Showing 9001 words to 12000 words out of 22971 words

Chapter 4 - KADDARAR SARAUTA COMPLET BOOK BY SAIYYID WRITER.doc

Advertisement

na zarwata hadari, sunfi na zarwata bushewar zuciya , sanan sunfi na zarwata mugun nufi.


A shekara goma sha biyar da suka huce, lokacin da Asalin sarkin Masarautar Kumbu zaiyi murabus ananne akayi gasar tsafi tsakanin zaratan yaransa maza guda uku, anan kiyayya tajini tafito, sarauta tazama gaba amma dukda haka sai wanda kaddarar sarauta ta giftawa zai mulki masarautar.

Shekara goma sha shida baya

Sarki munayas yana da yara 5 mata biyu saikuma maza uku a cikin mazan akwai

(1). Lamsar
(2). Lahab
(3). Munasa

Saikuma matan akwai

(1). kudusiya
(2). lamra, ita kadai ke da aure


Gaba daya yayan sarki Munyas suna su gaji babansu, suna suyi mulki, mulki na tsafi, hakan yasa Sarki Munayas yabasu dama suje su hallarci koyan bakin tsafi domin yin gasa na shekara daya.

A sharakara ta 2015 aka gudanar da mahaukacin gasar tsafi tsakanin yayan masaruatar Kumbu gasar tsafin da tazama karewar kwanciyar hankali, tazama gabar jini ta zama gasar tsafi a tsakanin yayan masaruta.

17/03/2014


Dare ne mai duhu iya kacin duhu wanda baka iya banbance yanayin lokaci. Bishiyoyi masu tsawo sun haWa rassansu har sama, sun rufe sararin sama, suka hana wata dama da haske zai keco dajin. Iska mai zafi ta ratsa ta ko ina tana kadaw bushashin bishoyi da babu ganye suna fitar da ihu iskar tana Wauke da wani irin kamshi  ?amshi mai kauri wanda yake gauraye da wari kamar na jikin abu da ya daWe da mutuwa.

?asa tana lumshe a ?ar?ashin ?afafu, tana yi wa mai tafiya ?ara kamar ana taSa gangar tukunya. Daga can zurfin daji, ana jin ?ara kamar an busa sarewa mai sautin ban tsoro, sannan ana jiyo wata irin magana, muryoyin da ba na mutane bane, suna magana cikin wani idin harshe da ba a fahimta.

Muje zuwa&
_Daga alkalamin Saiyyid writer_


=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*


Page (13&14)

400 complete document via 08165383931

A gefen hanyan kuwa ?asa kuwa ta hade tayi baki kamar anzuba ruwan kwalta daga gefen dajin kuma akwai gumaka masu siffar dabba amma suna da fuskar mutane  wasu suna murmushi cikin mugunta, wasu kuma suna rufe idanu kamar suna jiran wani abu ya faru.

Aljanu ne suke zagaye bakar huta mai koren hayaki suna magana da yaren da babu wanda yakeji.

Yarima Lahab ne ya bayyana yana sanye da bakaken kaya daga gefe kuma bakar aljanar data kawoshi dajince wato Aljana Jumana hannunta rike da bakar hutu, manyan kawun wun ta su murde.

Magana Aljana Jumana tafara:

>  Karamar Aljana mai karancin shekaru ce bayyane a gaban ku tare da Yarima Lahab dan gidan Sarki munayas jikan kudunayas, yazo ne domin sadaukar da jinin yan uwansa guda uku domin bashi Mulki.

Wata muguwar dariya ce mai kidima hanjin mutane tafito daga gefe da gefe, wayanan gumakan ne sukayi sai kuma murya daga gefe tafara fadin:

>  Lahab sadaukarwa ta amso zaka zama sarki na masarautar ko sai dai akwai lokaci da zaka biya wanan Kadadarar sarauta daga wata masarautar zata shafeka zata bayyana gaskiyyar ko da baka raye.

