Showing 1 words to 3000 words out of 54616 words

Chapter 1 - MANSURAT Book Complete by Mimi Queen .txt

MANSURAT
HAUSA NOVELS






_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.


Allah bani ikon fad'an daidai, yanda na fara lafiya Allah sa na qare haka.
Wannan book din ba qirqirarran labari bane abune daya faru da gaske da kuma qawata na jikina dan haka wannan littafin true life ne dan Allah a guje zargi da yad'a labaran qarya, duk wacce ta zageni ni na yafemata duniya da lahira ina rokon nima duk wacce nayima ba daidaiba cikin sani ko akasin haka data yafemin dan ubangijinmu me yafiyane kuma yanasan me yafiya.










































1&2.




....."Wawuya jaka mara hankali....."
Yafad'i sakamakon ruwan lemun da yarinyar dake tsaye ta watsa mishi suna tsaka da party shida abokanshi, tana sanye da bakin hijabi har kasa daya rufe har takalmin kafanta, gefen fuskarta nake hangowa, farace sosai tana sanye da farin eye glasses, gashin idanunta bakin kirin dogaye, lips dinta kananu sunyi pink sosai sun bushe


Qaton Cake din dake gabanshi da alama birthday dinshi akeyi duba da irin kyau da shigan da yayi duk dashi ma'abocin adone ako da yaushe daga gani gayen yayi bala'in waye wa kuma ya had'u ta ko ina baya da makusa domin da waye wa da kyau kesa a shiga Aljannah sae dae nace yayi sa'a.




Gaba daya ta dauka cake din ta watsa mishi a fuska gaba d'aya mutanen dake gurin suka miqe cikin mamaki, hannu yasa ya fizgota se lokacin nasamu daman ganinta sosai doguwar mace ce kyaykyawan gaske, fara ce fat kana ganinta kaga fulanin usul, tana sanye da fararen eyeglass idanunta ba kwalli saidai eyeliner dataja a saman ido dayama idanun wani irin cool kyau, giranta acike da gashi, gashin bakin kirin, sai dogon hancinta da dan karamin bakinta daya bushe, black hijabi ne jikinta wanda hulanshi ya rufe goshinta sosai dan saura kadan ma yarufe giranta amma dudda haka kana hango kwantaccen gashi a forehead dinta, dogon hijabi ne ajikinta dahar kafafunta ya rufe bama ka hango asalin kayan datasaka.


























































Tasss taji saukan Mari a kuncinta ya daga hannu da nufin kara marinta tayi saurin sa hannu ta tare cikeda fushi da tsananin tsana tace. "Karka kuskura hannunka ya kara ta'ba jikina inba hakaba zaka sha mamakin abinda zan maka....."
Wani irin 6ari jikin sa keyi idanuwan sa sukayi jajir sbd tsananin 6acin rai yace. "Ke... Ni kike cewa zansha mamaki abinda zakimin...."


"Kai waye da bazan ce maka hakaba sakarai kome....look lemme tell you one thing *ARYAN* I hate u
I hate u i am absolutely hate u bagidaje kawai wanda bai san abinda yakeba sakarai......"
Karfinta tasa ta turashi kan cakes din ta juya ko a jikinta ta wuce.






































































Tana shiga falon tasaki kuka, Mommy dake zaune ta tashi da sauri. " _MANSURAT_ meya faru keda Dikko ne ko....? "


Batareda taba Mommy amsaba tayi ciki da gudu tana kuka,


da sauri ta zare hijabin ta ijiye akan gadon, kyaykyawan yarinya ce Mansurat bana wasaba, gawani irin shape da Allah yamata mai bala'in kyau tana sanye cikin simple riga da skirt na wani poker dot silk material skirt din yabi jikinta yafito da fine curve hip dinta rigan ma yakamata yay mata shegen kyau, kitson shiku ne akanta manya manya dabaza su wuce guda gomaba, gashinta dogon gaske gashi ya kwanta akan goshinta sosai, babu dan kunne a kunenta,looking naturally beautiful, sake goge hawayen daya zubo mata tayi mommy data biyota tace "Ya isa kukan haka wuce kije kiyo wankan ki kinji Mansu zanyi magana da Dikkon. " gyadamata kai tayi ta wuce tabude bayi ta shiga.






































































