Showing 3001 words to 6000 words out of 21511 words

Chapter 2 - KARIN KUNAMA Book 1 free pages by Ameera Adam.docx

17 Oct 2025

1030

Allah, Allah Ya tashi kafaɗunta, na gode.

ZAHIDA

Kallon fuskar matashiyar budurwar da ta shigo take yi gabanta na ci gaba da dakan lugude. Cike da ƙarfin hali ta iya furta mata,

"Ki ƙaraso mana Haulat"

Harara ta watsa mata, ba tare da ta furta mata komai ba ta wuce cikin ɗaki kaitsaye, tana ganin shigewarta ta sauke wata ɓoyayyiyar ajjiyar zuciya tana fata ace Haulat ɗin ta gama abin da zata yi har ta fice daga gidan wani abu bai haɗa su ba. Ba ita tabi takan Haulat ba ta koma inda take girkinta ta ɗora kasko ta zuba mai ta yanka albasa, bayan ya yi zafi ta zuba dankalin turawan da ta feraye shi ta tsaftace shi domin ta soya.

Haulat kuwa na shiga ɗakin ta ajjiye ledar da ta shigo da ita, ta cire hijabin jikinta ta kwanta kan kujera, zumbur kuma sai ta miƙe ta shige ɗakin gado wato bedroom tana yatsina fuska haɗi da taɓe baki. Sai da ta gama kalle-kallenta kana ta fito tana sake yatsina fuska ta ƙara komawa ta zauna kan kujerar ta janyo jakarta 'yar ƙarama ta zuge zip ɗin ta shiga zaro wayarta, lambobin sirrin dake kan wayar ta cire ta soma kiran wata lamba. Ringin biyu aka ɗaga a hankali ta soma magana kamar wacca aka yi wa dole.

"Kin ga Aziza ba zan samu shigowa ba ina gidan yaya ma yanzu haka."

Ta ɗan yi shiru tana sauraren ɗayen b'angaren kafin ta sake furta,

"Eh ya yi tafiya ne tun jiya, da man ya kirani ya ce inzo in zauna masa a gida in saka masa ido saboda mai ɗan halin ɓera, kin san abinka da babu a gida sai kiga ana ɗauka ana kaiwa tsofaffi."

Waɗannan kalaman nata sunyi daidai da shigowar zahida ɗakin da ta kammala soya dankalinta shigowa da shi acikin wata ƙaramar roba, sai shayin da ta haɗa domin ta samu ta karya dan tun ɗazu cikinta ke kukan yunwa. Jin kalaman haulat da suka ratsa kunnuwanta ya sa ta ji duka gaɓoɓinta sunyi sanyi, kaf cikin kalamanta babu abin da yafi tsaya mata a rai da sukar zuciyarta irin iyayenta da ta ambato, wannan wace iriyar rayuwa ce haka take yi? Ita kuwa idan har haka auren yake tana jin dama bata yi shi ba, shekaru hud'u zuwa ta biyar anata abu ɗaya babu canji, ba ga mijin ba ba ga dangin nasa ba, to gwara-gwara ma mahaifiyarsa tana ɗan sake mata, wani lokacinma ita ke hana shi rawar gaban hantsin da yake taka mata. Ba ta iya ƙarasawa inda za ta je ta zauna ba ta ja sagaggun ƙafafunta ta fice daga falon, tana sake jiyo muryar haulat na sake gargasa mata maganganu kala-kala, sai dai sam hakan baya damunta, baya yi mata ciwo idan ta danganta shi da yadda take jefa iyayenta cikin cin kashin da take yi mata. A haka ta koma kicin ta zauna sai taji ma gabaɗaya abincin ya fice mata sam duk kuwa da yunwar da take sassaƙarta. Ashe tafiya zai yi amma ba ta da ƙimar ya sanar mata, ko da yake ba wannan ne farau ba, amma kuma wannan ɗin yafi mata ciwo saboda yadda ya turo haulat wai tazo ta saka mata ido taga abin da take aikatawa. Wasu hawaye ne masu zafi suka shiga kwaranyo mata, tana jin duk duniya babu wanda ya kaita muzanta.