>  Lahab ya amince.

Aljana Jumana tafada, saikuwa wata dariyar takara fituwa busasun bishiyoyi sukafara wani irin ihu, wani bakin haske mai duhu yafito yana zagaye asama

Can Sai kuma& *Wani irin shiru mai nauyi ya mamaye wurin*.
Shiru irin wanda ke nufin akwai wani abu mai girma da ya bayyana& .

Aljana Jumanace takalli Yarima Lahab tace:

>  Komai ya kammala.


Haka Yarima Lahab yadawo daga nan suka tafi wajen bokam masarauta yashiga koya musu tsafi

Ranar 17/7/2015 ranar da za a gudanar da gasar tsafin masarautar Kumbu


Wurin da aka shirya gasar ba daji bane kawai, amma *mafaka ce ta duhu*  inda hasken wata baya iya ratsa bishiyoyi masu girma da suka kakkafa rassansu tamkar ?aho. Tsuntsayen dare sun yi shiru, iska ta tsaya cak, kamar kowa da komai a dajin na jiran abu mai girgiza duniya.

A tsakiyar fili mai siffar tauraro, aka kafa *tukunyar tsafi* mai cike da ruwa ba?i kamar gubar kwalta.

A gefen kowane maki na tauraron nan, akwai kujerar dutse, inda  yan uwa biyar suka zauna. Kowannensu yana ri?e da *abin tsafi* nasa:

* Na fari yana ri?e da ?ahon zakara mai jini.
* Na biyu yana da sandar itacen da aka shafe da garin ?ashi.
* Na uku ya zo da ?aton kwandon macizai masu ja da kore.
* ta hudu tana ri?e da kwando wanda zalal fatar macizai ne a ciki.
* ta biyar kuma, itana ri?e da Wan ?aramin madubi da aka kebe musamman don nuna mutuwa kafin ta faru.

Boka mai tsaron wannan gasa, tsoho ne wanda fatarsa ta rine zuwa launin toka, idanunsa sun nutse cikin ?ugun idanu. Waga hannunsa yayi sama, yafara magana da wasu kalmomin da suka sa ?asa ta fara girgiza:

> *"Na kira ku bisa sunan iyayenmu na ?asa da sama& Daga yau, Waya ne kawai zai ci nasara, sauran kuwa za su zama gurasar aljanu!"*

Nan take, kowannen ya fara aikinsa.

A can bangaren su Aljana jumana da shugabanin takuwa nan sukafara aikin sauya Kaddarar sarauta daga kan Gimbiya Lamra waccw itace kaddarar ke kanta kafin su sauya.

* Na farko ne ya yanka zakara, nan jinin zakaran yafara bin kasa yana shiga cikin tukunyar, ya fitar da wani irin wari marar dadi da ya kama hancinsu da ?arfi.

* Na biyu ya kuma ya tashi ya soka sandarsa cikin ?asa, nan da nan ?asa ta fara girgiza wani irin ihu yafara karade jejin yin.
* Na uku yatashi ya buWe kwandon macizan hannunsa, suka zubu zuna zagaye tsakanin kujeru, amma ba sa cizon kowa.
*Ta hudu kuma tatashi ta watsa farar macizan cikin tukunyar, nan take ruwan ya fara tafasa yana fitar da ?ura mai kama da hannun mutum.
* ta biyar ta Waga madubinta, ta yi wani kallo mai zurfi  cikin madubin, kowa ya fara ganin fuskarsa yanda zata kaya zuwa safe.

Nan da nan Iska ta canza, sai kuma ?arar dariyar aljanu daga ko ina cikin daji:

> *"Ku yi gaggawa! Lokaci ku yana ?arewa& jininku yana WanWanon baki!"*

Wata wutar duhu ce ta rufe filin gaba Waya, Wajen kuma yazama koren hasken ba abinda akeji sai ihun Waya daga cikin  yan uwan, amma ba a iya gane wane ne  sai dai ruwan cikin tukunya ya yi ja, ya fara motsawa kamar yana numfashi.

