Showing 15001 words to 18000 words out of 23304 words
tsira mata idanuwa yana kallon fuskarta,ya shagala sosai da kallonta,ita kuma a lokacin ta buɗe idanuwanta da sauri ta tashi tana kallon wajen kamar bata san tazo ba.
Da sauri ya tashi bayan ya dawo daga hayyacinsa ya amshi rigarsa daya cire ya saka yana kallon Basma kamar zai cinyeta,Hafsat ta ruƙo hannuwana muka fara tafiya.
Wani abu yaji mai kamada kishi saboda yadda mutanen wajen suke kalle masa matarsa,don shi har ya yi mata don tunda ya ke zai iya cewa bai taɓa ganin macen da ta ƙwanta masa arai irin Basma ba.
Motar su ta sojoji ya shiga ya kafa glass ɗinsa a fuska wato no respect suma sauran sojojin ganin ogansu ya shiga mota da sauri suka shiga suna sara masa.
Muna fitowa waje Hamza ya taho da sauri yana ce wa"iyayen ɗakina lafiya me ya faru?naga Basma duk jikinta ya jiƙe tana rawar sanyi haka?.shiru hafsat ta yi masa ganin ya dage da tambayar sai ta ce"Hamza don Allah kaja mu mu tafi Basma ce ta faɗa ruwa yanzu".
da sauri ya juyo yana ce wa"subhanalillahi sannu Basma,amman babu abinda ya sameta ko?shiyasa banji daɗi ba da muka baro wancen wajen tunda na ga cen ɗin babu irin abubuwa nasu hatsari".
har ya gama maganarsa babu wanda ya ce masa ƙala har ya gaji ya yi shiru,muna zuwa gida Anty shamsiyya ta dinga yi mana faɗa akan mudinga kula da kanmu,daga cewa zamu super market shine muka tafi wani waje harda swiming pool,ganin ranta ya ɓaci ne muka bata haƙuri tare da yi mata alƙawarin ba zamu ƙara fita ba har mu koma kano.
Sosai suke gudu a motar don su gano inda motarsu Basma take,amman sun duba ko'ina babu su babu labarinsu,dukan sitiyarin motar ya yi ya kifa kansa yana addu'ar da ma yana ɗago idanuwansa ya ganta,tabbas babu abinda zaisa yabar Abuja idan har bai ga Basma ba.
****
Yau ake ɗaura auren Ahmad da amaryarsa,amman fa kana ganin fuskarsa kasan ƙwata ƙwata baya cikin hayyacinsa don tunda ya rasa Basma gani ya ke tamkar ya rasa komai na rayuwarsa,tunda aka dawo daga ɗaura auran na sa yaji baki ɗaya kansa yana wani irin sara masa ya cire kayansa ya shiga wanka bayan ya fito yasha magani ya ƙwanta.
Yana ƙwanciya babu da ɗewa Hajiyarsa ta shigo ɗakin nasa,ganinsa ya rufu da blanket sai taji gabanta ya yi mugun faɗuwa sosai,a hankali ta isa inda ya ke ta zauna a bakin gadon a hankali ta yaye blanket ɗin ta shafa fuskarsa,wani zazzafan zazzaɓi taji a jikinsa yana tashi harda huci.
Cikin tashin hankali ta kira sunansa tana haɗa baki wajen ce wa"Ah.Ah..Ahmad tashi mu tafi asibiti ba kada lafiya jikinka ya yi zafi sosai.
"Mama ki barshi na fara jin sauƙi yanzu".ya faɗi hakan yana dafe kansa"gaskiya Ahmad bakaji sauƙi ba,ga kanka nan har yanzu zafi zau kamar wuta."
babu yadda ta iya dolenta ta haƙura ganin ɗan na ta ya dage,tana addu'ar Allah ya bawa ɗanta abin sonta lafiya,tunda ta takura masa akan wannan auren shikkenan ya shiga ciwo yau lafiya gobe babu lafiya,ita kanta amaryar ta kasa gane kansa sam,don irin wannan zancen da ake zuwa shi ko sau ɗaya bai je ba,sai dai ita idan har ta matsu tazo da kanta.
