Showing 15001 words to 18000 words out of 22971 words

Chapter 6 - KADDARAR SARAUTA COMPLET BOOK BY SAIYYID WRITER.doc

Advertisement

dan uwana fa Nasara, kuma matarshi tana cin amanarsa ya zaayi kace bazan damu ba?.

 Hakane zaki damu amma yakamata ki dauki komai da sauki.

 Shikenan bari nashiga nayi wanka.

Bata jira cewarsa ba tayi ciki, shima ya tashi yafice.

_____________

Sai da su Sarah sukayi tafiyar kwana uku sanan taswirar ta sada su da wani karamin kauye, wanda shine inda Baru ya turasu.

Kauye ne mai wani irin yanayi, kamar ba a cikin duniyar da muke ba, gaba daya bukkokin kauyen ruwan tokane, sanan dogayen bishiyo marasa ganye sunyi wa kauyen kawanya.

Mutanw kauyen duk kaninsu bakake ne, sanan masu kama daya, Kauye ne wanda tsafi yasamu asali domin daga shigar ia kauyen yanayin jikinka zai sauta gaba daya.

Tafiya suke, a hanakali suna bin Taswirar hannunsu, mutane sai mu amalal su suke ba tare da ko daya ya kallesu ba, kamar ma basa ganin su.

Kananan yara suna tawasa da tsafi wani yana maida kanshi doko, ya koma giwa, ya koma rakumi sauran kuma suna ta dariya, sanan wata kuma tana wasa da yan kananan yara tana daga su sama da tsafi su kuma suna ta kyakyata dariya.

Komai nasu tsafi ne haka suke rayuwa, har su kai ga wata kofa wanda nanne karshem taswirar, kallon juna sukayi Sarah tace:

 Munzo karshe.

Hannu Jidda tasa a aljihu tafito da takardar da Baru yabasu wacce basu bude taba.

Kutsa kai cikin kofar Sarah tayi Jidda na biyemata baya, wani karamim daki ne mai koren haske sai kuma wani dattijon mutum daya yana zaune, shi ba asama ba shi ba akasa ba, ya tankwashe kafafunsa.

Suna shigowa yabude idanunsa wayanda suke koraye ya sauke su akam Sarah, sakkowa yayi daga zaunen dayake yataku zuwa inda suke.

Satah bataji ko dar ba sabanin Jidda tayi tsuru tsuru, mikamasa takarda Sarah tayi ba tare da tayi magana ba yasa hannu ya karba.

Budewa yayi yafara karantawa, yana Karantawa yana kallonsu Sarah sai da yagama karantawa sanan ya rufe idanunshi sanan yadaga hannayen sa sama, kusan mintina goma sanan ya sauke su.

Bude fuskarsa yayi korayen idanunsa suna fitar da bakin hawaye kusan minti goma sanan yafice.

Cikin kanin Lokaci yatara mutanen dake kauyen gaba daya yafara musu magana:

>  Tsafin bakaken Aljanu yakashe mana Baru, sanadiyar mulkin zalunci na masarautar Zarwata.

Wani irin ihu aljanun suka fara kowanne yana fitar bakin hawaye a fuskarsa, saida sukayi mai isarsu sanan mutumin ya juyo ya kalli su Sarah ya nunasu da hannu.

>  Wayanan sune Asalin mulkin Zarwata ke hannunsa aka sauya musu Kaddarar Sarauta, aka bawa wayanda batasu bace ba, sanan a yau ankashe musu mahaifi da mahaifiya tare da Baru.

Wani irin abu Sarah da Jidda suka Zit yashiga kansu yakuma fita, da sauri Sarah tace:

 Ba akashe su ba.

Kallonsu Mutumin yayi sanan yadaga hannu ya bude, nan kuwa hoto ya bude kamar majigi dai dai lokacin da Sarki Tukur yasare kan mahaifinsu, sanan kuma ya kara nuna musu daidai sanda aka sare kan mahaifiyar su tare da na Baru.

