Showing 3001 words to 6000 words out of 27196 words

Chapter 2 - HALACCIN SARAUTA Book 1 to End by Benaxir Omar.txt

fanninsu tanufa, lalle yakamata tabar
fada duk tsanani saidai anya zaa barta? Baridai ta saci
hanya, shigan kamala tayi kaman bakuwa ce tazo tasami
kayan agun bilki wacce tamata kashedi kala kala, sannan
tafice gydanta tanufa tabude dakinta har gurin yayi kura,
wanka tafara shiga tagoge jikinta sosai sannan tanemi riga
da skirt na atamfa yakamsta sosai,tayi sallah sannan tuni
tajawo littafanta da abubuwan zane zanenta tafara tunanin
yadda zatayi da waziri toh ashe inhakane zaman fada
baikamata ba, yakamata tafice takashe waziri tukun, saidai
baridai taga mezai faru, tana zaune har bacci me nauyi ya
kwasheta tayi bacci sosai sannan tashinta tacigaba da
zane zanenta tayadda zata ci karo da waziri. Gani tayi dare
yayi bata damuba dama tariga data yiwa jakadiya bayanin
zataje ganin wata kakanta, inbaa gantaba, kuma ta amince
bilki ce dai hankalinta yatashi sosai.l, karfe tara na dare
zaman dakin ya isheta tuni tanemi dogon abaaya tasa
sannan tafice tana tafiya tana danna wayanta wani hotel ne
wanda akwai restaurant aciki tunda tazo garin kafin ta isa
fada agun takecin abinci,shiganta tazauna tayi ordering
indomie kawai,tanajira don saisun dafa kafin sukawo
agefen gun taji hayaniya a hall mikewa tayi tanufi gurin ga
mamakinta ganin yarima yusuf tayi, wanda kwalban giya
ne ahannunsa babu dogari, gashi yafara layi aliya taja tsaki
tareda cewa “useless” harzata tafi taga mutumin dake aiki
a hotel din yana jan yusuf akan yafice yusuf sai zuba
hauka yakeyi yana surutai, abun yaci mata rai. Tanufi gun
shi sannan tace “yarima yusuf ne don Allah kubarshi”
mutumin baice komi ba yatafi tajuya zata tafi yusuf
yakamo hannunta ta mugun tsorata anma dai tadanne
azatonta yaganeta ne, anma tunanin yana cikin maye hala
ne inyaganen yaki saketa donhaka ta fizgeshi suka bar
hotel din ,abincin da bataci ba kenan, fitowansu tasakashi
akan hanya takare masa kallo, asalin dolo ne, no wonder
dan fari ne ashe dole yayi wawanci tace cikin rashin kulawa
da rashin damuwa ” kawuce katafi gida, wani dolonci ne
yasa kafito ba dogarai?yakalleta baice komi ba can kawai
yafara yunkurin amai, amai yakwara mata haushi taji
kaman takamashi da duka. Taja wani tsaki sannan tace
saikayi ai , juyawa tayi tana tafiya harta isa kofan gidanta
juyowan dazatayi taga mutum ashe biyota yayi babu yadda
batayiba yaki,tashigar dashi tareda cewa “wlh ba yarima
ba ko sarki kake inkamin amai anan duka zaka sha”
saiyace “nifa dan sarki ne kuma sarki!” Bata kulashiba
ganin baya hayyacinsa toilet tashiga tacanja kayan jikinta
takara wani wankan sannan tace “kashige kayi wankan
kaima, abun haushi bacci tasamu yafarayi wani salati tayi
tared[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 4
 benaxir  September 21, 2015
 Hausa Novels  122 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR OMAR ruwa ta debo
ta watsa mishi,tuni yafarka sannan tace “wuce muje” har
toilet takaishi tazuba mar ruwan zafi sannan tarufo tafito,
