Showing 9001 words to 12000 words out of 21511 words
Chapter 4 - KARIN KUNAMA Book 1 free pages by Ameera Adam.docx
tarin matsaloli da yawa, ya rasa kuma hanyar da zai bi don gyara mata zamanta duk yadda yake tunanin abin Ayla ya sha kansa yafi ƙarfinsa, idan ya ɓullo ta dama sai ta toshe hanyar hakazalika idan ya koma hagu shi ma sai tasan yadda tayi ta toshe wannan hanyar, shi abin nata ma yanzu ya daina ba shi mamaki da al'ajabi ya kawo ido ya zuba mata yana jiran ya ga iya gudun ruwanta.
Da gudu-gudu sauri-sauri ya fice daga gidan, yana kallon kwanukan da ke barbaje a tsakar gidan wani takaici na ƙume zuciyarsa a haka ma don jiya ya wanke kwanukan da kayan sai sunfi haka yawa da munana wajen. Haka ya haye kan mashin ɗinsa ya ja shi.
Ayla kuwa tana kwance bacci take sha abinta hankali kwance, babu ruwanta da tashi ta samarwa da mijinta abin kari balle akai ga shirya shi ya fita wajen nema. Ƙarar da wayarta keyi ne ya sakata motsawa tana runtse idanuwanta, ji take yi koma waye ya yi masifar uzzura mata da tsakin da ke fita daga bakinta ta janyo wayar da ke ajjiye kan bedside durowa ta ɗaga tana sakata a amsa kuwwa.
"Kar dai ace baki tashi ba Ayla."
Tsaki taja can ƙasan maƙoshinta yadda mai maganar ba zai zama ta ji ba kafin ta iya buɗe bakinta da ya yi mata nauyi saboda baccin da ke tsikarinta ta ce,
"Baccin ne akaina Hasina ki barni don Allah"
"Kai Ayla anya kuwa? Anya hanyar da kika ɗakko za ta ɓulle da ke? Kina ganin rayuwar za ta yi haka kuwa? Yanzu ina Nazeer ya fita ko? Kuma baki taimaka masa ba ko?"
"Don Allah ki ƙyale ni Hasina, mijinki ko nawa?"
"Ko ɗaya, amma a matsayina na ƙawa mai sonki tsakani da Allah dole ne in faɗa miki gaskiya Ayla."
"To ki riƙe kayarki bana so" Ayla ta ce tana jan siririn tsaki wanda wannan karan Hasina ta ji shi sosai.
Ƙwafa ta yi kafin ta yi magana Ayla ta saka hannu ta katse kiran tana juyawa wayar baya bayan ta ajjiyeta kan dirowar ta ci gaba da baccinta.
ZAHIDA
Tun daga ƙofar gidansu yayanta Kamal yake tambayarta amma ta kasa buɗe baki ta ba shi amsa saboda wani ƙullutun abu da ya yi mata babakere a maƙogwaranta da hanzari ta shige gidansu kai tsaye kuma ɗakin da ƙanwarta Huwaila ke ciki ta nufa 'yar ƙaramar katifar da ke ajjiye tsakar ɗakin ta nema ta zauna a kai, sai a lokaci taji wasu zafafafan hawaye sun surnano mata saman dandamalin fuskarta.
Mama da take mahaifiya a wajenta wacce kuma ta ga shigowarta sai dai ko kaɗan ba ta da ra'ayinma bin ta ciki ta ji me ya kawota gidan, kasancewar mace ce mai kawar da kai ga 'ya'yanta, idan abu dubu zai rufar musu muddin ba sakota suka yi a ciki ba ba ta taɓa tanka musu ba, iyaka da su zata sanyasu a addu'a ta nema musu sauƙi wajen Mahalicci.
Inna wacce ita ce mace ta farko a gidan sai dai Allah bai sa ta taɓa haihuwa ba ita ce ta zame musu tamkar uwa, duk wani kulawa jin damuwarsu ita ce wannan. Yanzu ma tana hangota ta shige ɗaki ta ajjiye butar da ta fito daga banɗaki tayo ɗakin Huwailar.