Ihu Sara ta sake hakama Jidda, Kuka sosai sukayi a wajen sai da suka gama sanan mutumin yakare cewa:

>  Baru ya aiko su da Saqo, sanan saqon ya bayyana ita wanan.

Yafada yana nuna Sarah, sanan ya cigaba da cewa:

>  Itace zata kawo karshen Tsafin bakaken Aljanu, itace Kaddarar Sarauta ke yawo a jikinta wanan shine yasa Baru ya turuta nan karbar horo kafin lokacin fada da Aljanun tsafi.

Durkusar da Kansu Aljanun suka farayi ga Sarah a hankali kuma duka suka durkusa mata har kasa, sai da suka dau mintina sanan suka dago, shikuma mutumin ya dora da cewa:

>  Zamu koyar da ita, Zamu horar da ita, za kuma mutaya ta yaki domin daukar fansar yan uwan mu da Aljanun Bakin tsafi suka kashe.

*Zarwata*

Rana na faduwa Gimbiya Zulfa mai babban daki tanufi bangren mai martaba, wanda shima zaman jiranta yake.

Karamar bakar hanya suka nufa, sanan suka fara magana.

>  Ya ruhin daddo, Ya ruhin bakaken Aljanu muna neman had i ba jejin haske.

Hanyar ce ta canja zuwa karaman jejin daza subi yasa dasu da jejin haske


Tafiya sukayi mai tsayi acikin dogon jejin,mai bakin duhu, suna cikin tashin hankalin da har yakasa sasu ganin nisan tafiyar dasuke fada a kowanne lokaci ina sunzo

Ihu da karar iska kadai kakeji a cikin dajin kafin suka karasa bukkar matattarar Aljanu.

Yadda bukka take a ko yaushe karama haka take a yau ma, sai mugun duhu da kuma bakin hayaki dake fitowa daga cikinta.

Mai martaba sarki Tukur ne yafara magana:

>  Sarki Tukur daga masarautar zarwata dan wajen sarki iliyasu dan sarki Abbas ne,tare da gimbiya Zulfa mai babban daki a masarautar zarwata yar gidan Fulani Rumana yar gidan Fulani Zullaziya, mun karaso fadar aljanu muna neman hadi da karamar aljana mai kimanin shekara dubu 29 Aljana Jumana.

Wata murya ce daga karkashin kasa tafara magana:

>  Sarkin Aljannu Kudumuya ya amshi zuwanku, sadaukarwar asalin ku ta amso.

Maganar nafitowa ne dakafa da ihu, yanayin da shikadai zaisa kaji hanjin ciki ka na motsawa

Daganan wanan karamar bukka ta girma zuwa babba, wata siririyar hanya ce tafito daga cikin bukkar.

Hanyar suka fara bi, sai da sukayi tafiya mai tsayi a cikin wanan karamar bukkar, kafin suka karaso fadar Aljanna Jumana.

>  Mungaida Aljana jumana,Karamar aljana mai aikin manya.

Wani uban kallo Aljana Jumana ta watsa musu sanan tace:

>  Aljanun bakin tsafi, sunyi fushi ! Sunyi fushi mai tsauri.

Narai narai da idanu sukayi sanan Gimbiya Zulfa tace:

>  Ayi hakuri Aljana Jumana.

>  Kwanan ku nawa baku kusanci junanku ba?.

Kallon Kallo suka farayi, domin tun ranar da Jidda ta gansu basu sake ba dan babu nutsuwa a tattare dasu.

>  Sanan kai kwana nawa bakayi mu amala da Yaro ba.

Kara tsuru tsuru yayi da ido, shi gaba daya babu nutsuwa ma a tattare dashi, harya manta da wayanan abubuwan.

