Showing 3001 words to 6000 words out of 22971 words

Chapter 2 - KADDARAR SARAUTA COMPLET BOOK BY SAIYYID WRITER.doc

Advertisement

gefe kuma ruhin aljanun daji ne zagaye dasu suna wani irin ihu da kara jikake.
 Hoooooooooow.
 Yooooowh.
Malamin tsafi Baru ne ya zuba jinin zakara a hannun Yarima Abbas sanan yadora fatar maciji akansa.
Sanan Yarima Abbas yafara
**rantsuwa**:

> * Na rantse da ikon kakanni,
> Zan bi dokar tsafi,
> Zan yi abin da aka umarta,
> Ko da kuwa rayuwa ta ta salwanta. *

A can bangaren Aljana Jumana kuwa tsugunne take a tsakiyar rami mai zagaye da fitilun tsamiya bakwai. Wani ?amshi mai sanyi ya bazu daga turaren ?un?uni da yake ?ona a cikin kwandon ?arfe.
A ganta akwai kan gimbiya Rumana wanda aljanu suka dakko bayan Yarima Tukur da Gimbiya Zulfa sun kashe ta.

Aljanu sun sato kanta wanda yake can kuma ba asalin kan nata bane sai kuma.

* ?asan ?ofar fada da ya saco a daren baya
* gashin tsuntsun aku mai she?i
* jinin akuya ba?a
* da zoben **Yarima Abbas**, wanda duk jama a suka yi imanin shi ne ya dace ya hau kan mulki.

Duk cikin wayanan abubuwan babu wanda Yarima Abbas ko Gimbiya Zulfa suka sato da kansu face Aljanu dasukayi wanan aikin

Aljana Jumana ta daga hannayensa sama, muryarsa na rawa da ?arfin iko tace:


> **"Ya ruhun murWa, ya ruhohin kurciya, ku tashi daga asirin ?asa, ku shige cikin zuciyar mai gaskiya ku cilla shi daga gadon mulki!
> Ku shigar da wanda babu hakki, ku ba shi kujerar sarauta, ku rufe idon jama a da ganyen tsamiya!"**

Iska ce ta taso daga babu, tana zagaye fitilun, tana murWa wutar turare. Cikin rami can kuma sai aka fara jin wani irin ?ara kamar murya tana fitowa daga ?asa:

> **"Mun ji ka& mun amsa& za mu juya kaddara."**

Tashi Aljana Jumana tayi ta zuba ?asar fada cikin kwandon, sanan ta shafa jinin akuya a kan gashin aku, ta naWe su da zoben Yarima Abbas a ciki. Da sauri ta Wora wannan kullin a tsakiyar ramin.

Ta sake kiran maganin ?arshe:

> **"Kurciya ta ruguje, hasken gadon ya mutu, mulki ya juye.
> Wanda bai cancanta ba, ku Wora masa rawani, wanda ya cancanta ku jefa shi cikin inuwa!"**

Da sauri Gimbiya Zulfa tace:

 Ajefa shi rana.

A lokacin, fitilun tsamiya suka bushe gaba Waya. Duhu ya lullube wurin, iska ta yi ?ara kamar ana hura ?aho daga wani duniyar daban.

Lokacin da wutar ta sake haskowa, Aljana jumana ta yi murmushi mai cike da mugunta. Tsafin ya kammala. Kaddarar mulki ta riga ta juye.

****Dajin Kogon Haske*****

Daga cikin Kogon Gada, Malamin tsafi Baru yana cigaba da gudanar da nashi tsafin Yaji Kogo na juya, ruhinka aljanun daji ya baci, iska mai karfi tayi cillo da yarima Abbas Zuwa rana.

Wata kara ta karade Dajin gaba daya,sanan wanj bakin haske yafinga fitowa.

A dai dai wanan lokaci mai martaba da mutane, suna zaune gaban gawar Fulani Rumana, gaba daya jikin mai martaba yayi sanyi,tabbas a yanzu yake tunawa da kuma yarda da abunda yarima Abbas yafada masa.