Shikam DrAryan rasa abinda zeyi yayi dan Mansu tayi dizgin dinshi a gaban friends dinshi na qasa Nigeria dana waje, tashi yayi daga party covet din yayi part dinshi yana shiga ya zauna kan cushion yanajin zuciyarshi namai zafi kud'i me dinbin yawa ya kashe dan birthday dinshi amma gayinan jakar yarinyar nan da yafi tsana duk duniya ta 'bata mishi dole se yayi maganinta, Atif abokin shine ya shigo. "Dr mutanefa suna jira ka fito a yanka cake......"
Se Lokacin ya tuna da fuskarshi da Mansu ta 'bata da cake, tashi yayi ya shiga bedroom gaban mirrow ya tsaya yana kallon yanda ta 'bata mishi cute face da cake, hannu yasa da karfi ya kaima mirrown naushi nan danan mirron ya fashe, cikin tsawa yace. "Get out from here Atif kaje ka sallami kowa an fasa yin party din....."
Jikin Atif na rawa ya fice dan yasa halin abokin nashi in ranshi ya 'baci.


". I hate yhu dole se na dau fansa Dr. Aryan Sameer Simran baya barin bashi I must consent revenge........" Idanuwanshi sunyi jajawur duk duniya ba wacce yakejin ya tsana sama da Mansu bacin su Mommy da tuni ya kashe yarinyar dan da tsanan yarinyar aka haifeshi.


Bangaren Mansu hakane itama ba wanda ta tsana sama da Aryan dan da tsananshi ta taso.






















































Toh fa yanzu aka fara.


Mimi queen.
2022-09-10, 7:07 a.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._
















































_____________________________________


Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.


3&4.


. "Damn it I will kill her saina kasheta......


Tsaye Farhan yayi bakin kofa yana kallon yayan nashi dake fadin seya kasheta ko ba'a fadaba yasan rigiman nasu be wuce da Mansu,
Cikin sand'a ya karisa bakin bed din yakai hannu a hankali ya taba Aryan,


A fusace ya dago tareda raruman fasasshen glass din mirron daya fasa yayi kan Farhan a firgice Farhan yayi baya ganin yanayin dan uwan nashi,
Idanunshi sunyi jajir as usually yanda sukeyi in yana cikin tsananin bacin rai.
















































































Runtse ido yayi ganin Farhan ne cikin cool voice yace. "Am Sorry please forgive me I don't know what got in to my head am sorry okey....."


Kwafa Farhan yayi. "Ka dinga control din fushinka bro have you forgotten what mommy always told you about your anger issue eh ya..."


Shiru Aryan yayi kafin Farhan yace. "Okh naji kana cewa u will kill her wazaka kashe eh bro dama likitoci ba ceton rai kadai suke yiba harda kashe rai....? " hararanshi Aryan yayi, murmushi Farhan yayi. "Bro ya birthday din hope yayi nice....?"


Bata rai yayi da sauri tunawa da abinda ya faru da yayi, lura da hakan da Farhan yayine yasan wani abu ya faru dan haka yace "Let go Daddy ya dawo..."


Qin tashi Aryan yayi hakan yasa ya janyo hannunshi. "Let go jor...."


Ya jashi suka fice.


Mommy da Daddy suka samu a dinning
wani kallo daddy yabishi dashi wanda daga gani yasan na tuhuma ne karisawa sukayi dukkansu tareda gaida daddy, be amsaba ya dauke kai,


Daidai lokacin Mansu ta sauko tayi wanka ta canza shige zuwa doguwar rigar abaya brown as usual tana maqale da eye glass dinta sakamakon kananun idon da Allah ya bata ba komai take gani sosaiba,


Wani kallon tsana Aryan ya bita dashi harta kariso kallo guda ta mishi ta sakinmai mugun harara ta dauke kai taja kujera kusa da Farhan ta zauna tana gaida daddy.


Cikin fara'a ya amsa, cikin fushi Aryan ya miqe ze bar gun daddy yayi saurin cewa. "Dikko dawo ka zauna.."


















































Cikin bacin rai ya dawo se wani daddaurewa yakeyi, daddy yace. "Mansu yi serving daddynki tun dazu ke muke jira.. "
Murmushi tayi ta bude warmer din abincin da tayi inda kamshi ya bude falon,


Daddy da mommy ta zuba mawa se Farhan ta zuba nata ta maida warmer din ta rufe, daddyne yace. "Bazaki zubawa yayanki Dikko ba.......
Tunkan tayi wani action Aryan yace cikin isa. "Allah kyauta daddy naci kazantar wannan kazamar yarinyar...."