***
"Wallahi mama tunda Basma ta yi tafiya na kasa gane kai na baki ɗaya,hankalina duk yana kanta Mama na rasa wani irin so na kewa Basma a tarihin rayuwata babu yarinyar da ta taɓa shiga zuciyata irinta".
"Aliyu kenan ni dai duk wannan tatsuniyar na gaji da jinta idan har kana son yarinya to kaje gidansu kawai ayi komai a gama,don daman a addinance ma idan kaga yarinya kana so to babu abinda yafi sai kaje gidansu ayi maganar aure a wuce wajen,ba azauna kullum ana soyayya ba,iyayen yarinya su gaji har su ba ta wani".
da sauri Aliyu ya ƙwalalo manyan ƙyawawan idanuwansa ya ce"caɓɓi jan ai wallahi mama idan har aka aurawa Basma wani to fa ki siyo likafa ni ji ajje don tabbas margayawa zanyi".
dafe ƙirji mama ta yi ta ce"to Allah ma ya kiyaye Aliyu kai kaɗai fa na ke dashi a duniyar nan?idan har ka mutu ni yaya zanyi da rayuwata,ni dai ina maka fatan akhairi akan Basma don insha Allah ina ji ajikina matarka ce insha Allah."
Ɗan murmushi yayi sannan ya sumbaci goshin mahaifiyar ta sa ya fita,yana mata bye bye,Ɗan murmushi ta yi tana kallon Ɗan nata sannan ta tashi ta saka myafinta,don taga idan har ta biyewa Ɗan nata to fa zaiyiwa kansa biyu babu ne gwara taje gidansu yarinyar da kanta ayi komai a wuce wajen.
Tana fitowa direbanta yaja ta sai gidansu Basma,da sallamarta ta shiga har cikin gidan,hjy saratu tana daga cikin Ɗaki ta ce"Kai wannan wani irin sallama ce tun daga ƙofar gida kamar masu neman gafara".tana faɗar hakan ta fito waje ta saman bene tana hango wata hamshaƙiyar mata tun daga kan suturarta har kan kayan jikinta babu na banza.
Da sauri hajiya saratu ta sakko tana ce wa"lale marhabun hajiya".tana washe baki kamar wacce aka yi wa albishir da shiga aljanna.
Kai tsaye ɗakinta ta kai ta nan da nan ta saka maryam ta kawo mata lemo da ruwa a fridge sannan ta zauna suka ƙara gaisawa,jikin hajiyar Aliyu dai har yanzu ba a sake ya ke ba ta ce"don Allah hajiya ke ce mahaifiyar Basma"?.
Wani irin mummunar faɗuwar gaba Hajiya saratu taji ta ce"eh.eh.amman ba ni ba ce".
ta faɗi hakan duk hankalinta ya tashi don arayuwarta ta tsani taga arziƙi yana ƙetaro Basma ba tare da ya ƙetaro ƴaƴanta na cikinta ba.
Hajiya ta gane wani abu a dangane da matar sai ta ce"oky to don Allah a haɗani da maman na ta".?
babu wanda ya yi magana acikinsu don faɗuwar gaba sai maryam ce ta yi ta maza ta ce"am Hajiya gaskiya ba nan gidan bane ki dai nemi gidansu".
mamaki sosai ne akan fuskar Hajiyar Aliyu ta kalli Hajiyar Aliyu duk taga yadda idanuwanta ya yi zuru zuru saboda tashin hankali bata ƙara ce wa komai ba ta tashi ta buɗe labulen ɗakin a hankali ta fita,tana mamakin waɗannsn mutanen.