 Inaji a jikina kamar KADDARAR SARAUTA zata canja mun komai daga farin ciki zuwa damuwa.

Juyowa yayi ya kalli waziri yace:

 Aika da mutane zuwa kogon dajin haske,aje atawo mun da dana.

Tashi waziri yayi yafice zuwa bada umarni,sai dai kafin suje KADDARAR SARAUTA tariga fatansu,domin su tarar da Dajin yagama bakim hayaki, Yarima Abbas yana gefe a zube haka malamin tsafi Baru.

Kamawa sukayi suka tawo dashi, a ranar hankalin fada yatashi, Masarautar Zarwata tashiga damuwa da tashin hankali.

Ga mutuwar Fulani Rumana, wanda kowa ya tabbatar da kashe ta akayi, sanan ga Halin da Yarima Abbas ke ciki.

Mai martaba Sarki Iliyasu yaga mummunan dare yaga mummunar rana, Masarautar Zarwata taga tashin hankali.

Haka kwanaki sukayi ta shudewa anata faman neman maganin Yarima Abbas, Mai Martaba sarki Iliyasu yashiga damuwa, wacce ta kwantar dashi, ana haka Gimbiya Sadiya Matar Yarima Abbas ta haife cikin ta, inda tasamu yarinya mace.

Ciwo ya kwantar da Mai martaba, Yarima Abbas na kwance shi ba mai rai ba, shi ba marar rai ba.

Ganin haka yasa wakilai suka bukaci a nada Yarima Tukur, wanda a farko Gimbiya Zulfa suka bukata,sabida a tsarin Al addarsu itace akan layi, sai dai dakanta tace bata bukata.

Mai martaba bada son ranshi ba aka nada Yarima Tukur A matsayin Sarkin Masarautar Zarwata.

Inda yafara gudanar da Mulki, buri ya cika KADARAR SARAUTA ta tabbata, bayan hawanshi kan mulki yayi aure, inda ya auru mata guda biyu lokaci daya, wanda kuma har a lokacin Kusanta tsakanin sa da Gimbiya Zulfa ya zama ruwan dare.

=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*


Page (5&6)


Shekaru sun shude, Yarima Abbas sai da ya shekara goma sha biyu a kwance sanan ya iya motsi.

Lokacin Sarki Tukur yana gudanar da Mulki shida gimbiya Zulfa, yanda sukaso suka ga dama, Maihaifin su Sarki Iliyasu ya rasu, tun ciwon da ya kwanta, sakamakon rashin lafiyar Yarima abbas dakuma rashin Matarsa Gimbiya Rumana.

A bangare daya kuma saratu mai suna Sara, yar gidan Yarima Abbas, tataso ne jinin Fansa na m yawo a jikinta, KADDARAR SARUTA na mtasowa da duk rayuwarta, Tsanar Sarki Tukur da Gimbiya Zulfa sune abinda ta tashi dasu, da kuma alkwarin daukan fansa tare da kwato mulki zuwa ga ahalin su.

Aljana Jumana ta sanar da Gimbiya Zulfa akwai wani jini daga cikin jinin gidan sarauta, zai yakesu zai zame musu damuwa, zaisa su kuka,zaisu danasani, zai kuntatace su.

Wanan Abu ya matukar kada Gimbiya Zulfa,sanan gashi Aljana Jumana, bata bayyanata mata wanan Jini ba.

(2020)& & & ..

*MASARAUTAR ZARWATA& *

Sarah yar gidan Yarima Abbas ta taso yarinya mai dakakkiyar zuciya, yarinya mara tsoro, yarinya mai kokarin fada. a yanzu tana da shekara 6 a duniya, amma Sara bata da wajen zuwa da yahuce, Kusungo.

Kusungo waje ne da ake koyarda mayaka fada, a ko dayaushe Sara na fitowa daga cikin masarauta taje kusungo.

