Showing 6001 words to 9000 words out of 21511 words

Chapter 3 - KARIN KUNAMA Book 1 free pages by Ameera Adam.docx

17 Oct 2025

1028

ya ɗaga kasancewar daga can bangaren da yake babu wani aiki da yake yi, hasalima tare yake da wata yarinya suna soyewarsu, ganin lambar Haulat yasa shi ɗaga wayar yana karawa a saman fatar kunnensa na dama.

"Hello yaya don Allah ka dawo, Zahida ce ta gaggaura min mari fuskata har ta kumbura." ta yi maganar cikin muryar kuka. A wani irin zafin rai da ƙuna ya soma yi mata magana,

"Me? To akan me ta mareki?"

"Wai dan na iske ta rufe kicin nace ta bani key ɗin zan dafa abu na saka a cikina shi ne kawai babu zato babu tsammani ta wanke fuskata da mari, wallahi yaya har wulgawar taurari na gani ta cikin idanuwana."

"Kan bala...." ya ƙudundumo wata ashariya ya lailayo kana ya ɗora da faɗin,

"Ina zuwa bari zan kirata, kuma ki saka a ranki marinki da tayi bata ci banza ba." bai jira amsarta ba ya kashe wayar ji kake ƙitt. Yana yanke wayar ya shiga neman layin Zahida sai dai kira uku ya yi mata ba ta ɗaga ba, saboda tana zaune kawai taji ɓarin kanta na hagu na ciwo, lokaci guda ta soma ganin wasu irin layuka, ƙarar wayar da yake sake ta'azzara mata ciwon kan ne yasa takai hannu da nufin kashe wayar gaba ɗaya sai taci karo da sunan Ahmad, hakan ya sa ta ɗaga tare da sakata a amsa kuwwa. Ba tare da ya yi mata sallama ba ya soma zazzaga masifa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.

"Ke har kinyi kaurin wuyan da zaki sanya hannu ki mari 'yaruwata Zahida? Hala kin sha omo ko? To bari ki ji wallahi baki mari banza ba dan sai ta rama marin da kika shimfiɗawa lafiyayyen kuncinta, kuma na baki nan da sakan ɗaya ki ba ta key ɗin, daga yau kar ki sake sanya ƙafarki cikin kicin ɗin idan ba haka ba wallahi sai na sa kin gane banbamcin dake tsakanin shayi da ruwa kuma..."

Ba ta bari ya ƙarasa ba ta katse kiran tare da kashe wayar ma gaba ɗaya tana kifeta, ji take ciwon nata na ƙaruwa da duk daƙiƙa ɗaya, ba ta san me yasa Ahmad sam kwata-kwata baya ganin daraja da ƙimarta ba, ba ma haka ba idan shi baya ganinsu me yasa ba zai sanyasu cikin idanuwan 'yanuwansa ba, idan yaso su ganta da su, wace iriyar rayuwa ce wannan haka? Idan har haka rayuwar auren take wallahi tana alla wadai da ita domin ita ba ta ga ci gaban da ta samu a cikinsa ba tsawon waɗannan shekarun da ta shafe tana tare da shi in ka ɗauke; ƙyama, hantara, tsangwama da zubar mata da aji.

Jin yadda ta yanke masa kirin ya sake hasala zuciyarsa, a ƙufule ya furta,

"Kuut! Ni har za ta yankewa kira, lallai ma ta ga makwancina dole, amma wallahi zan yi maganinki zahida zaki gane Ahmad ba kanwar lasa ba ne."

Lambar wayar Haulat ya laluba ya dannawa kira, kasancewar da man jiransa take ai tana fara ringin ta ɗaga tana karawa a kunne.

"Yaya ya kuka yi da ita?"

"Kina ji na, ki nutsu ki kwantar da hankalinki zaki rama marinki dan wallahi ba ta isa taci banza ba, sannan ki je ki amso key ɗin kitchen ɗin kuma ban yarda ko da wasa ki buɗe mata ba idan tana buƙatar hakan, ke idan bake bama ban lamunce ƙafar wata ta sake taka kicin ɗin ba kinji ko?"