Mommyne tace. "Dikko meyasa kake haka..... "
Daddyne ya katseta ta hanyar fadi...."wai wai wai this a disaster tasty food gaskiya my daughter kin iya girki my baby is now a big girl se aure gaskiya u deserve a reward....... "


Hannu yasa a aljihu ya ciro vanilla chocolate gudu biyu manya ya miqa mata, hannu biyu ta amsa cikin murna tana godiya, kafin yace. "Nakine karki sanma kowa ko Farhan karkiba naga yana hadiye miyau the only Princess in my house..."
Farhan ne yace. "Daddy kafisan Mansu duk gidan nan harkasa nafara jealous....."
Dariya Mansu tayi. "Lol am only princess in dis house....." tamai kwalo


Daddy na dariya yace. "Forget duk brothers dinki are kobo u are d only naira in my life oya laugh kinji......"












































































Tashi Aryan yayi tareda ture kujeran dinning din da karfi ya bar gun, dukkansu ido suka bishi dashi harda Mansu dake murmushin jin dadin maganan daddy,


Karan fitan mota sukaji da gudu alamun yabar gidan, ijiyar zuciya mommy ta sauke tareda duban Farhan. "Farhan ka gama ka maida Mansu gida tunda d'an mulkin yayi tafiyanshi......"


Ijiyan zuciya Mansu ta sauke ta gode Allah da ba'ace tabi Aryan ba dan tasan zataci ubanta a hannunshi yanda ta bata mishi rai yau.




Seda suka gama a tsanake sannan tamasu daddy sallama Farhan ya dauki key din motanshi sukayi parking lot nagidan.


Gaban motanshi kirar kia Lamborghini ta bude ta shiga gurin me zaman banza, ya shiga mazaunin driver yaja sukabar gidan.












































Barnawa complex
Suka nufa suna fira suna kwasan dariya,


Horn yayi a makeken gate din gidan aka bude ya shiga yayi parking kusa da motan Aryan, fitowa sukayi suka yi cikin gidan suna dariya,


Batareda ta luraba taji ta bangaje mutum har glass din idanta ya fadi kallon kallo suka tsaya yiwa juna wanda ke nuna tsananin tsana, Farhan ne ya duka ya dauko mata tareda fadin. "Let go in baby gurl...." hararanshi Aryan yayi yaja hannun Mansu sukayi gaba.




Ayya na zaune akan kujera baccima yafara daukanta, sedai taji Farhan na fadin. "Tsohuwa me ran karfe bude idonki ga sarki me jiran gado yazo......"
Bude tsofaffun idanunta tayi tana fadin."wannan yaron bakada hali duk mugun halin Dikko kai kamaso ka fishi...."
Murmushi Farhan yayi. "Ai nidin kenan...."
Mansu ne tace. "Ayya na dawo..."










































Murza ido tayi. "Se yanzu kikaga daman dawowa. "
. "Ayya mommy cefa tace na jira daddy ya dawo... "


"Uhmmm ni jeki girkamin wani abu yunwa nakeji sosai..."


Farhan ne yace.."Yanzu tsohuwa girkinma bazaki iyaba se Mansu ta dawo zata miki gaskiya kin kusa tafiya...."


Throw pillow na cushion ta dauka tajefeshi dashi. "Kajimin ja'irin yaro inna kusa tafiya ubanka ma haka...."
"Haba aini ubana ba yanzuba seya aurar dani kuma ai kin fishi kwararra'bewa....."
Wani pillon ta dauka ta jefamai ya kauce da sauri tareda fadin. "Mansu kidan hadomin black tea Kinji kanwata.... "


Wani kallo ta mishi. "Saboda na zama kuku dinka ni Ayya kadai nakema girki ba qato ba...."
Dariya Farhan yayi. "Yarinya man kaza ai naji ni qatone saboda ni sama dakene.... "


Hamma Ayya tayi tana fadin. "Mansu ki kawomin Pepe chicken din da kikamin dazu...."
Da sauri tace. "Ki bari Farhan ya tafi saboda kinsan acicine...."


Riqe haba Farhan yayi. "Black belly kawai saboda karnaci to kuma se naci...."


