Showing 18001 words to 21000 words out of 21511 words
Chapter 7 - KARIN KUNAMA Book 1 free pages by Ameera Adam.docx
ne babu wani aure da zaka ƙara."
Wani nishi kamar mai naƙuda ya saki kafin ya iya furta mata,
"Don Allah Yasira, don Allah ki yi mini kyakkyawar fahimta ki fahimce ni kiyi mini uzuri, babu yadda zanyi in fasa wannan auren Yasira idan nayi haka ita yarinyar sam ban kyauta mata."
"To kuwa wallahi ka sani babu kai babu zaman lafiya a gidan nan na rantse da sarkin da ya busa mini numfashi duk wacce tayi gigin aurenka ta tabbatar ta shigo kabarinta domin gidan nan sai ya zame mata kushewarta wallahi."
Tana gama faɗin haka ta miƙe ta shige banɗaki tabar shi a wajen kamar wani mutum mutumi, shi fa gaba ɗaya tsoronta ya mamaye shi, ya san tana da kishi amma ko da wasa bai tsammanin zafin kishin nata zai kai haka ba.
Ganin ba shi da wani zaɓi face ya ƙyaleta har zuwa ta sakko, zai ba ta lokaci wataƙila ta daina fushin da shi, sai ya tattara 'yan ƙafafunsa ya fice daga ɗakin, ɗakinsa ya shiga yana mai neman wajen zama gefen gado, agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya kwance ya ajjiye gefe yana saƙa wasu tunanuka ƙasan ransa,kafin ya ƙarfafawa gangar jikinsa ya miƙe ya shige banɗaki, ruwa ya watsa kana ya fito, gaban madubi ya tsaya yana goge sumar kansa da ɗan ƙaramin towel, bai shafa mai ba saboda yanayin garin ana ɗan zafi-zafi, sai kawai ya ɗau turare ya fesa ya shiga neman kaya masu sauƙi ya saka suma ya fesa musu turare duk da ƙamshin da suke yi, aikin Yasira ne da duk kayansu duk sati sai ta turare musu su, kai har turaren cikin sif ta sanya musu shi yasa kayansu basa rabo da ƙamshi, ƙamshin ma ya zauna a jikinsu ko an wanke sai ka ji wannan ƙamshin mai sanyi.
Wayarsa ce tayi ƙara ya ɗauka yana kallon sikirin wayar, sunan Fatu ne ya bayyana kasancewar da FATUNA ya yi saving lambar, duk halin da yake ciki bai hana shi ɗan murmusawa ba kafin ya amsa kiran yana kara wayar saman fatan kunnensa na hagu.
"Uhm barka da hantsi" yaji saukar muryarta cikin kunnuwansa.
Murmushi ya sake fitarwa yana son hirarsa da ita wasu lokuta dan kawai ya yi nishaɗi yake zuwa wajenta taɗi, a ƙauye aka haifeta ta kuma taso, tana shekara sha huɗu ta dawo hannun kawunta ƙanin mahaifinta ne wanda shi ma cirani ne ya kawo shi Kanon, sai ya nemi waje ya zauna har ya yi aure ya tara iyali, yana da mace ɗaya sai yara biyar uku mata biyu maza sai kuma ita Fatun da ya ɗakko sakamakon rashin mahaifinta da tayi, zuwanta kanon kawu ya sanyata makaranta wacce yaransa ke zuwa, kuma Alhamdulillah tana ja don babu laifi kam, bayan ta gama sikandire sai manema suke ta zuwa da fari taso basu dama sai dai kuma ita har ga Allah so take yi tayi karatu mai zurfi idan da san samu ne ta zama 'yar jarida a dinga jinta a gidan radiyo ko a dinga ganinta a gidan TV, Suhaima 'yar kawun nata kuwa da taji kalamanta ita ce ta ba ta shawara akan sai dai ta kori duka samarin ta fuskanci karatun shi ne kaɗai za ta cinma abin da take so, hakan kuwa aka yi dan gaba ɗaya ta daina kula samari, har Allah yasa ta samu gurbi a makarantar BUK, ta dage sosai tana karatunta, tana level 2 suka haɗu ita da Bash a wajen siyan kayan marmari, kawu Manu ya turo ta ta siyo musu ita da Suhaima, shi kuma lokacin yaje siyawa Yasira. Abin da ya soma jan ra'ayinsa da ita tsiwarta, ganin yadda take yiwa mai siyar da kayan marmarin tsiwa akan zai yi musu runto, da yake ma mutumin ba babba ne ba sai tafi zagewa tana yi masa tsiwarta ta, da sannu-sannu ya bibiyeta ya samu kusanci da ita, har ya yi mata alƙawarin aure, san da ya fara magana da ita tashin farko ya fahimci ita wace asali ce saboda har yau HE tana bakinta, wasu abubuwan ma na ƙauye basu barta ba, ita kanta tana mamaki sosai da ya ci ace yanzu ta daina yinsu.
