Showing 6001 words to 9000 words out of 26260 words
Chapter 3 - Zazzafan Rabo Part 1 Complete Hausa Novel By Aisha Umar Indabawa.docx
nayi wai naxo yana kirana axuciyata tana bugawa nashiga office din ya kalleni koda ace baki fadaba ainasan kinada masu baki kudi bawai dani kika dogaraba,nidai nayi masa shiru koda yake aibabu me tuhumarki tunda agida kike taba barikinki Na dago idona da sauri nakalleshi yace ko karya nayi miki yasha kunu mace idan kagama inada laccar da xanshiga yanxo,koda acema kinxauna baci xakiyiba sai a shekarar karshe xan nunamiki nidin sunana Abdul Aziz nidai banyi mgnaba sai a lokacin nace dan Allah malam menayima katsaneni hk kayi hkr kabarni hakan in kuma da abinda nayima katsaneni kagayamini saina daina wlh kema kinsan laifinki a wajena dabaki aikata laifin danafi tsanaba da babu ruwana dake kinsan ni natsani dan iska kumake itace shiyasa natsaneki tsana kuma tahar abada karki ta6a tunanin xan 'kaunaceki nadago idona da sauri Na kallesa,yace tabbas abinda nafada gaskiyane ni daman haka nake kowa yasan irin tsanar da nayiwa wanda besan ciwan kansaba,tunda nidai nayarda da kaina nace ngd xan iya tafiya yace idan kinxauna uwar mexakiyimin,nafito inajin haushin abinda yayimin no kuwa xantayin addu,ar Allah yahadashi da mara kamunkai,tunda bashida aikin da yawuce aibata yaran jama,a idan Allah yabashi agidansa saimuga yadda xaiyi , muna bakin bishiya nida fauxee take cemin Salwa wlh lamarinki da Mlm Abdul mamaki yakebani kingadai shi bedamu darayuwar kowaba shidai kawai ayi karatu, shiyasa nake xargin akwai wani abunda yake tsakaninku,Na kalleta nace Amman kinbani mamaki kinsan ai yadda yatsaneni Amman har kikeyin wannan tunanin dan Allah karki sake yin wannan tunanin,a haka dai muka dinga hirar karatu har yakeyimin mitar rashin xuwa gidansu,nikuwa kullum ina hanyar xuwa inda kike nace yi hkr sai dai idan kinsake xuwa saiki yanbayi umma da kanki saitafi barina tace to ai kuwa wannan satin a gidanku xanyi, nace to Allah yasa tabarni tace amin,wajen axahar saiga fauxee nan nadinga murna sbd banida wata 'kawar da nakeso kamarta koda yake gaba day an 'yan matan layin basa Shiga harkata wai sunfi 'karfina basa shiga harkata sbd in "yar talakace,tace tafiyafa naxoyi dake nace nidin tace eh saikije kiyimana kwana biyu nace gakiga umma nan ai kinyi sa,ama Abba yana nan, tace yauwa shima xantanbaya,inajin suna fafatawa da Abba yanace mata Amman banda kwana tadinga magiya yace to shikenan banda yawo dan xai turo Abdul yagane masa abinda mukeyi tace babuma abinda xamuyi Abba, anacikin mgnar saiga malam Abdul muka gaisheshi ya amsa mana a yangance,yace da Abba lfy naganku a tsaye wai kawar salwace tace nabarta taje gidansu tayi kwana biyu,yasha kunu gaskiya ni Abba banyardaba saidai tayi kwatancen gidan gobe da safe nakaita da dare nadaukota Abba yace to kunji abinda yace ko,tace dan Allah Mlm Abdul yace kinsanni bana mgn biyu in nafada angama magana ki daiyi hkr sai wani lkcin,bata dadeba tace xata tafi narakata har bakin titi,tace gaskiya Salwa Mlm Abdul yana takura miki sai kace wani wanki ko kanin babanki,nace ni ai duk Abba ne yajamin sbd shine yace yabashi amanata bari kiga goben cewa xaiyi sai wani satin koma yahanani xuwa gaba daya,tace nidai gobe ina jira nace to Allah yasa mudace tace amin dana dawo daga rakata naganshi shida sultan ,sultan din yadinga kwalamin kira nayi masa banxa,inajin sa yana masifa wai babu Wanda yaisa yawulakanta masa yaro daman shine yasa shi yayimin mgn
💕💕💕ZAZZAFAN RABO💖💖💖
Na Aisha Umar Indabawa marubuciyar littafin Meka Maidani💖💖💖
🤳Typing🤳
🦚page 7🦚
Sadaukarwa
Na sadaukar da wannan littafin ga malaifiyata hjy Khadija Allah yajikanki yasa kin huta Allah yasa kina cikin makwanci me kyau amin ya Allah
Jinjina
Jinjina ta musanman ga masoyan wannan littafin ina godiya sosai sisters💗💗💗
Baxan manta dakuba "yan uwana Allah yabarmu tare Allah ya'kara hada kanmu ameen ya Allah .