Hango gilmawar mama ta yi ta shiga kitchen kuma sai taga kamarsu ɗaya da Basmar Aliyu don yasha nuna mata hotunan Basma awaya don bashi da aiki idan ba kallon hotunan Basma ba.
da ɗan sauri ta bi bayan mama kitchen ɗin,mama taji tsoro don jin mutum a bayanta,da sauri Hajiyar Aliyu ta ce"sannu baiwar Allah nasan baki sanni bako"?.
ɗaga kai mama ta yi sannan ta ce"eh amman lafiya kuwa baiwar Allah"?.ɗan murmushi Hajiyar Aliyu ta yi sannan ta ce"yauwa don Allah ke ce maman Basma"?.ta faɗi hakan tana kallon fuskar mama duk da ko da bata faɗa ba kammanin da sukayi zai tabbatar maka da ita ce mamanta.
*Miss green ce*
[08/08, 14:11] Miss Green🍀: *🍏BASMA🍏*
BOOK 2📃
BY
UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)
Wattpad user name
Rabiatu333
Arewabooks
rabiattu0444
---------
SIRRINKI👂🏻
*addu'ar samun lfy ga ko wani irin ciwo*
an rawaito daga Aisha (R.A),tace manzon Allah(S.A.W)ya kasance idan mara lfy yazo wurinsa da kokena rashin lfy ya kan ɗauka hannunsa na tsakiya ya sanya a bakinsa sannan ya dangwali ƙasa sannan ya ɗaura a inda kewa mutumin ciwo,sai ya karanta wannan addu'ar kamar haka;
"bismillahir turbati ardina biriqati ba'dina yashfa Taqimuna bi'izni rabbina".
------------------------------------
27🟡28
. . .."eh ni ce mahaifiyarta amman lafiya kuwa"?.ɗan murmushi Hajiyar Aliyu ta yi sannan ta ce"masha Allah daman nazo wajenki ne,amman dana shigo wancen ɓangaren sai ta ce min wai ba nan gidan bane?".
ɗan murmushi maman ta yi sannan ta bawa Hajiyar Aliyu damar shigowa,bayan sun gaisa ne da fara'a hajiya ta ce"yauwa,Ƴar uwa nasan baki sanni ba sunana Hajiya Aisha mahaifiyar Aliyu mai son ƴarki Basma".
wani irin sanyi Mama taji tun daga ƙafafunta har zuciyarta,sannan ta ce"Allah sarki da ya ke yanzu sunyi tafiya ne,amman bata ko kafin su tafi bata sanarmin da zuwansa ba,amman a hakan ma ina godewa Allah kuma ina gode miki,da har kika iya tattaki ki ka zo gidannan,Allah yabar zumunci".
anan dai sukayi ta hirarsu gwanin sha'awa mama ta faɗawa hajiyar Aliyu idan har Basma ta dawo taji daga bakinta insha Allah komai zaizo da sauƙi sai ayi bincike aturo a wuce wajen.
Sosai Hajiya Aisha taji daɗi ta ce"to Hajiya na gode sosai Allah yabar zumunci kuma Allah ubangiji ya dawo mana dasu lafiya".sosai mama taji daɗin addu'ar ta ce"Amin Hajiya na na gode a kuma gaidamin da surukin na wa,sannan ya kamata yazo mugaisa ".
murmushi Hajiya ta ce"ai in dai Aliyu ne yau ma sai ki ganshi don ba kunya ce dashi ba,musamman ma akan Basma".dukkansu sukayi dariya mama ta rako Hajiya suna ta dariyarsu kamar daman sun san junansu.
