Showing 18001 words to 21000 words out of 27196 words

Chapter 7 - HALACCIN SARAUTA Book 1 to End by Benaxir Omar.txt

dazai cika,
yasa hannu sannan yace afara duba jinin , jininsu yazo
daya atake aka diba , leda biyu yabayar yakwanta don
yahuta bayan kwana uku zaa cire kidney dinshi daya
abawa aliya, har kuka saidayayi akan gadon, yanason yar
kanwarsa Bangaren yusif kuwa yarasa mezaiyi murna?
haushi?takaici? Dole dai yayi dukka dole yayi farincikin
cewa sufyan yayanta ne ba aure a tsakaninsu balle
yadamu , nabiyi kuma dole yaji takaici da aliya taboye
masa asalin cewa sufyan yayanta, tabbas hakane abdullahi
yasanar mishi sufyan dan marigayi galadima ne anma
baitaba kawowa aliya ba, lallai shi soko ne, meyasa aliya
taboye mishi wannan bayan yasan babban sirrin ta balle
wannan, shidai yanzu duk yarude damuwansa tafarka Inna
kuwa duk ta tsure duk yanuwa na nesa saidata kira tasanar
musu, antynsa ta abj ma tace zata biyo jirgi ta taho
washegari, anan yusuf yasan cewa lallai aliya tanada gata,
anma meyasa suka barta take bulayi agari? Abdullahi kuwa
ayanzu yatabbatar da inda yasan aliya. Tun randa yafara
kallonta yasan cewa yasanta awani gu!, tabbas itace
kanwar sufyan wacce suke wasa da ita ya kyalla yace
yana sonta, wacce yanemeta yarasata, akacemasa tatafi
abuja dazama, wacce itace first love dinshi, ba shakka itace
shiyasa duk lokacin dayaganta cikin wani hali baya
sharewa saiya taimaketa, tabbas itace innalilahi yazaiyi?
Yanzu yafarajin sonta danye, ruwa tsundum yadawo,
yazaiyi da yusuf? Yazaiyi yatabb[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 23
 benaxir  October 15, 2015  Hausa Novels
 105 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Tunaninsa
duk yajuya, alokacin suka nufi fannin da aka kwantar da
sufyan abdullahi ne ke zaune agefensa inda yake zura
masa ido sufyan yayi murmushi sannan yace “karka damu,
zageni kawai raina baxai baci ba,” hakan yasa abdullahi ya
makeshi dakarfi tareda cewa “soko, wawa!ka cuceni wlh,
kacemin harda ita a rasuwa meyasa ka boyemin tana
raye?”sufyan bai damu da zagin ba yace “yazama dole
ne,dole in boye wa duniya wacece ita, ko so kakeyi itama
abimin ita akashe?” Shidai abdullahi baice komi ba yasan
cewa abun yanaciwa sufyan rai shiyasa baiyi wani rikici ba
har suka sallameshi daga bed rest din dasuka bashi
alokacin sukaje dubata, tafarka anma ta jigata sosai, har
ranta taji haushi asalin haushi taji don tabbas tasan cewa
tanada matsalan kidney tanemi nasayarwa ko zata siya
asaka mata tafasa daga baya acewanta kar tazo tafara
ciwo bata cika burinta ba, gwara tagama idda cika burinta
kafin ta kwakulo wani ciwo gashi yanzu sun nemo, kuma
sunaso sucire tasan duk yadda zatayi suhakura bazasu
hakura ba dole tabari su saka, fatanta Allah yatada
kafadunta don ta cimma burinta Sufyan ne da abdullahi
suka shigo dakin ta tsaya ne taga ko zataga yusuf bata
ganshiba nan da nan zuciyanta ya sosu sosai, abdullahi
kuwa saiyake ganinshi kaman bakon mutum agareta,
kaman bakon fuska, tayaya zaifara fuskantarta? Shikam
yadawo ruwa tsundum!, zama sukayi agefe sufyan yariko
hannunta cikin tausayi, yanason kanwarsa gani yake itace
sauran bangaren jikinsa, ganin basuda niyya magana ta
bude baki da kyar sannan tace “meye haka kaman na
mutu!” Sufyan yayi murmushi tareda cewa “bazaki mutuba
ko raina zan iya cirewa nabaki don na sadaukar dakaina
agareki”abdullahi hawaye ne ke zuba masa a ido anma
yanata kokarin yaga yadanne yashare saboda kar agane,
duk lokutan dasuka kasance tare suna yara yatuna, yatuna