A zaune ta tarar da Zahidan sai dai ta cusa kanta tsakankanin cinyoyinta tana riskar kuka. Jin hannun inna kan kafaɗarta bai sa ta ɗago ba sai dai jin kalamanta cikin kunnuwanta ya sake haddasa mata ƙarfin kukan nata.
"Kar ki zama gafalalliya Zahida ki dinga mantawa da ambaton sunan Allah" abin da innar ta sake ce mata ke nan, bayan maganar ɗazu da ta yi mata akan lafiya. Jin haka yasa Zahida saisaita kukanta ta soma ambaton La'ilaha illaha, kafin ta sake furta Inna lillahi wa inna ailaihir raji'un! Take taji wata nutsuwa na saukar mata ba ta san lokacin da ta faɗa kan inna ba ta sake rushewa da kuka ita kuwa inna bubbuga bayanta kawai take yi alamun rarrashi.
_Wannan littafin na kuɗi ne akan #700 idan ya zama complete kuma 1k_
8160675983
Maryam Abdulaziz
Opay
Maiƙosai.
08160675983
[10/2, 5:53 PM] Maikosai(Matar Abduul): ƘARIN KUNAMA
©Mai ƙosai
_Ban amince a juya min littafi ta kowace siga, ba tare da izinina ba. Yin haka na iya kaiwa ga hukuma, a kiyaye._
BABI NA BIYAR
Daga Marubuciyar:
•Hafsatul-kiram
•Ƙaddarata ce a haka
•Ƙayar ajali
•Zahra
•Da mun bijire
•Matar Mamman
•Wani yanayi
•A dalilin son zuciya
•Budurwar wawa
WAHIDA
Zaune take kan kujera mai cin mutum ɗaya, gabanta fitilar nan ce da masu yin tiktok suke amfani da ita wato ringlight, sai wayarta da ke saƙale jikin fitilar. Doguwar riga ce a jikinta ta yane kanta ta ɗan mayafi wanda ya sakko har ƙirjinta ya suturce mata shi. Sai da ta tabbatar ta saita komai sannan ta soma magana.
"Ina faɗa miki sisy karki kuskura ki ce zaki ɗagawa namiji ƙafa, ki nuna masa wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa. Idan ance mace tabi mijinta ba shi ke nuna ki zauna ya mayar da ke baiwa ba, mace ba baiwa ba ce ba. Ko kin san dan ance ki nemi aljannarki ƙarƙashinsa ba wai yana nufin ki zama shakatafi ba ki zama baiwarsa, sai yadda ya juyaki kamar wata waina a kasko, idan ya ce miki kule, ki ɗaga murya ki ce masa caass."
Tana ida maganar ta saki wani ƙayataccen murmushi mai cike da ma'anoni kala-kala, ji take tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha saboda tsabar farincikin da ke tattare da ita saboda yadda take ganin magoya bayanta na sake tururuwa kan abin da take aikatawa, ta sani da wannan damar ce kaɗai zata samu abin da takeso, da wannan damar ce kaɗai zata cika nata burin shi yasa kullum take ji babu gudu kuma babu ja da baya, domin shi ja da baya ga rago ma tsoro ne, ita kuwa ba ta ga abin da zai ta taja baya ba tunda ita ba raguwa ba ce.
Har ta ajjiye wayar ta kishingiɗa da jikin fuskar kujerar ta ji ƙarar wayarta ta alamar kira ne ya shigo, sai da taja tsaki ganin sunan da ke bayyane kan sikirin ɗin wayar kafin ta kai hannu ta ja alamar amsawa.
"Kai jama'a wahida kinga yadda kike wuta kike gwara kan matan aure kuwa, wai mene ne sirrin ne?"
Dariya ta ɗan saki kafin ta iya bata amsa da,
"Yana wajenku ai, yo to an faɗa miki borno gabas ce ai duk macen da ta ce zata zauna namiji ya juyata ita taso, shi yasa nake biya musu karatun idan sun fahimta sun tashi sun ƙwatarwa kansu 'yanci su suka so, idan sun kwanta anzo an sauke musu jujin shima su suka so haka."
