Showing 21001 words to 24000 words out of 27196 words

Chapter 8 - HALACCIN SARAUTA Book 1 to End by Benaxir Omar.txt

Advertisement

ta tsure
hankalinta yatashi tuni tamike a tsaye tana cewa “inna
nikam ko dai zanfita ne? Ina yaya?” Duk a gigice take hakan
yasa inna tarikota tareda cewa “kwanta, barin kira miki
yayankin” fita tayi don tanemo sufyan bata ganshi ba
donhaka saitayi magana da nurse daya don su samu
sudubata a lokacin shigowansu jikin ya rikice aliya duk ta
tsorata sosai nurse dinne ta rikota itakuwa duk ta gigice
dakyar aka kwantar da ita wani irin kuka take mai shiga
zuciya tana kama jikin inna, “inna kitaimaka kinemomin
yayana” batasan meye matsalarta na, anma ta tsorata
bashiri tafita duk da batada tabbacin ko zataga sufyan din
filin asibitin tanufa tazaga bataganshiba donhaka takoma
ta dakin abdullahi tanufa ganinshi azaune a rikice tace
“yarima ina sufyan? Kataimaka ka nemoshi munshiga uku
aliya” agigice yamike yacire kalulan hannunsa sannan yace
“muje” dagudu gudu suka nufi dakin alokacin aliya ta
bankade nurse din tana cewa akaita gun sufyan, abdullahi
ne yakomota yariko hannunta sannan yace “aliya kikalleni”
kallonsa tayi agigice tarude anma yadda ya zura mata ido
tuni taji wani nutsuwa yashigo mata, ya kwanto mata,
hannunta na bari tace “yariiiiiim” “Shhhhh karkiyi magana
kiyi shiru” Shirun tayi kaman yadda yace addua yatofa
mata sannan yace wa inna insha Allah bazata kara firgita
ba, zama yayi dirsham agefenta acewarsa sai sufyan yazo
zaitafi, wata nurse ce tashigo tareda rokonsa yakoma
daure fuska yayi kaman yaga malaikar mutuwa yana cewa
ba inda zanje kuma karta nima takurashi, hakan yasata fita
don tasanar da manyanta, inna tayi tayi dashi yamike
yafice anma yaki yarda, tuni tafara nadamar kiransa anma
abdullahi yakafe, aliya kuwa tana jingine a kwance tana ta
tunani, tarasa tayaya zata tambayeshi inkuma yabata da
zuciya daya ne fa? Yazatayi? Wani irin nauyinsa takeji
yanzu fa duk gadaranta akwai kidney dinshi ajikinta, ita
damuwanta sufyan yazo ta tambayeshi gaskiyan alamarin,
Sunfi minti talatin ahaka kafin yashigo, shigowarsa yasamu
aliya tayi bacci abdullahi na gefenta, tuni yanufo kansa,
“kaida bakada lafiya kazo gadin wata marar lafiyan?” “Kai
nake jira kadawo, firgita takeyi shiyasa nayi hakan” sufyan
ne yajashi suka nufi dakin da aka kwantar dashi, sannan
yadawo dakin da aka kwantar da aliya sannan yazauna
cikin mintuna kadan saiga bilkisu dama sufyan yaroka
abarta tafito don sunfi sabawa da aliyan yakolo ta amince,
shigowan bilkisu dole tajira aliya ta tashi bayan farkwanta
alokacin sufyan yanufi gun abdullahi , aliya naganin bilki ta
wangale baki sanin cewa zuwanta bana banza bane bayan
bilki tamata jajen yajikin sannan tamika mata wani takarda
tare da cewa duk abunda kikeson sani yana cikin nan, Allah
yabaki saa, bashiri tafice don tsoro takeji Aliya ta paki idon
inna tasaka tacikin bargo taboye sannan takoma ta
kwanta, can dai tamike tasaka akasan katifan tamayar ta
kwanta, Bayan sun watse daredare anbarta da inna wacce
tabude baki sai bacci take, taciro takardun tabude hotuna
ne tsoffi dakuma wani enlarger karami, mahaifinta ne da
alh.hamidu mahaifinsu yan biyu saikuma sauran biyun su
uku, da mahaifinta dawani wanda take kyautata zaton
cewa shine dan biyun mahaifinta hussieni sai alh.hamidu
gabanta ne ya tsananta fadi, ta mugun tsorata asaninta
tace bilki ta bincika mata alakan alh.hamidu da fadan gidan
kusancinsu ta bakin tsoffin bayin dasuka san kan gydan,
karshe kuma ga abunda bilki takawo mata, tasan bilki
batayi makaranta ko ilmin dazatayi wannan binciken ba,
dole akwai wanda yasan sirrinta, waye toh? Sufyan? Inhar
shine toh bazai bawa bilki ba dakanshi zaiboye. Abdullahi?