Dariya tayi. "Aini namafi black belly white belly nake...."


Kitchen ta shige,
Farhan ya dubi Ayya cikin mamaki. "Ohh wai tsohuwama tasan dadi ta iya kwadayi..."
Pillow ta dauka ta sake jefanshi dashi tana fadin. "Dan ubanka zoka barmin gidana....."


Mansu bata jimaba ta fito tama Ayya faten arish, ta d'auro a plate tareda Pepe chicken din, a glass cup ta zubo black tea din ta turamai. "Gashi naughty spoiled brat kawai....."






















































"Kaikai kai nine spoiled bra? black belly kawai dan karna shane kuma wallahi sena sha....."


Daki ta shige tana dariya.


Mimi queen.
2022-09-12, 8:23 p.m. - ~Mimi~🥰😍: *MANSURAT*


_Daga Alƙalamin_🖊️
Haleema Isah (Mimi Queen)


Marubuciyar:
Rayuwa Sai dakee.
Labarina.
Barrister Shulaifat.
Son Zuciya.
Nisful hayat.
And now on _MANSURAT_






















































*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION📚🖊️ M.W.A*


_Ƙungiya ɗaya tamkar da dubu. Masu nazari da aiki da ilimi, burin ƙungiyar a koda yaushe shi ne ta faɗakar, ilmantar tare nishaɗantar da makarantanta._








































Wannan book din Sadaukar wane gareki My real Fans Ummin Yahzeed (Mansurat), wanda sanadinki aka samo sunan wannan book din wato.. _MANSURAT_
Alherin Allah ya same ki a duk inda zaki kasance.


Book din MANSURAT gaba d'ayanshi nakine se wanda kikaga dama ze karanta 😁.




Bismillahir rahmanir raheem.


5&6.


_Asalin labari_


Alhaji Muhammad Simran haifaffan garin maiduguri ne cikakken kanuri shi kadai iyayenshi suka mallaka a duniya, yayi karatu me zurfi boko da arabi, cikakken ma'aikacine na gomnati anan garin maiduguri ya hadu da zinatu wacce ake kira da Ayya bayan sun amince da juna sukayi aure suka tare a garin kaduna garin gwamna.


Basu jimaba Allah ya basu karuwa Ayya ta haifi Sameer wato daddy, seda Sameer ya kusa shekaru takwas sannan Ayya tasake haihuwa ta haifi 'ya mace wacce aka samata suna Fatima,
Daga kan fatima Ayya bata sake haihuwaba.




















































Shima Sameer su Ayya sun bashi tarbiyya da ilimi fannin arabi da boko har Allah yasa ya kammala karatunshi kaf a lokacin Allah yayiwa mahaifinsu rasuwa sunji mutuwan sosai .


Sameer ya rike mukamai da dama ta fannin siyasa,yayi mulkin siyasa state rep sau daya,house of rep a abuja har sau uku,senator sau daya,ya rike minister sau 2,yanzu haka ambassador ne na Nigeria a Russia.


A kaduna ya auri maryam wacce suke zaman lafiya da Ayya da kuma kanwarshi Fatima wacce yake mutuwan so kuma itama maryam nasan Fatima sosai.


Fatima batayi wani karatu me zurfiba ta nuna aure takeso hakan yasa Alhaji Sameer be matsa mataba dan yanasan farin cikinta yace ta fito da wanda takeso, wani Muhammad ta kawo wanda asalinsu fulanin Cameroon ne amma yana lecturing a ABU zaria dan haka acan yake zaune.


Bayan dogon bincike suka aminta dashi akayi aure inda suka tare a Zaria.


Ita kuma a daidai lokacin Maryam ta haifi danta namiji me matukar kama da mahaifinshi wanda aka sawa Aryan suna kiranshi da Dikko sakamakon zuciyanshi da miskilancin shi.












































Fatima ma suna zaune lafiya ita da mijinta kuma yana nuna mata kauna sosai.