lokacin daya mata alkawarin zama da ita ko wani hali na
rashi ko samu, yamata alkawarin taimakonta cikin kowani
hali ko da kuwa zai rasa ransa ne, cikin sanyin murya yace
“yajikinki?” “Dasauki ranka shi dade” a karo na farko kenan
dayaji wani iri data kirashi haka yasan ada takan ce masa
“yayana” bazai iya zama ba bai amsata ba yafice yabar
dakin waje yafita yashiga motarsa kuka yafarayi sosai,
tunda yataso yayi wayo baiyi kukan dayayiba, nadama duk
ta isheshi, toh ni benaxir damuwan meyakeyi? Aiba laifinsa
bane, yusuf ne yashiga dakin alokacin inna tagama
jimaminta tana zaune itama agefe shidai sufyan yaki
motsawa, yusuf yazauna agefe tareda cewa “yajikin?” Bata
amsa shiba anma ta gyada masa kai, hakan yasa yaja gefe
yazauna duk yadamu, likitan ne yashigo don dubata bayan
dube dube yace sufyan yazo su gwada kidney dinshi, yabi
likitan inda sukaje akayi scanning aka duba kidney dinshi
da lafiyansu sannan ko shima zai iya badawa wani bayan
dogon bincike likitan yakirashi kanshi a sunkuye yana cewa
“kayi hakuri sufyan, bazaka iya bawa aliya kidney dinkaba
saboda kaima naka basuda isheshen lafiya,” wani dogon
salati inna tayi sufyan kam daskarewa yayi agun, yagagara
motsi shikan hankalinsa yatashi, yazaiyi da rayuwansa?
Anan yafara rokon likitan yakawo dabara ataimakawa yar
kanwarsa anan likitan yakawo shawarar akira yusuf, nan
da nan suka kirashi atake ya amince zaibayar inda akace
yashiga don amasa scanning shima, bayan ankammala
likitan yace washegari zasuji result tunda dare yayi,
hankalinsu duk yatashi innace ta kwana a asibitin abdulahi
da yusuf suka koma gyda, ko yusuf dayaga falmata zata
dameshi fitowa yayi yabar masu gidan, Washegari karfe
tara anty ta iso asibitin yusuf, abdullahi da sufyan suma
duk suna gun, likitan yakirasu inda yabawa yusuf hakuri
cewa “yusuf you are not a donor donhaka bazaka iya
bataba, kidney dinta bazai karbi naka ba” tunda sufyan
yake baitaba fuskantar tashin hankali irin wannan ba
baisan sanda yafara fidda hawaye da gumi ba, yusuf kam
kuka yake wiwi, yarasa yazaiyi anan duk suka fito abdullahi
yagagara tafiya, hankalinsa yatashi office din yakoma
tareda cewa “dr. Kidney dina guda dayace tayi saura, ko
akwai hanyan dazan iyabata ? Tunda kunce agobe
kukeso!,” Likitan yakalleshi alaman mai tababben hankali
sannan yace “kayi hakuri kanaso ka mutu ne?” Cikin tsawa
abdullahi yace “meruwanka da mutuwa ko rayuwata!
Kagayamin hanyan dazanyi”cikin tsoro likitan yajawo files
dinsa sannan yace “Inhar zaka bada sauran kidney dinka
zakadawo bakadashi ko daya, toh munada dialysis
machine wanda yake aikin da kidney yakeyi, dashi zakana
amfani har lokacin da jikinki zatayi resistn ,” abdullahi yayi
hamdallah sannan yace duba kagani ko zan iyabata inyaso
kacire ayau dinnan kanemo danwanka zanbiya ko nawane,
kusamu kusamata kozata sami lafiya, sannan karka yadda
kafadawa kowa!” Likitan ya tsorata shikam yakasa gane
kansu, gashi dai danuwanta bazai iya bada nashiba, yusuf
kuma falmata ce ta aiko wa asibitin wasika cewa karsu
yadda su dauka nashi susawa wata banzar bawa ko
dukkansu zasu rasa aikinsu, hakan yasa duk suka tsorata
suka cemasa nasa bazai karbu ba, ga abdullahi mai mata
anma ya yanke shawaran yahakura da duniya, dahaka
yaduba yaga komi daidai atake yayi magana da likitan
dazasu cire, adaren ranan suka cire masa kidney dinshi
kwaya daya, masha Allah sadaukarwar soyayyaya da cika
alkawari tabbas abdullahi yanuna nagarta da hallacin
sarauta, yanuna cewa inhar baicika alkawari a matsayinsa