>  Bakusan wayanan abubuwan sune suke karawa aikin ku karfi ba?, duk ranan da kuka daina karfin aikin ku na raguwa, dan haka yanzu kuyi maza maza ku aikata sanan ka tabbatar a yau ka nemi yaro.

Daga haka tabaci, sai kuma muryar ta suka jiyo tace:

>  Idan kungama mayi magana.

Babu kunya babu tsoron Allah Sarki Tukur da Gimbiya Zulfa sukayi abunda suka saba, sai da suka gama sanan Aljana Jumana ta bayyana.

Kallonsu tayi sanan tace:

>  Ina Hasken?.

Gimbiya Zulfa ce tace:

>  Ya Aljana Jumana, munsan Hasken amma kuma yabaci mana.

>  Hahahahahahahahahahhahahahahahahhahahahahahahahahahahahahahahahahahhahahahahahahahahahahahahahahahahahahahahhah, Karamar magana kenan, Kunsan wanan hasken zai zamar muku matsala nan da mako uku.

Sarki Tukur ne yace:

>  Aljana Jumana nawa zamu bada asa bakaken Aljanu sukawo manasu.

>  Wanan aikin bana bakaken Aljanu bane nakume, domin kuma bakaken Aljanu ne suka saku.

 Yanzu mene abunyi?.

Wata shegiyar dariya mai tsayi Aljana Jumana takara saki sanan tace:

>  Ko ku kawo su, ko kuma matslal ku tafara.

Daga haka Aljana jumana ta bace bat, Kallon juja sukayi Gimbiya Zulfa tace:

 Kaine Sarkin Zarwata kuma Zarwata babbar Masarauta ce a dulhaniya kuma dole yaran nan suna Dulhania, dan haka kayi amfani da karfin ka akawo maka su.


 Amma wanan abun namu ne duka, dole mu dawo dasu Zarwata sanan mukawo su.

Daganan suka dawo Masarauta Zarwata.




Muje zuwa&
_Daga alkalamin Saiyyid writer_


=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*


Page (23&24)




Gaba daya mutanen Gari Sarki Tukur yatara, hakama Gimbiya Zulfa duk wasu mata dake cikim masarautar Zarwata:

 Kunsan Sara kunsan Jidda sun bace daga Masarauta gabaki daya, dan haka masarauta ta badan umarnin nemo su ga kowa wanan aiki na Msarauta sanan Hadiman bangaren Gimbiya Sadiya duk akamesu a kullesu har sai sun bayyana inda suke.

Daga haka zama ya tashi, sanan mai marataba ya aika da sako ko wanne gari dake karkashin zarwata harda masarautu.

A bangaren Aliyu kam bayan rabuwarsa dasu Sarah kai tsaye karamin kauyensu ya nufa, Zuciyarshi cike da bage da kuma kaunar Sarah.

Yaso sun samu zamu domin ya bayyana musu a kidarshi da addininshi, domin yayi musu fatan samu rahamar ubangiji.

Sai da ya tsaya wani karamin kauye, yasamu rawani yanade fuskarsa sanan yasamu bakin tabo ya shafa a fuskar tashi yanda zata rage haske.

Tafiyar kwana biyu ce ta sadashi da garinsu, da matukar mamaki daukakim mutane kauyen ke kallonshi kasamcewar kauyen bawnai babba bane kuka ba tarin mutane bane a ciki, hakan yasa kowa yasan kowa sanan duk wani abu idan yafaru kowa ya kansani.

To kamar dai haka kowa yasan Aliyu ya tafi wajen iyayenshi, binshi suke da kallo har ya ida fadar sarkin su.

Bayan kai gaisuwa sarkin ya kalli Aliyu sanan yace:

 Malam Aliyu mai yadawo dakai wanan kauyen.

Gyara zama Aliyu yayi sanan yace:

 Allah ya taimake ka a tafiya ta naga rayuwa, naga abubunwan rayuwa masu ban mamaki da kuma Al ajabi.

