Showing 1 words to 3000 words out of 26260 words

Chapter 1 - Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel By Aisha Umar Indabawa.docx

💗💗💗ZAZZAFAN RABO💖💖

💔na Aisha Umar indabawa💕

editing

Kamal sanee malumfashi 08162538316

Marubuciyar littafin Meka maidani

🤳typing🤳

🦚page 1🦚

*Da sunan Allah merahma mejin kai,yadda nafara wannan novel din Allah yasa nagama lfy ,ameen

Bismillahi rahmanir rahim

Gudu kawai yakeyi a motar ,sbd mugun saurin da yakeyi,yana tukin yana duba agogon hannunsa,Tara dai dai yatsayar da motarsa a cikin makarantar ,dalibai sai kawai gaisuwa sukeyi ,suna cikin farin cikin ganinsa sai babban yaya Allah yaja da ranka ,sai daga musu hannu yakeyi yawuce inda xaiyiwa dalibai darasin,yana shiga suka gaisheshi yafara karantar dasu cikin gwanancewa .

Cikin sauri wata matashiyar budurwa tashigo cikin hol din kamar xata fadi dan sauri ,kallo daya yayi mata ya juyar da kansa ,yayi mata alama da hannu ta juya ,cikin muryar tausayi ta fara bashi hkr amman yayi mata nuni data juya tasan halinsa baya mgn biyu,tanaji tana gani ta rasa wannan darasin ,tanemi bakin bishiya ta xauna tayi tagumi,ga bakin cikin da yake damunta gashi ya sake kara mata wani,gashi ko karyawa batayiba tafito,yana fitowa ya kalleta yace dama kin tashi kinkoma inda kika fito .gantalalliya mara kamun kai,yayi offices dinsa yabarta a wajen ta kalleshi sai hawaye sosai a fuskarta,

Da akatashi tana tsaye a bakin get din mkranta ,kwai sai taganshi ya xuge gilas din motarsa yace gida xakiyi ta kautar da kanta yace dake nakefa Salwa harta bude murfin motar xata shiga kawai sai yaja motarsa da gudu ,kunya ta kamata ga dalibai sai dariya sukeyi mata sosai ,wasu har suna xuwa gabanta suna dariya wani yace kadan kenan da aikin malam abdul,ina dawowa gida naganshi shida sultan a kofar gidansu nawucesu inaji abdul yana cewa gantalidai babu kyau ga diya mace nayi wucewata,sultan kuwa sai kirana yakeyi nayi masa bamgn

aunty dan Allah kitsayani ko kallansa banyiba,

Yau da wuri natask'a dan nasa inada laccar wannan mugun mutumin,dan nasan xai iya hanani shiga ,ko karyawa banyiba,sbd saurin da nakeyi,kowa daya ganni sai dayayi mmakin ganina da wuri k'awayena kuwa cewa sukeyi Ashe yau xaki kar6i kyautar Mlm Abdul, ni dai kawai nayi musu shiru.

Tundaga nesa muka dingajin ihun samarin,axuciyata nace gashinan ya karaso,yashigo yana wani taku gaba daya ya bude holl din da kanshin turarensa,shaddace milk anyi mata aikin Kofi,yasa hularsa Kofi da ratsin milk yayi kyau sosai,inajin wata yarinya tana cewa inama itace matarsa ,nace dakin gama yawo,laccar yayi sosai harya gama yafita sannan kowa yasamu yasake,ni kuwa daman yinwa nakeji sai danaci abinci sannan naji dai dai,ina dawowa kawayena sukacemin wai Mlm Abdul yaxo nemana shida wani yaro,gabana ne yayi muguwar faduwa ,nace Allah yasa bada sultan yaxominba,to ina makarantar to ko 6ekaishiba,nidai gaba daya hankalina ya gama tashi,nakoma cikin holl din naxauna banyi auneba sai ganin yaro nayi a kaina yanacewa aunty ina kikaje inata nemanki ko yawo kikaje ,bakisan ancul ya hana yawo ba,shiyasa yacemin kincika yawo ,sbd tsabar haushi Na kwada masa mari nace ni sa,arkace ko wasa nake maka fice kabani waje kuka sosai yafita yanayi da alama dukan ya shigeshi fita nayi cikin mutane Na xauna,banyi auneba kawai sai jin mari nayi a fuskata,yana sharewa yaron fuska yi hkr kaji sultan dina ai kaga naramama ko,ya kalleni karki sake ta6amin yaro idan kuma ba hakaba wlh duk matakin dana dauka akanki kekikajawa kanki dan matakina me tsaurine a wajenki,banxa ballagaxa.