"Hello my yallaɓai kana ji na?"
Maganarta cikin siriryar muryata ya dawo da shi daga duniyar da ya wulga.
"Uhm!" ya ce, ta kuma fahimce me yake nufi da haka, sai kawai ta ɗora da abin da take son faɗa masa.
"Da man kawu ne ya ce ina sake tambayarka da gasken iyayen naka za su zo jibin?"
"Uhmm za su zo Fatu, amma kin san me?"
Sai da gabanta ya bayar da sautin rass kafin ta iya amsa masa da,
"A'a"
Ya lura da yadda muryarta tayi rauni, ya san baya rasa nasaba da yadda shi ma ya yi mata tambayar, yana jin cewa ta shiga fargaba ne kuma yasan fargabar ba zai wuce tayi tunanin ko dai ya fasa.
"Ina jin kamar idan sunzo su saka sati guda bikin nan."
"Hmm!" ya jiyo ajjiyar numfashinta, da kuma sautin murmushinta kafin ta ce,
"lokaci komai zaizo a muhallinsa fa yaya."
Yadda ta ƙare maganar sai da gashin jikinsa suka tashi, yana sonta don ba zaice baya sonta ba wannan ma zance ne maras tushe, ita ce macen da ya fara kalla da sigar so, ba zai ce ba ya son Yasira ba amma a kaso ɗari kaso arba'in yake jinta a ransa sauran kuwa duka sun tafi wajen Fatu.
"Shi ke nan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi."
"Amin yaya."
"Ok zan kiraki anjima, yanzu ina gida kin ji. Kin ga lokacin aunynki ne ko?"
"Tom ka gaishe min da ita, na gode sai anjima ka kula min da kanka ka ji."
Ba ta jira amsarsa ba ta kashe wayar, wani murmushi ne ya suɓce masa, murmushin da ya yi daidai da shigowar Yasira ɗakin sai shaiɗan ya yi mata huɗubar da ta tafi akan gaɓa, ta ji cewa ai da wacce zai aura yake wayar har yake mata wannan tsadadden murmushin da ita kaɗai ya canci ta ganshi, lallai ma ya rainata ita zai yiwa haka, namiji kenan, namiji ƙayar ajali, namiji ƙarin kunama.
Wannan littafin na kuɗi ne akan #700 book 1&2,idan ya zama complete 1k.
8160675983
Opay
Maryam Abdulaziz
Maiƙosai
08160675983
[10/16, 11:20 AM] Maikosai(Matar Abduul): Follow the MARYAM MAI ƘOSAI NOVELS channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6lO6KJ93war7Sywv0G
ƘARIN KUNAMA
©Mai ƙosai
FCW ASS.
Book 1
BABI NA TARA
ZAHIDA
Bayan dawowar inna ne likita ya jona mata ruwa kamar yadda ya ce, sai kuma allurorin da ya dace da ciwon nata ya yi mata. Suna nan zaune har kusan mintuna talati kafin inna ta ɗau wayarta ta kira gida, nan ta shiga sanar da su halin da ake ciki. Nan take mama ta soma haɗa musu abinci domin yaya kamal da kansa ya ce da ita zai kai musu, Huwaila kuwa tana makarantar islamiyya ba ta dawo ba. Ko da ya karɓi abincin sai da ya tsaya wajen mai balangu ya siya musu ya haɗa musu da kayan shayi ya wuce asibitin kaitsaye.