"To yaya" ta ce da hanzari tana shigewa ɗakin, haɗi da sake furta,

"Eh, gani na zo zan amsa ai yaya, to sai ka dawo" tana gama faɗar haka ya katse kiran, ita kuma sai ta doshi cikin ɗakin da zahida ke zaune, tana shiga ta soma cika tana batsewa kana ta soma furta,

"Kin ga ikona yanzu ko ai hakan ya isheki hisabi, nan gaba sai kiyi lissafi da ƙwaƙwalwa ba zuciya ba, kuma kamar yadda na ce miki mari sai na rama ki rubuta ki ajjiye sai na rama tunda har yaya ya furta haka da bakinsa. Abu na ƙarshe ki bada mukullin idan kuma ba haka ba wallahi..."

Ba ta jira gama sokiburutsunta ta jefo mata key ɗin a fuska ba tare da ita ta ankare da haka ba, kwanciya tayi taja bargo ta rufe kanta ruf, ita kuwa Haulat tsugunnawa tayi ta ɗauka tana yada mata magana, kafin ta taka ta fice daga ɗakin.

WAHIDA

Kwance take tayi ɗaiɗai akan kujera mai cin mutum uku, domin kuwa ƙafarta ta hagu ta ɗageta ta aza bisa fuskar kujerar hannunta riƙe da wayar android ƙirar kamfanin Infinix, murmushi ne ya suɓcewa fuskarta da babu yabo babu falsar kyau a tattare da ita.

Shewa tayi ta miƙe zaune kan kujerar tana sake murmusawa. Kafin takai hannu ta taɓa maɓallin da aka dannawa wajen yin voice message ta soma magana,

"Ai wallahi duk macen da take ragawa namiji to mata ta rako duniya, shi namiji idan baki yi masa faka-faka ba ai sunanki sorry nickname naki die, don a sannu zai harɓa miki ƙarinsa wanda ke ɗauke da gubar mutuwa wacce za ta dinga ratsaki a hankali har takai ki kushewa, ke ni fa wallahi namiji ya yi kaɗan ya sakani abin da banyi ra'ayi ba, shi yasa na jima da takawa baban sadik burki da naga take-takensa na son kawo min wargi yo akan me ana zaune ƙalau sai ka ce a garin gaɓa-gaɓa, ki zau zauna garin kallon ruwa kwaɗo yayi miki ƙafa, don namiji ƙarin kuma ne wallahi ya harbeki ya karki har lahira."

Tana turawa ta kece da wata dariya da ba zaka iya gane manufarta ba, kashe datar tayi ta miƙe da hanzari tana ɗora hannu a ƙirjinta tare da zare idanuwa.

"Na shigesu lokaci haka yaja, yanzu yaya zanyi idan baban sadik ya dawo ban masa tuwon nan ba ai na shige su" tayi maganar tana rarraba idanuwa kamar wacce aka kama tayi sata. Da hanzari ta nufi kicin tana harɗe ƙafafu kamar zata kifa ta soma ƙoƙarin ɗora tukunya, addu'a da burin tayi komai akan lokaci take yi, tana kuma fata tayi komai daidai. Ta san ba ta da isasshen lokaci amma yaya zata yi haka zata daure tayi masa tuwon tunda ko da zai fita idan ba ta manta sai da ya sake jajjada mata tuwon alkama miyar ɗanyar kuɓewa yake so, ta saka kifi yaji sosai ga shi ko gyara kifin ba ta yi ba. Haka ta buɗe fridge ta ɗebo kifin yadda zai isheta ta zuba a tunkunya ta saka ruwa daidai wa daidai ta jefa lemon tsami rabi ta ɗora don ya tafaso. Yana tafasowa ta sauke ta tsame ta zuba ruwa ta ɗauraye sosai ta hau gyara shi, nan da nan ta tsayar da sanwar miya tunda gas ɗin nata biyu ne.

Cikin nutsuwa da iya taku ta kammala girkinta tsaf, ta shirya kayan akan dinning table, ta shiga wanka. Tana banɗaki ta ji shigowar motar baban sadik, wata ajjiyar zuciya ta sauke tana hamdala a zuciyarta da Allah Ya sa saida ta kammala ya shigo, shiri wannan ba mai wahala ba ne a wajenta kafin ya shiga ya watsa ruwa ta shirya kanta ta fito fes da ita.