na masoyinta ba albarkar sarautar gydansu zaisa yacika,
yagwada mata cewa agydansu yatashi da nagarta,
baimanta da alkawarin tun suna yara ba yau yacika. Yacika
mata alkawarinsa nacewa zai tsaya agefenta, zai taimaketa
koda kuwa zaizama ajalin rayuwarsa, acikinmu mutane
nawane suke cika alkawari????????? Sufyan kuwa yana
wata duniya daban don neman kidney dazaasa wa aliya
shida yusuf sai kiransu akayi aka sanar dasu abdullahi
yabayar yusuf dayake tuki saidayayi wawan reverse
yatsaya sanin cewa abdullahi kidney dinshi dayace tarage
suna nufin yabada wannan? Lalle kam akwai rikici,
abdullahi nason al[truncated by WhatsApp]

HALLACIN SARAUTA 24 & 25
 benaxir  October 16, 2015  Hausa Novels
 137 Views
[10/16, 7:54 PM] Benaxir omar: HALLACIN SARAUTA
NA BENAXIR OMAR sufyan ne yarikeshi tareda cewa “wuce
muje” bai iya tuka motan ba hakan yasa sufyan yafito
dashi yakoma yafara tukawa asibitin suka koma dasauri
suka shiga, alocin matan abdullahi kuka take sosai
hankalinta yatashi nan da nan magana yazaga gari, har
fada tunda yakolo take hankalinta baitaba mummunan
tashi irn na wannan karon ba, a gigice tabar fadan ta
umurceta da akawota asibitn, kuka take sosai alokacin data
iso asibitin yacika tam, mutane saisukaja gefe kawai suna
kallon ikon Allah, yakolo ne ta bukaci tashiga dakin anan
likitan yasa aka shigar da ita, don yace mata dan nata
yanada jiki mai kyau tun awa biyu dasuka wuce idonsa
biyu, hankalinsa akwance duk da zafin ciwo dake damunsa,
cikin zafin murya da raunin zuciya tace “meyasa zakayi
haka abdullahi? Baizama dole don zaka gwada mata kana
sonta kasa rayuwarka a hatsari, haba abdullahi yanzufa kai
rayuwa batada amfani agareka zaka iya mutuwa akoda
yaushe aduk lokacin da jikinka tagaji da wannan injin, haba
abdullahi!!” Tunda yake baitaba jin mahaifiyarshi takira
sunanshiba yasan cewa ta tabu matuka, donhaka yamika
mata hannunsa tarikoshi gam kaman bazata sakeba “tun
ina karami kin koyamin muhimmanci rikon alkawari da cika
alkawari, a tarbiyan gidanmu na sarauta natashi naga
mahaifina yana cika duk wani alkawari daya dauka ,
meyasa nima bazan kwatanta hakaba? Shin bakimin
kwadayin aljanna? Shin bakimin kwadayin rahaman Allah?
Don Allah ki kwantar da hankalinki, nasan ina son aliya
anma cika alkawari shine musababbin bata sauran kidney
dina, inban bataba duk nan babu mai bayarwa, sufyan
nashi ba lafiya, yusuf kuma nazo wucewa naji gimbiya
falmata ta aiko ace mishi karsu yarda subada na yusuf ko
abakin aikinsu, kuma nasan cewa ko batayi magana ba
bazaitaba yiwuwa yusuf yabada nashiba, tunda kinga yana
shaye shaye bazai yiwu ace kidney dinshi lafiya lao ba,
annemi nasayarwa baasamu daidai nataba, dole nacika
alkawarin dana mata nacewa koda raina zanbayar don
naceci rayuwarta, kitaimaka ki bano kwarin gwiwa don
insamu inwarke, mutuwa kuwa inna mutu lokaci nane babu
wanda yake mutuwa ba lokacinsa ba, ” yakolo kuka take
sosai tareda hamdala azuciyanta tana godewa Allah
dayabata yaro mai ingantarcen tarbiya, mai kyan hali tunda
take bata taba ganin abdullahi yayi alkawari yasaba ba,
mutum ne mai daraja dan adam, taja numfashi sannan tace
“nagode sosai daka fahimtar dani, Allah yarayamin kai
yabaka tsawon rai yataimakeka,Allah yadaga kafadunka”
anan tamike tabar dakin kuka yacita sosai balle matarsa
karshe gado aka bata anan likitan yasamu tanada ciki ga
murna ga bakin ciki, yusuf kuwa yana makale a gefen
dakin tiyatan dazaayiwa aliya, yaki motsawa azamansa