A ?arshe, wutar ta lafa& kujerar Waya ta zama Kasa babu ita babu mutumin dake kai

Tun a lokacin bokam tsafi yagane akwai matsala, tashi yayi ya tsaya a tsakiya, yana dube dube kallon su yayi duk idanun su sunyi ja kamar an kunna wuta a ciki. hannunsa ya daga sama, sannan ya ce:

> * Wanda yarasa rai a cikin ku shine wanda Rayuwarsa tafi baki yatafi kuma bazaku huta ba , a karo nagaba biyu ne zasu tafi& gasar ta na gaba za ta tabbatar da wanda zai hau gadon Mulki, sauran su rasa ransu gaba daya.


Nan take, ?asa ta buWe a tsakiyar fili. Wata tukunya tafito mai dauke da ruwan bakar dalma  ruwan nan yana da launin shuWi mai wal?iya, yana kuma Wauke da bakin hayaki.

Bokane yayi mgana:

> * Kowane Waya daga cikinku ya tsoma abin tsafinsa cikin wannan ruwa, ya fito da abin da zai nuna masa makomarsa!"*

Duka su hudun suka matso a tare suka tsuma abinda ke hannunsa, nan take isa mai karfi tataso ta zagayesu wani duhu mai kalal shudi ya shigo yana zagayesu.

Karar kamar ihu shima yana zagaye kunnuwansu, saikuma muryar Aljanu tana nata aikin

Kafin su zaro hannunsa Aljana jumana tashigo ta cikin hasken tazuba abinda ke hannunta cikin wutar, dai dai lokacin da iskar zata tsaya itama ta baci.

Hannunsu suka zaro gaba dayansu sai dai babu mutum biyu daga Yarima Lahab sai Gimbiya Lamra.

wata murya ce ta fito daga cikin ramin, tana fadin:

> **"Daya daga cikinku zai hau mulki& dayan kuma zai zama sandar ?arfinsa  ba tare da rai ba!"**

Cikin kiftawar ido, ?asa ta fara girgiza, bishiyoyi suka fito da bakin ganye, sautin dariyar aljanu yafito fili gumaka suka rusuna tamkar suna gaida wani sabon sarki.

Haske mai duhu ya lullube dajin gaba daya, kafin wani ya yi magana, iska ta Wauke Gimbiya Lamra tayi sama da ita, sai kuma shiru haske ya bayyana filin kamar babu abin da ya faru.

Mutanen gari yan kallo suka bayyana, Yarima Lahab tsaye rike da Sandar tsafi mai bakin haske.

Ihu mutanen gari suka saki suna fadin:

 Yeeeeh Ranka yadade Yarima Lahab.

Wani kafirin murmushi Lahab yasaki yana fadin Mulki ya dauwama a gareni.

Daganan Sarki yafara shirye shiryen murabus aka dora Yarima Lahan tare da hakkin wayanan yan uwan nashi.

Wannan shine Asirin dake lulube a masarautar Kumbu, amma duka wanan yafaru ne bayan Gimbiya Lamra tahafi danta namiji guda daya, wanda yake hannun baiwarta.

Bayan hawan sarki Lahab kan kujerar mulki yanemi yaron Lamra amma yarasashi tunda daman ba a masarautar take aure ba, amma kuma tazo da yaron masarauta wanda yake da shekara 7 a lokacin

Muje zuwa&
_Daga alkalamin Saiyyid writer_


=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*

Mai bukatar complete document 400 08165383931


Page (15&16)

2025& &

Masarautar Kambu.

Mai martaba Sarki Lahab ne zaune, cikin kasaitaciyar fadarshi daga gefe kuma yan majalisa masu zaman fada ne.

