Showing 15001 words to 18000 words out of 21511 words

Chapter 6 - KARIN KUNAMA Book 1 free pages by Ameera Adam.docx

17 Oct 2025

1033

zahida ta daina gane komai, tunani ta tafi yi tana hasashen yadda wasansu zai kaya da ahmad idan yaji samuwar cikin nata. Sai inna ce ta ce da likitan,

"To dakta babu damuwa, mu ai lafiyarya muke so. Sai dai ɗazu muna wajen gwajin tayi amai sosai."

Ya ɗan muskuta kafin ya ce da inna,

"Mama babu matsala zan rubuta mata maganin aman in sha Allahu zata daina, yanzu ga katin aje a fara siyo waɗannan tukunna ita kuma yanzu za azo a kaita ɗakin da za a kwantar da itan."

"To na gode ɗan nan." Inna ta ce, tana amsar katin. A nan tabar zahidan ta fice dan siyo abubuwan kamar yadda likitan ya ce, kasancewar akwai kuɗi a wajenta, dan da zasu fito ta ɗebo kuɗi masu ɗan yawa.

NAZEER

Sanyayyen ƙamshin da ya doki hancinsa ne yasa shi yin mutuwar tsaye, tunda ya shigo gidan yaga komai ya canza masa kamar ba gidansa ba, bai ƙara sumewa da mamaki ba sai da ya shigo falon yaji yadda wani daddaɗan ƙamshi na tashi, ya kuma ƙyallara ido yaga komai fes-fes kamar dai ba gidan da ya sani ba, yana jinsa kamar wani gidan daban ya shigo tamkar dai wanda ya yi ɓatan hanya. Sai dai hango Ayla da ke kwance kan kujera kanta babu hula, jikinta kuwa ɗaurin zani ne da ta kawo shi ƙirjinta ya tabbatar masa da gidansa ne ba wani gidan ba. Zuciyarsa da farinciki ya ƙarasa shigewa falon yana sake sakin wata sallamar.

Ayla da ke kwance tana typing ta amsa a yatsine tana wani yi masa kallon tara saura kwata kamar ba mijinta ba, madadin ta miƙe ta taroshi sai ta sake muskutawa ta ci gaba da abin da take yi.

Bai yi ƙasa a guiwa ba ya ƙarasa kan kujerar da ke kallon ta Ayla ya zauna, yana ajjiye ledoji biyun da ya shigo da su.

"Sannu da gida" ya ce yana duban Ayla da ke sakin murmushin da bai san me take yiwa ba.

"Yauwa" ta ba shi amsa cikin ko in kula.

Sai shima ya tattara ta ya watsar bai sake gangancin yi mata wata maganar ba, ledojin ya ɗauka ya fice da su zuwa kicin. Koda ya shiga ledar farko ya buɗe mai ɗauke da kayan fruit a ciki ya ɗibi waɗanda za su iya ci ya zuba a faranti sauran ya zuba a cikin fridge, sai ya ɗauki waɗancan ɗin ya hau wankesu kafin ya sanya wuƙa ya yanka su yadda yake so. Ɗaya ledar kuma naman kasuwa ne na ƙaramar dabba, shima cikin firinjin ya saka dan ya san ba lallai tabi takansa ba tunda ya ganta da waya a hannu, idan bai yi wasa bama shi ne zai yi aikinsu.

Fulas ɗin abinci da ya gani an jere akan babban faranti ya hau buɗewa nan yayi arba da white rice mai kayan lambu, sai ɗayan miyar albasa ce zalla sai kifin jiya da ya shigo da shi yaga an saka aciki. Gefe guda kuma jug ne aka haɗa lemo na lemontsami da cocumber. Mamaki iya mamaki ya mamaye shi, dan yasan ko giyar wake Ayla tasha ba zata yi masa wannan garar ba, amma bai sani ba ko wataƙila kuma shiriyar da yake ta nema mata ce Allah ya kawo

Abincin ya zubo a faranti, sai lemon da ya tsiyayo a wani ɗan madaidaicin kofi ya fito falon ya koma ya ajjiye su ya sake dawowa kicin ɗin ya ɗauki farantin da ya zuba kayan marmarin nan ya sake komawa falon ya zauna, har lokacin Ayla na nan yadda ya barta.

