Showing 21001 words to 21511 words out of 21511 words

Chapter 8 - KARIN KUNAMA Book 1 free pages by Ameera Adam.docx

17 Oct 2025

1034

yi ma yadda yake wani rawar kai kamar bai taɓa aure ba, lallai ɗan adam butulu mai manta halacci, duk haƙurin zama da shi da tayi bai duba wannan ba, ta tuna sanda aka aura mata shi aka rabata da manemanta, suka zauna dukansu basa son junansu yadda da fari ya fara ƙuntata mata ita kuma tana ƙoƙarin ganin farin cikinsa har Allah Ya sa daga ƙarshe ta samo kansa shi ne amma ya manta da wannan, shi ne yanzu Dan zai auri wata matar shi ne yake yi mata rawar ƙafa, lallai ciki mai manta gobe, ƙwafa ta yi tana ayyanawa a ranta ayi bikin yadda yarinyar zata shigo da ƙafafaunta haka zata fita da ƙafafunta dan ba zata taɓa bari wata ɗiya mace ta zauna mata da miji ba, idan rabon haihuwa ya tsaga ma shi kenan ita ta zama hotiho ko, ita kuwa abin da ba zai taɓa faruwa ba ne alwashi ta ɗauka babu wata mace da za ta raɓu Bash ɗinta har abada.

AHMAD

Kwana biyu da maganarsa da mom nasa amma ya gaza tunkarar gidansu Zahida, sai ya yi nufin haka sai wata zuciyar ta ce ka ƙyaleta da kanta zata dawo, ko kuma mahaifinta ya koro ta kamar yadda ya saba. Sai dai kuma haka nan yake jin wata kewarta da bai san daga ina take fitowa ba, duk da wani sashi na zuciyarsa na ba shi ba ita yake kewa ba kawai abin jikinta yake kewa saboda duk duniya shi shaida ne Zahida ta fita daban, tana gamsar da shi sosai fiye da yadda yake hulɗa da matan waje, hasalima aurenta shi ya fara rage masa bin mata, saboda duk wacce zai kusanta sai ya ji ta salam ba irin Zahidansa ba, ga kuma abincinta da shima tabbas yasan ya yi missing ɗin shi. Mirginawa ya yi kasancewar yana kwance kan lafiyayyen gadon da ke ɗakin, yana sakin hucin iska, dole nema yaje ya dawo da ita, da wannan tunanin ya miƙe ya faɗa banɗaki don yin wanka, yana fitowa ya sauya kaya ya feshe jikinsa da turaruka masu ƙamshi ya ɗau mukullin motarsa ya fice daga gidan, kai tsaye gidansu Zahida ya wuce duk da yadda wani sashi na zuciyarsa na ba shi gurguwar shawarar ya juyo, amma haka ya danne ya nufi gidansu kai tsaye ba tare da wata fargaba ba.

To fa,ƙaƙa-ƙara. Mene ne zai faru da Ayla da cikin jikinta?

Shin Ahmad zai samu nasar bikon Zahida? Shin Zahidan za ta yarda ta dawo ko kuwa za ta juyawa roƙonsa baya?

Ya ya zata kasance da auren da Bash ke son yi? Ya ya zai yi da rigimar YASIRA? Shin da gaske ne ta kwantar da hankalinta ta amince ayi auren?

Shin Wahida za ta samu abin da take so na cinma muradinta?

Ku dai biyo ni, cikin wannan littafi nawa mai taken ƘARIN KUNAMA domin jin yadda za ta kasance, kar ku manta ba a soma ba,yanzu ne za a fara wasan.

Za ku iya tura #700 akan wannan asusun 8160675983 opay, Maryam Abdulaziz.

Maiƙosai

08160675983

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login