 Kamar me dame kenan Aliyu?.

Sarkin ya tambaya, nan Aliyu ya bude baki yafara bada labari tun daga zuwan sa Masarautar su Mahaifinsa sa kuma Sarkin Kumbu da yaturo a tafe dashi da kuma kashe Antynsa Gimbiya Junaidiya har da haduwa da Sarah da Jidda, Sai dai ya boye gaskiyyar cewar yakamu da son Sarah.

Shiru Sarkin yayi sai da yakwashi yan mintina sanan yace:

 Lallai ne Aliyu kaga rayuwa, sanan wayanan yan mata da kagani guda biyu sune wayanda Sarki Tukur ke nema ruwa Ajallo, kuma kashe su yakeson yi.

Shiru Aliyu yayi yana tuanin Sarah da Jidda, daga nan Aka sallami Aliyu.

Kai tsaye Aliyu wajen babban Malamin Addini na garin nasu yaje tare da bashi labarin sanan yadora da cewa:

 Malam ko akwai hanya da xan iya taimaka musu dan Allah.

 Tabbas Aliyu akwai Hanya,akwia hanyar da zaka iya taimaka musu, itace kashiga Dakin ibada, ka ke bance kanka a wajen guda kayi tafaman bautar Allah da kuma addu oeh.

 Shikenan Malam nagide kuma zanyi.

Daga haka Aliyu ya nifi gida wajen Giggo wacce tarikeshi tun lokacin da aka tsince shi.

Dattijuwar matar na zaune gidan murhu tana faman hura huta taji sallama, da sauri tajuyo tana fadin:

 Wanake ji kaman Zaki.

 Nine Gaggo.

Da sauri matar ta tashi ta tawo inda yake tana rungumeshi, bayan ya zauna yaci Abinci yabawa Goggo labarin duk Abunda yafaru tare da sanar da ita abinda malam yace:

Goggo taba shi kwarin gwiwa sosai da sosai, hakan yasa yahada yanashi yanashi ya shige wani daki dake gidan goggo wanda yake a rufe tunda dadewa, kasancewar mai gidan Allah yayi mai rasuwa.


*Kasar jinnu*

Wasu irin kaya akabawa Sarah da Jidda suka saka sanan aka shiga koyarda su Babban tsafi, wanda tsafin yake mataki uku.

Mataki na farko shine: wanda ?ananan aljanu zasu koyar dasu.

Aljanun yan yara ne wanda a zahiri basufi yara ?an shekara biyar zuwa bakwai ba, amma su awajensu yara ne yan shekara duba Waya da Wari biyar zuwa dubu biyu.


Zaunar dasu sukayi a tsakiyar wata Sakar bukka mara rufi, daga tsakiya wata tukunya ce mai Wauke da shuWiyar toka, yaransu biyar ne ke xagaye da Sarah da jidda dake zaune Waya daga cikik yarance tacee:


>  Aeyo ba arisiwen okoba.

Nan da man yanayin wajen yacanja saman tafara fitar da wani koren hayaki, gurin yafara juyawa kansu sara, wacce tayi maganarce ta Waga hannu aikuwa tuni Sarah da Jidda sukayi sama, sai tayi gefe da hannun tunu suma sukayi gefe, tayi watsi da hanun suma sukayi gefe sana suka faWi a ?asa.


Jidda ce tace:

 Munuba yazaki yarda mu.

Dariyar Munuba tayi sanan tace:

 idan kun ?ware ku rama.


Dawowa sukayi suka zauna jidda tabude baki tafara magana:

>  Aeyo ba arisiwen okoba.

Shiru waje bai canja ba, babu abunda yafaru ?ara mai maitawa tayi

>  Aeyo ba arisiwen okoba.

Daya daga cikin Aljanun ce tace:

 Kunsha abunda Dallatu shugabanmu yabaku ko?.

 Munsha Jidda tafaWa.