_Wannan littafin na kud'i ne akan #700 idan ya zama complete 1k ne_

8160675983

Maryam Abdulaziz

Opay

[10/2, 5:30 PM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA

©Mai ƙosai

Daga Marubuciyar

•Hafsatul-kiram

•Ƙaddarata ce a haka

•Ƙayar ajali

•Zahra

•Da mun bijire

•Matar Mamman

•Wani yanayi

•A dalilin son zuciya

•Budurwar wawa

_Ban amince a juya min littafi ta kowace siga ba tare da izinina ba, yin haka ya sa'ba doka, a kiyaye._

BABI NA HUƊU

NAZEER

Yana tsaye har tsawon wasu mintuna bai motsa daga yadda ta wuce ta bar shi a falon ba, wani numfashi ya ja kafin ya iya ɗaga ƙafarsa ya soma tattakawa ya shige ɗaki shi ma, sai dai kamar yadda zuciyarsa ke ta hasaso masa ɗakin ilai kuwa haka ya tarar da man ya san ba baƙon abu ne wajensa ba tun da ta saba da haka, ya kuma lura ita sam ko a jikinta. Idan fa har yana son yaga tsaftar waje to sai dai shi ya share da kansa amma ba dai Ayla ba, yanzunma hakance ta kasance, kayan jikinsa ya sauya da wasu ya ɗauki tsintsiya ya soma tattare ɗakin, sai da ya gyara shi tsaf, dan ya yi mopping ya kuma killa ce komai ya ajjiye a bigirensa sannan ya koma falo, shi ma haka ya yi, bayan ya gama ya wuce tsakar gida ya gyara ya soma kiciniyar wanke kwanukan, wanke-wanken ya ɗauke shi tsayin mintuna dan suna da yawa tunda yana da tabbaci har kayan jiya, kai ba ma za a rasa na shekaran jiya a cikinsu ba don ita kwano ya yi sati ba komai ne a wajenta ba. Haka ya kammala tilliƙar aikinsa shi kaɗai Ayla na kwance a ɗaki tana chart, sannan ya shiga ƙoƙarin samawa cikinsa abin da zai ci.

A duk sanda zai zauna ya yi tunani sai yaji yama kasa tunani akan komai, saboda har yau tunani ɗaya ne kawai ke damunsa akan Ayla, shin da man ita haka ta ɗauki rayuwar auren? Shin a gida ba a tarbiyartar da ita yadda auren yake ba? Shin ba a sanar da ita haƙƙoƙin auren ba? Mata da yawa ai ba haka suke yi ba. Kuma yana ganin yadda inna ke yi a cikin gidanta, da yadda take tarairayar mijinta, har yana mamakin yadda soyayyar tasu taƙi tsufa kullum take zama kamar sabuwa.

Da sauri ya miƙe ya ƙarasa kicin saboda ƙaurin da hancinsa ya soma jiyo masa, ya zurfafa cikin tunanin da har ya manta da cewa girki yake yi. Ai kuwa taliyar ta kama sosai dan ruwan dake cikin ta ne ya yi mata kad'an sai ya ƙone ya ba ta damar kamawa, saukewa ya yi ƙasa ya ɗebo ruwan sanyi da ke zube cikin drum ya zuba ya ɗakko matsami wato colender ya tace taliyar, sannan ya ɗakko kasko ya tsiyaya mai ya suya manja, haka ya zuba taliyar a faranti ya zuba manja da yaji sai maggi ya dawo falon, a ƙasa ya zauna saboda shi sam ba mutum ba ne mai iya cin abinci a sama, baya jinsa daidai shi yasa yafi ganewa zama a ƙasan ya ci.

Ya kai loma ta uku ke nan Ayla ta fito tana murmushi ganinsa zaune bai sa ta tsagaita da murmushin ba sai ta nemi hannun kujera mai zaman mutum ɗaya ta zauna tana ƙarewa farantin nasa kallo kafin takai ga furta,

"Nazeer ka rage ne ko cikinka kaɗai ka dafa?"