 Ranka yadade zamu iya zuwa ganin mayakan a yanzu.

Wazirin Sarki wanda shika dai ke da damar magana a fada yafada

Sai da Sarki Lahab yadauki kusan mintina uku sanan ya miki, yana mikewa kowa da kowa yatashi suka rufeshi aka fita.

Akalla mayakan sunkai mutum dubu Ashirin da aka gama horarwa kuma kowanne a cikin su yasamu kwarewa.

Sai dai Sarki Lahab yagama zagayesu baki dayansu, sanan yakoma Fadarshi.

Kai tsaye cikim gidanshi yanufa inda bai tsaya ko ina ba sai bangaren, matarshi uwar gidanshi Mai suna Gimbiya junaida wacce ya auro ta daga masarautar da yar uwarsa Lamra ke aure acan.

Gimbiya Junaida macece mai matukar hakuri da kawaici, ta auri Sarki Lahab ba tare da ta taba sonshi ba ko kadan sai dan Umarnin mahaifinta, amma kuma ko da sau daya bata taba nuna masa hakan ba.

Tana Zaune tana faman tunanin rayuwa mussaman yanda mijinta ke gudanar da mulkin zalunci a masarautar Kambu, shigowar shi yasata tashi yana fadin:

 Barka da shigowa maimartaba.

Murmushi yayi sanan yace:

 Barka dai Fulani.

Guri tabashi ya zauna sanan ta tashi tashiga hada mai shayi.

Yana nan zaune takawo masa ta durkusa tabashi ya amsa, yana cikin shane tayi gyaran murya sanan tafara magana:

 Ranka ya dade, dazu nasamu sako daga masarautar mu cewar ansamu labarin akan dan wajen Gimbiya Lamra.

Da sauri yadago ya kalleta, domin a rayuwar Sarki Lahab ba shi da wani wanda yake nema yaga bayansa kamar wanan yaron, domin shi a jikin shi yaji cewa yaron zaizamar masa matsala babba.

Dukda bokayen tsafinsu sun sanar dashi bata bangaren yaron bane juyawar Kaddarar sarauta da Aljanun tsafi suke sanar dashi zatazo masa ba, Amma sarki lahab yakasa Yarda da hakan baki Waya.

Murmushi yasakar mata sanan yace:

 Gaskiyya Fulani kinzo mun da sa?o mai muhimmanci, wanda ya faranta ranata gaba Waya.

Murmushin itama tayi tare da tashi ta Wakko masa zuma tana faWin:

 A sani rayuwata dakai baby abinda kakeso kamar bayyanar Wan wajen ?ar uwarka, wanda muma jinine anamu gidan.

 Fulani bazaki ganeba, a gudanar da gasar tsafin man sai da narasa ?an uwana baki Waya, wanan yaron Wan wajen Gimbiya Lamra shikaWai yarage, du da inada nawa yaran amma wanan shine asalin jinin ?ar uwata.

 Tabbas hakane mai martaba, kuma zansanar da sarkinmu kam cewa a kawo shi yaron masarautar nann.

 idan kikayimun haka Gimbiya Fulani kingama yimun komai.


*MASARAUTAR ZARWATA*

Gimbiya Zulfa mai babban Waki ce tare da maimartaba sarki Tukur, zaune cikim Wakin bangarem Gimbiya Zulfa.

Mai Martaba ne ke magana cike da tsantsar tashin hankali da kuma damuwa:

 Yanzu ke Sangaren ki guda amma kisa sanin wa?anda suka shigo a rana Waya?, wanan fa va ?aramin abu bane.

Tashi Gimbiya zulfa tayi, tafara zagaye Wakin tana haWe hanyenta tana dukan juna dasu:

 Gaba Waya mutanen dasuka shigo Sangarena nasa ankamasu, wanan yarinyar Sara da ?anwarta ne kawai kuma su basukai ga shigowa ba.

