iya ya huta ana fara wannan yaki sai jaruma siyama ta cika da
tsananin mamaki bisa ganin irin jarumtakar jaruma rulaiya da kuma tsananin zafin namanta,
domin duk yawan dakarun su dari hudu sai ya zama na banza saboda duk inda ta kutsa a
cikinsu sai dai kaga maza na zubewa kasa domin gididdibasu ta rinka yi sassan jikinsu ya rinka
zubewa yana faduwa kasa suna ihu kuma jini na feshi da fantsama.
.
Nan fa aka rasa mutum daya daga cikin dakarun wanda ya sami nasarar koda lakutar jikin
jaruma rulaiya nan take jaruma siyama ta raina dukkan jarumtakarta ta fara tunanin cewa duk
yadda akayi wannan hatsabibiyar bakuwar jaruma wacce yarima hulkas yazo da ita ba mutum
bace Aljana ce. .
Koda gama ayyana hakan a cikin zuciyarta sai ta kasa hakuri ta dubi yarima hulkas tace yakai
dan uwana wai shin wacece wannan bakuwar jarumar da ka zo da ita kuma a ina ka sameta har
yanzu ta fa ka bani labarin inda ka tafi ba muka nemeka muka rasa koda jin wannan tambaya
sai jarimi hulkas yayi murmushi yace me yasa baki da hakuri ne yake yar uwata yanzu ina nake
da lokacin baki labari a cikin wannan yanayi da muke ciki ki bari sai mun gama da wadannan
abokan gaba namu tukunna mun isa can inda hular lamsara take in yaso bayan mun
daukota mun kashe sarki shardas sai mu zauna na baku labari keda iyayenmu a cikin nutsuwa
da kwanciyar hankali.
.
Koda jin haka sai jaruma siyama ta bata rai tace yama za ayi nayi ta hakurin jin wannan labari
har sai mun kai ga wannan lokaci me ye tabbacinka ma cewa zamu tsira da rayukanmu har mu
sami nasarar dauko hular lamsara har yarima hulkas yabudi baki zai ce da ita wani abu sai ya
ga jaruma rulaiya ta daka tsalle sama ta kama yin wata irin katantanwa a sama tana fille
kawunan dakarun sarki shardas nan da nan ta karar da sauransu gaba daya ya zamana cewa
babu dayansu da ya rage a raye saboda tsananin mamakin wannan gagarumar jarumtaka da
jaruma rulaiya tayi yarima hulkas da siyama basu sansa adda suka wangame bakunansu ba
suna kallonta. .
Koda jaruma rulaiya ta dago kanta ta dubesu sa adda take goge jinin takobinta a jikin gawar
abokan gabar da ta kashe taga ririn kallon da suke yi mata na al ajabi sai tayi murmushi ta dubi
yarima hulkas tace kuzo mu yi sauri mu karasa gaba tunda bamu san halin da sauran yan
uwanmu suke ciki ba ba tare da wani bata lokaci ba sai suka kara hawa kan wannan dokin sihiri
na jaruma rulaiya su ukun suka zabureshi da gudu izuwa gaba saboda girman wannan doki da
cikarsa duk su ukun sai da suka zamo yan kanana akansa.
++
Acan Inda yaki ya ruguntsume kuwa tsakanin su sadauki ruhaisu da su murzanu abin ya
kazanta babu kyan gani saboda karfin yazo daya domin ragargazar kowanne bangare ake yi
har ta kai cewa ana ta yin ragas sai da aka shafe sa a daya da rabi ana wannan mugun yaki har
ya zamana cewa an karar da gaba dayan dakarun kowanne bangare saura mutum biyu kacal
suna fafatawa, wato saura Sadauki Ruhaisu da Murzanu gashi dai kowannansu ya yiwa dan
uwansa raunika har guda uku uku jini na zuba a jikinsu juwa na dibarsu amma saboda tsananin
nacinsu da mugun buri na son ganin bayan juna kowannansu yaki yarda yaje kasa Lokacin da
bala'i yakai bala'i ya zamana cewa sun gaji likis sai suka zube kasa bisa guiwoyinsu suna haki
da numfarfashi kamar ransu zai fita bayan dan wani lokaci sai kowannan su ya mike tsaye da
kyar sannan suka ja da baya taku bakwai bakwai tamkar sun hakura da yakar juna kwatsam
kuma sai suka rugo da gudu izuwa kan juna suna masu kwalla ihu cikin mugun nufi duk wanda
yaga lokacin da wadannan manyan jarumai suka tunkari junansu kasan cewa mugun gamo za
ayi ko dai a mutu ko kuma ayiwa juna mugun lahani da zai iya zama sanadin Ajali, ai kuwa yana
ragewa saura taku uku kacal su hadu sai kowannansu ya daka tsalle sama suka kaiwa junan su
suka da takubbansu cikin sa'a kuwa kowannansu ya lumawa abokin
fadansa takobi a ciki ta faso ta gadon bayansa lokaci guda suka kurma uban ihu sakamakon.