Tasan abdullahi bazai taba kawo aikinta ba, don baigama
sanin alakarta da sufyan ba balle abunda yakawota(a
tunaninta abdullhi baisan cewa ita kanwar sufyan bane),
yusuf? Salati tayi tabbas yusuf ne shine kadai namijin da
yasan sirrinta , amma meyasa yataimaketa? Nanma dai
tagodewa Allah damuwanta burinta yakusan cika, yanzu
dole tasami hanya da alh.hamidu don taji daga bakinshi
meya sani, tunda duk shine mafi kusa acikinsu Batayi bacci
ba har asuba nurses sunzo sun dubata suka fice ana idar
da asuba bacci ya kwasheta, abdullahi ne yashigo dakin
don ganinta inna tana wuridi yadan zauna agefe, idonsa ce
tahango mai takarda, jaa yayi don yaga menene (Salam,
akwai batu jiya dayayi ta zagawa akan na rasu, ba ni bace
wata benazir muhd ce yar nasarrawa, nagode ga dumbin
masoyana dasuka kira donjin lafiyata, duk wanda aka tayar
ma hankali ko yashiga wani damuwa ina rokon afuwa don
Allah nidai ina raye, Alla[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 29
 benaxir  October 22, 2015  Hausa Novels
 106 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENNAXIR OMAR Jawowan
dayayi yaga bangon envelope ne donhaka sai ya ajiye
agefen pillow, yana zaune har yusuf yazo mikewa yayi
yafice don tun randa yusuf yaje yacemar yagode baikara
mishi magana ba. Har abdullahi zaifita yusuf yace
“tsohonka na memanka” gabanshi ne yafadi dum donyasan
ba maganan dazaamishi saina maganar bayar da kisney
dayayi shiyanzu matarsa yake jin tausayi karya mutu su
gaza kulawa da ita da dan cikinta, dakin yanufa yatatara
abunda zai dauka yafice gyda yanufa yayi wankarsa
matarsa duk ta tsorats don tasan baa sallameshiba
yadawo, ta so tabashi abun karyawa baikulata ba yafice
don ganin sarki mai ran karfe baisameshi ba don yana
bacci dole yahakura yakoma Yusuf kuwa zama yayi dirshan
agefenta ya tsura mata ido. Tadawo gangar jikinsa tadawo
wani gurbi arayuwansa itace tsoka da jininsa, tadawo
tamkar bugun zuciyanta domin duk numfashin datayi sai
yaji kaman daga jikinsa ne, bata farkaba sai takwas na safe
likitan yaga warkewanta dawuri yakuma ce taci abinci
sosai wanda ada ruwan lipton suke bata da abu mai ruwa
hankalin kowa ya fara kwanciya banda na aliya
damuwanta su sallameta awannan asibitin don tasamu
tafita ta cimma burinta, sufyan ne yashigo alokacin yusuf
yashiga gari anan ta mai bayani sannan tabada takardun
daya karanta shima ya yarda da magananta nacewa saita
gun alh.hamidu, donhaka yace zai danne damtse don
yasamu kusanci da mahaifin hassana, alokacin kuma ta
tambayeshi ko yasan dalilin dayasa abdullahi yabata wani
bangare ajikinsa, bayaso yatada mata hankali donhaka
yace “kinsan abokina ne, amintan dake tsakaninmu yabi,”
bata gamsu da bayaninshi dama yasan bazata yarda ba,
zatamai wani tambayan ya tallafota tare da cewa ta
kwanta tayi bacci, hakan yakara tabbatar mata akwai dalili
yusuf ne zaigayamata, saidai tatuna guntun kishin shi
donhaka ta share, tuni ta gargade zuciyanta da kartayi