AYLA

Ba ta tashi daga kan gadon ba sai wajen karfe ɗaya da kwata na rana, sannan ta kashe datar wayarta, ta jona wayar a caji ta miƙe ta shiga banɗaki, ta kuskuro baki ta fito falo. Zama tayi tana jan tsaki kafin ta miƙe ta shige kicin tana mita.

"Allah wadaran naka ya lalace wallahi, ace mutum ba zai iya karyawa da kyakkyawan haɗi ba, yanzu don Allah ba kamata ya yi ace zan karya da soyayyen dankalin turawa da wainar ƙwai ba sai kakkauran haɗin ruwan shayi amma wai kunu da dankalin hausa" Mits ta ja wani ƙaton tsaki tana dungure jug ɗin kunun .

"Ga dai gida iya gida, amma dai talauci ya yi masa sallama ya hana mutum kataɓus aikin banza aikin wofi." ta sake furtawa tana sangamo flask ɗin da dankalin hausan ke ciki tayo waje.

Falo ta dawo ta zauna ta soma ci ke nan ta jiyo ƙarar wayarta da hanzari ta ajjiye dankalin da take ƙoƙarin turawa bakinta ta miƙe da sauri ta isa wajen wayar, lambar da ta gani a jiki ce ya sa ta saurin haɗiye ɗan guntun dankalin dake bakinta ta sanya hannu ta latsa maɓallin amsa kira ta kara wayar a kunnenta.

"Shegiyar kina duniya da man?" ta yi maganar tana washe baki.

"Ke dai bari wallahi, jiyan nan na dawo kin san na ce miki zan je dubai to ban samu dawowa da wuri ba shi yasa ban neme ki ba to how fa yaya garin da kujiba-kujiba?"

Daga can bangaren aka yi maganar ana sakin murmushi.

'Hmm ka ji fa masu ƙumbar susa aje can a dawo a sake lulawa wata duniyar mu kuwa muna nan muna zaune waje ɗaya kamar shirgin kayan wanki' tayi maganar a zuciyarta, a fili kuwa cewa ta yi,

"Wallahi ke dai bari, gamu muna ta jujjayawa dai, sabgogi sun yi mana yawa, ni ma da yake bana gari shi yasa ban jima da dawowa ba."

"Ayya shi yasa, to ya zancen business kinsan na ce miki bana son wasa a lamarin tunda neman kuɗi kake ai da kuɗi ake neman kuɗin."

"Yana nan ke dai bari, da man ina jira na ji ta ɓangarenki ne."

"Ok babu damuwa, zan bayar da share na miliyan d'aya sai ki bada wanda zaki iya sakawa sai a fara saro kayan akwai shagon da baban Saifu ya bani za a zuba a can sai a saka yaron da zai zauna a ciki, idan yaso duk wata shida sai a dinga raba ribar ko yaya kika ce?"

Sai da ta nisa ta sauke numfashi kaɗan gudun kar ta jiyota kana ta ce,

"Eh hakan ma ya yi, tom zan taɓoki bari ogan ya dawo babu matsala."

"To babu damuwa, amma ina ta so zan shigo gidanki fa sai rowa kike yi min kuma ya kamata dai mu san juna"

Wani ƙuuu taji cikinta ya bayar, da ƙyar ta iya furta,

"Ok za muyi magana, ina so ne oga ya dawo sai ayita ta ƙare ko yaya kika ce?"

"Alright hakan ma is ok, sai na jiki bye."

Ba ta jira amsarta ba ta katse kiran, ita kam Ayla wata iska ta furzar tana samun gefen gado ta zauna jagwab wani tunani na ɗarsar mata cikin zuciyarta, wani sashe kuma na tambayarta ta yadda zata ɓullowa al'amarin karfa taje garin neman gira ta rasa ido, sunan da take son yi ba ta yi ba ta ƙare da jin kunya, koda yake shi ramin ƙarya da man ƙurarre ne amma ba ta so takai wannan gaɓar tana fata ta cinma ƙudirinta kafin komai ya faru.

