Showing 18001 words to 21000 words out of 23304 words

Chapter 7 - BASMA by Ummu Maher (miss green).txt

21 Jun 2024

4461

rasa wanda zai faɗa min za a kawo kuɗin kurma sai da aka kawo sannan za'a faɗa min?wallahi an zalunceni ai nasan duk wannan munafukar matar ce za ta hanaka to wallahi na ga ta yadda za'ayi wannan auren matuƙar ina raye".


tana faɗar hakan ta taho kamar za ta tashi sama,sosai Alhaji Saminu ya yi mamakin hali irin na matarsa saratu tun tasowarta na ƙuruciyarta haka yasha fama da ita don macece mai nuna baƙin ciki da hassada akan komai musamman idan taga ya yiwa wani abu ba tare da ya nemi shawararta ba,sam Hajiya saratu ba zaɓinsa bace zaɓin iyayensa ne kuma tun kafin su mutu sun danƙa amanarsu a hannunsa don haka wannan ya ke tunowa ya ke ƙeleta a dukkan abinda za ta yi.


Girgiza kansa kawai ya yi ya wuce don idan da sabo ya saba da halin Hajiya Saratu na mugun hali,muna zaune a farlo kusa da mama tana bamu labari Baba ya shigo,ni da Hafsat muka gaishesa muna shirin ta shi ya ce"a'a ku yi zamanku maganar ai ta shafeku".dawowa mukayi muka zauna kanmu a ƙasa.


"Wannan sadakin Basma ne gashinan naira dubu ɗari biyu ne,kuma an saka ranar aurenta nan da wata biyu kamar yadda aka saka na Hafsat don haka waɗannan kuɗin ki ajjesu a nemi mahaifinta yasan duk halin da ake ciki".


"Alhaji ba wai na ƙi ta taka bane amman fa sam a yanzu bazan faɗa masa ba har sai biki ya taho don wallahi zai iya wargaza duk wani shirinmu don mu kullum so muke muga rayuwar Basma ta yi ƙyau ba kamar yadda ya lalata rayuwar ƴarsa da kansa ba".ta shi Baba ya yi ya ce"to ni dai yanzu bari in fita wajen aiki daman ina shirin fita sai kuma ga su".
Adawo lafiya mukayi masa sannan na shige ɗaki da sauri wai ni kunyar mama,Hafsat ta bini tana tsokana ta wai ke ki ka ce kina so da baki ce kina so ba da ba'a baki shi ba.






"Wallahi Maryam in dai har ina raye wallahi wannan yarinyar bata isa ta yi aure ba,sai na lalata abin ni Alhaji zai munafinta har a saka ranar aure ni ina gefe?wallahi ayau zanje wajen Hajiya Salamatu ayi duk wacce za'ayi don wallahi sai na saka an lalata wannan auren".


"hmm ni fa Hajiya kaina baki ɗaya kullewa ya yi saboda mu an mayar damu ba abakin komai ba shine har za'ayi bidiri a gidannan har haka mu ba tare da mun sani ba?to wallahi bazai taɓa yi yuwa ba.


Salimat ta ce"Hmm Hajiya ni jin zuciyata na ke kamar za ta buga saboda tsabar tashin hankali wallahi,Hajiya ko kin san Aliyu ɗinnan dana tayar da hankalina akansa saboda sonsa ashe shine ya ke son Basma?ɗazu na fita Aisha take faɗa min wai ta taɓa ganinsu suna zance hanyar makarantarmu."


"kan uban cen ai wallahi ba zai taɓa yiyuwa ba,dole ne ma asan duk yadda za'ayi amman aure sai an fasa sa sai dai dukkaninku ku rasa wallahi,kurmar me?kurmar banza da wofi duk ta saka ƴaƴana dani kaina acikin matsala,to wallahi ki zanyi yawo tsirara dole ne ma inyi mai yiyuwa a fasa auren nan".tana faɗar hakan ta figi mayafinta ta fita.