binciken dalili balle yadawo mata tashin hankali, Dagari
yama wayewa abdullahi yakoma gun sarki inda a tunaninsa
fada zaimasa. Yamasa fadan kuwa sosai tareda cewa
inhar kanaso ka gwada hallacinka kamata yayi kasiya,
yanzu kai zaka iya mutuwa duk lokacin da jikinka ta gaji da
wannan injin, nan dai abdullah yasha fada anma daidai da
second daya baitaba nadamar abunda yayi ba, Satin aliya
daya aka sallameta tuni takoma gida ankara gyra fanninta
tasan aikin sufyan ne da antyn abuja wacce aranar tawuce
abj, duk da tadawo gida mutane basu dauke kafa ba. Don
gaydata alokacin sufyan yasami kusanci da nahaifin
hassana tuni yashirya randa zaimasa tambayoyin hotunan
yadiba sannan yaje gydan, hassana ta tarbeshi sannan
tamasa iso bayan sun gaysa sai sufyan yayi bayanin meya
kawosa tareda hotunan ya ajiye mai,alh. Hamidu yayi
murmushi sannan yace “dama nakai shekara sha biyu
inajiran rana irin ta yau, ranan da yayan cikinsa zasuxo don
jin bayani saidai nasan ku biyune, ina kanwarka? Kaje
kadaukota itama tanada hakkin tasan meyasami
mahaifinta” sufyan yace toh tareda ficewa gyda yaje ya
kinkimo aliya a mota yamata bayani tuni jikinta yayi sanyi
domun ta tsorata sosai, suka koma inda suka sameshi
kamar yadda sufyan yabarshi yafara dacewa “iyayenku
yan biyu ne masu son juna dakuma matukar kama, hakan
yasa shakuwa a tsakaninsa, sarauta da son mulki shiya
shiga ransubwanda shaidan yazo yashiga tsakani , bazan
taba fada muku waya kashe iyayenku ba saidai ina rokonku
dakuyi hakuri, ku yafewa kowaye ne, ku manta, don
tsananta bincike baya jawo komi sai bacin rai,” sufyan da
aliya duk sun kagu suji bayani anma sai waazi yake
akarshe yace “ranar karshe da mahaifinku da hussieni
suka gana adaki kafin hussieni yabar gari, bawanda yake
gun sai ni danake falo suna daki abunda naji kuwa shine
hussieni yace ko duniya zata juya saiya mulka garrinnan,
yayinda hassan ya musanta , hussieni kuwa yace su zuba
sugani” donhaka kuhakura da binciken haka” sufyan da
aliya sunyi sunyi anma mutum kam ya gunshe baki a bacin
rai suka fito suka fice, hassana wacce tashirya don soyewa
da masoyinta sai karar mota taji yafice, .gyda suka isa inda
akarshe suka yanke shawarar dole mutum dayane yazama
ansansu[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 30
 benaxir  October 23, 2015  Hausa Novels
 99 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR tuni suka
fara tunanin hanyar dazasu je su sameshi ko shi yazo,
Washegari sufyan yaje gun alh.hamid tareda rokonsa ko
akwai hanyar dazaayi asamu hussieni yazo, yace mishi
hanya daya ne kadai zaisa hussieni yazo, in ance mishi
anga ajiyan mahaifinsa, ajiya ne wanda kakanku yayi wa
hussieni haryau baasamu ba, donhaka dole kusamo
wannan hajiyan don hussieni yazo, sufyan ya amsa da toh
anma shi tuni ya shuka dabararsa, wasikar jaki yayi yasa
aka tura inda yake fadawa hussienin shine dan hassan
kuma ga ajiyarsa a hannunsa, yayi hakkanne don baida