agun falmata tasa akirashi yakai sau biyar daga karshe
tashi yayi yawanke dogarin da mari saida aka fita dashi
yace karsu dameshi, sufyan kuwa zuwa yayi yasiyo
abubuwan dazaa bukata na abdullahi da matarsa, Mai
martaba sarki yaji bakin ciki sosai musamman da falmata
tace masa wa baiwa yabada kidney dinsa, shikadai a fada
yarinka fada, daga baya ne da yakolo ta koma gida dakyar
a kukan nata sai ganin mai martaba tayi akanta yana
shigowa yafara fada akanme zatabarshi yafita haryaje
yabada jikinsa ganin yadda yake fadan tasan cewa falmata
ta shuka wani makircin anma yazatay? Dole tamai bayani
hakan yasa tazaunar dashi tamai bayani dalla dalla tana
kuka yaji tausayinta sosai yakuma ji son dansa yakaru,
rungumarta yayi yana lallashi [10/16, 8:21 PM] Benaxir
omar: HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Yusuf
kuwa tun yana jira yaji bazai iyaba, kuka yake wiwi sufyan
yafara lallashinsa anma duk dahaka yusuf yagaza yana
kuka yana cewa “aliya kitashi, namiki alkawari bazan kara
shan wani abuba, aliya na nutsu nadaina duk abunda
nakeyi, aliya wlh inasonki, dukkan kai nason dukkan ki, “jin
abun yadawo sumbatu yasa sufyan yabashi gu, antyn
abuja da inna dakuma yanuwa kakkani duk suna zaune ana
jira likita yafito yace ansaka mata lafiya nima benaxir ina
tsaye agefe inata adduan Allah yasa ayi aiki lafiya Bayan
awanni kadan sai gashi likitan yafito sun bazama kanshi
kaman zasu cinyeshi, anan yabukaci sufyan yazo nan da
nan yusuf yabisu likitan zaiyi magana sufyan yace
“badamuwa ana tare” binsa sukayi office suka zauna
sannan yafara bayani “anyi aiki lafiya alhamdulilah jikinta
kuma yakarba, yanzu bata tashiba don Allah duk wani abu
na tashin hankali kar ayi agabanta, sannan inaga kar
agayamata wa yabata kidney dinshi yanzu harsai ta
warke,” anan sufyan da yusuf suka mishi godiya sannan
yamusu bayani akan akwai nurse dazatazo tamusu
magana, suka fito ahaka sannan inna tamike tareda
tambayan sufyan yace anyi lafiya, dakin abdullahi yanufa
don suyi magana anan yace masa ai anyi aiki lafiya anma
bata farka ba, yayi murmushi sannan yace “ina rokon
alfarmarka” “Na mefa?” “Don Allah kasamu kayiwa yusuf
magana da duk wanda yasan maganan nan wanda kasan
zai iya fadawa aliya, don Allah kar afada mata nina bata
kidney acemata siya akayi, ” “Anma kasan dole tasani ko?
Tunda yanzu bakamn da ba, dole kana yawan zuwa asibiti
maganan gari baya buya” “Nidai kamin wannan alfarma
abari sai bayan raina afada mata, don fada mata yanzu
zaisa tafara diddigi banaso tagane cewa nine masoyinta
dana guje mata,” “Ba gudu mata kayiba, ita tagudu maka
kadena fadan haka” “A a nidai don Allah kar afadawa kowa
maganan nan tawuce, karta sani” Dahaka sufyan ya yarda
bayan fitowarsa yakira yusuf yamasa bayani anma yaboye
masa dalilin dayasa abdullahi yayi haka shidai yusuf yasan
cewa abdullahi na son aliya ne inbahakaba bazai taba bada
wani fanni na jikinshi yazabi mutuwa akan rayuwa ba,
dahaka sufyan yabarshi harzai fita yaci karo wani likita
wanda haushinsu yakeji alokacin akan meyasa zasu yadda
abdullahi yabada jikinsa, ba gaira a dlili ya makuro likitan
tareda tambayansa dalili, likitan yana neman hanyan
kwacewa karya mutu don numfashinsa daukewa takeyi,
dayaga zai wahala yace “gimbiya falmata ce tahana mu
yarda kabayar” ahankali yasake wuyan tareda cewa
“mekace?” “Gimbiya falmata ce ta aiko da wasika akan duk
wanda yacire wani bangare na jikinka abakin aikinsa”
Sakeshi yayi yabar corridor din mota yanufa yayi wani
wawan[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 26
