Showing 1 words to 3000 words out of 21511 words

Chapter 1 - KARIN KUNAMA Book 1 free pages by Ameera Adam.docx

17 Oct 2025

219

[10/2, 5:09 PM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA

©Mai ƙosai

Daga Marubuciyar:



•Hafsatul-kiram #700

•Ƙaddarata ce a haka #400

•Ƙayar ajali #400

•Zahra #800

•Da mun bijire #700

•Matar Mamman #300

•Wani yanayi #300

•A dalikin son zuciya #500

•Budurwar wawa #500

DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA DA JIN ƘAI.

TSOKACI

A cikin wannan labari akwai ɓangarorin da aka assasa labari akansu wanda a cikinsu ne za a ƙulla zaren labarin kuma za a warware komai na cikin labarin, ina fata zaku biyo ni sannu a hankali domin jin yadda labarin zai kasance,acikin labarin muna da ɓangaren ZAHIDA da AHMAD sai ɓangaren BASH da YASIRA, sai AYLA da NAZEER sai kuma WAHIDA da TAJUDDEN(TAJ)

Wannan littafin kacokam sadaukarwa ne ga duk wata matar aure, Allah Ya saka mata ɗawainiyar da take yi cikin gidanta da ɗumbin alkhairi.

Ban yarda, kuma ban lamunce a juya min littafi ta kowace siga, yin haka ya saɓa da doka, a kiyaye.

_Littafin kud'i ne, za ki iya biyan #700 8160675983 opay Maryam Abdulaziz_

BABI NA FARKO

AYLA

Kwance take bararraje kan makeken gadon da ya ji kayan shirgi da tarkacen da basu da daɗin kallo, tayi ɗai-ɗai da ita, ƙafarta ta hagu ɗage tana ɗan lilo ɗayar kuma ta miƙar da ita, hannunta riƙe da waya fuskarta ɗauke da wani tsadadden murmushi, kafin ta kece da dariya tana sake ƙarewa sikirin ɗin wayar tata kallo.

Idan ka duba gefe da gefen ɗakin da kuma farfajiyar wajen babu komai sai tsummokara da kwalin biskit da na lemoka da aka yar a wajen, ba zaka taɓa ɗauka ɗaki ne da ake kwana a cikinsa ba, balle ka zata mutum sukutum zai iya zama ciki ma har ya yi doguwar sabga. Sai dai ga Ayla nan kwance kan hargitsattsan gadonta tana charting abin ta hankali kwanci babu abin da ke ƙwarzanar ranta.

Wata dariyar ta sake kecewa da ita tana miƙewa zaune kana ta kai yatsanta babba ta ja wajen da ake yin voice message sama ta soma magana,

"Ai wallahi da man ke Ziza shashasha ce fa an faɗa miki ana rangwantawa namiji ne, ke baki san salon shaiɗancinsu ba ne da har za ki dinga ɗaga musu ƙafa, kin ganni nan wallahi ƙaryar Nazeer ya ce zai dubi cikin idona ya ce mini kanzil idan nayi masa wani abun, ke ni fa sai abin da na gindaya a gidana ake bi, wallahi idan na ce ya tsugunna yayi min sujjada yi zai yi caab an faɗa miki namiji ɗan goyo ne ai wallahi gwara ki taka kansa dan shi idan ya samu dama ba kai kaɗai zai taka miki ba har da gangar jikinki."

Tana kammalawa ta tura tana fita daga gurof ɗin nasu na 'yan makarantarsu ne da suka kammala a shekarar da ta wuce, sai dai basu fi su goma ba, sun ware kansu suna jin su ɗin manyan kai ne.