Godiya ta musamman ga kanina kamal da irin kokarin da yake yi akan wannan littafin.
" wajen 'karfe goman safe ya turomin da karamar takadda wai idan ng dama nashirya da wuri ,Na cewa da sultan din yace masa to kawai ,nayi shirina a tsanake nayi kwalliya sosai doguwar rigar shadda nasa naci daurina ni kaina nasan nayi kyau sosai,sultan yashigo da gudunsa aunty wai kixo mutafi nace to,nayiwa umma sallama tayimin nasihar na kare mutuncina nace to,ina fitowa yakafamin ido har saida naji kunya Na sunkuyar da kaina ,Na gaisheshi sai cemin yayi daban kwana ba kin gani sai kawai nayi shiru danni wani abun nasa yadaina bani haushi saidai yabani dariya duk lokacin dana dago kaina sainaga yana kallona ta mudubin motar ni kuwa nasha kunu,tafiya mukeyi ta kurame sai can kuma yace su Salwa xa,aci dadi xa,a tauna 'kashin kaji gaskiya ke dai me kwadayice daga ganin yarinya "yar masu kudi kinbi kin nace nata dan Allah Salwa ki daina irin wannan halin ,sultan yace uncle dan Allah kakaini gidansu aunty me kyau tabani alawar da take bani kasan ita tanasona Aunty uwa bata sona ai kamace karna sake kulata ko ,kumafa uncle ina Santa ,yace lalala baruwana da sultan dina kawo hannunka mukwance munyi fada,yace yi hkr dan Allah uncle nadaina Santa yace halintane banasan kayi kaga ita mekwadayice kaima kuma tafara koyama meye bana siyama da kakesan alawar gidansu babyna karka sake kaji danfa kai nake Neman kudin nan ,to yi hkr uncle mudaura munyifa alkawari baxamu sake yin fadaba yace to ai kaine kajawo ,kagani banasan Salwa kai kuma kanasanta to nadaina santa uncle ,in fada baxamuyi fadaba eh inajinka aunty Salwa tafi dayar aunty kyau mudaina xuwa wajen waccan mudinga xuwa wajen aunty salwa ,saiyasa masa kukan karya wayyo yarona nafisan waccan antin tafi tarbiya wannan batada kamunkai,toyi shiru uncle dina baxan sake ba to nayi suka wani tafa sukasa dariya saikace abokan juna ni kuwa haryasani nafara hawayen bakinciki yace ke kiyi mata waya kice mun 'karaso ,nadaga wayar nagaya mata tace to bara nafito ina cikin motar ta'karaso nafito nace ngd yace bana bu'kata,fauxee ta gaisheshi ya amsa dagyar ,salwa naji ankirani ungo wannan ledar kikai musu tsaraba sauran kuma kinuna musu halin rashin kamun kanki nace ngd kawai ,muna shiga gidan tamkar ansanni suka dinga murna kowa kuma yasan sunana tundaga kofar gidan nasan su fauxee masu kudine sosai ,takaini nagaida mommynsu na mi'ka mata tsarabar nace inji ummanmu ta bude turarurrurukan wutane masu kanshi sosai ko a ina yasamoshi oho tace ngd sosai salwa kiyi mata gdy nace to, dakin fauxee ma kawai abin kallone nidai haka nadinga kalle kalle sai kace wata "yar kauye ,muka dinga hira sosai nasake a gidan tamkar gidanmu ,lkcin cin abincin rana yayi tace Salwa xomuje kan table muci abinci nace nakoshi ,taja hannuna muna xuwa sai kunya ta kamani sbd harda yayansu namiji ,ya kalli fauxee yace sister axuba dani dan kinsan tare mukeci ta kalleni tace ya Muhammad yaufa nayi bakuwa yace to meye ai itama 'kanwatace,tace ai salwa kunyace da ita,mommy dai dataga nakasa sakewa saitace da fauxee mutafi dakinta ko acandinma kadan naci sbd kunya kuma