Aranar Aliyu yazo ansha sosai kamar babu gobe,na bashi haƙuri akan mutumin da ya ganmu rannan dashi,kallona ya yi sosai sannan ya ce"Basma a lokacin hankalina ya tashi sosai,ina sonki Basma bana son abinda zai rabani dake sai mutuwa,mutuwarma ina fatan ta ɗaukemu tare,ayanzu babu wani tunanin da zanyi tunda ko ayanzu na riga dana bada sadakin aurenmu,don haka abinda ya rage mana sai mu cigaba da addu'ah har Allah ya kaimu ranar aurenmu".


ya faɗi hakan yana kallon cikin idanuwa na,murmushi na yi ina kallonsa
ya yi min wani irin kallo mai tsayawa arai na tashi da sauri zan fita ya janyo bayan mayafina,sai ga Maryam ta zo wucewa ta saki ƙara.








*Miss green ce*
[08/08, 14:12] Miss Green🍀: *🍏BASMA🍏*


BOOK 2📃




BY
UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)




Wattpad user name
Rabiatu333


Arewabooks
rabiattu0444






---------
SIRRINKI👂🏻


Mu yawaita yin addu'ar fita daga gida da kuma ta shigowa saboda samun kariyar Allah da kuma ta mala'ikunsa.
------------------------------




29🟡30




. . .wani matsanancin faɗuwar gaba naji yadda Aliyu ya tafi cikin ɓacin rai ina addu'ar Allah dai ya kaishi gida lafiya ba tare da wani abu ya sameshi ba don a yadda yaja motar komai zai iya faruwa dashi.


Hafsat ta kalleshi sannan ta ce"haba bawan Allah yanzu meye amfanin biyomu har gida don Allah?".ɗan murmushi ya yi sannan ya ce"so ne ya janyo komai ba don so ba da babu abinda zai saka in biyo ku".


ni kam tsabar haushin korar min masoyin da ya yi yasa na yi shigewa ta cikin gidan ina jan kayan na mu daƙer,Allah ya taimakeni har na shiga cikin gidan babu wanda na gani a tsakar gida na yi hamdala sannan na ƙarasa shiga cikin farlon mama,tana kitchen ɗinta na farlo ta hangoni da sauri ta fito tana mana sannu da zuwa.


Da sauri na tashi na rungume mama kamar na yi shekara ban ganta ba,harda guntun hawaye na mama ta ce"ina Hafsat ɗin kuma ta tsaya"?.ko kafin in bata amsa sai ga ta ta shigo tana mita.


Mama ta ce"ke kuma me ya faru ki ke mita haka"?.sai da ta ajje kayan hannunta sannan ta ce"wallahi mama wani mutunne me shegen na cin tsiya ya biyomu mama tun a mota har gida sai da ya biyomu,wai shi son Basma ya ke kuma tunda naga Basma ta zungura ƙeya ta tafi cikin fushi wallahi nasan ba ta sonsa."


sai ta kalli inda na ke taga tuni ma har ma na shigewa ta ɗaki,mama ta ce"to ni dai wuce kitchen ki ɗakko abincinku a kula da faranti har kunun aya ma na yi muku yana cikin fridge".da sauri hafsat ta shige ta ɗakko abincin ta ajje a farlo sannan ta ɗakko kunun ayar ya yi sanyi sosai ta ajje mana a ɗaki,tuni ma har na shige wanka Hafsat ta ce"uwar tsoro kawai ai kema gashi nan jikinki ya gaya miki daga saukarmu a mota har kin shige wanka".ta faɗi hakan tana dariya taji ƙarar wayarta ta ɗauka munir ne ta yi ƴar dariya sai da ta cire kayanta ta ɗaura zani sannan ta ɗauka tana shirin katsewa ta ce"hello".wata ƴar dariya munir ɗin ya yi sannan ya ce"amarya ba ta laifi yau shan ƙamshinne ya motsa kome? Ya hanya ina fatan kun sauka lafiya"?.


nan dai suka cigaba da hirarsu ta masoya,ina fitowa daga wanka na ta da sallar isha'i sannan na yi addu'o'in da na sabayi na shafa na buɗe jarkar kunun ayar na zuba a gora na fara sha sanyin har raina.