Yadauki sultan a kafadarsa sukayi wajen motarsa,ni kuwa banda kuka babu abinda nakeyi wasu kawayena suka dinga tanbayata nace waidan yaro yayimin rashin kunya nadakeshi,shine yabiyoni ya rama masa ,kawai sai suka fara yimin tanbayoyi ni kuma nayi musu shiru domin banida amsar basu,kodana tafi gida a kofar gida naganshi shida yaron nasa,inajin yaron yanata kirana nayi masa banxa,yace to saime danta daina kulaka ,wlh idan aka sake ta6amin yaro sai ran kowa ya6aci,aikin banxa ,nidai kawai tafiyata nayi,yauma da kuka nashiga gidan sbd bakin cikin abinda Abdul yakeyimin,ya yaxid ne yatareni yake tanbayata ngy masa duk irin abinda Abdul yakeyimin a school yace to kiyi hkr dadina dake shagwa6a xanyi masa magana ya daina ,kema kuma kinada laifi karki sake ta6amasa yaro kinsan yadda yakeji dashi,nace to umma yana saune tanajinmu Amman baxaka gane abinda yake fuskartaba,akan abu yayi sauki sai karagaba yakeyi narasa abinda nayi masa ,babu dama naxauna acikin kawayena sai yaxo yacimin mutunci,

Yauma kamar kullum dawuri nashirya Amman shiru mugun bexoba har wajen taran safe ,saida wani mlmin yaxo yake bamu hkr wai bashida lfy,yanada wani mugun ciwan ciki Wanda inyatasar masa bayayi masa ta dadi,nidai murna axuciyata nadinga cewa Allah yasa ciwon yayi tsanani yakwana biyu bexoba kona huta ,haka mutane suka dinga kar6ar number sa ,wasu kuma suka dinga cewa hargida xasuje dubashi,addu,ata kuwa taci domin har gadan Asibiti,haka dalibai suka dunga tururuwar xuwa,ni kuwa duk 'yan gidanmu babu Wanda bejiba akace naje nadubashi nace munje da sauran dalibai aikuwa saida yayi sati uku sannan yafara suwa school, ai kuwa naga tsana a idansa sosai ko sannu bance masaba ko kallan inda yake banyiba ,shima kuwa yayimin hulakanci cikin kawayena ina xaune yaxo yace musu wai kamata yayi sudaina xama dani sbd su sunada tarbiya Karna ,6ata musu tarbiya tundani ballagaxace waisu yaran mutunxine ,kawai sainasa kuka shikuma yatafi yana dariya.

💖💖💖ZAZZAFAN RABO💖💖💖

💕💕💕na Aisha Umar Indabawa💕💕💕

Marubuciyar littafin Meka Maidani💖

🤳typing🦚



🦚page 2🦚

Ai kuwa yasake samin karan tsana sosai,sai ina xaune yaxo yace wai idan banyi wasaba saiya tunamin asiri naga ta tsiyar girman kai,kawayena kuwa suyita yimin mgn wai dan Allah me nayi masa yakeyimin irin wannan abun,dan kowa yasan bedamu da mgn ba bare yashiga harkar wani ,nace kunga nifa bansanshibama banta6a ganinsaba banda a mkrantarnan,tsanata kawai yayi yakeyimin hakan,suka yadda da abinda nagaya musu ,har sunacewa daman mutum Tara yake becika gomaba duk kirkinka sai ansameka da gibin wani abun,a haka dai mukabar mgnar muka shiga wata.