Duk wani irin training da ake bawa mayaka, Sarah na kallo, a lokacin da takai shekara 15 ne tafara kokarin gwada abubuwan dasukeyi.

Kokarin hawa kan doguwar bishiya da tayi ne yasata jin ciwo a jikinta, haka take to fada kaca kaca, jiki duk jini.

A hanya Gimbiya zulfa wacce ke da mukamin Mai babban daki a kaf Masarautar Zarwata.

Fadawa biyu maza a gaba, sai kuma mata hudu ita kuma tana tsakiya wanda yan mata hudun suke rike da farin kyale, mai walwali sunsaka mata a sama yana kare mata rana, kowaccw tarike kusurwa daya sai kuma wasu fadawa mazan guda biyu a baya.

Har sun huce ta Gimbiya zulfa tayi magana da jakadiyarta wacce ke binsu daga baya.

Takawa Jakadaiya tayi tana fadin:
 Gimbiya Sarah,Gimbiya.

Tsayawa Sarah tayi rai a baci, domin ita a rayuwarta babu abinda ta tsana sama da akirata da wani gimbiya ko ranki yadade.

ita a gaba daya rayuwarta bata taba daukan kanta a sarauniya ba, face mayakiya.

 Fulani na nemanki, tace kibiyo ta abaya.

Jakadiya ka fadin haka ta juya,itama Sarh ta juya zuwa bangaren Fulani Zulfa.

Bangaren dayaji kayan Alatu,kayan ado ko bangaren mai martaba bazai nuna masa jin kayan ado ba.

A caccanki dakinta ta sameta, tana zaune kam gado, tana jiran shigowarta.

 Ranki yadad e gani.

Sarah tafada tana sunkuyar da kai,sai da Gimbiya Zulfa tagama kare mata kallo gaba daya,sanan tabude baki cike da Isa da sarauta tace:

 Saratu me kikeson zama ne?, mekike son yi a rayuwarki ne?, haka kikaga duka yan uwanki sunayi, dan Allah jibi ke kamar ba waccw tafito daga gidan Sarauta ba, Sarauta ma kamar ta Zarwata.

Kasa Sara tayi da kai, ita ba taga dalilin wanan saka kayan adon ba, masu nauyin masifa, indai zatai wanka tasa kaya tafita Kusungo, yafi mata komai a masarautar zarwata sai kuma zuwa wajen Mahaifinta.

 Saratu ba dake nake magana ba.

 Ayi hakuri mai babban daki.

 Tashi kiji kiyi wanka ki canja kaya, sanan ki dawo.

Tashi tayi tafice a ranta kuwa tana cewa:
 Sai kiga wanda zaidawo badai Saratu Abbas ba.

Daga nan Sarah kai tsaye nasu bangaren tanufa, inda ta tarar da Mahaifyarta Gimbiya Sadiya tana koyawa kanwarta Jidda karatu.

Kallon Sarah Gimbiya Sadiya tayi sanan tace:
 Saratu zo.

Zuwa tayi ta zauna,ba tare da tace komaiba

 Daga ina kike?.

Turu baki tayi sanan tace:
 Kusungo, sai kuma naje wajen Gimbiya Zulfa, wai kuma tace nasake dawowa, kuma wallahi baranje ba.

 Saratu Mai babban dakin kike cewa bazaki kiranta ba? kina da hankali kuwa.

 Ina dashi mamana Maamah.

 Tashi kije kiyi wanka ki shirya, kizo kici abinci sanan muyi magana.

Tashi Sara tayi, ta fice zuwa inda zatayi wankan, bayan tayi ne tasaka wata doguwar riga marar nauyi, sanan tafito zuwa inda Maaman ta take.

Lokacin tagama koyawa jidda karatu, ita kadaice a zaune sai yan hadimanta, guda uku

Kallon Sara tayi sanan tace:

 Saratu yanzu kinfara girma, yakamata kisa a ranki cewa kema fa sarauniyace, dabadan KADDARAR SARAUTA ta gjfta ba, da yanzu Mahaifinki ne akan mulki,amma duk da hakan kanin mahaifinki ne akan mulki,kuma shima mahaifin ki ne.