Shiga tayi wani gurop da shi ma ake magantuwa sosai musamman akan abin da ya shafi zamantakewa ta aure, wasu su yabi mazajensu wasu kuma ka ji suna kwashe musu albarka.

karaf idanuwanta suka gano mata saƙon wata Fa'iza da take yawan yabon mijinta take kuma ja da maganganunsu akan kushe maza da suke yi, da kuma ba su shawarwari, yanzuma magana tayi akan maganar wata da take cewa,

_Kai mutanen gidan nan ashe da man haka ɗanyen kan maza yake, wai ni baban walid zai yiwa tijara saboda kawai na siyo awara da canjin kuɗin wanki da ya bani jiya aka kawo?_

Nan fa aka shiga tofa albarkacin baki, wasu na zugata suna nuna mata kaɗan daga aikin maza ke nan, shi yasa gwara ka taka kansu kaima ko a zauna lafiya, har wata na cewa,

_Ka ji fa matsiyaci, yanzu shi akan canjin kuɗi yake zaginki saboda tijararre ne, me aka yi akayi canji, mits ni wallahi kinga baban shahid ko canjin me zan ci baya cewa komai, ke hasalima da kansa yake cewa riƙe._

Yayin da wata ta ce,

_Ƙyalesu ai 'yan balaj'u ne sai kana nuna musu daidai kake da su._

Komawa tayi kan rubutun Fa'izan tana karantawa,

_Haba maman walid bai kamata ki zage shi ba idan baki yaba masa ba, wallahi ku muji tsoron Allah ku dinga duba yadda suke ɗawainiya da mu, su fita nema mana abin da zasu kula damu, baku san wahalar da suke sha ba, don Allah ku daina haka, baki san dalilinsa na yi miki faɗan kashe canjin ba, hasalima ke ce baki da gaskiya fa dan me za ki kashe baki mayar masa ba, da kin mayar kinga idan ya ce ki riƙe shi kenan, amma fa haƙƙinsa ne ba naki ba bai kamata ki ci ba._

Tsaki taja kafin taja saƙon ta soma yin reply akai.

"Mits! Ji wani zance maras tushe don Allah kema dai maman jawad, wai baki san halin su ba ne da kike wannan maganar, wataƙila ma tasa ce ta ciyosa yazo zai sauke mata tijararsa haka kawai ita bata kar zomon ba zai bata rataya, wallahi karki yarda maman walid idan ya yi miki kan kara ki yi masa na itace. Yo wace wahala suke sha, suna zaune a office sanyin AC na kaɗasu, idan ɗan kasuwa ne ma yana shago yaransa suke wahala, idan lokacin cin abinci yayi yaci abincinsa lafiyayye wataƙila ma ya barta da tunanin yadda zata ci na rana, ke ni fa babu wata maganar tausayawa maza wallahi, ai dole ne su fita su nemo ma ai sun san da haka suka yi auren."

ZAHIDA

Tun da aka yi kiran sallar asuba bata sake runtsawa ba, azaba da raɗaɗin da idanuwanta ke yi na rashin samun wadataccen bacci bai sa taji tana son sake komawa ta kwanta ba, a hankali ta naɗe sallayar da take kai wacce ta yi sallar asuba akanta ta bita da nafila raka'a biyu domin neman kusanci da mahaliccinta da kuma miƙa ƙoƙon bararta wajenSa domin neman sassauci daga raɗaɗin da take ji a kowace kafa ta jikinta ta mayar da ita ma'ajiyarta.

A hankali ta soma takawa ta fice daga ɗakin zuwa tsakar gidan, kurfoti ta soma gyarawa zamansa ta soma kiciniyar ɗiban gawayi tana zubawa akai a ƙoƙarinta na haɗa wuta, kasancewar babu kalanzir yasa ta shiga yin 'yan dabarunta na kunna wutar, sai dai ta ɗan jima kafin wutar ta kama, sanda wutar ke ci ta sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciya tana miƙewa kana ta nufi kicin domin ɗauko tukunya.