bayan minti goma saigashi yafito yana bin bango sanye da
jallabiyan mata, abun yaso yabata dariya saikawai yafada
kan gadon, wani matsanancin bacci ne ya kwasheshi yadda
taga rana haka taga dare tsoronta karya farka yamata wani
abu, saida asuba bacci barawo yakwasheta, karfe goma
daidai yafarka ga mamakinsa yaganshi akan gado lullube
da bargo, tunanin meya faru yafarayi, yatuna wani abun
yamanta wani anma yamike ganin jallabiya ajikinshi ya
tsorata kodai yazo daki da karuwa ne baisaniba?” Bashiri
yafara neman kayansa anma baiganiba nan yahango aliya
akan kujera saidai baiga fuskarba saboda gashinta yazubo
tagaban fuskan, yaje ahankali yabude bakace sedai bakinta
mai kyau ne, yabayyana kalan fatarta da kyan fuskanta,
yakare mata kallo gabanshi na tsananta faduwa
numfashinsa ne yahade danata hakan yasa ta farka
dasauri ganinshi akanta yasa tace “meye haka? ” yadan
bata rai sannan yace ” kinsan da yarima kike magana ko,
akanme zaki kawoni nan, ko nina kawo kaina ? Bani kayana
nasaka, takalleshi ta tabbata yadawo hayyacinsa sannan
tamike tsakar gyda tanufa ta tattaro masa tareda cewa
“kayi amai ajikinsu na wankema, sannan nan gaba in
zakace shaye shayenka ka tattari dogaranka,my plan is not
saving some kind of soul” abun ya harzukashi anma
yashare toilet yashiga yasaka kayan sannan yafito baiko
cemata uffan ba balle nagode yafice, taja tsaki tareda cewa
“halinsa sak uwarsa” nan ta harhada abunda zata hada
sannan tamaida kayan bayinta tarufo gidan saboda tassn
yagane gidan karyace zaimata wani mugunta. Fada
takoma inda ta tsinci bilki cikin tashin hankali tana cewa
ina kikaje? Aliya tace “gaysuwa” bilki taja tsuka tareda
cewa “yanzu da umma uwar soro tazo ta yi kirge fa?”
Ganin bilki zata dameta yasa aliya tafice tabarta, fannin
falmata ta isa bayan anmata iso tagayamata tadawo,
dawowanta daki taji bilki nafada itada wata baiwa agefe. Ai
yarima bai kwana agyda ba, jiya anata nemenshi harta
wayoyinsa yaki dauka,ko yakoma shan giyansa da neman
mata, sunata surutai anan aliya tatuna ashefa yaga
fuskanta, donhaka dole tayu kaffa kaffa da shi acikin gidan,
hakan kuwa tayi suka koma yin wasan boye boye duk inda
taganshi canja hanya take Watarana dasafe abisa aladan
gidan matan sarkin zasu hadu suje gaida sarki dasu da
yaransu insun dawo kuma, sai suma maaikatan sumika
nasu gaysuwan gun matan sarki, ahanyan dawowa falmata
tace anemo mata yarima yusuf, shiganta bayan wasu
mintinai saigashi yashigo yazauna akan kujerar dake kallon
nata, “inaso ka kasa kunne kasaurareni” tafada cikin rashin
faraa, “shaye shayenka yafara yawa, jiya abuge aka
kawoka. So kake kasakani a magana? Wazaiba wa dan
giya sarki? Yakamata ka nutsu wlh tun kafin lokaci
yakurema,” baice komi ba yana kallon hanyan kofa wanda
jakadiya ta aiki aliya tashigo da tray, ganinta dayayi yatuna
ta cak, itama tana ganinshi saidata tsorata anma tayi
kaman ba ita bane ya ce “KE! Zonan,” ta iso kanta akasa
“dago fuskanki” tadago yatabbatar itane anma yagane
mahaifiyarsa donhaka yace “jeki” falmata tace “meyene?”