Kallonta yayi sanan yace:
 Ni inaganin muhaWe harsu mukai dajin haske, shine kawai mafitarmu.

Kallon sarki Tukur tayi tare da girgiza kai sanan tace:

 Kana magana kamar bakasan me kake cewa ba.

 Yanda muka kawar da Mahaifinsu yazama kamar baya duniya, to suma zamu iya karki manta nike da sarautar gari, kuma zan iya komai domin sarauta ta.

Guri Gimbiya Zulfa tasamu ta zauna sanan ta kalleshi tace:

 A wancan lokacin idon mutane baya kanmu, yanzu kuma fa?.

 Zulfa kinaso asirin mu ya tunu ne?.

Girgiza kai tayi sanan tace:

 Kaje zanyi shawrara yadda za a Wauke yaran, ba tareda idon mutane yakai ba.

Jin alamun fitowa yasa Sarah dake tsaye saurij boyewa jikin bango, fuskarta na zubar da hawaye.

Ficewa Mai martaba yayi zuwa Sangarensa, itakuma Sarah tarasa ina zatayi, ficewa tayi kai tsaye zuwa Sangaren Baru.

 Yanzu lokaci yayi da zakadaina Soyemun duk abinda kake Soyewa.

?aga ido Baru yayi yakalli Sarah dake shigowa ba tareda yace mata ?ala ba.

 Nasan Mai martaba da Gimbiya Zulfa ne suka saka mahaifina a wanan halin dayake ciki, sanan Jiddah tagano wani sirrinsu wanda a yanzu suke shirya yanda zasu Waukemu sukaima wajen Aljanun haske.

 Aina kika samu wanan labarin?.

Baru yafaWa yana kallonta da mamaki sosai

 Baru da kunnuwa naji mai martaba da ita gimbiyar suna magaanr naje Sangaren nata, Maamah ta turani na gaidata.

 Sarah kiramini Mamanku.

Baru yafaWa yana tashi yanufi inda Yarima Abbas ke kwance ita kuma Sarah tafice.

Kallon Yarima Abbas Baru yayi sanan yace:

 Ranka yadaWe ina tunanin lokacin bayyanawa ahalinka gaskiyya yayi, sanan lokacin barinsu Zarwata yayi.

?aga kai Yarima Abbas dake kwance yayi, alamun ya amince dai dai lokacin da Sarah da Gimbiya Sadiya suka shigo.

Baru ne ya umarci Gimbiya Sadiya da zama, sanan ya kalli sara yace:

 Saratu kin daWe kina bibiyata akan sanin menen asalin ciwon mahaifinki, kindaWe kina bibiyata akan meyasa na hanaku sanar da ?an uwansa, samun sau?insa, kindaWe kina tambayata menake Soyemiki ko?.

?aga kai Sara tayi alamun  Eyh shikuma ya Wora da faWin.

 Shekaru 21 da suka huce, lokacin da mahaifinki ke karSar horan tsafin gasar haske, lokacin ne asalin tsana da hassada na ?an uwansa biyu yabayyana, lokacin sukaji zasu iya sadaukardar da Rayuwar mahaifiyarsu, su jefa rayuwar Wan uwansu a rana.

A dai dai lokacin da aikin gasar tsafin haske na mahaifinku ya kuskure, sai danayi kwana uku a sume, a cikin wanam suman tsafim haske na gaskiyya yakaini ga duk wani abu da Gimbiya Zulfa da Yarima Tukur suka aikata a wanan lokacin.

Sanan nagano yanda zaki zama sila guda 1 dazaki ruguza duka wanam tsafin, Sarah ?ADDARAR SARAUTA ta zaSa miki abubuwa masu yawa da wahala a rayuwarki.

Sarah Baki fara ganin komai na rayuwa ba, ?ADDARAR SARAUTA na zagaye dake, sai dai kuma yar uwarki zata zama ?arfinki,Zakuyi ya?i a tare kuyi nasara a tare sanan ba iya zarwata zaku bayyana gaskiyya ba duka duniya ne.