kudin dazaice zaije bayan haka baisan yadda kanin
mahaifin nasa zai karbe sa ba, gwara yajawo shi yazoshi
duk da taimakon alh.hamdiu yanemi address din yatura
Aliya ta warke garau haka ma abdullahi rayuwa tacigaba
da gudana musu, duk da aliya ta dan ja baya da yusuf
anma tana sonsa , daidai da kankanin lokaci sonsa baitaba
raguwa mata ba, abdullahi kuwa yanzu da taimakon injin
bature yake rayuwa, yariga daya cire rai wa duniya don
yasan wahalarshi tazo karshe, Acikin wata biyu wata rana
sai labari ta iso sufyan cewa ga hussieni yazo gari, ya tare
ne agydan alh.hamidu hakan yasa aliya da sufyan suka
shirya tareda inna don zuwa gayda shi, kasancewar
sunsaba da gydan shigansu sunyi mamaki don kammanin
mahaifinsu ne sak a fuskan hussieni sai yanmata guda
biyu wanda duk daga kallonsu ansan yan biyune, zasuyi
saan aliya, kyawawa dasu suma kammanin mahaifin suka
dauko, hussieni ya tarbesu sosai a matsayin yayansa, aliya
taji dadi ganin cewa itama gata da yanuwa tuni suka saba
da yanbiyun, sunsha tadi sosai sai can dare sannan su
aliya suka dawo gyda Washegari sufyan ne ya koma anma
wannan karon duk acikin gyda suke, alh.hamidu da
hussieni suna falo donhaka sufyan yashirya don yaje
yatambayeshi yarike hannun kofan zaishiga yakasa kunne
donjin mesuke fada, Alh.hamidu yace “kasan cewa
yarannan sundameni maganan mahaifinsu sai tsananta
bincike suke, ni bansan mezance musuba, kasan dai bazan
bude baki nace musu hussienin mahaifinsu shiyasa akashe
mahaifinsu don samun sarauta” “Nagode daka rufe
maganan baka furta ba, ni bansan tayaya zanyiba, nayi
nadaman abunda na aikata gashi idan ina kallon yaransa
duk sai naji na tsargu mussaman macen, itace na cuta da
maraici, hakika son zuciya da zugin shaidan su suka sani
na aikata abunda nayi,yanzu kunsamamin ajiyan ne? Don
da wannan ajiyan zan iya karban sarautar sarki bana
galadima kawai ba, nadawo gida bazan koma ba,” Sufyan
dake rike da hannun kofan yasake jiki a sanyaye yafice
batareda kowa yasaniba, gyda gun aliya yanufa yashiga
tana bacci don tace mai haka kawai takejin faduwar gaba
da ciwon kai yace tayi bacci inta tashi tasameshi agydan
alh.hamidu, zura mata ido yayi hannunsa na bari yana
shafa gefen fuskanta, farkawa tayi tazauna tareda cewa
“yayah” bai amsataba yafara kokarin share hawayensa,
tunda take bata taba ganinshi awannan yanayun ba, tuni
jikinta itama yahau bari “yayah! Meya faru? Waye ba
lafiya?” Hannunsa na bari yariko nata yarungumota kuka
yake sosai mai tsananta zuciya, tuni tafara itama duk da
batasan dalili ba, cikin yanayin tausayi yace “aliya hakika
agarin bincikenmu yau mun bincikawa kanmu tashin
hankali, aliya alh.hussieni shiya sa aka kashe mahaifinmu”
tsak ta tsaya tana kokarin daidaita numfashinta anan
wayan sufyan tayi kara cikin yanayin tausayi yadauki
wayan, “hello, naam” Salati taji yafarayi yamike cak
“abdullahi? Innalilahi!! Innalilahi wainnailaihirajiun!!