Wani malolon baƙin ciki ne ya cika zuciyar Hajiya Sara ta ɓalla musu harara tare da ce wa"munafuka ita dai duk wanda yazo gidannan sai ta shige masa,Indai wannan kurmar ce insha Allah sai ta janyo muku zaman gidan yari ko kuma ta janyowa kanta zaman gidan kaso,tunda har hulƊa take da ƳaƳan manya."maryam da Salimat suna taya ta zagin Basma,Maryam ta ce"Hmm ni wallahi wannan matar dana gani duk ta tsolemin idanu so na ke kawau nasan me tazo yi gidannan?don wallahi wannan matar kana ganinta ba sai an gaya maka ba kasan irin mutanan nanne waɗanda suka gaji kuɗi gaba da baya,dama Allah zaisa inyi sa'a in auri ko da ɗanta ne wallahi dana kerewa sa'a."
ta faɗi hakan tana dariya,Salimat ta ce"to uwar ja wa kai jaraba idan kuma ƴar mafiya ce fa"?.banxa maryam ta yi mata ta shige ɗaki abinta don ba ta son ƙanwae tata ta ɓata mata wannan farin cikin da take ciki,don tasan tun kafin taga ɗan na ta tasan shima ƙyau zaiyi kamar uwarsa.
Muna ta shirin dawowa kano munyi tsaraba sosai Hafsat ta kalleni sannan ta ce"hmm wai yaya naga kina ta farin ciki ne Basma?kina murna zakiga Aliyu ko?".
rufe idanuwa na na yi wata kunya ta kamani da yake anty shamsiyya tana wajen ta ce"Hmm bari in tashi kuyi hirarku don ni dai adaina jin kunya ta,amman dai ku shirya Hamxa ya kaiku ku siyo sauran kayan kunji?" amsa mata Hafsat ta yi da "to".sannan muka fito don tafiya.
Pakistan ne ajikina na yafa mayafin pakistan ɗin,"Wow"naji Hamza ya ce sannan ya ce"kai gaskiya Basma kinyi ƙyau wallahi,amman dai in dai mukaje wajan nan ba zaki fito ba ko?"
Mamakin maganarsa mukaji dukkanmu Hafsat ta ce"eh da yake mijinta ne kai ko ubanta ai dole ka hana ta zuwa?".ƴar dariya kawai ya yi sannan ya buɗe mana murfin motar muka shiga.
Hafsat jibgo kaya ta dinga yi tana ajjewa ni kuwa abu biyu na ɗauka nawa na karan kaina sannan na ɗaukarwa mama wanu mayafi mai masifar kyau,ina cikin ajje kayan na hango wani agogo mai shegen ƙyau naje na tambayi kuɗinsa na siya sannan na fita ina jiran Hafsat,tana fitowa muka tafi.
Zuwansa kenan ya hango lokacin da suka shiga motar da sauri sauri ya hau motarsa ya bisu abaya,hankalinsa yana kan inda suke bi,sunzo shan ƙwana kenan wata mota babba ta shawo ƙwana,da sauri ya yi gefe har yana shirin faɗawa cikin rami,kansa ya ɗan bugu da sitiyarin motar,sosai yaji zafin buguwar amman baiji zafin hakan ba ya janyo motar a hankali amman sai ya tarar motar ta rufe wajen baki ɗaya.
Dukan sitiyarin motar ya yi da ƙarfi sannan ya ce"oo shet me yasa bana samunku dream girl,wallahi matuƙae ban ganki ba bazan iya barin garin Abuja ba".
yana faɗan hakan yaja motar ya bisu amman bai gansu ba,ko ƙasa ko sama babu su babu labarinsu,wasu hawaye masu zafi suka zubo masa ya saka hannunsa ya goge,yaji ƙarar wayarsa ya amsa kiran daga cen ɓangaren Sarauniya Jidda ta ce"lafiyarka kuwa Sadauki me yake damunka"?.
"babu komai aiki ne ya yi min yawa".babu yadda ta iya dole ta katse kiran tana mamakin abinda ke damun ɗan na ta.
