Showing 12001 words to 15000 words out of 22971 words

Chapter 5 - KADDARAR SARAUTA COMPLET BOOK BY SAIYYID WRITER.doc

Advertisement

by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*


Page (17&18)

Tafiya sukayi mai tsawo kafin suka fito haske, taswirar hannunsa suka bude sanan sukaga hanyar da tadace su nufa, haka sukayita tafiya. har dare yacin musu amma basu tsyaba saida suka tabbatar sunyi nisa da Zarwata.

A cikin Masarauta kam, bayan fitarsu Baru ya kalli Gimbiya Sadiya yace:

 Duk sanda akazo daga masaruta nemam su kice Jidda na nan amsar magani ita kuma Sarah na kusungo.

Yafada yana daukan matashi yajerasu dai dai tsayin Jidda sanan ya rufe, jan gadon yayi zuwa ?aramin Waki domin yasan zaiyi wuya mai martaba ko gimbiya Zulfa su shiga man.

Itakuma Gimbiya Sadiya takoma Sangarenta.

_____________


A can ?angaren mai babban Waki itama tana can tana faman tunanin yanda zata fita da Sarah da Jidda batare da rashin dawowarsu zai bata matsala ba.

Haka ta yini tuanin har zuwa dare tana faman tunanin dakyar bacci Sarawo ya Wauketa, haka mai Sangaren mai martaba.

Shikam yagama yanke hukunci kam cewa kawai zaiyi amfani da ?arfin mulkinsa ne ya Wauke yaran domin yasan mahaifinsu ba magana zaiyi ba, domin yana kwance shiba mai rai ba shiba marar rai ba Mahaifiyarsu kam zai iya sawa a yanke mata kai idan zata zamar masa matsala.

*Washe gari*

*Masarautar Kumbu*

Sarki Lahab yagama tsara yanda zai tura a Wakko masa Wan wajen Gimbiya Lamra daga Masarautar Zau.

Tare da matarsa Gimbiya junaidiya za ayi tafiyar, domin ita yagama tsarawa sanan yagama shirinsa yadda a hanya zaisa a kashe mai yaron idan ma matar tashi zata zama matsala a haWa ita a kashe.

Gimbiya Junaidiya da fadawa guda biyar aka haWa suje masarautar Zau, kwana Waya yabata umarnin yi domin gaba Waya bashida wata nutsuwa sai yaga gawar yaron daku sunansa bai sani ba.

Isar Gimbiya Junaida masarautar Zau yasa masarautar kaurewa da farin ciki domin gimbiya Junaidiya mutuniyar kirki ce, sanan kuma Gimbiya Sadiya mahaifiyarsu Sarah itama daga masarautar kumbu take.

Su uku ne ?a?an sarki Qasim mata biyu maza biyu, wanda ke mulki yanzu sarki buliyaminu shine babba sai kuma yarima dauda wanda shine mijin gimbiya lamra, bayan mutuwar gimbiya lamra yakamu da ciwon damuwa wanda shi yayi ajalinsa.

Sai kuma Gimbiya Junaida itace ta uku, sai kuma Gimbiya sadiya su kam ahali ne mai haWinkai baby hassada ko ?yashi, suna son junansu.

Wanan kenan

Isar Gimbiya Junaidiya Masarautar Zau ya zama abin farin ciki sosai da sosai, domin masarauta na kewarsu gaba daya.

Bayan Gimbiya Junaidiya ta huta ta nemi ganin Wan Wan uwanta, Kallonta mai Martaba yayi sanan yace:

 Gimbiya junaidiya! Wanan yaron yazo da wani salo da kuma wani abu da bamusan dashi ba, wai shi Addinin Gaskiyya.

 Mene kuma haka?.

Gimbiya Junaidiya ta tambayi mai Martaba, Tashi mai martaba yayi sanan yace:

 Yanzu zansa a shigo miki dashi.

Bayan mintina kaWan da fitar Sarki, sai ga matashin yaro mai kimanin shekara 25 yashigo.