.
Tsananin zafi da zogin da suka ji suka rikito kasa a matukar galabaice suka kurawa juna idanu
sa adda suka fara kakarin mutuwa bisa mamaki sai sadauki murzanu yaji sadauki Ruhaisu ya
bushe da dariyar farin ciki don haka sai ya dubeshi cikin matukar karfin hali ya budi baki da kyar
yace yakai makiyi abokin gaba tayaya aka yi kai da zaka mutu amma kake yin dariyar murna,
koda jin wannan batu sai sadauki ruhaisu ya yi kakin jini ya tofar sannan shima ya budi baki da
kyar yace ina farin ciki ne zan mutu bayan na cika burina na yiwa takobina wanka da jininku
yanzu ne yan uwana da kuka kashe zasuyi barci mai dadi a cikin kabarurrukansu kuma idan
naje na riskesu zasu yi alfahari dani kai fa da wani farin ciki zaka mutu ? Shin zakayi alfahari ne
da cewa ka mutu dan bautar sarki shardas wanda ya maishe daku karnukan farautarsa ko
kuwa ?
Me kabar wa iyalinka wanda zasu cigaba da rike kansu bayan ka mutu ?
Na sani cewa kan yiwa sarki shardas bauta saboda kana tsoronsa amma ba don kuna samun
wani abu a hannunsa ba yanzu me ce ribarka a cikin bautar sarki shardas ga shi kayi mutuwar
banza idan ma shardas yazo nan yaga gawarka yawu zai tofa maka tunda baka cika aikinsa ba
wannan batu sai nan take sadauki murzanu yaji yayi nadamar rayuwarsa a karon farko domin
ya gane kuskurensa nan take hawayen takaici da bakin ciki ya zobo masa kawai sai ya sake
dannan takobin Ruhaisu a cikinsa ya zama cikakken Gawa.....
Wow Nima AlQuyraemey A nan zan dakata sai Allah ya kaimu Gobe zakuji ni da part na karshe
a cikin littafin tsatsuba Kafinnan nidinne dai AlQuyraemey
TSATSUBA
Littafi Na Tara (9)
Part D.
Marubucin Littafin
Abdul azis Sani M/Gini
Abubakar Saleh AlQuyraemey
.
Koda jin wannan batu sai nan take sadauki murzanu yaji
yayi nadamar rayuwarsa a karon farko domin ya gane
kuskurensa nan take hawayen takaici da bakin ciki ya zobo masa kawai sai
ya sake dannan takobin Ruhaisu a cikinsa ya zama cikakken
Gawa.
Shi kuwa sadauki ruhaisu yana cikin wannan hali ne
na kakarin mutuwa ya hango hailur bisa doki da a
sukwane tare da sauran tsirarun yan kabilarsu
Tun daga nesa da hailur ya hango sadauki ruhaisu
zaune a kasa dirshan ga takobi a cikinsa sai ya rusa
uban ihu cikin kwalla masa kira kuma ya fashe da
kuka yana mai karawa dokinsa kaimin gudu
Yana isowa daf dashi sai yayi turjiya ya sauko
daga kan dokin ya durkushe a gabansa sannan ya kamashi
ya rungume a kirjinsa yana mai sake fashewa da
sabon kuka cikin Karfin hali sadauki ruhaisu ya daga hannunsa
ya kama kumatun
hailur suka dubi juna kowannansu na zubar da hawaye
amma sai sadauki ruhaisu yayi murmushi a gareshi
yace yakai dan uwana bai kamata kayi mini kuka ba
tunda na mutu akan tafarkin cika burin kabilar mu
alfaharina guda daya ina so ka dauke gawata ka kaita zuwa
can asalin birninmu wanda sarki shardas ya baje ka binneta
wannan itace kadai wasiyyar da zan bari bayan
raina
koda gama fadin haka sai idanun sadauki ruhaisu
suka kafe suka daina motsi kuma gaba dayan jikinsa ya
sandare
koda ganin haka sai hailur ya sake kwarara uban ihu a
karo na biyu ya rungume gawar sadauki ruhaisu
kuma ya sake fashewa da matsanancin kuka
nan take ragowar dakarun nasa dasu shadila suka kamu
da tsananin tausayi kuma suka kama kuka
basu bar wannan waje ba sai da hailur ya sa aka je aka
dauko akwatun gawa na katako aka sa sadauki ruhaisu
a ciki aka kulle sannan suka kara gaba inda suka iske tawagar
sarki hulbasu da su yarima hulkas suna yin wata irin
tafiya ta ban Al'ajabi domin da karfin sihirin tsafi suke yinta
cikin tsananin gudu na ban al ajabi kuma