Showing 6001 words to 9000 words out of 22971 words

Chapter 3 - KADDARAR SARAUTA COMPLET BOOK BY SAIYYID WRITER.doc

Advertisement

namiji.

Dariya Lubaba tayi sanan tace:

 Ita can tasani, ni batayimun ba, haka ma Mamanta, har da babanta ma, nasamu labari daga wajen jakadiyarmu, wai Sarki Ilyasu yafison Abbanta akan kowa da kowa, KADDARAR SARAUTA ce kawai ta gifta shine Mai martaba yake kan mulki.

 Lallai kuwa idan hakane Sarki bai kyauta ba, gwanda ma da Abban nata yake kwance dashine sarki bazamuji dadi haka ba, kuma ba lallai yabawa Maman mu sarautar Mai babban daki ba, sabida kinga shi yayanta ne.

Cewar Labiba suna cigaba da tafiya,Lubaba takara cewa:

 Waccan figaggiyar matar tashi zaibbawa mana, ta dinga yi mana kallon hulakanci.

Karasawa sukayi zuwa wajen dasuke shakatawa,inda suka tarar da yar gidan Mai martaba Junaidiya wacce take kawarsu.

Su ukun nan kansu a hade yake,Zama sukayi suna hutawa suna hira kowacce naji da mulki.

Itakam Sarah zama tayi bayan ta gaida Gimbiya Zulfa mai babban daki, kallon ta Gimbiya Zulfa tayi sanan tace:

 A yanzu zan cika miki burinki sai dai kema inason ki daukar mum alkwari daya.

 Wane burine kuma wane alkwari ne?.

Sarah ta tambya kanta akasa,murmushi Gimbiya Zulfa tayi sanan tace:

 Burin ki na koyar fada, shine zancika miki,kekuma kiyimun alkwarin duk lokacin dakika tashi aure, sai mijin dana zaba miki.

Sosai Sarah taji dadi ba musu tace:

 Na amince.

Dariya Gimbiya zulfa tayi,domin ita tasan dalilin dayasa tayi haka sai da tagama dariyar ta sanan tace:

 Ki tashi kije ki samu Barde.

Tashi tayi tafice zuciyarta fari kal.

Tundaga wanan Rana Sarah tafar karbar horo a wajen Baru, duk kwarewar kanta da take gani, sai da tagane cewa Ashe bata iya komai ba.

Haka take karbar horo,kullum jiki babu dadi, idan ta kwanta sai antashe ta.

*Bayan shekara biyu*

Tabbas a yanzu Sarah ta mallaki hankalinta, ta kuma zama mayakiya mai taurin zuciya, da kwazo.

Babban abinda yakara tabbatar da Sarah a matsyain mayakiya mai kwazo shine, yanda tayi gasa da manyan mayaka majiyar karfi guda biyar wayanda kaf Masarautar Zarwata babu masu karfinsu, amma Sarah tasamu nasara akansu.

A yanzu ta canja yanda take tafiya, kuma shi jinin sarauta baya boya a ko ina saiya bayyana kansa.

Bayyanannen kyawum sara yafito, ga kuma tsayin da take dashi, wanda yakara mata kyau.

Tafiya take cike da Sarauta ga kuma takamar zama babbar mayakiya wacce babu kamarta a yanzu duk fadin Masarautar Zarwata.

Gefe kuma kanwarta ce, Jiddah wacce itama ta maida hankali ga koyan fadan. a hankali suke tafiya har suka isa bangaren mai babban daki.

Jin shiru a bangaren yasa Sarah cewa da Jidda:

 Ina kuma mai babban dakin tayi, ina hadimanta sunce tana ciki tare da mai martaba?.

 Haka sukace Yaya amma bari naje nakara tambayarsu.

Jidda tafada tana tashi, har takai waje sai kuma tagano, kyalin farin haske yana yawo asama wanda shine abin sonta, a lokacin yarinta haka take bin shikuma yana yawo asama.