YASIRA

Tun da bash ya fita ta shiga sake kimtsa gidan, bayan ta kammala komai cike da nutsuwa ta dawo falo ta zauna, wayarta ta ɗauka ta kunna data saƙonni suka shiga shigowa, ba ta fara bibiyar saƙonnin ba sai da ta ga kaf sun shigo sai waɗanda ake aikowa yanzu, group ɗinsu na manyan mata ta shiga ganin message ɗari uku da wani abu, a hankali ta soma bibiyar hirarrakin, wasu ta yi dariya wasu ta danna emoji wasu kuma ta wuce.

Kacokam hankalinta yakai kan wani saƙo da ta ga an tura da ta bibiyi maganar ta ga akan maganar ma ake tattaunawa, murmushi ta yi tana sake karanta saƙon kamar haka;

"Ni nan zan faɗa muku don wallahi ɗari bisa ɗari namiji ba ɗan goyo ba ne, namiji ƙarin kunama ne idan ya harbeki sai ya saka miki gubar da sai ta zama ajalinki, ke idan bai kasheki ba to ya saka miki jinya, ni nan ganau ce ba jiyau ba ƙanwata mijinta iskancin da yake zuba mata wallahi kuka gani sai kun koka mata, amma shegiyar yarinyar nan wai anzo ana son raba auren ta botsare wai ita tana son mijinta a barta da kayanta."

Aikuwa caa aka yiwa saƙon, a hankali kuma ta soma bibiyar raddin da ake mayarwa saƙon.

_"Ka ji shegiya ita ana ga gabas tana sai kudu, sai ka ce jaka ai sai taje idan ya kasheta a ɗakko gawarta."_

_"Wallahi kuwa bari ke dai, ai wallahi ni banga namijin da zai min kan kara ban masa na itace ba, yo jakarsa ce ni, iyayena basu min ba sai kai, in ɗau ɗawainiyarka kuma ka dinga zuba min juji akaina ai kayi kaɗan." _

Maganar da wata tayi ke nan ƙasan wancan comment ɗin.

Haka ta dinga bin comment kala-kala wani tayi dariya wani tayi murmushi fita tayi daga group ɗin tana shiga cikin group ɗinsu na family, message ɗin ta dinga bibiya tana amsa wasu kafin daga bisani ta fita a haka ta cinye lokacin wajen bibiyar message wasu tana amsa musu wasu kuma tana danna musu like, har wajen azahar sannan ta kashe datar ta ajjiye wayar tana nufar kicin.

Kaitsaye abincin rana ta shiga kiciniyar ɗorawa, so take yi ta kammala da wuri kafin Bash ya shigo, dan taga uku saura mintuna goma kuma duk inda uku da rabi take yana gida, ganin wankin hula na neman kaita dare ya sa ta yanke shawarar yin sakwara da miyar ganyen ugun, sai busasshen kifi da zata saka a ciki, nan da nan kuwa ta shiga aikinta bata kammala ba har wajen uku da ashirin da biyar, a gurguje ta faɗa toilet tayo wanka tazo tana shiryawa, tana cikin fesa turare taji buɗe gate ɗin da baba mai gadi ya yi wa bash ya shigo, tana jiyo horn ɗin motarsa wanda hakan na nuna mata alamun ne na ya iso ta fito taryarsa.

Cike da kewarsa ta ƙarasa fesa turaren ta fito fuskarta ɗauke da yalwatacciyar fara'a, babu kunya da jin nauyinsa ta rungumo kayanta ta manna masa kiss a kumatu shi ma taryarta ya yi yana mayar mata da martani, jin junansu suke yi kamar sun shekara ba su haɗu da juna ba, cike da nuna kulawa ta janyo shi suka shigo falon, sai dai kaitsaye ɗaki ta yi masa izini domin ya watsa ruwa, bai musa mata ba domin shi ma hakan yake so. Bai samu kansa ba sai bayan ya kimtsa sannan suka zauna zaman cin abinci cike da so, ƙauna, haɗi da kulawar junansu.