A yanzu dake da ?ar uwarki zaku bar zarwata.

 zuwa ina?.

Gimbiya Sadiya ta tambaya, kallonta Baru yayi sanan yace:

 Akwai inda zanturasu kuma bayan kwana biyu ke da Mahaifinsu zaku bisu.

Tashi yayi yashiga haWe kaya saida yagama sanan ya kalli Gimbiya Sadiya yace:

 kije ki da??o musu duk wani abu da zasu Sukata, sanan kihaWa musu da kuWi da gwalagwalai, domin sune zasu taimakesu sama da komai, yanzu a rayuwar nanda muke ciki kuWi keyin komai.

Tashi Gimbiya Sadiya tayi tanufu Sangarensu shikuma ya juyo ya kalli Sarah:

 A yanzu zaki fara sa ?afa a ?alubalen Rayuwa, sai dai inaso komai dakika gani ko kikaji, kar ya raunana ki, yazama ?arin ?arfin gwiwar ki.

GyaWa masa kai kawai tayi shikuma ya cigaba da magana:

 ?ar uwarki zata iya tashi kowanne lokaci, inaso kiyi amfani da wanan taswirar duk inda zaki nufa yana ciki.

YafaWa yana mi?amata taswirar,dai dai lokacin da Gimbiya Sadiya tashigo hannunta ri?e da kayan, mi?ama Sarah tayi tana faWin:

 Abun bauta yakaremun ku.

Rungumeta Sarah tayi itam ata rungumeta, dai dai lokacim da jiddah tafaraka tana faWin:

 Yayah Maimartaba da Gimbiya Zulfa yan iska ne, iskanci suke a tare ba kaya.

Da sauri suka dawo inda take suka ri?eta, sai da Baru yayi mata magani ta nutsu sanan tabasu labari, kowa yayi mamaki banda Baru dominshi yasan komai.

Kallon Sarah yayi sanan yace:

 Lokaci na ?ure muku Gimbiya, kitafi da ya?ini a ranki sanan duk inda kika ga gaskiyya ki karSa.

 Ina zamu?.

Jiddah ta tambya, Gimbiya Sadiyace ta rungumeta sanan tace:

 Su mai babban Waki sunsan kin gansu dan haka yar uwarki zata Soyeki na lokaci kaWan.

Hannun Jidda Gimbiya Sadiya takama sanan taje takama na Sarah ta Wora akai:

 Jidda ga ?ar uwarki man, kibita duk inda tasa ?afa, kekuma Sarah ga ?anwarki nan ki kula da ita kizama gatanta, kizama
da uba awajenta.

Kuka Sarah tafashe dashi itama jidda haka, hannunsa tahada da na mahaifinsu dake kwance yanajinsu shima yana zubar da hawaye.

Baru ne yasake magana:

 Gwanda kutafi tun yanzu, zuwa sanda zasu fahimta kunyi nisa.

Cika hannunsa Gimbiya Sadiya tayi sanan ta mi?amusu abinda ke hannunta tafara magana:

 wanan shine duk wani arzi?i namu, na haWa nabaku domin nakune, abun bauta yakareku.

Tashi sukayi Baru yabude wani labule saiga ?ofa ta bayyana yasa wani mukulli a hannunshi yabuWe, siriyar hanya ta bayyana kallonsu yayi sanan yace:

 Kubi wanan hanyar zata fitar daku bayan gari, bakuma ta hanyar da zaku hadu da kowa ba, amma kafinan duk wani abu daya dangancu Sarauta kucireshi a tare daku, domin wasu ganin wanan zaisa subiku.

Cirewa sukayi sanan sukabi hanyar suka fara tafiya


Muje zuwa&
_Daga alkalamin Saiyyid writer_


=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login