Dariya tayi sanan ta sakai zata huce sai kuma tace:

 Bari nakama abun nan.

Binshi tafarayi shikuma yana sama, bata daina binshi ba /sai da taji alum tashigo inda ba a shiga domin tabo taji tana takawa, Juyawa tayi tana fadin:

 bari nakoma tunda abun nan, yayi nisa.

Nishi tajuyo sama sama, hakan yasa ta tsayawa domin tabbatarwa ko kunnenta ne yaji ba dai dai ba, nishin takara ji da kuma alamun kamar ana magana.

Da sauri ta matsa domin a tunanin ta wanine yashigo kuma yakasa fita, sai dai kuma wajen a gine yake babu dama har tana shirin juyawa tagano wani siririn haske, da sauri takai idonta wajen.

Muje zuwa& . daga alkalamin
_Saiyyid writer_

Masu bukatar complete document suyi mun magana
08129553971

=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*


Page (9&10)


Dishi Dishi take ganin mutanen hakan yasa takara zura idon nata, da sauri tayo baya sanan tafara goge idon domin tabbas yagano mata ba dai dai ba.

Kara mai da idon tayi amma kuma mai martaba tagani babu kaya.

Daga kwance kuma Gimbiya Zulfa, sai da ta tsaya ta kallesu tsaf, domin ta tabbatar dinsu ne kuma abinda taga suna aikatawa din shi sukeyi.

Baya tayi ta jingina da jikin bango, zuciyarta na bugawa da sauri da sauri, sama da minti goma tana haka sanan ta iya saita numfashin ta.

Tashi tayi tafito a hankali, har ta koma inda yayarta take sai dai bata gantaba hakan yasa ita tafice.

A hanya sukaci karo, da sauri Sarah tace:

 Jidda ina kikaje?.

Girgiza kai kawai Jidda take hawaye na bin idanunta.

 Lafiyanki Jidda meyasa meki.

Sarah takara fada adabarbace,alamun itama tashiga tashin hankali, daukan ta tayi a hannu tafice da ita zuwa bangarensu.

Gimbiya Sadiya na zaune taji Sarah na fadin:

 Ki bude idonki Jiddah, ki bude idonki!!.

Da sauri tatashi tafito tana fadin:

 Sarah mene yasamu Jiddan?.

 Maamah bansani ba nima.

 Maza huce da ita wajen Baru.

Gimbiya sadiya tafada tana daukan alkyabbarta itama tasaka tabi bayansu.

A bangaren Gimbiya Zulfa da Maimartaba Sarki Tukur kam, bayan fitowar su daga dakin sirrinsu Gimbiya Zulfa taga Kokon da Aljana Jumana tabata na hayaki.

Da sauri tace da Sarki Tukur:

 Kalli wanan kokon yana hayaki.

Kalla yayi sanan yace:

 Lallai da matsala domin aljana jumana tace duk randa wanan kokon yayi hayaki to matsala ce, dan haka dole muje wajen ta yau din nan.

 Shikenan rana na faduwa zamuje.

Gimbiya zulfa mai babban daki tafada, shikuma yasa kai yafice.

A hanya yatsinci maganar anfito da Jidda daga bangaren Mai babban daki ba yanda take, amma hakan bai dameshi ba sanan bai kawo komai a ranshi ba.

Cikin bangaren shi wajen matanshi ya nufa Fulani Rumasa u da kuma Fulani Mero.

Bangaren Fulani Rumasa u uwar gida ya nufa,inda yabata umarnin hada masa ruwan wanka.

Sai bayan yayi wanka yaci abinci sanan yakoma zaman fada.

Itakuwa Mai babban daki, bayan fitarshi wanka tayi sanan tafice zuwa turakar mijinta Madaki.

A bangarensu Sarah kam wajen Baru suka huce kai tsaye,wanda yafara kokarin hada mata magani.