"Ai wallahi kam da gaskiyarki yo iskancin ɗa namiji ai yawa gare shi idan ka tausaya masa ma kai ne a ruwa tsundum, gwara ka tashi ka ƙwatarwa kanka 'yanci , shi yasa fa kike burge ni, ni dai ki taimaka ki bani adires ɗinki zanzo na kwashi wannan romon ilimin ga-da-ga."
"Karki damu soon zan sanar da ke, yanzu dai zan yi wani uzurin sai anjima bye."
Ba ta jira amsar matar ba ta katse kiran tana jan tsuka, can kuma ta fashe da dariyar har da riƙe ciki kafin ta miƙe ta ɗauke kayan aikin nata ta mayar da su wani ɗaki, tana faɗin,
"Indai ni ce yanzuma aka soma wasan wallahi muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura."
ZAHIDA
"Ina zahidan take" cewar baba malam mahaifinta ke nan da ya shigo inna na sanar da shi zahida ce ta dawo gidan kuma har yanzu ba ta ce uffan ba, shi ne ya nufi hanyar ɗakin nasu yana tambayar tana ina. Tana zaune saman darduma ba zata ce ga abin da take yi ba tasan dai ta fara addu'a tana kaiwa Allah kukanta daga nan kuka mai ƙarfi ya ƙwace mata sai da tayi mai isarta sannan ta tsagaita sai kuma taja bakinta ta yi shiru.
"Wai tana ina ne na ce, ke zahida" ya faɗa da ɗan faɗa-faɗa.
"Malam kabi komai a sannu don Allah" Faɗin inna tana matsowa inda yake, wata harara ya watsa mata yana sake faɗin,
"Ko sai na shigo ɗakin ne bazata fito ba ke zahida kina jina ko kika min kunnen uwar shegu lallai kin riƙa kin zama riƙaƙiyar kuɓewa."
"Gani baba" cewar zahida tana durƙusawa ƙasa.
"Me ya dawo da ke gida kuma, ance kin shigo kina ta rafka kuka kinƙi faɗin ba'asi me ya faru Zahida, ba dai auren kika kaso ba?"
"A'a baba cewa dai kawai ya yi in taho gida"
"A haf kinji ba, kice dai auren kika gurgunto, ai shi kenan sai kizo ki zauna ki ji idan zaman da daɗi tunda haka kika zaɓa."
A hankali cikin sanyayyiyar muryarta ta ce,
"Baba ai bai ce ya sake ni ba, kawai dai ya ce in zaɓa ne cikin zaɓi biyun da ya bani ni kuma na zaɓi tahowar."
"Ke Zahida ki fita daga idona, me ya haɗaku da har miji zai baki zaɓi ke kuma kika zaɓi tahowa gida?"
"Baba saɓani muka samu da ƙanwarsa shi ne ta je ta tsage masa ƙarya da gaskiya shi kuma yazo yake ta min ihu aka har da cewa wai sai ta mareni, ni kuma na ce wallahi ina matar wanta ba zan lamunta ta zabgawa fuskata mari ba shi ne yace aikuwa sai dai na fita na bar masa gidan ni kuma shi ne na taho."
Shiru baba malam ya yi yana nazarin al'amari kafin ya ce,
"To shi haka ake yi kawai sai ka bari ƙanwarka ta mari matarka kan wani abu daban, yo ai ko dukanta kika yi baya ce ta rama ba ko, shi ke nan tashi ki je idan yazo ya nemi ki koma kya koma gidan naki amma fa nima ba zan lamunta ace za a ƙasƙantar da ke ba, nayi kura kurakure da dama a baya amma ba zan sake yarda na ƙara maimaita kwatankwacinsu ba yanzu, maza tashi ki je Allah ya yi miki albarka."
"ameen" ta amsa tana mai miƙewa tare da shigewa ɗaki. Inna kuwa ji tayi wani farinciki ya lulluɓeta ko babu komai malam yau ya burgeta sosai domin da fari ta ɗauka zai ce da zahidan ne ta tattara ta koma inda ta fito kamar yadda a lokutan baya yake yi, sai ga shi ya basu kunya ya ce zahidan ta koma ta zauna har mijin nata yazo.