 benaxir  October 17, 2015  Hausa Novels
 122 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Ayadda ya
isa kofan gate din sukansu dogaran saida suka matsamishi
sunga yadda yashigo da motan, abude yabar motan da
mukullin ajiki yashige cikin gidan a birkice fannin falmata
yanufa a harzuke dogarai dasuke kofan gun suna ganinshi
suka matsa masa don ayadda yazo kaman guguwa ne ta
tunkudoshi tana zaune a falo rike da waya a kunnenta
yashigo fuskarshi a daure bata taba ganinshi haka ba, tuni
tasha jinin jikinta ta tabbata angaya masa, ajiye wayan tayi
tana kallonsa,cikin hushi da zafin murya yace “inaso kibani
hujjanki nashiga rayuwata, kibani hujjanki na takurani,”
dakewa tayi duk da ta tsorata “bakayi girman da zaka
yanke wani hukunci dakanka ba!, inbanda dolonci irin naka
nadan fari tayaya zaka cire wani fannin jikinka a
matsayinka na dan sarki, sannan kuma sarki anan gaba
kace zaka bawa baiwa?!” Murmushi yayi wanda tafi kuka
ciwo yace “yanzu na fahimci inda kika dosa, toh inaso yau
kisa aranki bakida da , sarki kuma kike can kinemi wanda
zai cika miki burinki, baiwa???? Itace ta nutsar dani,
takuma ladabtar dani abunda ke kika gagara yi!” Yana
fadan haka yajuya yafice, ji tayi kaman ya watsa mata
ruwan zafi, salati tayi tana rike kirjinta, yau dan cikinta
shine ke mata gori,haryazo corridor yaga jakadiya yasan
ita aka aika tafadi sakon, daya makuro wuyanta wani kara
tasaka domin a tsammaninta zata leka lahira ne, dakyar
dogarai suka karbeta suma yakoma kansu akarshe rikeshi
akayi don abunsan yafara dawo karamin hauka, kuka
yakwanta wiwi yanayi a daki tunda tahaifeshi baitaba tur da
halayenta irin na ranan ba, yayi wadaran da halin
mahaifiyarsa akan meyasa bazata koyi nagari ba don itama
nata suzama nagari, Matar abdullahi tafarka jikin nata da
dan sauki gashi cikin mai laulayi ne, duk tadamu kishin
mijinta yashiga ranta duk da yamata bayanin cewa arashin
na mutane ne yabada nasa, toh ita tambayan anan shine
yasan guda daya ne yasaura mishi akan meyasa zai
bayar? Yana nufin zai mayar da ita karamar bazawara!
Lallema duk tabi tadamu jira take yawarke don tasauke
masa farillai da mustahabban rashin mutunci,aliya sai sha
daya na dare tafarka da salatinta tafarka tuni sufyan ya
kirkira su kowa yanufo gun dama abdullahi na asibitin, sai
inna, yusuf kuwa yanacan shima bakanshi, bude idonta
taga sufyan akanta duk tarame tayi kashin wuya, lebenta
ya bushe idonta ya kumbura yayi jaa yariko hannunta yana
murzawa idonsa fir akanta, dakyar tadan murmusa sannan
tabude baki zatayi magana anma takasa, yace mata tayi
shiru kartayi magana Allah yabata lfy. Inna ma sai faman
tofa mata addua take taki motsawa daga baya kuma
tamike ta dauro alwala tafara sallah tana addua Allah
yadaga kafadun aliya, baccine yakara kwasan aliyan
sannan yazauna agefe shima ya gyangyada sai asuba
dayaji kiran sallah sai ya mike yafita dauro alwala yanufi
masallacin asibitin, inna kuma a dakin tayi sallah, aliya sai
karfe goma ta farka yusuf shima yashigo anma kana
ganinshi kassan yana cikin damuwa,idonsa radau radau ya
kumbura, yazauna agefenta itama kallonsa take yariko
hannunta jikinsa yayi sanyi lao itakuma zafi kaman wuta,
batayi magana ba har lokacin tagagara magana, yusuf
kuwa shi dazaa cire zafin yakoma kansa dayafi kowa farin
ciki, yazura mata ido alokacin likitan yazo dubata donhaka
suka fita bashi wuri. Dawowansu dakin bayan likitan
yagama yusuf yazauna agefe. Can dai aliya ta daure
sannan tace “wayaban kidney dinshi?