“Tamin kama da watane” alokacin aliya ta ajiye tray din
tajuya tafice, saida falmata ta tugeshi baice uffan ba yafice,
jakadiya tabada shawaran amasa aure dawuri ko mace
zata nutsarshi, namiji mai gagara ai macece mai nutsar
dashi, anma falmata tace itakam sam bazaa kawo wacce
zata kwace mata danta ba, anma tana ganin karshe
abunda zatayi kenan, acan fannin kuwa yanashiga falonsa,
yakira bilki wacce itace take masa hidimansa. Yabukaci
yasan sunan baiwar datake fannin uwarsa, anan bilki ta
tsorata sosai duk da tagane bayaninsa anma tayi kaman
bataganeba, daya watsa mata wani tsawa bashiri tace
masa aliya sunanta. Kuma tataba bauta agunsa yace
acanjata, anan yashiga tunani yazaiyi toh da ita? Yakamata
tadawo shiyanason ganinta donhaka ya aika aka kira
umma uwar soro, yace mata yaduba yayi nazari akan
baiwar dayasa aka kora, ayi hakuri adawo masa da ita
suna aiki da bilki yafi gane aikinsu. Ta amsa masa da toh,
adaren ranar umma takira aliya tasanar mata bataji dadiba
dontasan meyakesonyi, zaibata mata plans dinta, anma
haka bayadda ta iya, daredare bilki takai masa shayi ya
juye mata akaya yace ta aiko dayan baiwan, tana isowa
tafadawa aliya duk jikinta yabaci donma Allah yasa ba
tafashashe bane balle yakoneta, aliya cikin dacin rai tanufi
fanninsa bayan anmata iso sannan tashiga yana zaune
akan kujera ta tsuguna tamika masa sannan yace dama ke
baiwa ce kika fita? Da izinin waye? Kanta agefe tace
“gimbiya falmata” yaja tsaki sannan yace “da mummyna
kike aiki?” Yanzu zantona miki asiri kasheki zaayi baiwa
dake kinfita kinje kina tonamana asirin gyda ko?” Batace
komi ba, jiyayi kaman jikinsa na mararin jikinta, gashi
yadan sha giyansa kadan, kanta yanufa tamike tana
matsawa haka yakomota duk karfin datake jidashi
yahadata yadama wurgata kan gado yayi yafara sumbatu,
tana kokarin tashi yana kokarin danneta. Ganin zata masa
taurin kai gashi ji yake zuciyarsa na masa zogi, na masa
radadi kaman yarasa wani abu a fannin jikinsa yanzu
yasamu baisan lokacin daya rinka naushinta ba tuni tayi
laushi yakwanta luff ajikinta, tareda cewa nafiso injini
haka. Aliya tagama galabaita batasan lokacin data
gantsara masa cijo ba bashiri ya tsala kara tu[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 5
 benaxir  September 22, 2015
 Hausa Novels  123 Views
HALACCIN SARAUTA NA BENAXIR dogari ne yaleko nan
da nan yusuf yace “kaita cell” wani wawan damka yamata
tana fizgewa anma haka yafice da ita , rufeta sukayi a gun
,ko da falmata tayi cikiyanta domin taje tasawa abdullahi
maganinshi anan tasamu labarin yusuf yarufeta, donhaka
tuni ta nufi fanninsa fuska a murtuke tace “anma dai kasan
cewa wannan baiwata ce ko?” Batareda yadamu ba yace
“anma laifi tayi donhaka dole na hukunta ta” yana fada ya
sunkuyar dakai” falmata tamike tareda cewa dogari
“ciromin ita yanzunnan tazo tasamen” aikuwa ana cirota
wanka tayi sanmam tanufi gun falmata wacce take kunshe
da wasu kaya agabanta, laya ne dawasu kullin magani,
jakadiya tamikawa aliya wacce bata tsorata ba, don duk
takaranta a littafai salo salo na makirci da kishi, jakadiya
tamika mata sannan falmata tacigaba da magana ” zaki
san yadda xakiyi kikai dakin yakolo, guda biyune naraba ko
da zaasamu matsala da naki, gida biyu maganin gobara”
aliya tamike tareda cewa toh, fitanta tanufi daki tana
tunanin yadda zatayi saida tabari daredare sannan taje
baya tagida tabinnesu, mikewanta dasafe tanufi fannin
falmata tareda cewa “gimbiya bansan tayaya zanshiga
fannin ta ba” falmata tace “nasan yadda zaayi kixo nan
gobe dasafe” Washegari dasafe tajeta alokacin dukkansu
daga falmatan har yakolo suna zaune suna karban
gaysuwa saiga aliya, falmata na ganin aliya ta umurci
jakadiya data kamota, duk sauran bayin dakatawa sukayi