Surutai take wanda suka kasa gane mene take cewa, dakyar aka samu bacci yadauketa.

Zama Gimbiya Sadiya tayi tare da zuba tagumi haka Sarah ma,Baru ne yace:

 Mene asalin abinda yafaru da ita?.

Cikin muryar kuka Sarah tafara magana:
 Munje bangaren mai babban daki, sai muga bata nan nace taje ta tambayi hadimanta,domin da zamushigo sunce mana tanaciki, jin shiru batadawo ba yasa nabi sahunta ko da na tambayi hadiman sukace bata fito ba, na koma inata neman ta sai kawai naga tafito daga wani waje tana nishi tana kuka.

 Inane wajen?.

Baru ya tambayeta,cikim kuka tace:

 A cikin bangaren mai babban daki ne.

Shiru yayi sai can kuma yace:

 Inaso ku bunne wanan maganar tsakaninku kada kubari wani yaji.

 Amma meyasa Baba Baru?.

Sarah ta tambayeshi, kallon Sara yayi sanan yace:

 Ke yarinya ce bazaki gane ba, amma tabbas Gimbiya Jiddah tagano wani sirri ne a bangaren mai babban daki, wanda ya tsorata ta haka.

Jinjina kai sukayi duka sai kuma Sarah ta karacewa:

 Baba Baru akwai abubuwa da yawa da kake cewa mubarshi a tsakanin mu, ciki harda samun lafiyan Abbanmu shi meyasa?.

 Ki kara hakuri ranki yadade, ina tahada bincike ne amma tabbas akwai wani sirri mai wuyar gaske wanda duk randa ya fashe, jinin fansa ne zai fara gudana a masarautar Zarwata.

 Shikenan Mungode Baru.

Gimbiya Sadiya tafada tana tashi tafice,Sarah kam zama tayi sai da ta dauki lokaci sanan takoma wajen mahaifinta, wanda a yanzu yanaji kuma yana magana amma ba sosai ba.

Yana iya daga hannunsa tare da juya kansa amma kuma ba iya tashi balle ya zauna,Zama tayi kusa dashi tare da fara bashin labarin abinda yafaru.

Cikin Muryar rashin lafiya yafara magana:

 Ku dinga kula, bakowa bane abin yadda.

Kallonshi tayi sanan tace:

 Abbana me kake nufi dan Allah?.

 Saratu ke yarinya ce har yanzu,amma watarana zaki gane komai.

Girgiza kai tayi samam tace:

 Abba yanzu ni ba yarinya bace, na girma nasan abunda yake dai dai da wanda yake akasin haka abba.

Kallonta yayi sosai sanan yace:

 Tabbas a yanzu kin girma sai dai abinda kike neman sani zai iyafin karfin tunaninki, shiyasa nake kara cewa sai kin girma.

 Abbana a yanzu babu wani labari da zaifi karfin tunani na.

 Shikenan kibari yar uwar ki tasamu lafiya, sai ayi maganar.

 Tom abbana.

Bayan faduwar rana Gimbiya Zulfa da Mai martaba sarki Tukur suka nufi kogon haske


Tafiya sukayi mai tsayi acikin dogon jejin,mai bakin duhu tafiyar da suka kwashe shekara da shekaru sunayinta amma har yau sun kasa sabawa.

Ihu da karar iska kadai kakeji a cikin dajin kafin suka karasa bukkar matattarar Aljanu.

Yadda bukka take a ko yaushe karama haka take a yau ma, sai mugun duhu da kuma bakin hayaki dake fitowa daga cikinta.

Mai martaba sarki Tukur ne yafara magana:

>  Sarki Tukur daga masarautar zarwata dan wajen sarki iliyasu dan sarki Abbas ne,tare da gimbiya Zulfa mai babban daki a masarautar zarwata yar gidan Fulani Rumana yar gidan Fulani Zullaziya, mun karaso fadar aljanu muna neman hadi da karamar aljana mai kimanin shekara dubu 29 Aljana Jumana.