Yaukoda aka tashi daga school banwuce gidaba ,gidan kanwar ummanmu nawuce xan kar6omata sako,babdawoba sai wajen shidda Na yamma abakin layinmu aka saukeni,dan bansamu Wanda xai shigar daniba,bansan yana kofar gidansu a xauneba ,danni ko inda yake bana kaunar gani,shiyasa idan naxo kofar gidan ko kalla banayi sai dai Na sunkuyar da kaina yaudinma hakance ta kasance,sai jin muryarsa nayi yana cewa,idai addu,ar da xantayi miki Allah ya shiryaki yasa kigane hanyar gaskiya,dan wannan hangar da kika xa6arwa kanki bame 6illewa bace,ace atashi tun karfe biyu Amman ace kinwuce gantalinki Allah yaganar dake gaskiya,nadago kaina Nakalli wajen ,sai naga ashema sunada yawa a wajen sun shinfida cafet da lemuna a gabansu,nidai nawuce bantanka musuba ,sai dai bakin cikin abinda yakeyimin baxaibar xuciyataba,saidai nace Allah yasakamin tunda haka yadaukeni .tana wucewa wani a wajen yace meyarinyarnan tayi maka gaskiya katakura mata,sai kawai yasa dariya yace mgnin Mara kamun kai nakeyi kasanni inasan mace mekamunkai ,itakuwa ta xubar a tuti kaga kuwa baxamu ta6a shiri da itaba,kumafa dalibatace,gata Mara kunya,harfa ciwo nayi Amman ko sannu batasan tacemin ba,kuma muna unguwa daya,girman kan tsiyane da ita,wani daga cikinsu yace kodai santa kakeyine shiyasa katakura mata,ya mike da sauri wallahi nasir karka sake yimin irin haka,kayimin fatan samun tagari mana,Amman kahadani da wannan ballagaxar,ya dauki lemo ya kora ,yace kunkureni daga hirar,ya dauki mukullin mota ya shiga yaja da gudu yana kunguni,bedawo gidanba sai dare,yaxo ya tarar da rigimar sultan,yanata kukan nemansa,yana ganin shigowarsa yatafi da gudu yarungumeshi yana kuka,toyi shiru tunda gani nadawo,meyasa kakeda rigimane baga mutane nanba a gidan,da muryar kuka sultan din yace to banaga kadadeba,karnaje wani ya daukemin kai yagudu dakai nadaina ganinka,uncle kana sona? Sosaima kuwa dan duk duniya kowa yasan ina sanka ,yami'ka masa ice cream yaruga da gudu yana murna,sai alokacin ya shiga dakin mommynsa tana bakin gado a xaune ,tace kai kuwa Abdul ina kaje kabarni da dan rigimarka waika6a,yaki ya xauna nace yanxo xaka dawo Amman yaki yadda yana yiwa mutane kuka, yace aina sallameshi ,nima mantawa nayi natafi nabarshi,tace saika dinga kiyayewa sbd halin rigimarsa,yace bara naje nayi wanka nadawo dan nasan Daddy yana hanya,tace yanxo yakirani yace yana gidan hajiyane jikintane inajin yatashi,yace batadai da kudine kawai kinsanta da shegen San kudin tsiya,tayi masa dakowa tace banasan sharri mata tana ciwonma baxaka rangwanta mataba,to ai shikenan mommy,kinsan dai bakarya nayiba,tace wayafika karya Abdul .