Duk wannan kacaniyar da kwarafniyar da take yi mijinta Ahmad na kwance kashirɓan yana sauke numfashi ɗai-ɗai da ɗai-ɗai. Sai da ta ɗora ruwan shayi har ya fara zafi sannan ta jiyo tashin Ahmad ɗin, tana jin motsinsa ya tura ƙofar banɗaki ya shiga wanda hakan ke alamta mata zai yi alwala ne ya gabatar da sallar asuba, agogon dake manne a jikin bangon falonta ta zubawa ido tana ƙare masa kallo, kamar wacce ke son gano wani aibu nasa. Ƙyam ta tsayar da idanunta sosai akansa har Ahmad ya fito daga banɗaki ya janyo darduma ya shimfiɗa yana tayar da sallah, sai a lokacin ta kawar da idanuwanta daga kan agogon tana sauke ajjiyar zuciya, ta sake jinjina ƙarfin hali irin na Ahmad, shida ce har da motsi sannan yake gabatar da sallar asuba, a hakanma a cikin gida ba masallaci ba, ko da yake idan da sabo yaci ace ta saba saboda ba yau ne farau ba, sai dai duk sanda take kallonsa cikin wannan yanayi takanyi masa fatan ya zama na ƙarshe, takan yi masa fatan shiriya da dawowa hanya madaidaiciya. Tana cikin wannan tunanin taji sallamewarsa, har ya yi salla raka'a biyu cikin abin da bai fi mintuna uku zuwa ƙasa da haka ba, koda ya idar sallayar ya janye ya naɗe ya wurgata mazauninta, babu batun addu'a ya miƙe yana miƙa tare da hamma, sai sannan yakai kallonsa kanta yana yamutsa fuska.

"Ba ki gama abin karin ba ne?"

Ya jefa mata maganar yana komawa kan kujera ya zauna shagwab kamar an jibge kayan wanki.

"Shayin ne akai"

Ta ba shi amsa, tana wasa da yatsun hannuta. Wani wawan tsaki yaja yana ƙanƙance idanuwansa cikin tsagwaron masifa ya ce,

"Yanzu idan banda ke wawiya Zahida ace ki kasa kammala abincin sallamar maigida da wuri, kuma tun jiya nake faɗa miki da wurwuri zan fita amma da yake kwanyartaki bata ja kika kasa gane haka ko? To yanzu sai ki faɗa min yaya zanyi eh?" ya ƙare yana jefa mata kallo da shanyayyun idanuwansa da suka ƙanƙance saboda tijara.

"Ka yi haƙuri ba mantawa nayi ba, gawayin ne wallahi da ƙyar ya kama, kasan damina ta shigo ko yaya ruwa ya dake shi sai ya jiƙe ya yi ta wahalar kamawa, kuma yanzuma shayin na san zai tafasa, bari na haɗa maka ruwan wanka sai ka fara yi kafin na soya dankalin."

"Mits! Bar kayanki." ya ce yana miƙewa daga zaunen da yake, ya nufi cikin ɗakin. Bai fi mintuna goma ba ya fito sanye da shadda ruwan toka, sai hula baƙa ya yi kyau sosai domin Ahmad namiji ne da Allah ya horewa zallar kyau, duk da ba zaka saka shi acikin jerin fararen fata ba amma kuma kaitsaye ba zaka kira shi da baƙar fata ba, saboda yana da fata mai wata kalar kyau. Ko kallon inda take bai yi ba ya saka kai zai fice daga ɗakin.

"Don Allah ka tsaya ka karya ka ji" Zahida tayi maganar cikin roƙo, saboda tasan idan har bai ci ba ya fitan akwai matsala, shirun nasa tana da tabbaci ba alkhairi ne a gareta ba.

"Sai ki janyo ne ki zaunar da ni ai." ya ce yana saka kai gabaɗaya ya fice daga falon, har ta yunƙura zata bi bayansa sai ta ga ya dawo falon yana kallon fuskarta.

"Ban yarda ki dafa komai ba, ki sha shayin har rana wallahi idan kika taɓa min kayan abinci sai na nakaɗa miki na jaki, wawiya kawai." yana gama maganar ya fice, shagwab ta koma ta zauna tana sauke numfashi, wasu siraran hawaye ta ji na zubo mata, me yasa duk wannan ke faruwa? Wane laifi ta aikata masa haka da ta canci wannan hukuncin daga wajensa? Da hanzari ta miƙe ta fice daga falon, zuwa wajen shayin don tana da tabbaci yanzu ya tafasa, aikuwa tana zuwa ta iske sai tafarfasa yake yi, ta sauke tana ƙoƙarin ɗora kasko a wuta domin ta soya dakalin aka yi sallama, bata kai ga amsawa ba aka faɗo cikin gidan ganin wacce ta shigo yasa gabanta yankewa ya faɗi, wata fargaba da tsoro suka soma ratsa gaɓoɓinta.