Wata murya ce daga karkashin kasa tafara magana:

>  Sarkin Aljannu Kudumuya ya amshi zuwanku, sadaukarwar asalin ku ta amso.

Maganar nafitowa ne dakafa da ihu, yanayin da shikadai zaisa kaji hanjin ciki ka na motsawa

Daganan wanan karamar bukka ta girma zuwa babba, wata siririyar hanya ce tafito daga cikin bukkar.

Hanyar suka fara bi, sai da sukayi tafiya mai tsayi a cikin wanan karamar bukkar, kafin suka karaso fadar Aljanna Jumana.

>  Mungaida Aljana jumana,Karamar aljana mai aikin manya.

Wani siririn bakin duhu ne yafara fitowa yana zagaye wajen, sai kuma dariya daga sama, sai kuma bayyanar Aljana jumana, tana kyakyata dariya.

Sai da tayi mai isarta sanan ta bude hannu kayan tsafi suka bayyana:

Iska ce tafara hurawa ganyaye suka fara kaWawa kamar ana tafe da tambarin mummunan abu.

Sai gasu sun bayyana a wani bakin jeji mai mugun duhu daga gefe kuma aljanu ne kowanne yana harkar gabansa.

A tsakiyar jejin, an kunna wutar tsafi mai launin shuWi tana hura haya?i mai wani irin dandano da ?amshin ?ura da jinin tsuntsu. Mutane biyar, kowanne sanye da riga mai rufe fuska, suna zagaye wutar.

Aljana Jumana ce tace:

>  Tabbas a yanzu komai zai hautsine, komai zai birkece kaddarar sarauta zata fara, masarautar ku zata dau wani saiti, kuma wanan hautsinewar tafi karfin Aljana jumana, domin tabbas jinin dake guda naji a jikin hallitar mai zafi ne.

Tsuru Tsuru Gimbiya Zulfa tayi hakama Mai martaba Sarki Tukur, dukkansu sun san akwai matsala kenan.

Aljana Jumana ce ta cigaba da cewa:

>  Sabida haka na dakko wanan aikin na kawoshi, Fadar Aljanu ta duniya gaba daya domin dasu za ayi wanan yakin domin ba nasarar ku baci ku kadai ta gaba daya aljanu ce, haka ba faduwarku bace ku kadai tagaba daya aljanu ce dan haka a yanzu aiki zaifara.

Aljana jumana na fadin haka ta kankance ta koma yar mitsitsiya domin a yanzu tana gaban manya aljanun duniya ne.

Wata murya ce tafara magana:

>  A yanzu lokacin biyan bashi duk wani abu da kukayi ne, lokacin da haske zai bayyana a masarautar kuka ya gabato, sai dai wanan hasken yana shirin hadawa damu wanan shine dalilin dayasa zamu taimaka muku.

Gimbiya Zulfa mai babban daki ce tace:

 A yanzu munason ku bayyana mana mene yafaru a masarautar mu.

Dariya akayi mai cike da kara da kuma ihu iska, sanan akafara cewa:

>  Abinda yafaru a masarautar ku ba boyayye bane a wajen mu, sai dai Hasken dayaga fallasawar wanan abun boyayye ne gare mu.

Sarki Tukur ne yace:

 A sanar damu, mu zamune mo hasken, sanan muyi masa hukunci da kuka yanke.

Aljanu biyu ne suka bayyana kasa, sukafara zagaye wuta mai launin shudi suna magana:

Aljanin farko ne yafara magana cikin murya mai kauri, kamar tana fitowa daga ?asan ?asa

>  Mu duba cikin idon iska, mu ga sirrin da yake Soye cikin inuwa& 

Na Biyu ma yafara magana yana Waga hannu da sanda mai koren launi

>  Dutse ka buWe& ?asa ka faWi gaskiya& ku sanar da mutanen zarwata abinda yafaru

Iskace ta fara hurawa da ?arfi, ganyaye suna kaWawa da ?arar da ta shige kunnuwan Sarki da Gimbiya Wutar tsafi ta fara canza launi zuwa ja mai zurfi.