(Anriga gudanar da Gasar tsafin Kumbu kafin Zarwata)

 Assalamu alaiki.

Kallon yaron dake magana da yaren da bata ganeba tayi har ya matso inda take.

 Ya sunanka?.

Gimbiya Junaidiya tafaWa.

 Aliyu.

Jijjiga kai tayi sanan tacee:

 Kasanni?.

Girgiza kai yayi alamar  A ah

 Sunana Gimbiya Junaidiya, ni Win ?anwa nake a wajen mahafinka sanan mata nake a wajen yayan Mahaifiyarka acan Masarautar Kumbu.

Wani Murmushi kyakyawan matashin yaron yasaki sanan yace:

 Masarautar Kumbu, nayi rayuwa a wani ?auye dake wajen Masarautar amma bashi da nisa da masarautar, nataso a hannun wata mata Goggo lami Itace ta rikeni kamar mahaifiya.

Muntaso rayuwa mai cike da sauki da kwanciyar hankali, muntaso a karkashin Addini na musulunci wanda shine haske a rayuwa

mun tasaka da rayuwa ciwo yakama Goggo lami, ganin ciwon yaci karfinta yasa ta bani labarin rayuwata sanan kuma ta umarceni danazo naga ya uwana.

Kallonshi Gimbiya Junaidiya tayi yanda yake magana kamar mahaifinsa.

 To yanzu shi Addinin naka wane kala ne?.

 Addinina na musulunci addinine mai& ..

Baikai ga karasa magana ba aka sake shigowa cikin dakin, daga kai yayi ya kalli mai shigowa sarki Qaseem ne yashigo.

 Kuna tattaunawa ne?.

Mai martaba yafad a

 Eyh muna tattaunawa ne, mai martaba.

Guri yasamu ya zauna,sanan suka cigaba da hira gaba dayansu anan ne Gimbiya Junaidiya take sanarda mai martaba sakon Sarki Lahab.

Sarki Qaseem baiyi musu ba ko jayayya, sai dai shi Aliyu baiji son zuwa a ranshi ba, domin Goggo lami tasanar dashi wani sirri wanda ya canja masa tunaninsa gaba daya.

Gari na waye su Sarah suka cigaba da tafiya, da sunji yunwa zasu samu waje su nemi abinci suci, daga nan zasu kara tafiya ba tsayawa.

Sunyi nisa sosai da Masarautar Zarwata, kuma suna bin taswirar dake hannunsu.


_______________


A Can bangaren Masarautar kuma, Gimbiya Zulfa mai babban daki taje neman su Sarah amma sai Gimbiya Sadiya tace Sarah tafita Jidda kuma na wajen Baru, amma da tadawo zata tura mata ita.

Haka Gimbiya Zulfa ta bata dare jiran zuwan Sarah domin tasanar da ita gobe zasu fita tare, amma bata babu Sarah babu alamarta, hakan yasa Washe gari da sassafe ta aika hadimanta suke kira mata ita.

Ko da suka dawo sai sukace Sarah, tafita Kusungo abinda ya matukar bata ran Gimbiya Zulfa yasata fita a fusace.

Gimbiya Sadiya na zaune ta hada hannu da gwiwa tana faman tunani, ko ina yaranta suke yanzu?, ko wane hali suke?.

Gimbiya Zulfa mai babban daki ce tashigo tana fadin:

 Wanan wani irin iskanci da rashin mutunci ne da har zan nemi ganim yarinya tunjiya amma akasa turumunta.

Mikewa tsaye Gimbiya Sadiya tayi tana fadin:

 Barka da Safiya Ranki ya dade, naturata tun a daren jiya bansan ba tazo ba.

Wani mugun kallo Gimbiya Zulfa ta watsawa Gimbiya Sadiya sanan tace:

 Kisa hadiman bangarenki suki tara a yanzu ina tsaye.

Tsuru-Tsuru Gimbiya Sadiya tayi tana kallon Gimbiya Zulfa.

 Magana nake faa.