ZAHIDA

Zubar hawayen nata baisa ta ji sassaucin raɗaɗin da ke addabar zuciyarta ba, ji take yi tamkar an ɗora mata bulo akan shimfiɗar ƙirjinta, tana nan zaune har lokacin Haulat ta fito wannan karan ta sauya kaya ta saka riga da wando na kanti, sai hula da ke kanta, sai taunar cingum take yi kana jin tashin sautinsa yana ƙaras-ƙaras. Ko kallonta ba ta yi ba ta miƙe tana bin bango, har ta gota ta dawo da baya ta janyo kicin ɗin ta saƙala masa kwaɗo.

"Kicin ɗin na yayana ne ai ina da right nayi duk abin da nake so dan haka ki buɗe min." Haulat ta yi maganar cikin nuna isa da gadara, banza tayi mata ba ta kulata ba,sai ma shigewarta da tayi ɗaki. Ganin haka yasa Haulat take mata baya, tana yi tana mita.

"Wallahi ki buɗe min ko na kira shi in faɗa masa, idan yaso sai ki ga hukuncin da zai ɗauka."

Nan ma dai Zahida ba ta tanka mata ba, ganin tana ta kumfar baki yasa Haulat ɗin sake faɗin,

"Aikin banza ci ba auki, sai dai a cikawa mutane masai, a ɗabi na banza akai gidan tsofaffafi..."

Ai ba ta gama rufe baki ba taji saukar yatsun Zahida akan kuncinta, wanda ya sababa mata ganin gilmawar wasu ƙananun taurari. Hannu takai ta dafe kuncin ta saki baki galala tana bin ta da ido kafin ta iya furta,

"Ni kika mara? Wallahi ki sani baki mari banza ba, wannan marin sai na rama shi."

"Idan kin gama ramewa ke nan, an faɗa miki ja da baya ga rago tsoro ne, kar kiga kina yi ina shareki ba tsoronki nake ji ba wawiya kawai."

Tana gama furta maganar ta wuce ta koma ɗaki abin ta.

_Wannan littafin na kuɗi ne akan #700,idan ya zama complete 1k_

8160675983

Maryam Abdulaziz

Opay

08160675983

[10/2, 5:25 PM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA

©Mai ƙosai

Daga Marubuciyar:

•Hafsatul kiram

•Ƙaddarata ce a haka

•Ƙayar ajali

•Zahra

•Da mun bijire

•Matar Mamman

•Wani yanayi

•A dalilin son zuciya

•Budurwar wawa

_Ban amince a juya min littafi ta kowace siga ba tare da izinina ba, yin haka ya sa'ba doka, a kiyaye._

BABI NA UKU

AYLA

Tagumi ta zuba a duka kumatunta, tunani ne fal cike a kwanyarta ta yaya zata ɓullowa al'amarin? Ta ina za ta fara da kuɗaɗen da take son kafa kanta, ta san ko giyar wake tasha Nazeer ba zai taɓa ba ta su ba, hasalima ina ya gansu alhalin da, da yanzu ba ɗaya ba, da ace a lokutan baya ne tabbas ba ta da haufi ko nawa ta nema zai bata, to amma fa ita kanta ta sani ban da yanzu da al'amuran suka canza, saboda iftila'in da ya saukarwa dukiyar tasa, wacce har yanzu ga shi nan ko kwatanta bai samu ya mayar ba. Tsaki taja tana dafe goshinta, wata zuciyar na raya mata wani abu da take ganin kamar zai fissheta hanya mai kyau, wani sashen na raya mata karta kuskura sam ta ma ce za ta fara. Da wannan tunanin da taga ba zai amfaneta da komai ba ya sa ta miƙe ta fito falo ta soma safa da marwa kamar wata mai ɗawafi, kayan karin kumallonma gabaɗaya ta watsar da su gefe don tana jin yanzu ba ta da lokacinsu, lokaci ne take da shi na neman mafita saboda so take yi koda tsiya-tsiya ta samu jarin nan ta yi kasuwancin nan saboda ta kece reni ta wuce sa'a.

Ba ta iya taɓuka komai ba, sai tunani da hasashen abin da ba zai amfaneta ba, duk da cewa a wajenta mai amfani ne har lokacin dawowar Nazeer daga kasuwa ya yi.