"Sannu inna yaya mai jikin?" cewar yaya kamal bayan ya ajjiye kwandon abincin da kuma ledar biba wacce ya yi musu siyayya da ɗan abubuwan buƙatarsu da aka haɗo musu daga gida.
"Yauwa Kamalu, jiki da sauƙi gata ta samu bacci ma."
Kallo yabi Zahida da ke kwance da shi, ƙasan zuciyarsa na jin tausayin 'yaruwartasa, tun da tayi auren nan babu kwanciyar hankali, ita ce yau kaza gobe kaza,yaso a raba auren nan amma baba malam ya kafe ya tsare akan babu dalilin da zaisa akashe aurenta, dole ya tattara ya watsar da batun sai dai kullum addu'a yake yi mata akan idan da alkhairi a zaman nasu Allah ya daidaita mata lamuran, idan kuma rabuwar tafi alkhairi to Allah ya warware igiyar auren.
"Akwai abin da kuke buƙata inna?" ya jefawa inna tambayar.
"A'a babu, don na jima likitan ɗazu bayan ya jona mta ruwan yana faɗin wataƙila anjima ya sallamemu idan ya ga yanayin jikin nata, idan kuma kwanan ta kama ma dai gaskiya bana jin akwai abin buƙata."
"To shi kenan, Allah dai ya ba ta lafiya."
"Amin" cewar Inna tana ɗan gyara zamanta, sai da ya ƙara hutawa sannan ya yiwa inna sallama ya tafi.
Huwaila na dawowa daga islamiyya taji batun asibiti ta ajjiye jakarta ta wuto, don ko abinci ba ta tsaya ci ba, san da tazo ta iske har an jona mata ruwan na biyu wancen ya ƙare, kuma Zahidan ma ta farka tana cin abinci.
"Sannu yaya" cewar Huwaila ga Zahida. Tana bin ta da kallon tausayawa.
Gyaɗa mata kai kawai tayi, don wata yunwa take ji tana sassaƙarta, ga shi zura abincin take yi amma ji take kamar ma ba ci take yi ba.
"Ki ci a hankali idan baki ƙoshi sai a ƙaro wani akwai ai." Faɗin inna da ta lura da yadda Zahidan ke kai lomar abincin hannu baka hannu ƙwarya.
"To inna" Zahida ta ba ta amsa a taƙaice.
"A miƙo miki balangun?" inna ta sake yi mata magana cikin salon tambaya.
"A'a sai anjima." zahidan ta ba ta amsa tana kai loma bakinta.
Can gida kuwa sanda baba malam ya dawo ya riske labarin, da sannu ya bita da shi, tare da nema mata sauƙi a wajen Allah, mama kuwa itama tana gefe tana bin ɗiyarta ta da addu'ar samun sauƙi da rahamar Allah.
Ayla
Yau da wata irin kasala ta tashi, tun jiya kanta ke ciwo, wajen bayan magrib, tadai b'alli farasitamol tasha, sai dai sam babu sauƙi abun ma kamar ƙara gaba yake yi, yanzu kuwa da ta tashi har da wata juwa take ji, ga wata yunwa kamar an rarake cikinta.
Nazeer na kallonta yadda take yatsina fuska, da yadda ta mik'e a kasalance ta shige banɗaki, yana zaune gefen gado yana ƙoƙarin ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa, san da ya kammala ɗaurawa ita kuma ta fito ya ɗaga kai ya dubeta yana faɗin,
"Baki da lafiya ne?"
"Kusan haka" ta ba shi amsa a taƙaice, bai sake ce mata komai ba ya miƙe tare da zira hannunsa cikin aljihu ya zaro dubu uku ya ajjiye mata saman durowar gefen gado yana faɗin,
"Ga shi nan dubu uku ce babu yawa ki je asibiti, abinda ake ciki idan na dawo sai in gani."