suna kallon ikon Allah don sunsan halin falmata sarai,
jakadiya narikota falmata tahau fada wa aliya ” baki da
hankali ne? Tun karfe nawa nace kizo na aikeki? Ku bata
jikinta!” Bashiri suka hau dirkanta yakolo ce tabata hakuri
anma falmata taki saurarawa tunda aliya take bata taba
shan duka irin wannan ba , ana gama dukantan falmata
tace sukoreta, alokacin yakolo uwar tausayi kamar yadda
mutane suke mata laakaci, tasa aka kawo aliya tabata
uniform dinsu nacan sannan tace tadauketa aikin, shikenan
plan din falmata yayi daidai, alokacin hauwa yarinyar
yakolo ta tausayawa aliya sosai donhaka ta ce yakamata
tana aiki acikin gurin ko da zamane agefe tadan taimaka
dawasu abun, yakolo kuwa ta amince, fitowar aliya zuwa
dakinsu tuni jakadiyar falmata tanufota tareda cewa
“kinsam yanzu baza ana ganinki damu ba, donhaka kisan
yadda zakiyi kibada maganin, akwai wacce muka bata
sauran baizama dole kisantaba” dahaka aliya ta amince
aanma akasan ramta tariga datasan tabirne maganin,
saidai batasan wane aka bawa sauran maganin ba dazata
san yadda zatayi tahana, anma duk dahaka bata cire hope
ba, suna zaune watarana kawai saiga gimbiya tamike daga
kan gado, tacire laqqabinta ta fizge gashin kanta, tuni tafara
jan jikinta tana jan fatanta, hankalin kowa yatashi tuni aka
isar da sako ga sarki, ya umurce da ariketa, sannan ayi
addua ya iso gun dakanshi, yakolo tayi luf sai surutai takeyi
” bakuga bera bane suke bin jikina? Duk dakina kananun
bera, kutashi kuciremin ina jakadiya? Kiyi sauri kiciremin”
aliya dake gefe kuka take kallon idon falmata tana ta kuka,
oh ! Mata da kissa ita adole kishiyanta ba lafiya, can dai
dataga sarkin yazauna agefe sannan tafara tafara magana
“Allah sarki yakolo ta kiyi hakuri Allallah zai kawomiki
dauki, Allah karemin ke,”daga ita har jakadiyan sai hawaye
suke, abin yabawa aliya haushi yayin yakolo malamin
yafara mata adduoi, wani zobe yagani a hannunta sannan
yace tacire sarki dakansa yacire mata yamika masa, yakalli
sarkin sannan yace “wannan zoben mai girma na tsafi ne,
yawo ake da kurwanta asama,aina tasamo?” Sarki yakalli
jakadiya maanan yana neman karin bayani jikinta nabari
tace “nima haka nagani tana sawa bansan aina bane”
dasauri hauwa tace “kawowa akayi alokacin gaysuwan
sarakuna umma falmata tabata”falmata cikin kuka da kissa
tace nima inadashi bantaba sawa bane. Acikin kayan
sarakuna aka kawo(kayan sarakuna kyauta ne da matan
sauran sarakunnan garin suke kawowa don hada zumunci
kowa yakan hada nashi) sarki cikin zafin rai yace malam
gama aikinka zamu binciko wayayi wannan danyen
aikin,aliya taji dadin haka Koba komi zatasamu daman
ganin matan waziri, [9/22, 7:45 PM] Adda Bena: Ahaka aka
watse don barin yakolo tayi bacci, aliya tagaji sosai anma
duk tana tunanin yazatayi don tasan tsafin da falmata
tayine yake aiki, bata idda tunaninta ba taji hayaniya
mikewa tayi tafice tafannin yakolo ne, dogaran basu bari
ashigaa anma kasancewar sun wayeta suka barta, yakolo
ce itakadai tanata hada kanta da bango, tana kuka duk
jikinta jina jina, jakadiya dasauri tariko aliya tareda cewa
kitsaya da ita barin yi magana da umma uwar soro,
ficewanta aliya tanufi gimbiya yakolo wacce ganin aliya
take cewa “aliya kirike matannan tadena rikemin kai, ” aliya
duk tarude dagudu abdullahi da hawa suka shiga hauwa
tana zubar da hawaye, aliya cikin zafin nama take cewa
“kina lailalaha illahala, auxubikallimatti lahi tammat min
sharri ma kalaq” dasauri hauwa tafara fada aliya ma
nafada abdullahi nafada, kara yakolo tasake tanacewa
takamani sunayi dakarfi ahakan har tayi shiru tana nishi
mai karfi, can tace ” ga matan can tana kuka wai ina
konata, kuma zata dawo takasheni” aliya tadebo ruwa ta
tofa adduoi sannan ta watsa mata suka shafa mata ajiki,
nan da nan bacci mai nauyi ya kwasheta, juyowan