Babu yadda Anty shamsiyya bata yi damu ba,akan mu hau jirgi ba amman tsorona ya hanamu hawa ai kuwa Hafsat sai mita take wai da tuni mun keta hazo amman na yi musu baƙin ciki,ko da muka hau motar ma faɗan ta take ta yi na mita,don daman nasan halin Hafsat aƙwai faɗan tsiya.
Tun tana mitar har ta yi baccinta,na shafi gefen fuskarta a zuciyata ina ce wa"Hafsat kenan sarkin faɗa Allah dai ya bawa Munir haƙuri don zaisha mita.
Ni ban iya baccin mota ba haka na kafe idanuwa na ina jan carbina har Allah ya kawomu sai wajen ƙarfe 7 na dare sannan mukazo.
Alokacin Hafsat tana bacci ai kuwa ina tashinta daga bacci na ce mata sai yanzu mukazo ai kuwa sai ta hau mita tana miƙa,tana ce wa"ai kinga Basma shegen tsoronki ni wallahi yana cutata gaskiya, yanzu ba ga shi ba kin jawo mana tun safe muna tafiya sai yanzu mukazo kano Allah ma dai da yasa bamu haɗu da ƴan kidnapping ba?".dafe kaina nayi don wallahi mitar Hafsa har ciwon kai take sakawa.
"To Allah dai ya tsaremu ko ƴan mata?".da sauri na juyo don ganin me yi mana wannan maganar
Sosai na yi mamakin ganin bawan Allahn tun da muka shiga motar ya kafa min idanu da kuma mun haɗa ido sai ya sunkuyar da kansa kamar mai jin kunyata.
Ban kulasa ba sai Hafsat ta ti karaf ta ce"Hmm bawan Allah jirgi fa akace zamu shiga amman wallahi wannan ƴar uwar ta wa taƙi yadda mu shiga saboda tsabar tsoronta wallahi".
ƴar dariya ya yi sannan ya ce"hmm ai dole taji tsoro babbar yayarmu".da sauri Hafsat ta juyo ta ce"haba mlm yanzu ni ce babbar yayar ni fa shekarata 18 amman kace min babbar yaya?ai ido ba mudu ba yasan kima ai kowa ya kalle ka yasan ka haifeni a haihuwar kaji".dariya abin ya basa ya kalli Basma wacce ta haɗe fuska tamau kamar zatayi kuka.
Ya yi murmushi ya taso har inda Basma take ya kalleta sosai sannan ya ce"wai wanan beauty ɗin ba ta maganane?".
banza na yi masa ki albarkacin kalli bai samu ba na janyo hannun Hafsat,don na gaji da surutun ta ciwon kai ya ke sakani.
Tsabar maita wannan bawan Allahn tsabar naci har gida sai da ya biyo mu,abin mamakin Aliyu na hango a ƙofar gidanmu ajikin motarsa ya kafamin idanuwa,amman ganin wannan bawan Allahn ya biyoni a baya kamar maye sai magana ya ke min.fuskar Aliyu na kalla ya haɗe girar sama da ta ƙasa,ko kafin in ƙarasa har ya shige cikin motarsa cikin fushi yabar wajen.
*Miss green ce*
[08/08, 14:12] Miss Green🍀: *🍏BASMA🍏*
BOOK 2📃
BY
UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)
Wattpad user name
Rabiatu333
Arewabooks
rabiattu0444
---------
SIRRINKI👂🏻
1
*Yadda ake maganin ƙurajen fuska.*
Daga ummu maher
Asamu garin alim da ma'ul wardi cokali biyu a haɗa arinƙa gogawa a fuska abarshi ya kai minti 15.
2
ko kuma a samu zuma da lemon tsami a dinga shafawa idan mutum zan ƙwanta bacci idan ya tashi ya wanke.