Ina cikin sha Hafsat ta gama wayar sannan muka fara cin abincin lokacin Baba ya dawo muka gaisa ya zauna a farlo yana tambayarmu yaya muka barosu da yaranta da maigidan harma da abokiyar zamanta.


Duk muka amsa masa da suna nan lafiya sannan muka ɗakko masa tsarabarsa ta jallabiyya har guda biyu masu ƙyau da kuma hula guda biyu suma masu ƙyau,dariya ya yi sannan ya ce"ikon Allah harda wannan wahala kuma bayan duk wata sai ta aikomin da kuɗi kamar wani albashi? ina godiya Allah ya yi muku albarka ku dukanku.muka amsa da "amin".


mama kenan duk ƴaƴanta ta koya musu tausayin mahaifinsu tun suna ƙanana,bata koya musu rashin tausayin mahaifinsu ba iyaye da dama sai dai idan ƴaƴansu sun yi musu alheri su ƙullesa a bakin zaninsu suƙi su nunawa iyayen yaran baki san kanki ki ke cuta ba,ko kuma kaji uwa na ce wa kada ƴaƴanta su taimakawa mahaifinsu don wani dalili na ta,to wallahi kiji tsoron Allah domin shima mahaifi yana da nashi haƙƙin akan ƴaƴansa musamman idan ya manyanta.
*****


Har ya bar Abuja bai sameta ba ya duba duk inda zai ganta amman shiru don haka dole ya koma gida ba don yaso ba,saboda Fulani ta matsa masa sosai akan ya dawo.


Ranar da ya dawo kamar ko da yaushe ya idan zai dawo gidan kamar ana buki yana ana shiga ana fice komai dare kuwa don babu wanda ya isa ya yi bacci agidan idan shalelenta bai dawo ba.


Matansa ma kowaccensu tasha ƙwalliyarta gwanin sha'awa kowacce ganin ta take babu ya ita a ƙyau da kuma sarauta,sai da ya fara zuwa wajen mahaifiyarsa sannan ya wuce wajen fulani kishiyar mahaifiyarsa ya gaisheta suna gaisawar ta ce"yarima ni kuwa yaya naga duk ka rame haka?ko wani abinne ya ke damunka bamu sani ba?".


ɗan murmushi ya yi na jin daɗin kulawar matar akansa don ko mahaifiyarsa bata tambayesa abinda ya ke damunsa ba,ita dai burinta kawai ya dawo gida.


"Wallahi ammi ƙwata ƙwata bana jin daɗin rayuwata a yanzu,saboda wata yarinya da ta shigo rayuwata a ƙwana biyu kawai ta hargitsamin komai na cikin rayuwata,kuma abin takaicin ban san a inda take ba".?


ya faɗi hakan kamar zaiyi kuka,sosai fulani ta yi mamakin Abeed tun yana ƙarami bai taɓa saka abu aransa irin wannan yarinyar ba,shi ba ma mutunne mai saka damuwa aransa ba.


"Ina son mace wacce bata damu da rayuwa ba,wacce bata damu da mai kuɗi ko akasin haka ba,mai hankali nutsuwa rashin magana da sauransu,amman duk wannan yarinyar ta haɗa waɗannan abubuwan a ɗan zamanda na yi da ita."


sosai Fulani ta ƙwantar masa da hankali sannan ta yi masa alƙawarin za ta taya sa addu'ah da kuma taya sa nemanta.jiki babu ƙwari ya wuce ɓangarensa sai da ya yi wanka sannan ya wuce sashen matan na sa ɓangaren Abida ya fara zuwa tunda a musulunce ɓangarenta ya kamata ya fara zuwa tunda har ya tafi bai shiga sashenta ba.