Dagudu yagice da alama dai yau yana cikin farincki,wanka yayi yasa kananun kaya,yace a kira masa sultan yayi masa me aikin yace ainayi masa haryayi bacci ,yace ya akayi ya yadda tace wayo nayi masa nace Kaine kace ayimasa sbd xaku tafi unguwa,shiyasa ya yadda ,yace shikenan inadai fatan yaci abinci sannan ya kwanta tace yaci abakima nabashi harya koshi ,yace ngd miki da yadda kike kularmin da yaro, tiki barshi a wajen ki inxan tafi xanbiyo natafi dashi, table yawuce yana bubbuda kwanikan abincin yace yaukuma tuwo akayi masa miyar agushi yaxuba yaci sosai ya kora da kayan marmari,ya mike yayi wajen mommy yana kwala mata kira,tace kai kuwa Abdul baka girma irin wannan kira haka,yace daman sallama xanyi miki danni yauda wuri xan kwanta,tace to Allah yatashemu lfy ,yayi 6angaren masu aiki,yabuga musu ,yace amiko masa sultan tace daka barshi tunda yayi barci yace a a baxan iyaba dan nafiso najishi a kusa dani tace to shikenan saida safe yace Allah yatashemu lfy,

Yana shiga dakin yasaka kayan bacci yasawa sultan suka kwanta saidai yakasa baccin ,sai kawai yajawo wayarsa yabude face book yadinga duba sakon da akaturumasa yadinga basu amsa hardai yagaji yakashe wayar dan yasan gobe xaiyi fitar wuri gakuma kai sultan school,

Sauri kawai nakeyi dan nasan nagama makara ga test din da yake gabana,ta Mlm Abdul, ina tahowa shikuma yana shiga daguduna nakarasa,yadakatar dani haka nadinga rokonsa dan Allah yabarni nashiga koda ban amsa dukaba Amman kamar badashi nake mgnaba saidaya fito ya gallamin wata muguwar hara,yace suda sukafito da safe aisunsan muhimmancin abin,ni daman cos dina metsadane,bakowane wawane yakeciga,dan haka kisa aranki duk jarabawar da xaki xauna kixanamin kinyi abanxa dan baxaki ta6aciba wawuya ballagaxa Mara kamun kai,yawuce yayi tafiyarsa ,sauran dalibai kuwa sai mgnar sukeyi,wasu suna ganin laifinane meyasa banasan xuwa da wuri,nadinga binsa mana ta yadda yakeso mana. Idai yauma a cikin bakin ciki nakoma gida,ita kanta umma tagane nayau yafi nakoyaushe ,yaune ranar farko datace meke damunki, banji kunyartaba nagaya mata duk abinda Abdul yakeyimin,tace to ni ina ruwana,ranar danasanima tana gaba,duk abinda namiji yayi adone a wajensa ita kuwa mace har jikokinta ,kin6ata rayuwarki dasan xuciya,tawuce daki tarabu dani,nikuwa kuka sosai nadingayi dan gabadaya duniyar taficemin aka,wani me yasa ba ayiwa mutum uxuri dan wata kaddarar tafada masa,ya Allah kakawomin sauki,agida banji dadiba,awajema ban hutaba,nadaga hannuna