HALACCIN SARAUTA 27
 benaxir  October 18, 2015  Hausa Novels
 126 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Bai amsa
tambayanta ba yace “yajikin naki? karki kara magana” bata
kara cewa komi ba, tana tunani ne taga waye yabata, taga
yusuf garau donhaka tasan bashi bane, sufyan ma
taganshi tasan bashi bane, taga inna taga antyn abuja duk
sauran tsofi ne donhaka taciresu a lissafi, saikawai tasa
aranta na siyarwa aka saka mata, nan tafara adduan Allah
yasaka da alheri wa duk wanda aka samata kidney dinshi,
yusuf yaki motsawa agefenta itakuma idonta zur akansa
shima hakan jiyake kaman ya hadiyeta, inna ne suka shigo
anma duk dahaka yusuf yaki matsawa saidai kowa
yagaidata daga nesa, sufyan daya shigo yaganshi yasan
meyakeji donhaka yajashi dakyar yace yaje yahuta ganin
sufyan yadage yasa yusuf yanufi dakin likitan ranshi abace
yatuna da tsohon bacin ransa, likitan yazaro ido don yaji
labarin yusuf yasan mesuka aikata donhaka tuni yashirya
dazuwansa , zama yayi akan kujera sannan yace masa
“inaso infarajin bayani daga farko meyasameni , me kuma
kuka shuka da gimbiya kuka min karya!, ” yayi gyran murya
sannan yace “yarima duk abinda yafaru kadaukeshi
kaddara tun asali dana dubaka kai kanka bakada ishesshen
lafiya, abubuwan dakake sha sundan maka lahani kadan,
kidney dinka basu da lafiyan dazaka bawa wani, ana cikin
haka kuma mahaifiyarka ta isar da sakon karmu cire,
dafatan zaka fahimceni” yusuf bai ce komi ba yatashi
yanufi kanshi fitsarine likitan baiyi a wando ba domin ya
mugun tsorata yusuf yariko kwalan rigansa sannan yace
“daga yau duk abunda yashafi aliya, babu wasa aciki inaso
kasan dahakan” Juyawa yayi yabar office din dakin da aka
kwantar da abdullahi yanufa idonsa biyu yanaso
asallameshi anma likitan yace bayanzu ba saiya kara
samun sauki donhaka duk asibitin tahau masa kai, Yan
biyu ne hassana da hussiena suka shigo kowacce taci
kwalliya dakin da abdullahi yake aka nuna masa suka
gaysheshi da jiki sannan suka ajiye ledan hannunsu yusuf
yafita alokacin, harzasu wuce abdullahi yace kucika
ladanku mana ku gayda aliya, hussiena kaman tace a a
anma tana kunyan abdullahi donhaka tace masa toh, dakin
da aka kwantar da aliya suka nufa, idonta biyu bakowa a
dakin sai inna suka gaysheta kamar abun arziki sannan
suka nufi gadon aliya hassana tagaidata yayinda hussiena
ke mika mata sakon harara, aliya murmushi tayi don tasan
dalili, can dai hussiena takalli tareda cewa “anma kinsan
yarima yayi asaran kudin tara? Ace wannan zaicire sauran
kodan shi kwaya daya yamika mata? Dasunan soyayya?
Mayya duk yaran sarkin kin mamaye” inna ce tanufo kansu
tareda katseta tanacewa “kuyi hakuri baason daga mata
hankali” aliya ce ta katse ta tareda cewa “wani yarima?”
Hassana taja tsaki tareda cewa “wanne kuwa abdullahin
dakika nakike wa” wani nauyi taji akanta kaman ansauke
mata dutse (Kuyi hkr kumin uzuri for today , ciwon ido ya
matsoni kar na muku typing shirme lols, and plx masu
tambaya ko benazir macece ko namiji letz make it these
way , ni Macece, a 20yr old single lady, nd plx masu
dropping numbansu a blog dina kudena plz

HALACCIN SARAUTA 28
 benaxir  October 21, 2015  Hausa Novels
 111 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Fita sukayi
adakin suka barta da bugun zuciya har cikin ranta ta
tsorata kwanyanta yafara caji, tasan haka kawai mutum
bazai cire koda yabayar ba, wani zuciyan tace yanzu haka
tsabar zumuncin dake tsakaninku ne, harta bar maganan
ahaka saikuma ta tsorata data kara tunawa sunce guda
dayan data rage masa yabayar, inna ce tariketa ta kwantar
da ita anma aliya ta gagara kwanciya duk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login