Koren Hasken ya bayyana a cikin haya?in sama da wutar, yana nuna siffar mutum da ba a iya gane fuska.

A kunnunwansu kam ji suke ana cewa:

>  Anganku kuna kusantar junanku, wani wanda yake da hade da sarauta, wanda zaizama kalubale gareku, tashin hankali zaifara, kaddarar sarauta zata juya.

Wani irin ihu Gimbiya Zulfa mai baban daki tasaki tana fadin:

 Karyane! karya ne!! bazaiyu ba, babu mahalukin daya isa ya juyamun kaddarar sarauta, babu mutumin da yaisa ya tuna asirin dana binne shekara da shekaru.

Muje zuwa&
_Daga alkalamin Saiyyid writer_


Masu bukatar complete document akan 400 suyi mun magana
08129553971


=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*


Page (11&12)




Wata razananniyar dariya aka saki wacce ta kidima bakin jejin gaba daya, korayen bishiyo sa babu ganye suka fara hayaki, sai kuma murya tafara fadin:

>  Wanan jinin daya ganko yagagara bayyana a garemu, domin baitaba biyo hanyar mu ba, sanan akwai babban malami atare dasu da yashafe shekara da shekaru yana kula dasu, daga ranar da kuka bayyana manasu zamu karbe aikin nan gaba daya yazamana mu, sanan ku dauwama a mulki.

Sarki Tukur ne yace:

 Munyi alkwarin bayyana wanan jini a gareku.

Dariya aka rayi sanan jejin yafara juyawa, rufe ido gimbiya zulfa mai babban daki tayi haka shima mai martaba sarki tukur, bayan yan mintina sanan sukaji jejin yadaina juyawa.

Bude ido sukayi kowannensu yadawo cikin dakinshi, da sauri gimbiya zulfa tanufi kam gadonta tazauna tana fadin:

 Bazaiyu ba! Bazaiyu ba!!, waye yashigo bangarena jiya.

Da sauri Labiba da Lubaba suka shigo suna fadin:

 Ummah Ummah mene yafaru.

Shiru tayi ta daina kukan ba tare da tace dasu komai ba, haka suka kara tambayarta.

 Kaina ke ciwo, ku tashi kufita.

tashi sukayi suka fice ganin yanda tayi maganar suna fita takara rike kan nata.

Haka mai martaba yana bayyana a bangarenshi ya zauna gefen gado yana fadin:

 Waye wanda yaganmu, wanan wane jini ne?.

Haka yadinga zagaye a cikn dakin, ko zama yakasayi, har sai da Mai dakinshi tashigo tana fadin:

 Ranka yadade meyafaru, yaushe kashigo.

 Fulani banason magana dan Allah.

Yafada yana zama,shiru tayi itama daga baya kuma tafice.

Haka Gimbiya Zulfa mai babban daki da Maimartaba Sarki Tukur suka gagara zama suka gagara tashi, bacci ma basu samuyi ba.

A can bangarensu Sarah ma haka sukayi tafama da Jiddah sanan Malamin tsafi Baru yahanasu sanar da kowa abinda yafaru dan haka ko acikin masarauta babu wanda yake da labarin rashin lafiyar Jidda, kuma dama mutanen masarautar ba bibiyarsu suke ba.

Washe gari Gimbiya Zulfa ta tara gaba daya hadimanta tana tambayarsu, waye da waye suka shigo bangaren ta jiya.

Shiru sukayi takara maimaita maganar cikin fushi:

 Nace waye da waye suka shigo bangarena jiya?.