nadinga tuno abinda Mlm Abdul yacemin sai nake ganin kamar yana gabana,bayan la,asar naga sabuwar number ankirani da ita nadaga da sallama ,akacemin idan kinga dama ina waje ina jiranki nace masa to,nace salwa Mlm Abdul yana wajefa tace naxata mune xamu maidake da daddare nace tabdijan aiga kanin babata yaxo duk mukasa dariya,takaini wajen mommy mayimata sallama tabani kaya a leda nayi gdy muka fito bakin motar tasa,saiga ya Muhammad nan yace to kanwata sai kuma yaushe sai kawai nasa dariya ,yace Mlm Abdul barka da yamma ya hidimar 'kannanmu yace kashinan muna fama suka dinga hira kamar sunsan juna ,yaciro kudi a aljihun wandansa yace to gashi 'kanwata nace kabarshi yace to bara nabawa yayanki ya ajiyemiki yasako cikin motar,yaci uban kwalliya da kananun kaya, yayi kyau sosai ,niko "yar mutan Indabawa nace salwa kodai kin yabane🤪 har munfara tafiya yatsayar da motar yace waye direbanki nabude motar nakoma baga,yace salwa gayamin medame kikaci nace babu komai sai nakoma gida yasa dariya yace salwa 'kawata dasauri nadago idona nakalleshi ,naga munata tafiya ba hanyar gida mukayiba nace ya Abdul ina xamu ,yace saidake xanyi sbd nagaji da ganin ki ,nace dan Allah kamaidani gida umma xata yimin fada ,yace muna taren salwa nasan abinda kike nufi nafi karfin nayi wani abun dake niba dan iska bane irinki ,kekoda inayima nafi 'karfin nayi dake wlh ,nace ainaga samarin yanxo basuda amana ne yace ya isheki ni nafi karfinki daga haka yasha kunu sai dai yaxubamin ido ko canjamasa nayi oho masa.
Wani 'katun gida muka nufa yayi hon din motarsa megadi yataho a guje yabude masa get sai wani kirari yakeyi masa shikuma yana dariya, yace inafatan sweetheart din tawa tananan ,yace ai kasan bafita sukeyiba sbd yana yin alhajinsu,yace ai yanada kyau hakan,ya kalleni fito karki yimin sata a mota ,kuma wlh sauran ki kunuatani a gidan surukaina kinga yarinyarnan ita xan aira nayi murmushi me ciwo ,naja gefe Na tsaya,megadin ya dawo yace tana xuwa ,bata wani dadeba tafito cikin shigar mutumci tace barka da xuwa ya Abdul yace barkanki dai ya gida dasu hjy tace kowa lfy ,tace xuwa babu bayani yace wayarki a kashe tace tabbas tace ina yarona yace yana gida yace agaisheki,yace to mushiga daga ciki mana yace a a sauri nakeyi sbd muna tare da bakuwa tace tana ina yace gatacan a tsaye tanasamin ido sbd munafinci tayi dariya tace kai ya Abdul tace bara nashiga da ita ciki yace a a bawatafa me mihimmanci ce ba me aikin mommy ce tace wannan din yayi dariya kawai ,taje inda nake tace taho muje ciki nace a a nanma ya isa,inajin yana cewa rabu da ita tayiwa kanta,naji haushin abinda yayimin sosai haka tarabu dani ,suka cigaba da hirarsu suna dariya sai dasukayi sallama tace min tana xuwa tashige gida ni kuma harna shige motar,tamikomi mai abu aleda tace abawa,'kanwarmu duk da bansan sunantaba yace salwa kenan,yadinga gdy muka fito daga gidan run,a mota yafara yimin mitar wai ban iya gdy ba ,Amman tunda naga tafito da Leda a nake kallanta nidai nayi masa banxa dan banida abin cewa ,muna tafiya yatsayar da motar a wani wajen saida kaxa yayi leda biyu yace gashi in temaka miki ,ki daina yawan bin