Gamunan zuwa! Innalilahi!” Fitsari tasake awando wani
kuka yaci fuskanta, gabanta ya tsananta fadi, “yayah meya
sameshi?” Baikulata ba yace “shirya mutafi” dankwali
kawai tadauka tabishi, nima benaxir gabana yana fadi
nabishi don ganin meya faru!

HALACCIN SARAUTA 31
 benaxir  October 24, 2015  Hausa Novels
 132 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR Mota ya
fizga dakarfi sai alokacin aliya taga jikinta ajike anan ta
tabbatar da aefa fitsari tayi anma wayake tanan yanzu,
tunda kayan jikinta ba nunawa zaiyi ba goran ruwa tagani a
motan tabude ta watsa ajikinta, fada yanufa dasu suka
sami gurin acike, dakayar yasamu gun parking yana tafiya
aliya tabi sahunshi fannin yakolo suka nufa wacce babu
matsaka sinke ancika, tundaganan jikin aliya yayi sanyi
komawa tayi tazauna, agefe wasu hawaye masu zafi suka
fara bin kumatunta sufyan ne yakamo hannuta suka shiga
shima dataimakon hauwau. Wacce tanuna cewa su yan
gida ne suna shiga dakin acike agefe aliya ta tsaya sufyan
yakarasa gun, abdullhi ne akwance agun macecce, duniya
inazakije damu, mun aikata alheri mun mutu munbarta,
dole kowani rai mamace ne, sufyan durkusawa yayi agun
tuni dogarai sukayi gefe dashi don baabarin kowa kusa da
gawan. Yakolo ma ba kanta dakyar aka danneta, aliya
kuwa wani kyalli kyallu take gani a idonta tuni ta fizge
dankwalin kanta tajuya dagudu zata nufi kan gawan rikota
akayi, tuni sufyan shima yamike yarikota yusuf wanda ke
can kuryan daki tuni yafito ganin aliya tuni ya nufa kanta
rikota akayi anma yadda kukasan karfin aljannu gareta
wani fizga datayi bashiri suka fada tabaya kan abdullahi
tanufa zata budeshi anma nanma dogarai suka kara rikota,
tuni umma uwar soro tace a fice da ita, daukanta cak akayi
akafice da ita, wani irin kuka takeyi wanda duk mai kallonta
sai ya tausaya mata, itakanta tadawo abun tausayi ,
sumbatu takeyi “yarima meyasa zakamin haka? Yarima
meyasa zaka tafi baka amsamin tambayoyin dake raina
ba? Kasan cewa sanadina kamutu anma baka gayamin
hujjanka ba! Innalilahi wainna ilaihi rajiun!” Kuka takara
fashewa da, yusuf ne yajata, yasa aka nemo bilkisu tarikota
suka koma gefe acewarsa akaita fanninshi harsaitayi shiru
kafin tashigo cikin jamaa, Anyiwa abdullahi wanka yadda
ake kowani mamaci, abdullahi kuwa yasha fatan alheri
agun alumma, iyayensa sun sakamishi sunkuma nema
mishi aljanna, hatta mtanem gydan dsuke karkashinsa
suna aiki kowa alheri yake fada akan abdullahi, duk wanda
yazauna da abdullahi yasan mutum ne mai tausayi, marar
son fada, mai son gaskiya, mai adalci mai kuma bin hakkin
dan adam, matarsa da mahaifiyarsa sunbada kyawawan
shaidu suma akansu, a inda sarki dakanshi yake jawabi
amfanin zuwa duniya kenan, kazamto nai kyautatawa
mutane , kazamto mai tausayi karkace don kafi karfin
wane, ko wane yana aiki akasanka ka wulakantashi , kasani
cewa shaidun duniya shine shaidan lahiranka, muguji
duniya muzamto masu shiri akowani lokaci don ziyartar
kabari, musani cewa aikin damukayi duk yana cikin
littafanmu, yakuma yi jawabin cewa kar mutane suce don
abdullahi yabada kidney dinshi shiyasa yamutu, wannan
bahaka bane lokacinsa yayi, daya bada da bai bayarba
dukka Allah yayi zaimutu yau, kuma mutane susani cewa
akullum idan aka tambayi abdullahi maganan kidney dinshi
da dalilin bayarwa yanada hujjojinsa anma babbar hujjarsa
itace yayi alkawari kuma a matsayinshi na dan musulmi, na
wanda yataso cikin mutunci da daraja a matsayinsa na