Tana jin tafiyarsa da sauri ta wuce ta zauna akan faffaɗan gadonta tana gyara zaman haɗaɗɗiyar rigar baccinta wacce ta gaji da haɗuwa kusan rabin jikinta duk a bayyane ya ke.
Da sallamarsa ya shiga Abida ta tsura masa idanuwa kamar mayya tana hangota kawai a jikin abeed yaya za ta yi kuwa tsabar murna,bata iya ɓoye ƙwaɗayinta ba ta isa gareshi ta faɗa jikinsa tana masa sannu da zuwa,Abida kenan aƙwai kissa da kuma kisisina,ita kuwa Bilkisu babu abinda ya shafeta don bata ma iya yadda za ta janyo hankalin miji ba tafi gane tasha maganin mata kawai.wanda kuma rashin ganewa ne hakan a wajen mace wajibine ki iya waɗannan saboda ki zama star a gidan aurenki ba wai mace ta zauna da ƙazanta hammata duk jiki yana wari ba.


So ya yi ya biye mata amman sai ya basar da ita a daƙile ya ce"ki saka hijabinki ki biyoni sashen bilkisu yanzu".wani malulun baƙin ciki ne ya cika mata ciki jin an ambato sunan bilkisu don yadda Bilkisu take wani jijji da kai wai ita ƴar sarauta itama ƴar sarautar ce kuma babu abinda masarautarsu za ta nunawa ta su.


Babu yadda ta iya dolenta ta bishi ba don ranta ya so ba,tana tunanin abinda za ta yi don ta ƙular da Bilkisu.


Haɗasu ya yi dukkansu ya yi musu faɗa sannan kowaccensu ta tashi tana wani taƙama da kuma jijji da kai,ya.kallesu ya yi ƴar dariya sannan ya ce"duk zanyi maganin wannan ɗagawar ta ku don sai na koya muku menene zaman aure don yaga suna neman ilimi akan hakan.




Bayan sunyi sallah ne Sarauniya jidda ta aiko musu da farfesu da kuma kayan marmari,kamar ba amarya ba haka Abida ta buɗe cikinta taci ta ƙoshi ya kalleta da gefan idanu,azuciyarsa ya ce Allah ya ƙyauta sam shi a rayuwarsa bai son mace mara kunya kuma a hasashensa shine Abida buɗaɗɗan ido ne da ita sosai don ta fi Bilkisu ma.


Ko da ya ƙwanta har ta fara baccinsa mai daɗi ya fara mafarkin Basma,kawai sai yaji ana shafa ko ina na jikinsa,sam bai son yin wani abu a yanzu don baya son wahalar da jikinsa da kuma ita amman dole sai da taja ra'ayinsa sai dai fa yana ɗaukar hanya ta fara gane mutan garinsu.






*Miss green ce*
[08/08, 14:12] Miss Green🍀: *🍏BASMA🍏*


BOOK 2📃




BY
UMMU MAHER(MISS GREEN🍀)




Wattpad user name
Rabiatu333


Arewabooks
rabiattu0444




[07/08, 11:59] Miss Green🍀: Duk mai son magana dani ga no ɗita ta whatsapp sai ka yi save number na inyi ta ka👇🏻👇🏻
07068606171
---------
SIRRINKI👂🏻


ƳAN UWA MU RAGE HASSADA DA ƘETA,DON YANA CIRE MANA IMANIMU BAKI ƊAYA.
-----------------------------------




33 🟢34


"Na shiga uku na ni Maryam iskanci da rana tsaka kuma Basma".sosai na tsorata da jin ihun da maryam ta yi ni da Aliyu,kafin ince wani abu Maryam ta shiga cikin gidan,na kalli Aliyu naga shima ni ya ke kalla ya ce"wai wannan ignorance ɗin a gidanku take"?.ka sa ce masa komai na yi saboda ban san ma me zance masa ba sai da ya ƙara maimaita wa sannan na ce masa"eh anan gidan take mamanta ita ce uwargida".