Gimbiya Zulfa takara fada a tsawace, daya daha cikin hadiman Gimbiya Sadiyace tashigo tana fadin:

 Ranki yadade ansamu sako daga wajen Baru.

 Ke fita kije kinemo mun yarinyar nan Sarah.

Kasa Hadimar tayi dakai sanan tace:

 Ranki yadade Gimbiya Sarah bata kwana bangaren nan ba.

Wani mugun kallo Gimbiya Zulfa ta watsawa Gimbiya Sadiya sanan tace:

 Bangane ba?.

Shiru Gimbiya Sadiya tayi, Gimbiya Zulfa takara cewa:

 Ina yarinyar nan, ina kuma Jiddah.

Shiru Gimbiya Sadiya takarayi, tuni Gimbiya Zulfa tafita kai tsaye Wajen Baru ta nufa, ba tare da sanarwa tashigo ciki.

Baru naganinta ya mike tsaye da fadin:

 Ranki ya dade?.

 Ina yarinyar nan Jiddah?.

 Tana ciki.

yafada yana nuna mata dakin, shigewa cikin dakin tai dai dai lokacin da Gimbiya Sadiya tashigo, Girgiza mai kai tayi alamar A ah inda Gimbiya Zulfa daga cikin dakin tace:

 Tana ina?.

Gaba daya ta kiWime kamar wacce ta zauce jin shiru yasata fitowa, kallonsu tayi gaba daya sanan ta kalli fadawanta

 Ku kama su gaba daya.

Shigowa sukayi suka kama su gaba daya, dai dai lokacin kuma Yarima Abbas ya bude baki yace:

 Kar wanda ya kuskura ya tabamun mata.

Da kallo suka bishi gaba daya, nan take idonun Gimbiya Zulfa suka fito waje da matukar mamaki, inda labari kuma ya ishe mai martaba.

A Fusace mai martaba yataso, kai tsaye bangarem da dakin Baru yake yanufa sauri yakeyi kamar ba shine sarki Tukur mai sarauta da izzaba, domin tun a jiya yasanarda Gimbiya zulfa shi zai dauki yaran ta karfi amma tahana, yanzi ga labari ya iske shi kam cewar sun boye a masarauta.

Shigar dakin yayi dai dai da sanda, Yarima Abbas yake magana:

 Duk wani wanda yayi yunkurin kai hannunshi jikin matata, to wallahi sai yabar duniya, Yaya ne nawa ne kuma na dauke su, sun bar masarauta baki daya, kuje kuji da kunyar abun kunyar da sukaga kuna aikatawa.

Cike da Izzah da isa da kuma gadara Gimbiya Zulfa tafara magana:

 Kayi kuskure ku Abbas, yanzu lokaci ya canja Zamani ya shuWe, Kaddarar Sarauta ta juye ta sauka,Muke mulki Zarwata tamuce, Zarwata a hannun mu take, dan haka ko kamesu.

tafaWa tana kallom fadawan.

 Ku haWa hardashi.

Sarki Tukur yafaWa, aikuwa tuni fadawan sukayi kansu baki Waya suka huce dasu wajen ajiya.

____________


A Can ?angaren Masarautar Zau kam, Gimbiya Junaidiya da Aliyu sun shirya komawa zuwa Masarautar Kumbu tare da fadawansu.

Sai da Gimbiya Junaidiya suka Sallama da mutanen Masarauta kan cewar Aliyu Zaidawo bayan mako biyu sanan suka dau hanya.

Sunyi tafiya mai nisa wace ta rabasu da Zau sanan kuma akwai wata tafiyar mai nisa da zata kaisu Kumbu.

Kamar daga sama mutane suka fara fitowa suna yowa kansu, abinda ya matukar tsorata Gimbiya Junaidiya, hakan yasata Umarce fadawansu dasu kara sauri, amma kafin kiftawa sun iske su.

Sara suke kai musu da takofin dake hannayen su, inda sukuma suke tarewa, ganin anan cinsu da yaki yasa Gimbiya Junaida cewa da Aliyu:

 Sauka mukama hanya.