AYLA
Kwance take da yake ba ta da wani aiki sai kwanciya da chart a cewarta ba zata mayar da kanta jaka ba, aikin gida ba zata yi ba idan ya gaji da ganin ƙazantar gidan ai dole ya samo mata 'yar aikin kamar yadda take tayi masa mita, tunani take yi yadda zata samu kuɗaɗen da take son saka hannun jari akan maganar business ɗinsu da zasu yi su biyun da suka tsara, idan har bata samu kaɗaɗen nan ba tabbas kashinta ya bushe kuma tasan duk group ɗin zasu ɗauketa maƙaryaciya ba koman komai domin tana da tabbaci sai Hidaya ta fesawa group ɗin cewa sun haɗu business ashe ƙarya take faƙiriya ce ita ba ta da ko asi, ita kuwa da ta ji kunyar nan gwara tasan abin yi, don yadda take gigita mutan group ɗin take nuna musu itafa matar mai ƙumbar susa ce, matar kece raini, kuma duk abin da ta shimfiɗawa mijinta baya ƙetarewa komai na rayuwa ta ce tana so sai ya bata. Tana cikin tufka da warwararta ta jiyo bugun ƙofa, cike da mita ta miƙe ta yi hanyar waje ta buɗe ƙofar. Hasina ce tsaye tana zuba mata murmushinta mai sanyi, gefe taja ta bata hanya ta wuce, daga yadda taga gidan kawai jinjinawa Ayla take cikin zuciyarta, ba zaka ɗauka gidan mutum ne ba mutum ɗin mace, macen ma kuma wai matar aure.
"Yanzu don Allah Ayla kin kyauta?"
Hasina ta jefa mata tambayar bayan ta zauna. Da wani kallo Ayla ta bita tana yatsina baki kafin ta ce,
"Uwar iyayi yanzu kuma me na yi?"
"Au tambayata ma kike yi, kalli fa gidanki, wai a haka kike amsa sunan matar aure ke yanzu ko tsoro bakya ji"
"Tsoron me kuma ana zaune ƙalau"
"Hmm Ayla ke nan ba zaki gane duk abin da nake faɗa miki ba amma wallahi ko dawo kan turbar gaskiya idan kika kai Nazeer bango fa zai iya yanke miki hukuncin da sai kin gwammace kiɗa da karatu, ina nan da ke wata rana sai dai kiji ana gafara za a shigo da amarya ya ƙara aure don dai namiji yana buƙatar tattali da kulawa, idan baya samu kuwa dole zai tafi tunanin ƙara aure don samun mafitarsa."
Tsaki taja kafin takai ga furta,
"Ka ji wani sakarcin zance, yo to sai me don ya ƙara aure kin ganni nan ko akwalar rigata, ke bari ki ji shi kansa yasan zance yake idan ya ce ma zai ƙara aure dame zai yi auren yana faƙiri matsolo da shi, me ya ajjiye ai ko kyauta aka ce za ayi masa auren baya sanya hannu ya karɓa ba, domin yasan idan ya kawota gida ba shi da abin da zai kula da ita."
"Ai kuwa dai kema kin san faɗa kike yi kawai, babu wanda zai kalli Nazeer ya ce masa faƙiri, idan banda ma ƙaddarar iftila'in da Allah ya jarabce shi da ita har a kalle shi ace masa faƙiri, kuma ko a yanzu bazai amsa wannan sunan ba kin sani sai dai ki faɗi ba daidai ba, tunda har yau banga ya rageki da wani abu ba Ayla, ki dai nutsu wallahi ki kama aurenki da kyau kina ganin yadda matan ke neman shiga daga ciki ido rufe kin ganni dai yadda kullum mama sai ta min shaguɓe saboda har yau ban yi aure ba, to ke bazaki godewa Allah ba ki amshi ni'imar da ya yi miki hannu bibbiyu ki samo aljannarki ƙarƙashin digadigin mijinki ba."