 Maamaah kina nufin da tuni Abba ne a kan karagar mulki?.

 Kwarai Saratu,da KADDARAR SARAUTA bata gifta tabbas yanzu shine akan mulki.

 Wacce KADDARAR SARAUTA ce haka Maamah.

 Sara Kaddarar kowacce kala sunanta Kaddara dan haka, ki nutsu ki maida hankali akan sha anin Sarauta.

 Mamaah bana sha awar Sarauta, bana sha awar duk wani abu da yashafe ta, ni a barni nazama mayakiya.

 Tashi kije kici abinci, kihuce wajen mai babban daki.

Tashi Sara tayi tafice zuwa can bangaren da Baru malamin tsafi ke kula da Mahaifinta.

Kallon mahaifin nata wanda ke kwance take, hannu ta dora samna fuskarsa sanan tace:

 Baba Baru baccin yake ko?.

Daga kai Baru yai sanan ya cigaba da shafa mai abinda ke hannunshi.

 Baba Baru,Abba na yakai shekara nawa a wanan kwancen?.

 Shekara goma sha biyu.

 Ina shekara uku kenan ko, ita kuma Jidda tana yar karama?.

 Ey kina shekara uku,kanwarki koma ba a haifeta ba.

Yabata amsa yana cigaba da abinda yake,tashi tayi zata fice sai kuma tadawo ta zauna tana kallon Baru, kusan minti biyar kamar maiyin tunani sanan tace:

 Wane ciwo ne ke damun Abba na?.

Kallonta Baru yayi,yanda tayi maganar kamar na ita yar shekara goma sha biyar ba, girgiza kayi yayi alamun baisani ba.

 Amma kai kake kula dashi, taya zakace bakasan meyake damunshi ba?.

 Bansaniba Saratu.

Yafad a a tsawace, tashi tayi tafice a ranta tana cewa.

 Dole akwai wani abu kuma ni Sara saina nemo shi.

 Amma kifara bari kizama babbar mayakiya mana.

Wani bare daga cikim zuciyarta yafada mata, daga kai tayi alamar  eyh sanan tace:

 Tabbas.

Daga haka tahuce zuwa bangaren Gimbiya Zulfa, zama tayi acan gefe dai da Gimbiya Zulfa tace:

 To yar masu bakin hali,sai na kiraki kizo?.
Tasowa tayi ta matso inda Gimbiya Zulfa take sanan ta zauna,kallon ta Gimbiya Zulfa tayi sanan tace:

 Saratu me kikeson zama a rayuwarki?.

 Ni dai inason na koyi fada dan Allah, inason akaini Kusungo.

 Wai saratu baki da hankali ne, so kike mubarki mutane suyita yawo da Masarautar mu suna cewa, munbar yayan dan uwan mu a wulakance?.

 A ah mai babban daki, to a saka shi barde din yadinga koyamun a cikin masarauta.

Gimbiya Zulfa tabude baki zata magana,wasu yan mata guda biyu suka shigo, wayanda a kalla zasuyi shekara 13 alamun Sara ta girmesu,amma kuma sunfita tsawo suna sanye cikin doguwar riga, Jikinsu yaji ado kana ganinsu kaga jinin sarauta.

Zama sukayi kusa da Gimbiya Zulfa take suna fadin:

 Ammi we re back.

Murmushi tayi sanan tace:

 Sannun ku da dawowa Gimbiyoyi na.

Murmushi sukayi sanan daya a cikin su tace:

 Me wanan takeyi anan?.

Tafada tana nuna Sarah, dayarce tayi dariya sanan tace:

 Yanzu wanan za a kalla ace tafito daga gidan sarauta,kamar masarautar zarwata.