balagagge wanda yasan hukuncin marar cika alkawari
hakan yasa yacika alkawarin, kuma shi sarki yana alfahari
dashi hakkika abdullahi abun koyi ne, Allah ya sa mucika
da imani Ansamu ankaishi makabarta kafin sudawo aliya
tasuma yakai sau uku, haka kawai takejin haushin kanta
gani takeyi kaman itace musabbabin dalilin dayasa
abdullahi yarasu, dakyar aka mata alluran bacci tasamu ta
kwanta Sufyan kuwa abun duniya tamasa yawa dawanne
zaiji, mutuwan amininsa kokuma bincikowan dayayi cewa
hussieni shiya kashe mahaifinsa da mahaifiyarsa, dawani
ido zai kalleshi duk yaga missed call dinsu anma bai dauki
ko daya ba, atunaninsa basuda abin fada mashi gun inna
yanufa yatarar tana kan sallaya tana ganinshi tashafa
addua tareda cewa “sufyan ya akaji da hakuri?” “Alhmdlh”
“Allah yajikanshi yamishi rahama” “Amin inna, dama nazo
muyi maganane akan alh.hussieni” “Inajinka” “Kinsan
shiya kashe iyayena shiyasa kika boyemin ko?” “Hmnm
abdullahi kenan, rasuwa fa aka maka yakamata kayi hakuri
ai yanzu ko” “Yanzu nakeson kifadamin amsata” “Nasani.
Sannan alh.hamidu ma yasani, munga babu amfanin
gayamuku ne,kuma nagayamaka anan nagayamaka,
sufyan kadaina bincike, addininmu ma batason irin wannan
binciken, tasar da kwantaccen magana,ana zaman lafiya
kunje kun binciko abunda zai hanaku zaman lfy, yanzu
dakasan cewa shine mezakayi?” “Lallai inna kinban
mamaki, tambaya kikayi mezanyi? Kotu zamu shiga!,
bazan hakura ba harsai anyiwa iyayena adalci, kina nufin
muna ji muna gani ankashe iyayenmu a banza kenan? Da
ke! Da duk wani wanda yakeda hannu aciki wanda yasani
da komi duk sainakaiku kotu, zaku fuskanci hukunci ”
Baikulataba yafice duk da ta tsorata tana kokarin yimasa
bayani, fada yakoma har lokacin ance aliya bata tashiba
ganin yusuf yayi donhaka yaje shima yazauna agefensa,
yusuf na zubarda hawaye yace “kasan dalilin da yabata
kodan shi?” “Nasani” “Menene” “Don yamata alkawari zai
kareta koda ranshi zai cire yabata” “Bayan haka” “Yana
sonta!! Itace mace tafarko daya fara so a duniya” Yusuf
dama yasan dahakan yana son ya tabbatar dinne, ajiyan
zuciya yayi wanda shi sufyan yagagara ganewa ko na
farinciki ne ko na bakinciki Acan cikin fada kuwa fannin
falmata jakadiya ce tashigo tana murmushi, falmata ta
kalleta itama murmushin take, jakadiya tafada kasa tana
kirari Sai ke Jaruma a cikin jarumai, jaruma acikin
jagororin ma jagoranta Idan akaji ance kasaita in anduba
kin cancanta taimako dare zuwa rana kin sabayi wa
al’umma mai dukiya mai ran karfe Mai kudi uban matsiyata
baki fushi ko anzage ki Baki zagi ko anzageki ja muje kece
gimbiyar magimbiyata kara masu kece babbar su Mai girma
agidan girma sannan kuma matar mai girma,uwar gida a
gidan mai girma,Mai hidima a gidan hidima sannan kuma
matar mai hidima, farin cikin mai hidima, zuciya hasken
annurin mai hidima, zakanya saidai aganki anesa badai a
matso kusa ba,” Wani irin murmushi da dariya falmata tayi
cikin jin dadi, ta daga giranta sama sannan tace “kinga na
kashe da’ saura uwarsa sannan uban gayyan uban gidan,
yusuf[truncated by WhatsApp]

HALACCON SARAUTA 32
 benaxir  October 26, 2015  Hausa Novels
 145 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR jakadiya
tana rusune harta mike ta fice. Bawanda yakai falmata
farin ciki aranan saboda tana ganin wanda zai tare mata
sarautar danta yafadi kasa yamutu, shehu kuwa baiyi
hankalin dazata sashi a sahun masu karban sarautan ba.