 To ku tsayarda zuciyar ku waje Waya, ku da hankalinku akam tunaninku, ku& 

Bata ?arasa ba sukaji muryar Sarah tafara:

>  Aeyo ba arisiwen okoba.

Tuni iskar wajem tafara canjawa, koren haya?i yafara tashi,sama tayi da hannunta aikuwa duk sukayi sama harda jidda, gefe tayi da hannun amma aljana munuba ta ri?e hannun da nata tsafin, ?o?arin kwacewa Sarah take Aljana munuba tacee:

>  Ai b aiya Wagawar ba, akwai faWa asama.

Sauke jidda ?asa Sarah tayi tare da cewa:

 Dalla gwada ki hawo.

Rufe ido Jidda tayi tare da dai dai ta numfashinta

>  Aeyo ba arisiwen okoba.

Tuni itama tayo saman, a lokacin kuma Aljana Kalmasa tace:

>  Aei bobo ekow.

Tuni Sarah da jidda suka farawa rawa a sama kamar zasu faWo ?asa.

 Zamu faWi fa.

Jidda tafaWa, dariya suka kwashe da ita sanan Aljana Kalmasa tace:

 ai faduwarku na hannuna.

Haka taita hujjijagasu har sai da hanjin cikin su yakada amma Sarah da jidda sun kasa maimaita abinda tafada, haka suka yini a azabce.


*Zarwata*

Sarki Tukur da Gimbiya zulfa sun rikeci sun rasa nutsuwarsu neman Sara da Jidda ya hanasu zaman lafiya, gaba daya masarautar zarwata da makotanta sun rikice, gida gida ake bi neman su Sarah.

Gashi Aljana jumana har Cikin masarauta tazo jiya ta sanar musu da sakon tashin hankali daga jejin haske, domin suma jejin hasken babu kwanciyar hankali a tare dasu domin ya tabbata Sarah ce zata kawo karshen tsafinsu.


Gimbiya Zulfa na zaune a dakinta gaba daya tayi baki ta rame ta kuma fita hayyacinta, babu wanan kwalliye kwalliyen ba kayan sarauta.

Yaranta Labiba da Lubaba ne suka shigo cikin dakin suna hira suna dariya, kallonsu tayi a ranta tace:

 Bakusan damuwar dake damuna ba, bakusan cewar duk abinda yabaci kuma zai bata goben ku domin ku din ba yayan madaki bane yayan kanine.

 Momy wai lafiya kike kuwa?.

Labiba tafada tana zama, lubaba ce tace:

 Ta ina take lafiya bayan ta yarda hankalinta tasaka damuwar yaran nan.

 Ku tashi kifita.

Gimbiya zulfa tafada a tsawace, tashi sukayi suka fice suka barta da tarin damuwa.

Fadar sarki Tukur

 Yazaayi ace yara guda biyu sun gagareni, sungagari karfin masarauta ta bazau faru ba.

Sarki Tukur yafada

 Ranka yadade yaran nan anduba su ko ina amma ba a samesu ba.

 Banason maganar banza, ku tashi ku shiga nemansu ko ta wani hali.

Tashi sukayi suka fice shikam ya shiga faman tunani.


Muje zuwa&
_Daga alkalamin Saiyyid writer_


=?Q?=???*KADDARAR SARAUTA*=???=?Q?
*Jinin wanda aka zalunta baya shudewa*

*Written by
'?=???*
SANI MUHAMMAD LAWAN
(Saiyyid Writer)
*_Garkuwar taurari_*


Page (25&26)


*Jejin haske*

Babban Aljani mai shudiyar fuska ya gano cewa nan da kwana biyar za azo a farmakesu farmakar da zata iya zama ajalinsu da kuma karshen jejin haske.