"Sannu da aiki, na gode." ya ce da ita yana kallon fuskarta.

Ajjiye wayar dake hannunta tayi ta tashi zaune tana yatsina fuska kafin ta ce da shi,

"Kar ka ɓata bakinka domin ni ban girka maka komai ba, kai duk abinda ka gani a gidan nan ba aikina ba ne aikin Hasina ne, dan haka ita zaka yiwa sannu ba ni ba, saboda ni na faɗa maka ba 'yar aikinka ba ce, banzo gidan nan dan na yi bauta ko wata wahala ba shi yasa ma na ce ka ɗakko mai aiki kai kuma da taurin kai kamar mutanen farko kaƙi ai shi ke nan sai ayi ta zama a haka."

Ta ƙarasa maganar tana yarfar da hannu, haɗi da komawa ta kwanta.

Saƙaƙe ya yi yana bin ta da kallo, kaf kalamanta babu wanda ya ƙona masa rai irin abu biyu, na farko cewar ba ta isa ta girka masa abin da zai ci ba, na biyu kiransa da tayi da mai taurin kai kamar mutanen farko.

"Ayla ni ne mai taurin kai kamar mutanen farko?" ya jefa mata tambayar da mamakin da har yanzu bai bar shi ba.

"To ƙarya na yi da zaka wani tsattsare ne da na mujiyarka, ka ga ni daina kallona haka don Allah kar na sake lalacewa."

Ta ƙarasa maganar tana wurga masa harara. Bai san yaushe aka yi daren da gari ya waye har ya yi saken da ta raina shi har haka ba, bai san me yasa ya kasa ɗaukar hukunci mai tsauri akanta ba. Idan aka ce masa Aylansa ce wannan wacce ta so shi a baya yake ganin kamar za ta yi masa sujjada ce a yanzu haka sai ya musa ya ce sam ba haka ba ne, a yanzunma idan mamaki ya cika shi ji yake wani sashi na zuciyaraa na ayyana masa cewa wata ce ba ita ce ba canza masa ita aka yi.

"Ayla kin san kuwa girman miji da haƙƙoƙinsa da ke kanki?" ya watsa mata tambayar yana sake kafeta da idanuwansa.

"To ustaz masanin Allah da manzonsa da anyi magana sai ka wani wage baki kai ga wanda ya san Allah zaka yi wa mutum wa'azi, koda yake ance wai gwano baya jin warin jikinsa shi yasa kai kake kasa fara yiwa kanka wa'azin kafin ka yiwa wasu tunda kana ganin baka da laifin komai baka kuskure ko?" ta kai ƙarshen maganar da watsa masa tambaya.

"Idan har akwai abin da nake yi miki ba daidai ba sai ki sanar dani ai, sau nawa nake zaunar da ke ina tambayarki laifin me ne yi miki kina ƙin faɗa Ayla"

Taɓe baki tayi kafin ta ce da shi,

"Eh fa nan fa ɗaya, to ai matsalar ko an faɗa maka baka yarda shi yasa nace gwano ne kai da baya jin warin jikinsa. Idan ba haka ba kai har kana da bakin magana, sau nawa ina rattaba maka abin da ya dace ayi a gidan nan na ga ko ɗakko min mai aiki sau nawa muna zancen dakai amma ka toshe kunnuwanka ka mayar da ni wata mahaukaciya wacce ban san mena ke yi ba ."

"To kin san me kike yi ɗin ne Ayla?" Ya ɗan tsahirta yana dariyar gefen baki kafin ya ce,

"Idan har da kin san me kike yi da baki zauna kina faɗawa mijinki waɗannan kalaman ba, da kin rungumi aurenki kin duƙufa wajen nemo aljannarki Ayla."

"Allahu akbar kabiran!" Ta yi maganar haɗi da shewa kafin ta sake furta,

"Nazeeru idan kai kake da aljanna da wuta don Allah idan na mutu ka saka ni a can ƙarƙashin wuta ka ji."