Tun da ya buɗe gate ɗin gidan da yake madaidaici ya tabbatarwa kansa babu abin da Ayla ta taɓuka, domin kallo ɗaya zaka yiwa tsakar gidan ka tabatar babu shara, da yake gidan gida ne flate irin safecounter ɗin nan wanda da ka buɗe ƙofa ana kallo falon gidan. Ko ina biji-biji tarin shara, ga da ma kwandon sharar ya cika fal yana ta alla-alla yau idan ya dawo ya fitar da ita. Wani kallon takaici yake ƙarewa wajen, da ƙafa yasa ya ture kwanukan wanke-wanken da aka barbajesu ya samu hanyar wuce wa, yana shiga ledar biskit da kayan abincin da ta ajjiye a falon suka yi masa maraba, wani irin ƙamshi ya shaƙa da ba zai ce yaji daɗin shaƙarsa ba, tana kwance saman kujera mai cin mutum uku, idanunta a lumshe sai dai ba bacci take yi ba hasalima tana jin duk wani motsinsa.

"Ayla!" ya kira sunanta cikin wata tattausar muryarsa, kallo ɗaya zaka yi masa ka san ya cika namiji cikakke, domin yana da kyau da haiba da wani irin kwarjini, wanda shi yake sawa Ayla ma wani lokacin rashin kirkinta yake yin ƙasa idan taso yi masa tijara.

"Ayla!!" karo na biyu da ya sake kiran sunanta, sai dai tana kwancen ba ta motsa ba har sai da ya sake kiranta a karo na uku sannan ta miƙe zaune tana taɓe baki tare da jan tsaki.

"Wai mene ne kake ta kirana sai ka ce na ci maka bashi?"

Wane yawun takaici ya haɗiye yana jin yadda zuciyarsa ke tafarfasar ɓacin rai, sai dai duk da haka cike da nutsuwa ya yi mata magana,

"Yanzu abin da kike yi Ayla kina ganin shi ne daidai a rayuwarki? Kina ganin wannan ya dace da rayuwar matar aure? Fisabilillahi ba za ki yiwa kanki karatun ta nutsu ba ki fuskanci ibadarki Ayla"

Da wani irin sautin amo mara daɗi a lafuzan nasa ya ƙarashe maganar. Galala Ayla tayi tana binsa da kallo, kallon ka ji mini mutum, kallon ba fa zai takura mata ba haka kawai, dan tayi aure ba shi ke nuna sai yadda aka yi da ita ba, ba shi ke nuna ba ta da 'yanci ba sam.

"Dakata min Nazeer ni fa ba baiwarka ba ce, ba an kawo maka ni don ka dinga bautar da ni ba ehen, wallahi ashana wannan idan ban ji ra'ayin ƙyasta ta ba bazan kunna ba, balle aje ga ɗora tukunya ko wanke-wanke da ma dai sauransu, ni ba wannan ya kawo ni ba."

Zuruu yayi yana ƙare mata kallo, duk da cewa ba wannan ne karon farko da idan irin haka ta kasance yake kallonta ba, kuma kallo na al'ajabi da mamakinta.

sai dai a lokuta irin haka baya bari ya rasa faɗa mata abin faɗa, yanzuma haka ya danne zuciyarsa ya soma furta mata magana.

"Idan har ba su ne suka kawoki ba, mene ne kenan Ayla?"

"Hutu da jin daɗi" ta ba shi amsa a gatsale.

"Haka kika ce?"

"Yah" shi ne amsar da ta ba shi, tana miƙewa tsaye haɗi da tattakawa ta shige ɗaki abin ta hankali kwance.

ZAHIDA

Zaune tayi kan bakin gefen gadonta, tunani kala-kala ne ke zagaye kwanyarta, mafita kawai take nema sai dai ta san wannan ƙaddararren auren babu mai warware shi sai Allah, amma da ace yau tana da iko wallahi sai ta datse igiyar auren ta huta da cin mutuncin da ake yi mata.

Yadda ta tafi tabar Haulat na nan tsaye a wajen ƙiƙam kamar bishiyar da aka dasa, hunnunta na hagu dafe akan kuncinta, tamkar wacce aka tsikara da tsinin mashi haka tayi zaraf ta faɗa ɗakin tana neman layin yayanta, cikin ikon Allah ringin ɗaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login