ina rokon Allah ya yafemin,idan wani laifi nayi bansaniba,ko abincin dare kasaci nayi sbda bakin cikin da yake raina,awajen umma badadi nakejiba shikuwa,Abba gaisuwace kawai take hadamu dashi ,hakurin duniya nabashi yaki hakura,kwana nayi INA kuka kodana tashi babu Wanda yatanbayeni abinda yake damuna ko me yasa idona yayija ba bansamu wannan gatanba,haka nashirya natafi makaranta,kodanaje Mlm Abdul kin barina yayi nashiga,magiyar duniya Amman yaki barina ,ni kuwa tsabar bakincikin da yake raina ga wani irin Cowan kai cikina ya murda darashin cin abincin da banyiba yasa nadinga kwara amai naruwa kawai,sukansu kawayena abin wabasu tsoro sosai, wasu sukace akaini gida wasu sukace akaini Asibiti,, Suns cikin takaddamar saiga malam Abdul ya kalleni yasha kunu yace meke damunki,kasa yimasa magana nayi sai kawai naga ya girgixa kansa, yace ke fauzee sakamun ita amota xankaita Asibiti, takamani takaini nakin motar Amman sainaki shiga,nace ngd anemarmin mota natafi gida,ya sha kunu yace fauxee kushiga mutafi,adolena nashiga,domin dishi -dishi nake gani,gashi har,a lkcin bandena amanba ,yawani tsayar damota afusace,ke da Allah karki lalatamin mota,komeyema bakece kikajawa kankiba,ko dan kinga natausaya miki,xan kaiki hospital nima kawai abinda nakesan sani,wani karamin Asibiti yakaini sai cewa yayi da fauxee ta xauna a nan yashiga dani,tace masa to kawai,inarike da cikina muka shige wajen likitan,suka gaisa da alama sundade da sanin juna,dai kawai jinayi yace dan Allah Dr dubamin yarinyarnan muke danmunta,Amman kafinnan inasan ayi mata test din fitsari muga meke damunta sai kawai Dr yace haba abokina mekake nufi daman kayi aurene bansaniba,aisai naga kamar budurwace,koka canja haline bansaniba,dai kawai yasha uku har yanxo inanan a yadda kasanni,kawai dai kayi abinda nace maka kona canja Asibiti, da Sauri likitan,yace a a yanxo xanyi muku,ya kalleni 'yan mata shiga cikin toilet dinnan kiyi fitsari a cikin wannan robar,ya mikomin,namike kawai nafice daga dakin inata kuka,Ashe abinda yake nufi dani kenan,ya Allah kayimin sakayyar gaggawa,da sauri yabiyuni ,kinsan bakida gaskiya da kinada ita kistaya mana,sai kawai nakoma nayi yadda likitan yace namika masa,agabana yaxaro wani dan tsinke ya tsoma acikin fitsarin yaxare ya kalleni yace da Mlm Abdul babu komai yace beyaddaba,yace wlh babu komai kasan baxan 6oyemakaba,yace toya dubani dan yaga nawahala sosai yabani makunguna yace nadainasa damuwa araina dan hawanjini yana gafda kamani.