Ai kuwa tuni suka dirgi suka fara gudu tare da wasu fadawan nasu, nan kuwa makasan suka rufa musu baya.

Gudu suke a tsakiyar filin mai cike da sahara ga kwalleliyar rana da ta take.

Daga bangare guda kuma,Sarah ce ta kalli Jidda sanan tace:

 kamar munbace daga kam taswirar nan.

kara kallon taswirar Jidda tayi sanan tace:

 Kamar dai hakan, inaga wajen wancam hatimin muka canja hanya.

Juya kan dokin dasuke kai Sarah tayi sanan Jidda ma tajuya kan nata dokin, sai dai mutanen dasuka hango suna guda ga kuma wasu na binsu a baya ya matukar tsorata su, a tsorace Jidda tace:

 Mu suka biyo.
Kallon mutanen jidda tayi sanan tace:

 Kallesu da kyau, mace da namijin dake gaba suke bi.

Kura musu ido Jidda tayi sanan tace:

 Eyh hakane, yaya kitaimakesu tunda kun iya fada.

Kallon Jidda Sarah tayi sai kuma ta fara tafiya, Aliyu da Gimbiya Junaidiya suna ta fama gudu suka hango doki na tawowa inda suke, ga kuma mutumin dake kan dokin na miko musu hannu alamun zai daukesu.

Kallon Aliyu Gimbiya Sadiya tayi sanan tace:

 Aliyu karka kuskura kaje kumbu, domin wanan makasan daga kumbu suke.

Tana fadin haka tarike hannunsa dai dai lokacin da Sarah takaraso inda suke, hade hannunshi da na Sara tayi inda sarah ta dauke shi caf ta direshi bayanta, ita kuma Gimbiya Junaidiya huka tasamu shiga ta wuyanta jikake  Kyeet.

Da sauri Aliyu ya dauke idonsu, domin bazai iya ganin kan Gimbiya Junaidiya daban ta gangar jikinta ba, inda Sara tazaro ta ta hukar itama jikake  Kyeet ta sare kan wanda yasare na Gimbiya Junaidiya sanan tayo kan dayan

Shima ba imani tatafi da kanshi sanan tamaida hukar ta bayanta, Aliyu kam da matukar mamaki yake kallon mace, wacce a kalla zai iya girmarta tanan wanan kisan babu imani. wanda shi a addinin shi musulunci ya killace mata.

Muje zuwa&
_Daga alkalamin Saiyyid writer_


=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*


Page (19&20)


*Masarautar Zarwata*

Gimbiya Zulfa mai baban daki tare da Mai martaba sarki Tukur ne zaune, sai kuma Yarima Abbas, Baru da Gimbiya Sadiya a durkushe.

 Tambaya ta karshe, ina kuka kai yaran nan?.

Sarki Tukur yakara fada cike da fusata,domin ta gama fusata matuka.

Yarima Abbas ne yayi dariya sanan yace:

 Da Tukur da Zulfa basu isa sauya abinda Kaddara ta rubuta ba, sanan basu isa suhana abinda zaifaru faruwa ba, dan haka duk abinda kuke gudo da tsoro zai faru, mugun aikin ku zai bayyanaa& & 

Bai kai ga karasawa ba sai ji sukai  kyeet
Sarki Tukur ya raba gangar jikin Yarima abbas da kansa, ganin kan yana yawo a kasa yasa Gimbiya Sadiya fashe da wani irin ihu mai karfi da kara sanan tafara fadin:

 Zalunci da kuka aikata bazai barku ba, Abin bauta ya aiko da fitina da tuzarta da la ana gareku azzalumai.

Hanni Sarki Tukur yakai itama zai sare nata kan, Gimbiya Zulfa tarike hannunsa tare da girgiza masa kai.

 Mutuwar hulakanci zasuyi, Mutuwar to zarta.

Daganan tafice tare da bada Umarnin hada mata mutanen gari.