-----------------------------------
*31🟢32*
Sosai abida tasha wahala a wajen gwarzon mijinta yarima Abeed,shima da kansa yaji jiki sosai don kullum shan magani ya ke amman kuma kullum abin ƙara gaba ya ke,ya sha zama a ɗaki shi kaɗai ya yi kuka sosai,don irin wannan matsalar ba kowacce macece take zama da miji a haka ba,sai wadda Allah yasa lalurarsu ɗaya.
Abida tasha wuya don haka ko iya motsi ba ta iyayi da ɗan yatsanta saboda tsabar wahalar da tasha,shi kuwa da wuri ya fice zuwa sashensa don baki ɗaya jikinsa mugun ciwo ya ke masa.
****
Ta gumi sosai na yi ina tunanin Aliyu yau ƙwananmu biyu kenan da dawowa amman sam ya ƙi zuwa inda na ke,na yi kuka sosai don na saba da Aliyu sosai har ba na jin zan iya rabuwa dashi.
Mama tana gama wayar da take ta kalleni sannan ta ce"jiya Alhaji sunyi magana da iyayen Aliyu gobe insha Allah za'a saka rana har da sadaki".mamaki sosai na yi na fito da idanuwa waje ina mamakin hali irin na Aliyu.
"wallahi Basma kinyi dacen mijin aure da kuma dacen uwar miji sai dai inyi miki fatan samun zaman lafiya agidanki,Allah ya tsare gabanki da bayanki".murmushin jin daɗin addu'ar Mama na yi cikin jin kunyarta na tashi da sauri na shige ɗakinmu,itama Hafsat tana waya da munir.
Ƙwanciya na yi na ɗaga idanuwa na sama ina tuna wai yau ni ce za'a kawo kuɗina harda na sadaki,rufe fuskata na yi ina dariya ni kaɗai,Hafsat ta kashe wayar sannan ta ce"ikon Allah Basma me kuma ya faru ki ke dariya ke kaɗai"?.biro na samu kusa dani na rubuta mata na miƙa mata.
"Wayyo Allah Basma gaskiya na ji daɗi wallahi Mama kuma bata faɗa min ba?na yi murna wallahi Allah dai ya kaɗe duk wata fitina da za ta ɓullo cikin wannan auren".Amin na ce a zuciyata sannan na tashi na shiga wanka don ina da waɗanda muke karatu tare dasu,karatun mu na kurmaye na ƙware sosai a fannin koyar da karatun ta yadda zasu fahimta sosai kamar masu ji.
Wannan baiwa ce da Allah ya kewa bayinsa,sai kaga makaho baya gani amman kuma ya iya rubutu da karatu,ya Allah ka sa mu cika da imani amin.
Washe gari da wuri iyayen Aliyu sukazo a babban farlon gidan Baba ya tarbesu,ko da Baba ya timtiɓi mama akan sanarwa da mahaifina ce wa ta yi a ƙelesa kawai da bai san da ƴar ba sai yanzu?ya manta da ƴarsa tilo a duniya ya biyewa sharrin ƴan bariki suna kaɗa masa ganga.
Baba bai ce komai ba ya wuce amman tabbas zai faɗa masa ko da bayan an kawo kuɗin sadakinne,an saka rana nan da wata 2 an kawo sadaki naira dubu ɗari biyu,suna tafiya Baba ya shigo kana ganin bakinsa kasan yana cikin farin ciki,kuɗin suna jikinsa ya wuce ɓangaren Mama.
Hajiya Sara tana kallonsa ta biyosa tana ce wa"Alhaji lafiya naga kana ta murmushi haka?kamar wanda aka yi wa albishir da gidan aljanna?".murmushin ya ƙarayi sannan ya ce"ai dole kiga ina murmushi Saratu kuɗin wannan yarinya Basma aka kawo harda sadakinsu tare kuma da tsayar da ranar aure.
Da sauri hajiya Sara ta da fe ƙirjinta tana zare idanuwa har ƙwallar azaba sai da ta fito mata ta ce"innalillahi wa inna ilaihi raji'un,yanzu Alhaji ina gidannan a