Aryan nada four years maryam ta sake haihuwa ta haifi Farhan, wanda Aryan yataso a miskilance ga nuna iko da isa duk da yasamu ilimi da tarbiyya sosai,


Farhan nada shekaru goma mommy tasake haihuwa ta haifi me sunan Ayya da suke kira da Angel,


Angle nada shekaru uku Fatima ta haifi 'yarta mace kyakykywan gaske me matukar kama da mahaifinta wacce taci suna MANSURAT mahaifiyanta na mutuwan santa, ta haifeta da shekaru uku Allah ya mata rasuwa ba wanda beji mutuwan taba, hakan yasa mommyce ta dauketa taci gaba da kula da ita lokacin shekarun Angle shida, Mansu Allah ya bata kananun idanu wanda yasa bata gane abu daga nesa kuma in rubutu ya cika kananu bata ganewa hakan yasa tun tana karama aka yanko mata medicated glass wanda dashi take amfani.
























































Yarinyar ta shiga ran kowa sosai angle da farhan suke nuna mata soyayya ba wanda besan yarinyar wani soyayya suke mata sosai kowa ke bata kulawa hakan yasa shikuma Aryan yaji ya tsani yarinyar baya santa, a lokacin ko falo ya shiga yaganta ya dinga zare mata ido kenan harse tafara kuka,


Tanada shekaru biyar Allah yayiwa mahaifinta rasuwa ba wanda beji ya kara tausaya mataba amma badda Aryan sema tsanan yarinyar da yaji ya'karaji.
Saboda tsanan da yake yiwa Mansu yasa ya tattara yabar gidansu yakoma gidan Ayya da zama dan dai karda ya dinga ganinta Mansu tun batasan meye tsana da soba harta fara fahimta hakan yasa itama ta taso bata kaunar Aryan saboda ta gane tsana yake nuna mata


Lokacin tana primary school shikuma ya tafi India danyin karatun doctor,
































































Koda ya dawo lokacin Mansu na Queen Amina boarding school anan garin kadunan tana jss3 ya taras ta koma gidan Ayya wanda besan dalilin hakanba ranshi yayi mugun 'baci yaso yabar gidan yakoma gida amma daddy yace bada miyan shiba in Aryan yaga yabar gidan sedai aure yayi bakin ciki kan bakin ciki domin a gidan haka Ayya ke nuna ma Mansu so duk week se anje visiting dinta inta dawo hutu an dinga nannan da ita kenan, hakan ya karasa yaji ya tsani Mansu itama anata bangaren hakane kullum kara tsana shi take.


Aryan babban likitane wanda duniya ke alfahari dashi yanada private hospital guda uku anan kaduna miskiline naqin karawa ko hanyane ya hadashi da Mansu seya mata abinda zatayi kuka tun tana kyalewa har abun ya dameta ta rainashi inya mata tayi Allah ya isa ta gudu daga bayama ta dena guduwa ta dena tsoronshi,


Mansu kyakykyawace ta ajin karshe amma ba ruwanta da kula samari yanzu haka tana ajin karshe a queen Amina boarding school yanzu suna hutune wanda suna komawa se exam,
Farhan ya kammala karatunshi yanzu haka aiki yakeyi a banki, Angle kuma na karatu a America yanzu haka tana ajin karshe ne fannin Law.
Mansu nada 19 yanzu yarinya ce me bala'in kokari da kwazo tun tana 13 ta haddace alqur'ani me girma kuma tana amfani da iliminta yanda ya kamata , duk da kasancewarta a boarding school hakan be 'bata mata tarbiyya koya canzata ba domin ita kam bata da wasu qawaye bata kula kowa kawarta dayace Nadiya itama dan yarinyar kawar mommyce shiyasa kuma tasu tazo daya duk ko yanda yarinya taso da suyi kawance sedai tayi hakuri amma kam bata shiga harkar kowa harkan gabanta kawai takeyi hakan yasa take burge da yawa a makarantar ba d'alibai kawaiba har cikin malamai maza da kuma mata,


























































































Aryan saboda miskilan cinshi yasa bashida budurwa saboda shi a ganinshi ba yarinyar data dace dashi indai yarinya tace tana sanshi to ya tsaneta kenan in a karkashinshi take aiki koranta yakeyi amma kuma duk miskilancin shi da zuciya bayada wulaqanta dan Adam dan yasan karramawan da Allah ya mishi sannan kuma yanasan temako gashi da raha in yaso yanajin maganansu daddy sosai ta wannan bangaren yanada award abokinshi dayane yaron abokin daddy Atif wanda ke matuqar hakuri da Aryan, Aryan kam na bala'in kaunar Farhan,


Duk da maraicin Mansu na uwa da uba ba abinda ta rasa dan su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login