Dariya suka fashe da ita sanan Gimbiya Zulfa tace:

 Kuyimun shiru, ke kuma Sarah ina gayamiki a karo na karshe kicire ranki daga maganar wanan zama mayakiyar.

 Ai ni inaga wallahi da anbarta tazama mayakiya,domin dasu tafi kama.

daya daha cikin yan matan tafada,tashi sara tayi tafice,kai tsays Kusungu takara nufa akwai wajen da take zama tana kallon duk abunda suke.

Sai da taga rana na shirin faduwa ta tashi zata huce ciki,amma sai tafara zuwa wajen barde ta sameshi.

 Barde barka da aiki.

 Barka dai Sarauniya Saratu da me zan taimakamiki?.

 Barde akaro na ba adadi na kara zuwa wajenka, kan koyar yaki, inaji a jikina kamar koyan yake yadace dani ba zama sarauniya ba.

Kallonta Barde yayi tabbas yayarda da yarinyar nan tanason wanan koyan fadan,domin tun tana karama take zuwa wajen nan, kallonsu kuma ko yaushe sai tayi mai maganar koya,kuma a yanayinta tabbas zata iya.

(2022)& & &

A yanzu Sarah na da shekara 17,kuma har a yanzu tana nan da burin zama mayakiya, ko da yaushe tana wajen barde domin yanzu data girma ta rage fita kusungo.

A sanda Sarah take girma,a lokacin kyauwun ta yake kara bayyana, a lokacin zuciyarta ke kara tsayawa, halinta ke kara mudewa, zuciyarta kw kara bushewa.


Zaune take cikin zauren Masarauta, tana jiran mutanen fada su fito, tasami shiga zuwa wajen mai martaba, akaro na ba adadi neman sahaliwa kan koyan yaki.

Tsawon mintuna goma sha biyar tana tsaye, sanan mutanen ciki suka fara fitowa,sai da tajira suka gama fitowa sanan tashiga ciki.

Mai martaba Sarki Tukur yana zaune tare da babban dansa Yarima Faisal, kallonta sukeyi har takaraso.

Zama tayi tare da fadin:
 Aminci ya tabbata ga sarki,kuma shuga a masarautar Zarwata.

Murmushi yayi ba tare da yace komai ba,Yarima Faisal ne yace:

 Meke tafe dake?.

Shiru tayi na yan mintina sanan kuma daga baya tabude baki tana fadin:

 Ya adalin sarki a masarautar Zarwata,yau ma yarka tasake dawowa a karo ka na babu adadi neman sahalewarka.

Kallonta yake sosai,yarasa meyasa wanan yarinyar jinin sarauta baya yawo a jikinta,gyaran murya yayi sanan yace:

 Kije zansame yayata Mai babban daki muyi magana,koma menene zakiji daga baya.

 Nagode.

Tafada tana tashi ta fice,karamin wajen data ware a bangarensu tanufa, cire rigar alkyabba dake jikinta tayi, wacce daman kamar ta shimfida kaya akan ta haka takeji.

Wani k aramin dutse wanda aka sarrafa mata shi yazama kamar abin dauka na masu koyan karfi, shi takai hannu tafara dagawa.

haka taita faman dagashi tana ajiyewa,nishinta kawai kakeji

=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*


Page (7&8)

*A cancikin Bangaren Mai babban daki*, daga can dakin ta dake baya wani k aramin kusurwa ne da babu wanda yasan yanda yake,babu wanda ya isa yashiga ciki ko ya tunkari wajen.

A takaice ma babu wanda yasan da wajen,sabida daga cancikin dakin Gimbiya zulfa yake.

Kwance take kan gado haka yayin da shikuma mAi martaba sarki Iliyasu yana tsaye, yana mayarda kayan jikinsa.

Sai da yagama saka kayan sanan ya kalleta yace:

 Mai baban daki, mekike gani akan lamarin yarinyar nan?.

 Wacce yarinya?.

Ta tambaya tana tashi zaune.

 Yarinyar nan Saratu.