dazasuyi sukaga umma uwar soro tana labe agefe. Tana
kallo ta tsorata sosai anma tace mutum biyu suzauna anan
sauran sufice, hauwa da jakadiya ne suka zauna, alokacin
aliya tafito domin tawuce dakinsu tana tafiya abdullah dake
bayanta yace “baiwar Allah” tajuyo a hankali tareda
sunkuyar dakai yace “nagode da taimakon mahaifiyata
dakikayi, Allah bar zumunci,” aliya tace ameen yarabb,tana
tafiya yabita da kallo shidai yasan kaman yasanta awani
guri anma dai yawuce dakinsa. Tana isa daki takwanta luff
sai bacci Dasafe tafito dontaje mika gaysuwanta agun
yakolo, dogarai ne suka tsaya akanta tareda nuna mata
hanya tabisu baki alaikum har fannin yusuf, yana zaune
akan kujera dagashi sai singlet ko a jikinta don ko lokacin
training dinta mazan da singlet suke training ganin bata
damuba yasan yana dealing da babbar yar bariki, cewa
yayi danna zakimin!, zaro ido tayi anma ya katseta dacewa
“kiy[truncated by WhatsApp]

HALACCIN SARAUTA 6
 benaxir  September 25, 2015
 Hausa Novels  134 Views
[9/25, 2:21 PM] Adda Bena: HALACCIN SARAUTA NA
BENAXIR OMAR Aliya ta runtsa sannan tace “mekakeso
dani?!” Cikin rashin damuwa yace “kenake so” bata
kalleshiba tadauko towel, tashiga toilet tajiko da ruwan
sanyi, tana zuwa ta maka masa dasauri yace “awhsh meye
haka?” Fuska a murtuke tace “danna kace kana so!” Tana
fada tana danna masa kafan lumshe ido yake cikin dadi
don shikam har ransa yadda yakejin sanyin haka yakeji
aransa, sonta yake don jiya dakyar yayi bacci tun taimaka
masa datayi take idda mishi gizo, mintsinansa tayi bashiri
yabude ido, “meye haka?” Yadda yabata rai, saikace
meshirin kashe barawo, bata kulasa ba tamike tareda cewa
“nagama” tajuya zata fita , samata kafa yayi tuni ta tuntsire
tayi kasa, cikin tausayi yace “wayyo kiyi hakuri ” bata
kulashiba tamike tafice, dadi yaji aransa. Itakuwa inbanda
kwashe masa albarka ba abunda take a zuciyanta, fannin
yakolo tanufa, jiki dasauki hamdallah, shima don sarkin
yadauko malamai sukayi saukan qurani, sannan malamin
yayita bayani ” wannan adduan dakuke rainawa ance
kunayi kunaga kaman wasane,kuyi zikirin safe dana
yamma ,Allah yana kareku, fatiha,falaq da nas , ayatul
kursiy,ga lailaha illa anta subhanaka inni quntum minal
zalimin, lailaha illalahu wahdahu la sharika lahu, lahul
mulku walahul hamdu wahuwa ala kulli shay in qadr, akwai
su dayawa kunemi hisnul muslim shine makamin mumini,
duk sharri da asiri da jinn Allah zai kareku, inhar kanayi
kuma kaga wani abu yasameka toh kadauka wannan
kaddara ce kuma jarabawa, don annabi SAW anyi masa
asiri kuma takamashi, anma kuma yakarya. Don haka dole
kuyi imani da kaddara, ku yarda Allah shiyake komi, babu
yadda zaayi dan wani abu yasameki saiki bude baki kice
wacce ce tayimin haka, a a nikam anmin asiri, zato zunubi,
Allah bayason haka, duk abinda yasamu mumini anaso kayi
imani kakuma fuskanceshi, zama kace anmaka asiri kana
biye biye ba daidai bane, safe da yamma ko yaushe ka
kasance da adduanka,” yakalli jakadiya tare dacewa
“abasa qur’an” tamika masa yakalli qur’anin gashinan dai
anma sai kura alamun cewa andade ba a budeba, yace
“toh kunga wani matsalan meye amfanin fansar quranin da
zaa ajiye don ado?,ba gwara kubayar sadaqa a masallatai
ba?,sai kuga agyda ansiya qur’an sama da goma, an ajiye
wato acemuku musulmai kuba arna bane, ina amfanin
haka baka karanta qurani, anma kullum zaa kunna tv, zaa
hau whatsapp, facebook, wata inbatahau ba kaman zatayi
zazzabi, zaatashi tsakar dare ayita waya kuma sai akwanta
goshin asuba, anmanta da Allah waiyazubillah, yakamata
duk mu tsarkake ranmu, bature yazo mana dawani cuta
mai wuyan magani,duk wannan social media din cutane,
Allah ya tsaremu, yakuma kara mana imani, anma dole
mucanja inhar munaso muga mai kyau, rashin bin Allah da