YASIRA

"Bash, my bash haba ka tashi mana" Yasira ke maganar cikin kunnen Bash, tana kamo haɓarsa.

Yamutsa fuska ya shiga yi irin ta waɗanda aka hana bacci ko ake son tashinsu ta ƙarfin tsiya.

"Haba mana" ya ce yana sake yamutsa fuskar tasa.

"Ga fa breakfast naka can yana jiranka so kake sai ya huce, kasan fa baka cin abinci da sanyi don Allah ka tashi."

"Ki rabu da ni beb ban ƙoshi da baccin ba." ya yi maganar yana cakumo bargon da ta yaye masa yana rufe kansa. Aikuwa ta sake kai hannu ta finciko bargon tana kai masa cakulkuli, babu shiri ya miƙe zaune yana kai hannu cikin sumar kansa yana yamutsa ta.

"Allah sai ka tashi fa, ka sakko ka yi brush kazo kayi breakfast." ta sake faɗi sai dai a wannan karon sauka tayi daga kan gadon tana barin ɗakin.

Tana fita ya koma yaja bargon, jiyo maganarta ya saka shi miƙewa da sauri ya yaye bargon gabaɗaya daga jikinsa ya ziro santala-santalan kyawawan ƙafafunsa ya soma tattakawa yana shigewa toilet.

Sai da ya kwashe a ƙalla mintuna ashirin sannan ya fito, kaitsaye dinning area ya nufa, tana zaune tana shan lemo har ya ƙaraso bata kalli sashen da yake ba, ganin haka yasa shi murmusawa yana zagayawa daidai saitin fuskarta, ba ta ɗago ta kalle shi ba hasalima sai kawar da kanta gefe tayi, sai kawai ya zagayo ta bayanta ya rungumota yana kwantar da kansa saman gadon bayanta.

"Sorry gimbiya" ya ce a hankali cikin kunnuwanta yana kaiwa fatar kunnenta cizo.

"Auch!" ta ce da ɗan ƙarfi, kafin ta sake furta,

"Allah ka cire min kunne sai an yanko naka an saka min dan ba zan lamunta ba."

"Shi ke nan shi yafi komai sauƙi ai." Bash ya bata amsa yana sake murmusawa.

"Oya sit and eat" ta faɗa tana ja masa kujera bayan ta miƙe tsaye, zama ya yi yana daidaita zaman nasa tare da ɗaukar shayin da ta haɗa masa ya soma kurɓa.

"Don Allah ki kurɓi shayin nan beb ki ji wallahi salam yadda kika san ba a halicci sugar a cikinsa ba."

Harara ta wurga masa tana faɗin,

"Babu wani shayi da zan kurɓa, kuma haka zaka sha shi koma mene ne."

"Don Allah!" ya faɗa yana marairaice fuska.

"Ni fa ba zan sha shayi ba, kasan dai ba na sha haka kawai idan zaka sha ka sha malam babu wani sugar da zan yarda ka ƙara."