"Ba ni ke da ita ba, amma ga dukkan alamu idan baki gyara ɗabi'unki ba zaki tafi can ƙasan-ƙasan wutar ai Ayla."



"Mits to ai sai ka sakani aikin banza aikin wofi ka ji da yawarka. Wallahi ni Ayla na sha gabanka nafi ƙarfinka ehe dan baka isa ka mayar da ni jaka baiwarka ba, bar ganin ka biya sadaki an baka ni, ba shi ke nuni da cewa na zauna ka takani yadda kakeso ba, nima ina da gata kuma gatan ne zaisa na samarwa da kaina 'yanci, dan ba zan yadda nazo a sahun mata gidahumai ba da suke jin kamar su kai goshinsu ƙasa su yiwa mijinsu sujjada, suke jin kamar su kwanta miji ya taka ruwan cikinsu ya tsallake ya yi gaba."

"A ra'ayinki kenan da idan mace ta yiwa mijinta biyayya shi kesa ta zama jaka baiwa, amma ita macen da tasan ciwon kanta tasan darajar Allah da Manzonsa tasan darajar iyayenta da ta mijin nata ita ce kaɗai zata fahimci cewa yiwa miji biyayya ba shi ke sakawa ta koma jaka baiwa ba. Ina miki fatan shiriya Ayla, idan kuma ba zaki shiryu ba ina fata Allah ya yi mini maganinki, ya kawo min sauyi da mafi alkhairi."

Yana gama maganar ya miƙe ya wuce ɗakinsa, ji ya yi ma abincin kwata-kwata ya fice masa a rai, ga shi dai yana jin yunwar amma kuma abincin baya da wajen shiga. Har ya zauna sai ya dawo falon ya ɗau farantin kayan marmarin ya koma ɗaki da niyyar ya shasu ko sa toshe masa wata kafar.

Wannan littafin na kuɗi ne akan #700 book 1&2 idan ya zama complete 1k.

8160675983

Opay

Maryam Abdulaziz

Maiƙosai

08160675983

[10/12, 9:50 AM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA

©Mai ƙosai



FCW ASS.

Book 1

BABI NA TAKWAS

Marubuciyar:

•Budurwar wawa

•Hafsatul-kiram

•Ƙaddarata ce a haka

•Zahra

•Da mun bijire

•Wani yanayi

•Matar Mamman

•Ƙayar ajali

•A dalilin son zuciya

BASH

"Da man hajjo cewa na yi ko za a haƙura da zuwa neman auren nan."

Bash da ke zaune gaban mahaifiyarsa hajjo ya yi maganar yana sunkuyar da kansa ƙasa.

Kallon ɗan nata take yi, tana son gano mene ne ya sauya shi, ɗazu-ɗazun nan ya bar nan kuma bai tafi ba sai da suka ajjiye magana akan jibi za a je nema masa auren yarinyar da ya ce mata yana so ɗin, kuma bawai ɗazun ne tasan yarinyar ba hasalima har bincike duk anyi akanta, basu gano wani aibu nata ba.

"Ita yarinyarce ta ce ba ta yi da kai?"

Sake sunkuyar da kai ƙasa yayi, yana miƙa hannu ya sosa ƙeyarsa kafin ya ce da ita,

"A'a hajjo"

"To me ya faru?" ta watsa masa tambayar idanuwanta na kansa har lokacin.

Gaba ɗaya dirircewa ya yi musamman yadda yake jin idanunta suna yawo a jikinsa, yasan da man tambayar da za ta yi masa kenan idan taji cewa babu laifin Fatu ɗin, sai dai har ga Allah bai shiryawa amsarta ba, bai ma san me zai ce da Hajjo ɗin ba.

"Kai nake sauraro Bashir me ya faru da za a fasa zuwa nema maka auren yarinyar?"

"Am da man hajjo Yasira ce..."

Sai yayi shiru ya kasa ƙarasawa.

"Uhmm ina jinka, cewa tayi ba zaka yi auren ba ko me?"

"Eh to hajjo kusan haka, ɗazu bayan na bar nan to sai nake faɗa mata cewa zan ƙara aure, wallahi hajjo baki ga yadda hankalinta ya tashi ba gaba ɗaya ta fita hayyacinta."