Wani sheƙeƙe ta bi shi da kallo don har yakai bakin ƙofa, kamar yasan zata raina kuɗin shi yasa ma ya yi hanzari ficewa, yana jiyo tsakinta da furucin da ta jefe shi da shi.
"Tsiyar talauci kenan, kai wallahi talauci baiyi ba a rayuwa.Yazu a rasa abin da za a bani sai wata shegiya dubu uku ita ce zanje asibiti da ita, idan banda ma dai mutum ba mutum ba ne ba kamata ya yi ya ɗauke ni ya kaini da kansa yadda ba sai na sha wahala ba."
Haka ta gama mitarta ta fito falo, tana jiyo tashin babur ɗinsa da fitar daga gidan, sai a sannan ma ta wuce kicin tasan ya ajjiye mata abin kari, ai kuwa ta tarar da wainar fulawa da kunu. Tsaki taja tana mai kushe kayan karin, waɗanda wasu na can suna neman kwatankwacinsa ita ta samu amma ta kasa godewa Allah ni'imar da ya yi mata.
Falo ta dawo ta zauna ta soma cin wainar, dan bama ta zubo kunun ba sam ba ta jin za ta iya shansa. Nan ta miƙe tabar farantin a wajen ta koma ɗaki tana dafe kanta da yake sara mata, jirin ne dai kam ta rage jinsa wataƙila hakan nada nasaba da yunwar ma da take ji. Wanka ta faɗa banɗaki tayo, ta fito tana tsane jikinta kafin ta murzawa fatarta wani lotion da takanas ta siye shi wajen wata mata da suka haɗu gidan biki, ta ce mata yana saka hasken fata sosai, ga laushi da sulɓi, ita kuwa abinda take buri kenan aga fatarta na walwali ta yadda duk wanda ya kalleta dole ya sake kallonta.
Sai da ta gama tsirface-tsirfacenta sanan ta zira kayan ta yafa wani shara-sharan mayafi ta ɗau jaka ta zira takalmi mai tsini sai dai ba can sosai ba ta fice daga gidan ba tare da ta kalli gidan ta gyara shi ba, asibiti ta nufa bayan ta tare mai napep ta shiga, ana sauketa kuwa ta wuce sashen karɓar kati ta amsa ta koma layin ganin likita tana jan tsaki a ranta tana raya yanzu da Nazeer wani hamshaƙin mai kuɗin ne da sai dai su je firabet a mutunce a yi mata komai ba tare da ta wani biyo layi ba, katin ma tasan file ne za a buld' mata da anje kuwa babu wani sanya za a zak'ulo shi, wani ƙululun baƙinciki ne ya taso mata ya tokare mata maƙoshi, tana nan zaune kafin ta shiga sai ga wata mata nan da ka ganta kasan kuɗi sun zauna mata sosai, domin ko suturar jikinta ma kaɗai abar kallo ce, Ayla bin ta kawai take yi da ido, tana ayyana inama ita ce, musamman yadda ta ga tana zuwa ta shiga wajen likita.
"Shegiya naira." cewar Ayla tana hasaso kanta a matsayin matar, har matar ta fito layi yazo kanta tana tufka da warwara.
Bayan tambayoyi likuta ya turata wasu gwaje-gwaje ciki kuwa har da na juna biyu, ita dai jinsa kawai take dan tasan babu yadda za ayi ta samu wani ciki, tunda tana tsarin iyali ta hanyar shan ƙwayar maganin tsarin iyalin, kuma bata fashin shan maganin, hasalima ita yaushe rabonta ma da Nazeer tana jin a ƙalla anyi sati biyu zuwa uku. Haka dai taje aka yi mata tasa-tasan ta kawowa likitan sakamako.
"Congratulation madam kina ɗauke da juna biyu, sai kuma bp ɗinki da ya yi ƙasa kaɗan amma zan ɗoraki kan magunguna in sha Allah komai zai zama normal."
Tunda ya ambaci kalmar juna biyu ta daina fahimtar komai, ta yaya ma haka zai faru, wallahi ba zata saɓuba ai kuwa sai ta zubar da cikin nan don har yanzu ba ta shirya haihuwa ba, yaushe ma akayi daren da har gari zai waye.