Agida ya saukeni ,itakuma fauxee yawuce da ita makaranta wato daman Mlm Abdul yasanni kenan yake nuna besanniba,komadai meye susuka sani,dake fauxee bame surutu bace babu wanda tagayawa.

💖💖💖ZAZZAFAN RABO💖💖💖

Na Aisha Umar Indabawa

Marubuciyar littafin Meka Maidani💕💕💕

🤳typing🤳



🦚page 3🦚

Duk Wanda yatanbayeta sai tace daga Asibiti gida akayi da ita,sauran dalibai kuma sunxata tausayin da yake nunawa sauran dalibaine shiyasa yayimin hakan su basusan da shirinsaba niya kawai yayi yatuxartani,sai kuma Allah bebashi iko ba,ciwo sosai nayi sai danayi kusan sati biyu a kwance,Amman kullum sultan yana xuwa dubani,dan wani lokacin hardasu kayan dubiyarsa idan nace waye yasiyama yace kakawomin sai yace uncle mana kuma yace yanayi miki sannu harma da mommy nace to duk kace ngd,ina xaune da yamma a tsakar gida saigasu mommy da Mlm Abdul, da sultan anyi masa kwalliya yayi kyau sosai,Na mike da saurina inayiwa mommy sannu da xuwa mommy ce kawai ta amsa nagaishesu,shi kuwa kamar Wanda aka takurawannan yaxo wajena,mommy tadinga yimin nasiha akan nadaina sadamuwa a raina komai mewucewane,wataran sai lbr,ina hawaye nace ngd,ita kuwa umma ko kallan inda suke batayiba ni kuwa kallan kudin da suka ajiyemin kawai nakeyi. Da umma tafito daga daki nanuna mata kudin da suka ajiye,tacetunda San xuciya yasaki kar6a to ni inada wadatar xuciya,kuma Na iya ri'ke talaucina bana nema a wajen wani sai dai Allah, kedai da kikesan abin hannun wani sai dai nace Allah yashiryeki yasa kigane gaskiya ajiye kudin kawai nayi a wajen nashige daki naciga da aikin tunanin rayuwar duniya wai yaunice kamar banida iyaye banida mebani shawara ko idan wani abun yana damuna nagayawa wani nikam nayi bakin cikin xuwana duniya naso ace inada yayye mata Amman banidasu sai tarin maxa,kuma maxanma mutum dayane yake tausayina yake damuwa da damuwa,nikam rayuwa tagama ficemin araina,Allah dai yadawomin da ya yaxid kona gayamasa damuwata,dagyar nasamu naci abincin dare,dan nasan babu mecewa naci sai dai idan da yinwa xan kwana kadan naci nakwanta inajin umma da Abba sunata hirarsu harda dariya nidai nayi namo a daki,saiga umma nan tashigo da leda ta diremin a gabana,idan kingadama kidauka kici in kuma bakiga damaba kibarshi yalalace nidai banyi mata mgn ba Na sakko daga kan katifar nabude namane yaji kuli-kuli sai kanshine yake tashi naci sosai kuwa dan yayimin dadi sosai,namike naje gaban Abba nace angode Abba Allah yakara budi,ko kallona beyiba namike natafi Na kwanta Amman in kaina nasan bawani bacci xanyiba inajiyo hirarsu,har Abba yana cewa nifa xaman yarinyar nan yafara isata duk dadai yaxidu yadage sai tayi karatu,Amman nafiso tayi aure tacigaba a dakinta tace hakan yayi dai dai,inajinsu har bacci yadaukeni koda natashi da safe shirin mkranta nafara sbd nasan inada aiki a gabana gashi munkusa fara exam nayiwa umma sallama nafito a kofar gida naganshi shida sultan yayi shirin mkaranta da alama kaishi xaiyi yana ganina yataho da gudu ya rungumeni nadagashi nace katashi lfy ya gida yace lfy lau kinji saukine aunty xaki mkranta xumuje nace da uncle ya kaiki Na girgixa kai nace karku makarakaji yace to nace ayi karatu da yawa yace to ,nace to jeka kutafi yagarasa da gudunsa yana dagamin hannunsa sai danaxo daf dashi harnayi niyar gaisheshi kawai saina fasa sbd yanxo xanjawa kaina wata masifar sai jinsa nayi yace sultan karka sake kula wannan aunty tunda bata ganin darajar manya ko banci darajar Wanda yagirmetaba ai naci darajar malamin shi kuwa sultan cewa yakeyi nima baxan sake kulataba tunda bata kula uncle dina yace yauwa yaron kirki ,ina kallansa yamika masa hannu suka tafa yabude masa mota yashiga a bakin titi suka ganni sultan ya kautarda kansa,waishi irin yaji mgnar da aka gayamasa dabe hanashiba da idan yadinga kwalamin kira harsai nagaji nidama yadaina kulani gaba daya dana huta.

Daman umma basan xuwanshi takeyiba,yana sauke sultan yawuce mkranta abinka da motar haya harya rigani xuwa sai dai bashine da laccar farkoba ina murnar yau dayadai xansamu darasinsa Amman yana shigowa yace nafita koshi yafita yabarmin ajin sainayi musu abinda xaiyi musu nan da nan dalibai sukace basu yadda ba haka nafita ina kukan bakinciki shikuwa banda dariya babu abinda yakeyi kuka sosai nayi gaskiya nakusa daina xuwa wannan mkrantar tunda batada wani amfani a wajena ,Abdul yatsaneni narasa abinda nayi masa Amman xansamu lokaci nabashi hkr koya sauraramin axuciyata tayi saurin gargadina karna soma idan ba wani bala,in nake nemawa kainaba haka dai harya fito yaxo kaina yatsaya ni kuma nayi saurin sunkuyar da kaina yace kinsan wani abu Salwa natsaneki banta6a tsanar wani abuba kamar yadda natsaneki har bana kaunar nadaga kaina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login