Tabbas ba ta shan shayi, ko mai kuwa zaka saka a cikinsa, duk daɗinsa kallo ma bai isheta ba, tafi ganewa kunu shi ma wani lokacin sai idan na gyaɗa ne ko kuma ta sha lemo amma shayin kam sun yi hannun riga da shi. Ya kuma san ba zata ɗanɗana ba tunda ba shan take yi ba, yana da tabbaci ba za ta ƙara masa sikarin ba. Sai kawai ya saki ƙayataccen murmushi yana sake girmama ƙauna, soyayya da karamcin da Yasira ke yi masa, ba zai ce auren so suka yi ba, domin aurensu aure ne da aka haɗasu ba tare da kowannensu na son juna ba, sai dai a zaman da suka yi farkon shekararsu ta aure bayan sun rufa watannin aurensu wata biyar zuwa bakwai sun so junansu suna jin ma kamar da man can ba haɗasu akayi ba, suna yi wa junansu wani irin so da ƙauna, har zuwa yanzu da suke da shekaru hud'u cikin ta biyar da aure, matsalarsa ɗaya da Yasira shi ne kishinsa da take yi na a mutu, muddin za ta ganshi ko ta ji shi da mace to ranar ba zasu yi kwanan farinciki ba, wannan yasa yake kaucewa duk wata alaƙa da zata haɗa shi da mace, duk da shi mutum ne mai burin auren mace fiye da ɗaya, ba wai don ɗayar ba zata gamsar da shi ba sai dai kawai yana jin cewa hakan na cikin ƙaddararsa ne da alƙamin ƙaddarar tasa ya rubuta masa. Uwa uba a yanzu yana jin wannan burin nasa na sake tumbatsuwa saboda yadda yake so ya ga ya tara iyalai, mutum ne shi mai son yara sosai da sosai, ga shi har yanzu Yasira Allah bai kawo ba, ba kuma wai dan akwai wata matsala ba ce a'a, sun je asibitoci da dama an gwadasu duka su biyun kuma an tabbatar musu da komai lafiya kawai lokaci ne idan yazo za su haihu, abin bai dame shi ba sosai, amma a yanzu yana jin son yaran na sake ƙaruwa cikin zuciyarsa, ƙarin daɗawa ma; ko hajjo(mahaifiyarsa) na son ganin jikokinta daga tsatsonsa ba ta da wani zance sai ina son ganin ɗanka ko 'yarka Bashir, Allah ya nuna min wannan lokacin. Wannan magana tata ita ke sake jin cewar ya ƙara auren, wataƙila ya zama sanadin samun zuri'arsa da Yasira, tun da akan ce wai idan matarka ba ta haihuwa idan aka yo wani auren akan yi dace ita ma sai ta samu.

"Bash!!!" muryar Yasira ta tsamo shi daga duniyar da ya tafi, kallonta ya yi yana murmusawa ba tare da ya ce mata komai ba.

"Wai fushi ka yi?" ta sake magana sai dai wannan karon cikin sigar tambaya.

"A'a ni na isa." ya ce yana ɗan darawa.

"Har ka yi yawa ma."

Ba ta jira amsarsa ba ta ɗora da,

"Ka yi haƙuri kasan fa an hanaka shan zaƙi sosai, idan ban kiyaye lafiyarka ba tawa kake so naje na kare, ni da nake so na ƙare rayuwata da kai gaba ɗaya."

"Shi kenan, ki karya ina so na fita da wuri, kin san kuma ba zan iya fita ba baki karya ba."

Sai kawai ta saki murmushi tana kamo hannunsa tare da kai masa sumba.

Sun ɗan jima kafin su kammala karyawa, ita ta shirya shi ya fito fess, har bakin mota ta raka shi tana sake jaddada masa ban da kula wata mace, ko magana tayi masa ban da ba ta amsa. Shi dariya ma ta ba shi amma sai ya gimtse dariyarsa gudun karya b'allo ruwa, da ƙyar ta sake shi ya fita daga gidan tana ɗaga masa hannu.

Ba zan koɗa muku labarin ba sabida karku ce na so kaina da yawa, amma dai daga jin tafiyar kun san dai ba banza ba. Labarin sabon salo ne kuma sabon kafce daga alƙalmin Mai ƙosai,ku ci gaba da kasancewa da ni domin jin yadda labarin zai kasance.

Mai ƙosai.

08160675983

[10/2, 5:17 PM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA

©Mai ƙosai

Daga Marubuciyar:

•Hafsatul-kiram

• Ƙaddarata ce a haka

•Ƙayar ajali

•Zahra

•Da mun Bijire

•Matar Mamman

•Wani yanayi

•A dalilin son zuciya

•Budurwar wawa

_Ban amince a juya mini littafi ta kowace siga, yin haka ya Saba doka, a kiyaye._

BABI NA BIYU

Ina neman afuwarku bi sa rashin jina jiya, hakan ya samo asali ne saboda rashin lafiyar da ƙanwata ke yi wacce ke kwance a gadon asibiti, muna barar addu'arku don

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login