Wani murmushi ta saki tana kana ta ce,

"Karka kuskura ka zama lusari acikin gidanka Bashir, ba zan hanaka abinda kake so ba amma ka sani ba zaka mayar da ni ƙaramar mutum ba, kai da bakinka ka shaida min yarinyar nan ta kori samarinta ba ta kula kowa sai kai, kuma kai ka ba ta wannan umarnin ka kuma tabbatar mata da kai zaka aureta shin ita ba mutum ba ce da ba zaka yi mata adalci ba, saboda kawai matarka ta tayar da hankali sai ka ce ka fasa auren? To ka buɗe kunnuwanka da kyau ka jini aure babu fashi wallahi sai anyi da yardar Allah, ka koma ka je ka ci gaba da rarrashin matarka duk wata mace da man ai tana da kishi dole idan taji za ayi mata kishiya hankalinta ya tashi, kaje ka rarrasheta ka kwantar mata da hankali ka nuna mata kai kake da gida, ban ce ka cutar da ita ba amma dai ka nuna mata kai tsayayyen namiji ne ba lusari ba."

Ya san za a rina da man wai an saci zanin mahaukaciya, hajjo ba za ta fahimce shi ba duk da yasan gaskiya take faɗa masa, amma irin wutar da yaga tana neman kunno masa acikin gida tafi gaban haka shi yasa da yake so ya yiwa tufkar hanci tunda wuri, amma tunda ya ji zancen hajjo yasan ta gama magana, kamar yadda ta ce ne aure kam yasan babu fashi sai dai idan Allah bai ƙaddara Fatu matarsa ba ce.

Jiki babu ƙwari ya miƙe ya yi mata sallama ya fice daga gidan, cike da kallon tausayi tabi ɗan nata. Tasan hakan da man zai faru, dole Yasira zata tayar da hankalinta musamman da ya kasance ba ta taɓa haihuwa ba, tasan zata iya hasashen domin haka zai ƙara auren, kamar yadda wasu matan da dama suke tunanin haka wasu ma suke gani idan aka auro musu kishiyar tazo ta haihu shi kenan miji ya daina sonsu, sun zama ababen wulaƙantawa uwa uba suzo su haɗu da kishiya mara tsoron Allah da imani ta tarwatsa musu kan gida wata ma ta yi musu farraƙu da mijin tana jin ta ci dubu sai ceto. Amma fa hakan ba zaisa ta goya masa baya ya fasa auren ba, tabbas tana son ganin jikokinta daga tsatsonsa sai dai idan Allah ya ƙaddara ba shi da rabon kuma ba ta yi masa fatan haka, ita babban burinta da fatan tama Yasiran ta fara haihuwar kafin wacce ta shigo ɗin tayi, tana kuma yi musu addu'a akan haka.

WAHIDA

Kujiba-kujiba da zirga-zirga take tayi tsakanin falonta da kicin, abinci take so ta kammala haɗawa kafin shigowar mai gidan nata wato abban sadik Taj ke nan. Wayarta ce da ke kan kujera zube a falo ta hau ƙara daidai lokacin da ta ɗakko ɗan ƙaramin fulas mai ɗauke da miya zata ajjiye akan dining ɗin, wayar ta fara ɗauka ganin sunan maigidan nata akan sikirin ɗin wayar yasa ta ja wajen da ke nuna alamar amsa kira, a handsfree ta sakata ta ƙarasa wajen dining ta ajjiye fulas ɗin taja kujera ta zauna.

"Assalamu alaikum my abban sadik"

Tayi maganar da sanyayyiyar muryar da take da tabbaci tana ɗaukewa maigidan nata hankali. Tana jiyo sautin murmushinsa kafin ya amsa mata sallamar.

"Wa'alaikumussalam da farar aniya mai sanyaya zuciya, hope komai normal?" ya ƙare da yi mata tambaya.

Tana ɗan murmushi ta ba shi amsa.

"Lafiya lau kai kawai muke jira."

"To ma sha Allah. Me kika dafa mini?"