"Enough Hasina ba ni da wannan lokacin wallahi, ai duk wacce ta zauna miji ya mayar da ita baiwa to ita taso, kin ganni nan ba a haifawa namiji ni don na zama baiwarsa ba, ke dai da kika ga zaki iya bautar sai ki jira kiyi auren sai a mayar da ke jaka baiwa ballagaza amma ba dai Ayla ba."
"Hmmm! Ke kike ɗauka duk macen da take yiwa mijinta biyayya jaka,baiwa ballagaza amma a wajen Allah ba haka ba ne, kuma shi ne ai neman ladan baki san shi kansa auren ibada ce mai zaman kanta ba, wallahil azeem ko da mijin da zan aura zai dinga yankar naman jikina zan jure matuƙar, ke ko da zai dinga zunduma min ashar duk safiya zan shanye ba, ballantana ma nasan Allah zai dubi zuciyata ya bani mai tausaya min da jinƙaina, ai idan kika ga namiji na cutar da mace to ɗayan biyu ne, ko dai bai san darajar mace ba ko kuma ita macen ce ta bayar da dama, wato tun farko ita ta nuna masa ita ba kowa ba ce ba mutum bace mai daraja shi yasa yake hawa kan keken rashin mutuncinsa yake taketa yadda ransa keso."
"Yah na ji ustaziya, ni kin ga tashi don Allah ki gyara min gidan kin ji plz"
Hasina ba ta musa mata ba ta miƙe tana zare mayafinta ta ajjiye kan jakarta, ta fice daga falon ba tare da ta sake tanka mata ba, itama ba ta sake tanka mata ba sai ma murmushi da tayi wani lokacin tana jin daɗin mu'amalarta da Hasina ko za su yi ta gwabzawa za dai su sake haɗewa kuma zasu yi kamar ba su yi ba, uwa uba tasan ma ko ba ta ce ta gyara mata ba zata yi akaran kanta. Kwanciya ta yi ta janyo wayarta ta kunna data, take sak'onni suka dinga shigo, fita tayi daga whatsapp ɗin ta koma kan tiktok nan taci karo da sabon videon da Wahida ta wallafa ai kuwa ta dinga doka murmushi tana yaba mata har da tsayawa ta rubuta mata sharhi.
A haka ta shagala shiga nan fita cen, ita ce intsgram, facebook har da twiter kafin ta dawo kan whtsapp ɗin kai tsaye kuma group ɗinsu ta shiga, nan take ta tura musu bidiyan wahida tana faɗin,
_Hey guys ga fa mutuniyartaku ta saki sabon update, to ya kuka ce kai wannan mata takai maƙura wallahi shegiyar tana wanke kawunan masu kwanya a duhu fa._ sai ta saka emojin dariya.
YASIRA
Lokaci ƙanƙani taji wani abu mai kama da saukar aradu ya dira tsakiyar kanta, ko a mafarki bata taɓa kawowa Bash zai iya tunkararta da kalmomin da yake fesa mata ba, ashe da gaske ne da ake cewa namiji ƙanin ajali, namiji ƙarin kunama ne da idan ya ɗana miki dafinsa ya wuce duk yadda hasashe zai kawo, yau ga shi Bash ya ɗana mata nasa ƙarin ta kuma kasa gano mizanin da zata aza yadda take jin zafinsa. So take yi tayi magana ta faɗi wata kalmar amma ta kasa, bata san sanda sagaggun ƙafafunta suka miƙe tsaye ba ta kwasa da gudu ta wuce ɗaki tana sakin wani irin kuka mai tsuma rai da zuciya.
"Innalillahi" Bash ya faɗi yana dafe goshinsa, shi yasa yaso yin shiru da bakinsa sai dai Hajjo ta nusar da shi wannan sam ba mafita ba ce gwara ya faɗa mata ayi komai a wuce wajen, yanzu ga shi ya sanar da ita ga kuma abinda hakan ya haifar, bai san ma ta ina zai soma rarrashinta har ta fahimce shi. Ganin zaman ba zai amfanar da shi komai ba yasa ya yi ƙundunbala ya bita, tana kwance kan gado sai rasgar kuka take yi, a hankali ya ƙarasa inda take ya miƙa hannunsa kan saman