Kayanta ta dauka a kasa tafara sawa,sai da tagama sanan tace:

 Da ina ganin kamar wanan abun da takeso bai kamace taba,sabida jinin sarautace amma daga baya kuma na fahimci ai jinin bora ce, a cikin jinin sarautan dan haka kawai mubarta.

Kallonta yayi sanan ya fashe da dariya sai kuma yace:

 Nima kuma nayi wanan tunanin, domin wanan rashin son sarautan nata mu taimakon mune kinga zamu iya hadata da can wani cikin bayi ya aureta.

 Shikenan ba,idan ma bazatayi auren ba can dasu gada.

Gimbiya zulfa mai babban daki tafada,sanan suka tashi suka fito mai martaba sarki iliyasu ne yace:

 Yanzu zan sanar da barde, yasan yadda zaiyi sanan itakuma yarinya sai kisa a sanar da ita.

Daga haka yafice, ita kuma ta umarci hadimanta dasu hada mata ruwan wanka.

*A cikin fada* mai martaba yasa aka nemo masa barde, bayan barde yashigo ne mai martaba yace:

 Ya bangaren mayakan mu?.

 Abun bauta yadafa  Mai martaba komai yana tafiya yanda ya dace, mayaka suna huruwa.

 Toh haka akeso, yanzu kasamu kari.

Dagawo Barde yayi ya kalli mai martaba sanan yace:
 Mai martaba karin wa muka samu?.

 Yarinyar wajen Yarima Abbas.

Murmushi barde yayi sanan yace:

 To to dama Gimbiya Sarah ta dade tana zuwa wajen mu tana kallon mu,tabbas tana sa ra ayi a tare da ita.

 To yanzu anbata dama, tunda takai matsayin da zata zabi abinda takeso.


*Bangaren Sarah* kam yau tana wajen Mahaifinta, domin a jiya Baru yasamu nasara, akan rashin lafiyarsa, hannushi yayi motsi sanan yana juya kanshi yana kuma kallon mutane.

Abinda yafi komai daurewa Sarah kai, yanda Baru yahana a sanar dasu mai martaba.

Sarah tayi mamaki iya makaki akan wanan abun, data matsa masa da tambaya sai cewa yayi da ita:

 Sarah duk randa kika zama babbar mayakiya, koda bana duniya akwai inda zansa a baki labarin komai da yashafi mahaifinki.

Hakan yasa Sarah takara dagewa akan burinta, shigowar ta bangaren su kenan mahaifiyar ta tace da ita:

 Sarah mai babban daki na nemanki.

 Me kuma zanmata, wallahi Maamah bana kaunar zuwa bangarenta wayanan yaran nata su Labiba da Lubaba basu da mutunci.

 Kece bakya mutunta kanki shiyasa,Saratu kina abu kamar namiji kece fada,kece gudu haba Saratu.

Kallon Mahaifiyarta tayi sanan tace:

 Ni haka nakeson kaina, banida burin zama wata mace da zata zauna komai sai anyi mata, wai ita sarauniya.

 Ai shikenn Saratu,amma kiyiwa kanki fada,kinsan abinda yakamata kece babba a wajen mahaifinki, ki nutsu ki nemawa gidan ku mutuncin shi.

 To ai Maamah bazama sarauniya bane zai fito da mutuncin gidan mu ba.

Ganin Sarah bazata fahimci abinda take nufi ba, yasata cewa:

 Tashi kije wajen mai babban dakin.

Tashi Sarah tayi tahuce, kallon yanda take tafiya tai a fili ta furta:

 Wanan yarinya kamar bajinin sarauta ba.

Sarah kam nafita tahuce bangaren Gimbiya Zulfa, a hanya ta hadu da Gimbiya Labiba da Lubaba zasu huce wajen dasuke hutawa.

Bata kallesu ba, suma basu kalleta ba haka suka huce, sai bayan sunyi gabani Labuba tace:

 Nikam Labiba wai sarah jinin Sarauta ce, kinga yanda take tafiya kamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login