Daya daga cikin manyan hadimanta wato jakadiyarta, ta iya bude baki tace:

 Ranki yadade da kamar wane lokaci?.

 Tun waye war gari har zuwa faduwar rana.
Tafada cike da tashin hankali, sai kuma can tace:

 Bayan Mai martaba yashigo bangarena.

 Ranki yadad e mutane dayawa sun shigo ciki harda fadawan bangaren Gimbiya Sadiya.

 Meya kawu so bangare na?.
Tafada da alamun tambaya, wanda yayi maganar dazu ne yakara cewa:

 Ranki yadade muna tsaye bakin kofa, sai Gimbiya Sarah da yar uwarta suka shigo, har zasu shiga sai ta tambaye mu kina ciki mukace kina ciki, ba afi minti biyu ba kuma Gimbiya Sarah tafito tana kuka dai dai lokacin da fadawan bangarensu suka zo wucewa.

 Bangane abinda kafada ba gaba daya.

Sake maimaita mata yayi, itakuma tana binshi da kallo.

 To menene yasaka ta ihun?.

 Ranki yadad e muma bamu saniba.

Tashi tayi tafice zuwa bangaren su Sarah, a farkon bangaren ta tarar da Sarah tana fitowa tsugunnawa kasa Sarah tayi tana fadin:

 Barka da Safiya ranki yadade?.

Kallon Sarah Gimbiya zulfa mai babban daki tayi a ranta tana cewa:

 Da yarinyar nan taga wani abu da bazatayimun haka ba.

Afili sai cewa tayi:

 Biyoni bangarena.

Daga haka tafice itakuma Sarah tabi bayanta, sai da Gimbiya zulfa tashiga ciki sanan ta tsaya tana kallon Sarah, sai da tagama kallonta sanan tace:

 Jiya mene yafitar dake daga bangarena kina kuka.

Gaban Sarah ne yafadi domin yanda taga Gimbiya Zulfa tasan akwai damuwa babba, da sauri tabude baki tace:

 Jiya munshigo wajenki zamu gaisheki nida Hauwa, bamu kai ga karasowa ba Kafar Hauwa ta rike takasa takawa, sai kawai naga ta zubi a kasa bata numfashi, hakan yasa nafita nakira mutane suka shigo muka kaita wajen magani har yanzu ma tanacan, amma yace ciwonta ne yatashi.

 Yanzu tana ina?.
 Wajen Baru mai magani.

 Tashi muje.

Gimbiya Zulfa tafada domin son tabbatar da abinda Sarah tafada, Gimbiya zulfa naga ba Sarah na binta har suka karasa wajen Baru.

Kallo daya Baru yayiwa Gimbiya Zulfa shima yagano damuwa a tare da ita.

 Barka da wanan lokaci mai babban daki a masaruatar Zarwata.

 Barka Baru, menene ke damun Jidda?.

 Ranki yadad e jidda na dawani ciwo ne wanda yakantshi lokaci zuwa lokaci, kuma ciwon yana da alaka da irin na dan uwanku Yarima Abbas m, kisan lokacin da ya kwanta ciwo lokacin ne tazo duniya.

Ficewa Gimbiya zulfa tayi ba tare da tabashi amsa ba, dole fa yau saita nemo wanan mutumi daya Aljanun koren haske suke magana akai.

Haka bangaren Maimarataba ba yana nan zaune shiba mai lafiya ba shi ba marar lafiya ba, tunani yake ta ina zaifara bincikon wanan jini da Aljanun Haske suke magana akai?

Chapter two: Masarautar Kumbu


Kamar yadda Asalin Masarautar Zarwata yake tsafi, haka ma Masarautar Kumbu Harma zamuce tsafin dake gudana a masarautar Kumbu yafi na zarwata

Duk masarautar Kumbu karamar masarautace batakai ko da rabin zarwata ba , amma mutanen dake Kumbu sunfi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login