"Taliya ce da source sai farfeson kan rago."

"Auch!" ta jiyo sautin furucin nasa kafin ya ɗora da faɗin,

"Taliya Wahida ita kaɗai, kin san fa ni ba ta wani riƙe mini ciki don Allah idan ba so kike na mutu ba ki sama min wani abu mai nauyi dai, ko kuma kinga kawai dafa min shinkafa idan yaso sai na haɗa da ita."

"An gama yallaɓai, isowarka kawai muke jira."

"Wait wai sadik ya dawo ne kike ta cewa kuke jira"

'yar dariya tayi kafin ta ce,

"A'a kasan sabo da faɗa shi yasa bakin ya saba."

"Haƙƙun ban manta ba fa." ya yi maganar cikin sigar tsokana.

Dariya tayi wannan karan sosai kafin ta ce,

"Kai abban sadik" cikin shagawaɓar da tasan zata narkar da zuciyarsa, ta kuwa yi sa'a dan yadda ta ƙare maganar sai da tsigar jikinsa ta motsa.

"Wash me kike tanadar mini sweet." ya ce da ita a kasalance.

"Komai ma, kai dai kawai Allah ya dawo mana da kai lafiya."

"Ki ce yau ɗan gata nake, amin sai na dawo bye." Ya ƙarasa kalaman nasa da kai mata sumba a wayar kafin ya katse kiran, lumshe idanuwa tayi tana jin ƙaunar mijin nata har cikin ranta.

YASIRA

Bakinsa ɗauke da sallama cikin nutsuwa ya turo ƙofar ɗakin nata, tana durƙushe yadda ya fita ya barta, bakinta babu abin da yake gauraye shi sai zallar ɗacin kalaman da ya dinga cusa mata cikin kunnuwanta, wai ita Yasira Bash zai kalli ƙwayar idanuwanta ya furta mata kalmar kishiya, da ranta kai ko babu ranta ai tana ganin ba ta canci ya yi mata kishiya ba.

Durƙusawa ya yi inda take ya kai hannunsa na dama ya ɗago fuskarta wacce tayi shaɓe-shaɓe da ruwan hawaye wasu sun bushe wasu kuma suna kan gangarowa. saboda ita shigowar da ya yi ma ba ƙaramin fama mata raunin da ya gama ji mata ya yi duk da cewa ba wani kamewa wajen raunin ya soma yi ba, amma ita kam ji take yi kamar tayi rauni ne ya ɗakko hanyar warkewa sai aka yi mata kamunsa.

Tar ta ware idanuwanta kan fuskarsa tana kallonsa tana kuma son ta gano sauyin da aka yi mata da Bash ɗinta na baya, kai ita fa so take yi ma taga ta farka dan tuni zuciyarta da ƙwaƙwalwarta sun faɗa mata tana duniyar mafarki ne.

"Don Allah ka tashe ni daga baccin nan Bash, ka ce min duk wasa ne abin da ka faɗa mini ba gaskiya ba ne." tayi maganar cikin karyewar murya tana sake cusa idanuwanta cikin nasa.

"Ki yi haƙuri beb ba mafarki kike yi ba da gaske ne, Bash ne gabanki tsugunne da ƙoƙon bara don Allah ki kwantar da hankalinki kar ki samu wani ciwon"

Wani murmushi tayi da ta gaza tantance muhallin da zata ɗora shi akai, kafin ta iya furta masa,

"Ciwo hmmm!" ta yi ƙwafa kana ta ɗora,

"Idan har babu ƙarya a cikin kalamanka ka tabbatarwa kanka da ciwo na riga da na jima da samun ciwo, kuma ciwon da zai zama silar ajalina. Bash me yasa za ka yi mini haka? Me na rage ka da shi? Ko dan ba na haihuwa? Ko kuma dan ni matar shige ce a wajenka?"

"Haba beb duk me ya kawo wannan zancen wallahi babu ko ɗaya, Yasira ni Bash ina sonki kuma tsananin ƙaunarki ki yarda da ni plz."

"Idan har kana so na gasgata ka to ka faɗa min ƙarya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login