dokiknsa shike sawa muke ganin jarabawa kala kala, ” duk
kowa jikinsa yayi sanyi sarki kansa yaji wannan waazin
don yamanta wen last yabude qurani, gwara sallah yanayi
dukka a masallaci anma baya farilla, falmata kuwa wacce
tazo daga baya , bindin shedan tamanta wen last tayi
sallah, donkuwa a maganin da akabata an umurceta da
kartayi sallah na kwana arbain, donhaka take zuane, yakolo
kuwa baiwar Allah wacce tayi imanin jarabawa take
fuskanta agun ubangiji taji dadin jawabin malam ko ba
komi zai kara mata tuni da mutuwa dakuma kwanciyan
kabari, bayan anwatse aliya tanufi dakinsu tasamu bilki
wacce ita tana kwance tana hutawa tamike tareda cemata
“matan sarakuna yaushe zasu kara zuwa?” Bilki tace “ran
laraba menene?”aliya tace ” babu kawai inason sanine”
dadi taji ganin plans dinta yana tafiya daidai, Ran laraba
dasafe tanufi gun dogari isa, shine wanda tasaba dashi
sosai kuma tarokeshi alfarmar yanema mata kayan dogorai
set daya, duk da yaso yakawo mata taurin kai. Dubi goman
ta mint tahada tabashi,ba bata lokaci ya amince, donhaka
ta karba tanufi baya tasaka tarufe kanta, tadauko fatar
gemu wanda tayo guziurin kayanta tun daga kudu, tsayawa
tayi a babban gate gurin da dole kayan sarakunnan
sushigo, a tsayawanta tafara gadi, dogari isa ne agefenta
abun mamaki dukka dogaran bawanda yace komi asalima
basu nuna sunsan bakon fuska bane, hakan yatabbatar
mata dacewa dogari isa yatoshe bakinsu, oh kudi samunka
mutunci, rashinka balai, karfe daya daidai suka iso, matan
sun shige yayinda kayansu dole aduba kamar yadda sarki
ya umurta, ahaka aliya tagama cuse cusenta takulla komi
sannan tacire kaya tabawa dogari isa, wanda tuni ya ajiye a
boyeyyen gu don kar asiri yatonu, anshiga anyi iso ma
matan sarautan harda mazajen nasu, lami lafiya anci
abinci anyi tadi, anan aka fara fitar da kayan kowa ana
dubawa, matan sarkin sun nua farincikinsu musammamn
ma yakolo wanda don ita akadawo dazuwan laraba
musababbin ciwonta, sarkoki ne, sai laces,shadoddi. Da
kayan kwalama, can kasan wani shadda gezner jakadiya
tana budewa sai ga laya da zobe, gaba daya hankalinsu
yayi kan gun don sun mugun tsorata , jakadiya wacce ada
take gudan farin ciki tana kirari saigashi tafara salati, tuni
hankalim kowa yayi gun, umma uwar soro ce tanufi gun
tareda cewa “kayan waye” jakadiya tace “na matan waziri”
falmata wacce ta harzuka sosai tace “ku kamata” bashiri
dogaran suka nufo kanta tareda bata hanyan fita, magana
kaman iska tuni fada tadauki hayaniya waziri wanda ke
fadar sarki jin abunda yafaru yasashi rudewa, bashiri ya
roki da abarshi yashiga daga ciki, anma sarki yace mai ”
uwar soro zata mata hukuncin daya dace, babu ruwan fada
ko sarki aciki”. Falmata kuwa abunnema yasamu duka
sosai matar waziri eshallo tasha, [9/25, 6:36 PM] Adda
Bena: Yakolo bataji dadiba acewarta yakamata ko darajan
sarautan mijinta a lamunta mata, anma falmata taki , dadi
takeji tasamu naman fansa akai, bakin ciki kaman zai
kashe waziri anma babu yadda ya iya, uwar gayyan kuwa
aliya taji dadi acewarta yanzu tafara daukan fansa, tunda
yarabata da kowa nata saita rabashi dakowa nashi da duk
wani wanda yasa hannu a kashe iyayenta, tana zaune bilki
tashigo tareda cewa kizo inji yarima yusuf, shiganta
tasameshi yana zaune da kwalban giyansa, da alamun
maye, tuni tadaure fuska, yakalleta tare dacewa “kinga ko
ni yarima ne, kuma kome nakeso ina samu, ina sonki kinji?
“Aliya bata furta komi ba, kwace kwalban tayi tareda
ajiyewa agefe. Kallonsa take sosai, yusuf namiji iya namiji
saidai yasaka shaye shaye agabansa duk yayi baki yadawo
wani iri, wannan wani irin rayuwa ne, itama zata iya
amincewa kanta cewa tana sonsa saidai soyayya yanzu
bashine solution dinba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login