Aikuwa cikin kankanin lokaci kowa da kowa yataru, duk wanda yaga Gimbiya Sadiya dakuma Malamin tsafi Baru a daure sai yayi mamaki.

Domin a cikin masarautar zarwata da wajenta, mutane dayawa sunason Gimbiya Sadiya da kuma tausayinta, kowa yasam mutuniyar kirkice hakan malamin tsafi Baru.

Haka mutane sukayi ta kana nan maganganu har zuwa lokacin da Sarki Tukur da Gimbiya Zulfa suka fito.

sunkuyar dakai mutane sukayi har sai da Sarki Tukur da Gimbiya Zulfa suka karasa inda suke tsayawa, kallon mutane sukayi sanan Gimbiya Zulfa tafara magana:

 A tsarin Masarautar Zarwata tun zamanin iyaye da kakanni har zuwa zamanin mu, duk wata matat sarki da aka kama da lafin cin amana hukunci kisa ake yanke mata, daga ita har mutum da suke aika tawa, dan haka muna kan wanam tsarin har zuwa yanzu.

Kananan maganganune suka fara yawo tsakanin mutane, rabi da kwata na mutanen wajen basu yarda da abinda Gimbiya Zulfa tafada ba, Sarki Tukur ne yafara magana:

 Dan uwana kuma yayana Yarima Abbas dake kwance bashi da lafiya shekara da shekaru, ya mutu a yau dinan amma da mukaje bincike sai muka gano matarshi da mai maganin dake kula dashi suna cin amanar aurenshi, hakan yasa muka fito muki dasu nan domin yanke musu hukunci a gabanku.

Shiru wajen yayi domin maganar mutuwar Yarima Abbas ta kidima gaba daya mutanen wajen, Gimbiya zulfa ce takara cewa:

 San Matarshi ta dauke yaranshi bamu san inda takaisu ba, duk wanda yayi naarar kawo su a yau zuwa gobe zaisamu kyautar mai girma daga masarauta.

Shikuma Sarki Tukur ya kalli mutumin dake tsaye daga gefensa, sanan ya kifta masa ido matsowa yayi zuwa inda Gimbiya Sadiya take tare da zara wukar dake jikinshi.

Hayaniyar mutane ce ke tashi sama sama dai dai lokacin daya daga hukar hannunshi Gimbiya Sadiya ta runtse ido, hawaye yafito daga idonta bai kai ga karasawa kasaba hukar tahuce ta kanta.

Shuu gurin ya dauka gabaki daya, domin yanayin fille kan da akayiwa Gimbiya sadiya ya taba kowa dake wajen, daga nan yadawo wajen Baru shima kuwa fitt yacire mai kai.

Shikenan Babu Baru babu Gimbiya Sadiya babu Yarima Abbas.

Haka kowa ya watse daga wajem jikin shiru babu dadi, hadiman bangaren Gimbiya Sadiya ne suka fashe da kuka bayam hucewar Sarki Tukur da Gimbiya Zulfa.

Kuka suka fara sukayi inda gangar jikin nasu take suna kokarin kwancewa, kowa dake wajen sai daya tausaya musu, domin tabbas kowa yasan kisan zaluncine akayi musu.

________________



Saida Sarah sukayi tafiya mai nisa tare da Aliyu sanan suka tsaya, sauka Sarah tagi daga dokin da take kai sanan shima Aliyu ya sauka.

Jidda ce ta kalleshi sanan tace:

 Wanene kai?.

Sunana Aliyu daga Masarautar Zau zanje zuwa Masarautar Kumbu, wanan da muke tafe kanwar Mahaifina ce.

 To su wayanan dasuka biyoku har suka kashe maka ita su waye?.

Girgiza ka yayi sanan kuma yace:

 Nima bansani ba, amma ku suwaye.

 Mu basu kowa bane.

Jiddah tafada Sarah kuma ta bude taswirar hannunta, tana dubawa.

Daga ido yayi yakalli Sarah wacce ta mayar da hankali akan duban Taswira yace:

 Nagode da taimako.

 Bakomai.