gidan 'kawaye sbd kaji,ni kuma nayi miki al'kawarin kullum xan saimiki kici inda xaki daina kwadayi ,shiyasa nakaiki gidansu Islam kici dadi ya isheki sai kikayiwa kanki nidai bankulashiba,har kofar gida yakawoni yamikomin ledar da suka bani data kaxata ko kallan inda nake banyiba nashige wata gida ,besan yagama 'kolar daniba yamayar dani wata mayya ,duk damu talakawane Amman Abba yana iya bakin 'kokarinsa,dan duk tsiya bama miya lami,bandade dashiga gidaba ya biyoni da sallamarsa,yace ga kayanki salwa ,yace kinga umma nakai salwa gidansu wadda xan aura itacema tabani wannan kayan tace abata,to Amman salwa taki kar6a ko rainawa tayi wlh laifinane daban gayamataba xamuxo da 'kanwataba,umma tace sai kace ajiya tabata kace angode Allah yabar xumunci ,yace amin umma,yace ga kudin ki har ina meman namanta ko akansa kikeyin fushin mantawa nayi salwa baxan gudu dasuba in kinaso saina 'kara miki,umma tace kaima dai Abdul kadaina biyemata yace to umma bakisan yadda nakeji da salwabane shiyasa ni kuwa nace munafiki yayiwa umma sallama ya tafi,daman ni tun ina 'karamata ya tsaneni idan aka aikeni gidansu kuwa yadinga tanbayata kenan wai naxo munafinci ko abu nata6a saiya sakominshi a Leda wai natafi dashi tun banganeba harna gane kuma niba meyawan surutuba bare nagayawa wani agida ,umma tabude ledarda msmans fauxee tabani mayafine mekyau da kuma kayan kwalliya sai budurwar Abdul ita kuma atamfa da kudi dubu biyu,umma tace to angode sai kaxar da Abdul yasaimin nace da umma ni banaci danni a 'koshe nake ,Amman idan angama tuwan dare xanci tayi tayi dani nakici danni ko sha,awa batabaniba ,washe gari da daddare yaro yaxo wai ana kiran salwa nace ace bananan umma tace a a kije mana saidai idan kinga irin "yan iskannan ne kidawo abinki ,nace to abakin motarsa naganshi yace sannu malama salwa nidai naxo wajenkine ina sanki domin da gaske nakeyi ina ganinkine idan xaki tafi mkranta nace madallah,idan mundai daita xanturo magabatana kallan farko da nayi masa naji be kwantaminba to Amman dan kar abinda akecemin yabini natsaya dashi wai nayi kwantai tun ana xuwa wajena har andaina sbd indai anxo neman airena sai ansami minafikin da yarushe mgnar,mukayi sallama ya tafi ni kuma nashege gida umma tace toya kika ganshi nace aiba a ganewa yanxo tace to Allah yatemekemu,nace amin,sultan yashigo da gudu yana cewa aunty wai kixo inji abokin uncle nace kace bananan yaran yatafi yagayamasa yace yace dan Allah kixo yanxo xaki koma sako kawai xaki kar6a umma tace jeki salwa ,nafita muka gaisa yace gashi inji Abdul yace da takadda a ciki nace masa to,takardar nafara dubawa kiyi hkr me kwadayi mantawa nayi jiya aci dadi lfy,Amman aguji cin nasamari dan yanxo duniyar sai a hankali dan nagake idan kinga nama tamkar mayya kike,dan wlh danasan abinda xantarar kenan daban kar6aba na mikawa umma nace ni nakoshi tace to angode taxubawa sultan yace yakoshi shima uncle yasiya masa kuma yace yadaina 'kwadayi tace to ainan gida Amman yaki kar6a ni kuma umma tace nadaina bakin hali sultan ya yiwa umma sallama yatafi tadinga yabonsa wai Abdul ya iya tarbiyya sosai sai dai Allah yasaka masa da alkairi.