"Amma na ce da man likita ana iya samun ciki kuma ana yin tsarin iyali"
Murmushi kaɗan likitan ya yi, yana dubanta kafin ya ce,
"Ƙwarai ma, ai tsari yana wajen Allah, idan baiso mutum ya huta ba to kome zaiyi ba zai huta ɗin ba, sau da dama wasu mata kanyi ƙorafi akan sun saka implan amma sun samu ciki, ko mace tana allura ta samu ciki wannan kuma duk cikin hukuncin Allah ne."
Wani numfashi ta sauke ba ta ce da likitan komai ba, haka ya rubuta mata magunguna tare da ba ta wasu shawarwari saboda jininta da ya yi ƙasa, da kuma kare lafiyar abinda take ɗauke da shi, ita dai jinsa kawai ta yi don tayi rantsuwa cikin nan bazai zauna ba balle ma akai ga haifarsa. Haka ta wuto gida ranta a dagule, ta yi niyar biyawa gidansu amma sai taji ta fasa ranta a ɓace ta dawo gidan tana jira Nazeer ya dawo ayi wacce za ayi.
BASH
Cikin hukuncin Allah sai ga shi ankai kuɗin aurensa har da sanya rana wata biyu masu kamawa, kasancewar kowanne tsagi a shirye suke sai hakan bai ba su matsala ba, ai kuwa Bash da Fatu sun yi murna sosai da man sun tsara haka sai dai ba su zata abin za su same shi ta sauƙi, don sun yi tsammanin za a ƙara akan wata biyun. Duk wani rigima da tashin hankalin Yasira bai sa an fasa ba, ƙarshe ma takanas hajjo ta taka tazo gidan ta dinga lallashinta tare da nuna mata auren da zaiyi ba shi ke nuna ba ta da ƙima da daraja ba, kuma tana da tabbaci yana sonta koda kuwa zai yo mata kishiya. Ba wai don ta gamsu da zancen hajjo ɗin ba, sai dai kawai don taga babu yadda zata iya, amma fa ba wai ta haƙura ba ne, alƙawari ta ɗauka ba za ta zauna da kishiya ba, za ta sauya salo, tana nan tana jiran wacce ta yi gigin cewa za ta shigo ɗin da sannu za ta saita mata hanya ta koma inda ta fito, don ta yi rantsuwa ko kaffara ba za ta yi ba, Bash ba zai zauna da wata ɗiya mace bayan ita ba.
Bash ya yi mamaki sosai da yaji ƙurar Yasira ta d'a lafa, ya ga ta saki ranta ta mayar da komai kamar ba komai ba, ita ce har da tambayarsa a ina zai ajjiye matar.
"Bana da burin raba kan iyalaina, a nan za ta zauna za a gyara ɗaya sashen ne, ko Kuma a gyaran can dakin ya zamana falonku ɗaya kicin ɗaya"
"Uhmm" ta ce masa, shi kuwa ya shiga washe baki, har yana faɗin,
"Wallahi Yasira na ji daɗin yadda kika watsar da komai, na gode miki Allah ya saka miki da gidan aljanna. In sha Allahu ba zan bari ki wulaƙanta ba"
Amin ta amsa masa a taƙaice tana zamewa ta kwanta, daman a jingine take jikin fuskar gado, shi kuma yana daga bakin gefen gadon.
Bin ta ya yi da kallon tausayawa, yasan dole za ta ji babu daɗi, amma zai yi ƙoƙari ya cigaba da kwantar mata da hankali, zai kuma kiyaye mata mutumci da darajarta ba zai bari Fatu ta shigo gidansa ta wulaƙanta ta ba ko babu komai ita ce ta fara sanin sirrinsa, kuma yana jinta a cikin zuciyarsa don a yanzu idan har ya ce baya son Yasira to shima yasan zance ne ya faɗa da babu bakin kamawa. Da wannan tunanin ya miƙe ya faɗa banɗaki, Yasira ta bi shi da harara tana jan siririn tsaki ƙasan zuciyarta kuwa babu abin da take binsa da shi face baƙaƙen maganganu, ita mamakinsa take