Mamaki haɗi da ƙarfin halinta yasa shi kai idanunsa yana dubanta, sai ya rasa wace amsa ma zai bata, hakan kawai sai ya ba shi damar yin ƙasa da kansa ya cigaba da cin taliyarsa, ganin bai ba ta amsa ba sai ya ba ta damar dawowa gabansa ta tsugunna ta zira hannu tana faɗin,

"Kasan kuwa yunwar da nake ji, ji nayi ba zan iya cin wancan abin ba sai na ajjiye shi wataƙila ma ai ka ganshi da kana wanke-wanke sai dai fa a zuba shi a shara."

Tsam ya cire hannunsa ya miƙe da man tun da ta fito sai ya ji gabaɗaya abincin ma baya masa daɗi, saboda kallonta kawai da ya yi yaji ɓacin ransa ya taso sabo fil, kaitsaye ɗakinsa ya nufa wannan karan saɓanin ɗazu da ya shiga nata, shi kam nasa babu laifi a tsaftace yake saboda da man kafin ya fita zai share abinsa ya goge dattin wajen.



WAHIDA

"Sannu da zuwa Abban sadik" ta faɗa tana sakin yalwataccen murmushi.

"Yauwa yaya gidan?" ya bata amsa fuskarsa babu yabo ba fallasa.

Ja masa kujerar dinning ɗin tayi, ya zauna yana tambayarta sadik"

"Ya bi Zuhra fa ɗazu tazo ta dawo daga school yana ganinta ya maƙale mata ya ce sai ya bita, shi ne kam ta ce a haɗa masa kayansa ko kala biyu ne su tafi, to dai haɗa kayan ma da ƙyar ya bari yana ta kuka shi a tafi-a tafi"

'Yar dariya ya yi kaɗan yana jinjina rigima irinta sadik kafin ya ce,

"Sadik ke nan, rigimarsa tayi yawa."

"Wallahi kam, ai a haka ma tayi sauƙi ka manta" Wahida tayi maganar tana ɗaukar jug ɗin lemon ginger da ta haɗa masa tasa a fridge ya yi sanyi tana tsiyayawa cikin kofi.

"Ina fa zan manta sadik rigima" Ya ba ta amsa yana kai lomar abinci bakinsa.

" 'yar ƙaramar dariya tayi, daidai lokacin da ta ajjiye masa kofin lemon a gabansa.

"Abincin nan ya yi daɗi sosai, musamman miyar tunda shi tuwo da man sai dai ace ya tuƙu."

"Hmm abban sadik kar dai santinsa yasa ka ce kaf duniya ni ce kaɗai macen da na iya girki" tayi maganar tana dariya kaɗan.

"Ai kuwa kamar kin shiga raina, amma fa banda mutum ɗaya."

"Wa fa" ta tambaya cike da ƙosawar jin amsarta.

"Hajiyata mana" ya ba ta amsa yana sake kai loma bakinsa.

Sai tayi dariya sosai kafin ta iya ce masa,

"Ai na ɗauka itama zaka ce na fita, kaga da idan ta kamaka sai in ce hajiya babu ruwana ban ma san anyi wannan maganar ba."

"Au haka ma zaki ce, to bai yi daɗi ba"

"Daga baya ke nan" ta ba shi amsar tana sake darawa.

Har suka kammala cin abincin kulawa take ba shi sosai ta musamman, ba zaka taɓa rantsewa ita ce wahidar dake sokiburutsu a social media kan maza ba, ita ce me cewa namiji ba ɗan goyo ba ne sai kina nuna masa ke ma jar wuya ce.

Ko da suka kammala, ɗaki ta ja shi don kallon idonsa kaɗai da tayi tasan a yanzu babu abin da yake da buƙata sai samun biyan buƙata wanda hakan ne zai ba shi damar hutawa sosai, kusan ita ce taja ragamar komai har sai da ta tabbatar ya samu nutsuwa, kafin ta miƙe ta shige bayi ta shiga haɗa masa ruwan wanka, sai da ya shiga ya fito sannan ta shiga tayo sai dai ba a ɗakin ta tsaya shiryawa ba ficewa tayi ta barshi domin ya samu ya huce gajiyarsa ta nufi nata, tana shiga ta ɗan mittsika mai ta gyara fuskarta ta zira riga mara nauyi sannan ta haye kan gado tare da janyo wayarta tana kunna data.