Kodaya koma sai cewa yayi Aunty taci abinda nakaimata yace duk abinda kake kai mata bataci umma tayitayi mata fada ,nima kuma da aka bani nace nakoshi yace meyasa yarona ai banda ganinka yace ai Allah yana ganina kuma kahanani yace yauwa yarona suka tafa suna dariya, yace uncle waini ina mommy na ,kowa tanada ita Amman bandani yace to baganiba mommynka ta mutu kuma kasan idan mutum ya mutu bayadawowa ko yace hakane ko inayi maka wani abunne Wanda bakaso yace kawai dai a school ne sai adinga cemin wai banida mommy komai saidai mace uncle yace to kayi hkr kadinga yimata addu,ar Allah yashiryeta ,yace kai uncle bafa haka akecewaba cewa akeyi Allah yaji'kan mutum yace auna manta taho mutafi masallaci yace to uncle daganan nakaika gidan aunty ya dinga murna,saida yayi masa wanka ya shiryashi sukayi kwalliya sannan sukayi wajen mommy tace sai ina sultan yace unguwa xamu tace sultan xumu xauna yace a a tace nima bana nema nidai wannan shakuwa taku Allah yabarku tare yace amin mommy, gidansu Islam suka nufa tadinga murna tajashi daki ta hadamasa kayan dadi Amman yaron yaki ta6awa wai uncle ya hanashi tayi tayi dashi Amman yakicin komai ,har saida tamayar dashi wajen uncle dinsa saida Abdul din yafara ta6a abinda aka kawomasa sannan shima yaci ,tace ni wayon sultan har mamaki yake bani ,Amman nasan yanada kokari a school ko,yace sosaima ai renonane tadaya yake dauka idan yayimin tabiyu ai nayimasa duka,koyarona ya gyadamasa kai, tace ainaga kunaji da sultan yace badoleba ,yana dan yayana guda danakeji dashi kuma dan kuwana dana rasa arayuwata tace mutuwa yayi ya daga matakai shikuma ya sunkuyar da kansa yana hawaye tace kayi hkr tace ina mamansa yace tana nan tace Amman bata garinnanko yace tananan bedai santabane sbd nema sukeyi surabani dashi shiyasa nace masa ta mutu tace tabdijan to Allah yajikansa yace ameen ,shifa besan kowa ba idan baniba banasan nasamasa tunanin bani nahaifeshiba tace Allah yatayaka riko yace amin duk wannan hirar da akeyi yana can wani gefen garinnan ko.
💖💖💖💖ZAZZAFAN RABO💗💗💗
Na Aisha Umar Indabawa marubuciyar littafin Meka Maidani💗💗💗
🤳typing🤳
🦚page 8 🦚
Hira sosai sukasha har yake cemata yakamatafa manyafa sushiga maganar nan dan wlh namatso ayi komai agama ,tace aikasan halin Abba ,yace to nifa aure nakeso tarufe fuska tana dariya,tace to kacire wannan a ranka danni sai naje Jami,a kuma kasan ra,ayin Abba kenan,tace mudaiyi hkr har lokacin yayi ,yace to anyi tayi dariya shi kuma ya kashe mata ido duk sukasa dariya,hidima sosai tayiwa sultan dan harda kayan sawa kamar tasan da xuwansu ,yadinga gdy ,tace dan nayiwa sultan abu sai kayimin gdy ai nima yaronane,haka dai suka rabu cikin farin ciki sultan yadinga yi masa tanbayoyi yana bashi amsa,Abdul yace sultan kanasan wannan auntyn ,yace tanada kirki Amman nafisan waccan ,Abdul yayi shiru sultan ya kalleshi yaga yasha kunu sai kawai yafara kuka Dan Allah uncle kayi hkr baxan dakeba,yace to Meka yimin to ni babu abinda kayimin yamiko masa hannu to mutafa,yana share hawayensa yamiko hannunsa, kasanfa banasan kukanka ko nima nayi kukan yace a a uncle, yace mutsaya musiyi ice cream din ko muwuce gida,yace nifa nasha a wajen Aunty kuma nakoshi yace aikoda safe kasha,suka tsaya akasai masa suka wuce gida,wanka kawai yasake yi masa shima yayi suka kwanta,ya kalli yaron haryayi bacci,yace gaskiya inasan sultan danni yara basu dameniba sai akan sultan, tunda aka haifeshi naji San yaron a xuciya ta ,yasake gyara masa kwanciya,yace Allah karka bani yaron kaina daxan fifitashi da sultan, yadaga hannunsa yana addu,a yana hawaye sbd tunuwa da dan uwansa,sannan ya kwanta har bacci yayi gaba dashi,da safe saida yagama yiwayaron komai nashirin school sannan suka fito sukayi wajen mommy suka gaisheta sannan sukayi wajen daddy yana dariya yake amsawa,yace idan anga wata xa,aga xara ,yace toya boy din naka komai dai lfy ko yace lfy lau daddy,yace wajen aikin fa yace komai nomal daddy yace to masha Allah, yace bara muyi sauri sbd kar sultan yamakara yace to Allah yabada sa,a yace amin,kan table suka nufa suka karya a gaggauce suka meke suka yiwa mommy sallama ,bakin get suka nufa inda ya ajiye motarsa yaxubawa sultan din komai a mota,sannan yafita da motar yace jikace aunty tayi sauri tafito mutafi,da gudunsa yanufi gidan daman tashirya shidin take jira,tayiwa umma sallama haryaxo da motar kofar gidan shiga kawai tayi suka tafi,dagyar ta gaisheshi ya amsa mata a ta'kaice,sultan daya gaisheta sai kawai tashareshi,sai yace