Sarah tafada ba tare da ta dago ba, Jidda kam cewa tayi:

 Yaya naji kamar wani abu yafaru a gida.

 Nima haka Jidda, naji kamar wani abu marar dadi yafaru da iyayenmu.

Zama sukayi a tare ko wacce tayi shiru, haka shima Aliyu.

Sai zuwa faduwar rana sanan suka tashi, suka hau kan dawakansu.

Sarah ce ta kalli Aliyu sanan tace:

 Kai ina ka nufa.

 Zarwata.

Kallonshi sukayi a tare sanan Jidda tace:

 A zarwata kake?.

Gyada kai yayi sanan yace:

 Amma ba kusa da Masarauta ba, ina nan a cikin wani kauye, mai suna Samunaka kauyen da ko mAsarauta batasan dashi ba.

 Kana da tafiya sosai, bari mu baka dokin mu daya, sai ka tafi.

Sarah tafada nan take jidda ta sauka daga nata dokin tabawa Aliyu ya hau, kudi Sarah tabashi sanan tace:

 Wanan kayi kuziri.

Daganan suka raba hanya kowa yakama tasa hanyar suka huce, Sai dai Gimbiya Sarah tayi sata ba tare da tasani ba.

Haka kuma shima Aliyu yayi sata ba tare da yasani ba, kan taswirar Hannunsu sukabi, haka shima Aliyu yabi hanyat Zarwata zuwa kauyen Samunaka

Chapter 3: Tsafi



Gimbiya Zulfa ta bazama komarta ta ko ina neman Sarah da Jidda, haka mai martaba amma shiru babu su babu labari.

Kwana daya da kashe Yarima Abbas da Gimbiya Sadiya da Malamin tsafi Baru yahuce , babu Sarah babu Jidda.

Kwana biyu yazo ya huce hakama kwana na uku ma yahuce.

Gimbiya Zulfa da Sarki Tukur suna cikin babbar damuwa da tashim hankali mai girma, sun rasa nutsuwa sun rasa zaman lafiya.

Tun lokacin da suka kashe Yarima Tukur dasu Gimbiya Sadiya da kuma Baru suma basu kara samun zaman lafiya ba a rayuwarsu, basu kara samun nutsuwa ba farin ciki yayi kaura daga garesu.

Gaba daya sunyi bijibi bijibi kamar basu ne suke mulkin Zarwata ba, kamar basu ne masu isa da iko ba masu fada aji a cikin Zarwata ba.

Zaune suke A cikin daki kowanne yana zaune, ya zabga tagumi, Gimbiya Zulfa ce tace:

 Zama da faman tunanin bai ishemu ba, ina ganin muje jejin haske ba yau bayan faduwa rana.

 Zulfa ina tunanin abunda manyan Aljanu zasu fadamana, ina tsoron su fadamana abinda nutsuwa zatayi kaura a garemu.

 To yanzu wace nutsuwa muke da ita, wace kwanciyar hankali muke da, ka kalli yanda mukayi fici-fici muka rame.



Muje zuwa&
_Daga alkalamin Saiyyid writer_


=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*


Page (21&22)


Kallon kansa yayi gaba daya yanda yarame ya figi kamar ba Sarki Tukur ba, sanan ya maida kallonshi ga Gimbiya Zulfa itama kamar ba ita bace mai babban daki.

 Shikenan muje din.

Tashi tayi tafice zuwa bangarenta, mijinta Madaki ta samu zaune a dakinta kallonshi tayi tare da shirin hucewa.

 Mai babban daki.

Yakira sunanta dawowa tayi sanan tace:

 A ah Kashigo.

Murmushi yayi sanan yace:

 Baki kula dani ba ma.

Zama tayi ba tare da tace komaiba

 Mai babban daki a zarwata.

Dago kai tayi ta kalleshi batace komai ba, shikuma ya cigaba da magana

 Kwana biyu kina cikin damuwa mai gima, wacce duk wanda yaganki yasan kina cikin damuwa.

 Madaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login