Gabaki dayan Aljanun jejin ne zaune cikin fadar zamansu, babban nasu mai shekara dubu dari tara ne yafara magana:

>  Jejin haske na shirin tarwatsewa Aljannu Kasar jinnu na shiri kuma mai dauke da fansa, kuma dukan mu nan musan yanda yakin fansa ke da karfi

Hayaniyace tafara rashi tsakanin kananan Aljannu da manya wasu nafadin  Mu guduwa zamuyi wasu kuma na cewa  wayakisu taba jinin fansa

>  Ku dakata.

Babban Aljanin yafada, shiru sukayi gaba dayansu sanan yafara magana:

>  Masu zama su fara shiri masu tafiya su tafi.

Cikin kankanin lokaci Wasu Aljanun suka fara bacewa amma wasu kuma basu bace ba, sai kuma wasu dasuka bayayyana yanzu a wajen, wayanda aka gayyato daga wani jejij Aljanun.

Nan suka fara shiri domin tarar babban yaki.


*KASAR JINNU*

A kwana biyu Sarah suka kware a wajen koyan fada na kanann Aljannu, yanzu kuma suna Mataki na biyu tare da Aljannu yan shekara dubu goma zuwa dubu sha biyar, su kam suna koya musu yadda ake fada a sama ne tare da wasu maganganun tsafi wanda zaka sarrafa mutum da tsafi a sararin samaniya.

Kwana biyu suka gangara matsayi na uku wajen Dattijan Aljanu su kuma suna koya musu Kare kai A cikin kwana biyar Sarah da jidda su kware A fadan tsafi kamar basu ba, suna iya tafiya a sama haka zasuyi tafada a sama tsakanin ta da Jiddah.

A bangaren Zarwata kam Haka kwanaki suka shude Zarwata babu zaman lafiya,Aljana jumana tazo daren jiya ta sanar dasu za ayi ga garumim fada tsakanin su Da Aljanu Kasar Jinnu idan sunyi nasara to masarautar su tayi nasara idan suka fadi masarautarsu tafadi

A daya bangaren Masarautar Kumbu kam Sarki Lahab na zaune Aljana Jumana ta bayyana a gabanshi, a kidime ta yatashi yana fadin:

 Aljana Jumana lafiya?.

Wata muguwar dariya Aljana Jumana tasaki sanan tace:

>  A daren yau za afafata tsakanin Aljanun jejin haske da Aljanun Kasar Jinnu, kasani idan munyi nasara Masarautar katayi, idan bamuyi ba masarautar ka batayi ba, yaron yar uwarka zaizo ya mulki kasar nan kuma da ranka.

Daga haka Aljana Jumana ta baci, tabar Sarki Lahad ba tashin Hankali


Chapter 4: Fadan Aljanun tsafi

FA?AR ALJANUN JEJIN HASKE DA KASAR JINNU

Jejin haske sun shirya komai da komai nasu, yana tsare domin sune za a kawowa farmaki amma dayake suna da wayo sai suka riga Aljanun Kasar jinnu isa babban filin yakin


Dare ne ya gauraye wajen kuma yana cike da duhu mai tsanani Iskar daji ta kadawa da sauri da sauri tana fitar da wani irin zafi tana Wauke da ?arar ihu daga can cikin jeji.

Tsuntsayen dare sun yi shiru, kamar su ma sun ji tsoron abin da ke shirin faruwa.

A cikin wani fili mai yalwa da duwatsu da kuma bakin haske mai shudi.

Aljanun Jejin Haske suka fito da ?arfi, bayan sun canja hallitar su zuwa halittu masu siffar mutane amma jikinsu yana wal?iya kamar wutar lantarki, idanunsu na haskawa da shuWi. Suna Wauke da makaman haske  kibiyoyi da takubba masu wal?iya.

Isar su wajen?asa ta Wauki rawar jiki saboda ?arfin ikon da ke tattare da su.

A can gefe kuwa Aljanun Kasar Jinnu ne suka fito daga cikin duhun ?asa. Su ba su da haske, jikinsu ya yi ?yalli da ba?in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login