Donhaka tuni tafara tunanin hanyan dashi kanshi sarkin zai
mutu, babu tsoron Allah babu tunanin lahira, tunaninta
shine takashe duk wanda tasan zaishiga tsakaninta da
mulkin garin, Sai dare sannan aliya tafarka atake sufyan ya
tallabota yadawo da ita gida yana ganin inna baikulataba
yashige da aliya ciki, saida yatabbatar takwanta ya rufo
kofan sannan yafito inna tana tsaye tana jira yafito,
baikulata ba tana kiransa, inba don babu gun da zaikai
aliya ba da gidan nata saisu tattara subar mata shi, Cikin
dare aliya tayita firgit tana wasu mafarkai, dolenta
tamike,alwala tadauro tafara sallah har asuba tana yiwa
abdullahi addua, tausayin matanshi da abunda zasu haifa
yacikata, Dasafe sufyan nazaune wayansa tayi kara
alh.hamidu ne yake cemasa yazo suna jiransa, baiyi
bacciba tsabar yana tunanin hanyan dazsi bullowa
maganan, motansa yaja yafice gydan alh.hamidu yanufa
suna zaune a tsakar gydan suna jiranshi, sun gaysa
yabasu girmansu sannan yazauna, inda hussieni yake
tambayansa alkawarinsa, sufyan yayi murmushi sannan
yace “komi zaizama naka idan kabani tarihin yadda akayi
ka kashe mahaifina!” Ba hussieni ba har alh.hamidu saida
yabude baki don mamaki,hussieni yagagara cewa
komi,hakan yakara tunzura sufyan, hawaye ne suka fara
zubo mishi yafara magana cikin sanyin jiki “Ashe karshen
duniya zatazo dahar danuwa zaisa hannu yakashe
danuwansa saboda dukiya?saboda mulki?” Bawanda ya
amsa mishi kaman tsoffin barayi da aka kamasu hussieni
kanshi akasa yafara magana “kai mahaifinka ne. Nikuma
danuwana , wlh tlh ba abunda nashirya yafaru ba kenan,
Allah dai yayi zanzama sanadi, tabbas munyi musu da shi
batun mulki anma ban kwallafa raina ba. Nasan na umurta
da amai dukka anma bance sukasheshi ba, bankuma ce
suhada da mahaifiyarka ba. Allah yayine lokaci yayi don
Allah kayi hakuri, karkuma kabari kanwarka taji alokacin
sufyan yayi kukan zuci daya tuna da iyayensa anma tuni ya
watsake saboda ayanzu zucuyarsa tabushe yana tunanun
daukar fansa, recordern dayake recordn yasawa stop
sannan yamike yafice batare da ya ce musu komi ba dama
yakira lawyernsa awaya tuni yadamka masa shaidansa
tareda basa go

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login