AHMAD

Tsabar masifa da tijarar da ke cinsa yasa bai kammala abin da yaje yi ba kadunan ya tattaro yanasa-yanasa yayo gida, kwatsam tamkar saukar aradu haka suka ga dirarsa musamman Zahida har gwanda Haulat tunda da man ta san kodayaushe yana iya dawowa.

Ba wai don ta daina jin zafinsa ba sai dan martabawa haɗi da girmamawa matsayinsa na mijinta yasa ta fito tsakar gidan inda ta jiyo muryarsa a sanyaye ta shiga gaishe shi saboda kwana biyu da ciwon kai da zazzaɓi take kwana take yini.

"Sannu da zuwa ina yini..."

Ai bai ba ta damar ƙarasawa ba ya sauke mata lafiyayyen tafin hannunsa saman kuncinta na dama, da wani irin kallo take binsa da shi, hannunta ɗaya takai ta dafe wajen da zafin marin ke ratsata har lokacin. Tana so ta buɗe baki tayi magana sai dai mamaki ya hanata aiwatar da haka.

"Ke har kin isa ki saka hannu kan fuskar 'yanuwana ban targaɗa ki ba, wai Zahida me kika ɗauki kanki ne ke har wace ce? Mene ne matsayinki da har yakai ki ɗaga hannu ki wanke fuskarta da mari? Sannu isasshiya kin ji, sannu na ce."

Ya ɗan tsahirta shi ma saboda ya zuƙi numfashi ne ya fesar ya sake furta,

"Zo ki rama marinki ke kuma."

Ya ƙarasa maganar yana kallon Haulat dake tsaye tana wani shu'umin murmushi.

'Kanbu' Zahida ta furta k'asan zuciyarta wani abu mai ɗaci na dukan zuciyarta, ai wallahi abin da ba zai taɓa saɓuwa ba ne wai bindiga a ruwa, sai dai ko me zai faru ya faru amma babu abin da zaisa Haulat ta mareta, wanda ya zuba mata shi ma dan babu yadda zata yi da shi ne. Tana wannan zancen zucin taga Haukat ta matso kusa da ita, ta ɗaga hannu da niyar sauke mata shi a kuncinta, ai kuwa kamar ƙiftawar ido Zahida ta kai hannunta ta riƙe hannun Haulat tana maka mata harara.

"Sake ni, yaya kaga ta riƙe min hannu" ta ƙarasa maganar tana juyawa ta kalli Ahmad.

"Sakar mata hannu, ai wallahi sai ta rama marin nan Zahida idan kuwa ba haka ba to sai dai ki fita ki bar min gida."

Yarfar mata da hannun tayi, ta ɗaga ƙafarta ta juya tana jiyo shi yana banbami, ita kuwa tana shiga ta ɗau wayarta da kuɗi ta fito ko kallon inda suke bata sake yi ba ta fice daga gidan.

"Wato iskancin naki k'ara gaba yake ko Zahida ni nake miki magana kika fice to wallahi kin fita kenan naga ta inda zaki dawo ba dai ni ke da igiyar auren naki ba kuma ni ke da ikon dawo dake to sai inga uban da ya isa ya sa na dawo da ke gidan nan."

"Wallahi yaya rainaka ma tayi shi yasa kana magana ta fita, caab jar ubancan ai wallahi karka bari ta dawo ko da za ayi yak'in duniya na uku." Cewar Haulat wacce ke ta faman hura masa wuta da sunan zuga.

Ai kuwa ya hau kan maganganunta ya zauna daram faɗa yake ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, ƙarshe ma bai zauna a gidan ba sai ya shura 'yan matan ƙafafuwansa ya fice daga gidan.

NAZEER

Shiri yake sosai yana sauri saboda gaf yake da makara, a ƙa'idarsa mutum ne sam da baya son saɓa alƙawari sai dai sauyi da canci da ya samu daga matarsa yanzu yana haifar masa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login