"oky i understand na gane Allah ya ƙyauta"da Amin na amsa masa muka cigaba da hirarmu gwanin sha'awa,amman fa zuciyata tana dukan uku uku saboda tunanin abinda zaije ya dawo,ai kuwa muna cikin hirar sai ga maryam ɗin ta fito ita da Salimat.


Wani baƙin kishi ke jan Salimat ji take kamar ta kashe ƴar kurmannan kowa ya huta,kallon sama da ƙasa take min tana wani hararata,sai da tazo dai dai inda muke a tsaye ta ce"Hmm Allah dai ya ƙyauta bawan Allah za'a cucesa a maƙala masa masifa sai da aka gama yawan duniya sannan za'a wani liƙewa mai kuɗi."


ban san sanda wasu hawaye masu zafi suka zubomin ba na goge hawayen,ganin hawaye a idanuna ba ƙaramin baƙanta ran Aliyu ya yi ba,ya kalli Salimat cikin fushi ya ce"look ki yi maza kibar wajannan saboda kin fara wuce gona da iri don wannan da ki ke gani a gabana ko me tayi a rayuwarta bazan taɓa gudunta ba,don haka kada ki ƙara laƙabawa matata wannan ƙazamin furucin idan kuma ƙinki zaki yi nadamar duk waɗannan maganganun da ki ka yi.


sheƙeƙe maryam ta kallesa sannan ta ce"hmm to idan aka ƙi me mutum zaiyi kuma"?.a zafafe ya kalleta zaiyi magana Basma ta tare gabansa ta kalli cikin idonsa ta girgiza masa kai alamar kar ya yi haka.


Kallonta ya yi sosai aduk sanda ya kalli idon Basma yana ganin tsananin sonsa acikinsa tare da wani irin sirrin da ba kowa ne ya ke gani ba sai shi kaɗai.
Bai ce komai ba ya shige motarsa Basma ta ɗaga masa hannu ya tafi yana kallon abar sonsa Basma.


Itama Basma ɗin murmushi ta yi tana addu'ar Allah ubangiji ya kawo musu lokacin aurensu lafiya.


Tana juyowa taga Salimat ta tsare mata hanya ta nuna ta da ya tsa ta ce"ke kina ganin kin tsira daga tarkonmu ko?to wallahi bari kiji Aliyu na wa ne shi kaɗai ba na wata macen bane don ni kaɗai aka haliccesa don haka tun wuri ki fita harkarsa idan kuma ba haka ba?wallahi sai kin raina kanki don gab ki ke da komawa makauniya daman ke ga ki kurma,kinga sai ki zama musakarki tsaf."


tunda na ke dasu Salimat ban taɓa ko da yi musu kallon banza ba amman yau ban ma san sanda na yi mata ba,saboda na ga rainin hankalin na ta har ya fi na kullum,mutum da saurayinsa amman ace wai sai ya rabu da ita saboda wata,wannan ma ai ƙarfin hali ne.


"Inye lallai kurman nan wuyanki ya isa yanka yanzu Salimat ɗin ki kewa wannan banzan kallon"?.cewar maryam wadda take kallona kamar taga baƙuwar fuska,bance musu komai ba na yi wucewa ta abina,ban gama shiga gidan ba naji maryam ta ce"ai kin banza aikin hofi ai gidan da ki ke wani gadara har ki ke iya ture mutane kina shiga ai ba gidan ubanki bane,idan gadarar ki ke so ki yi ai sai ki koma gidan ubanki ɗan caca kuma ɗan giya".


cak na tsaya saboda yadda naji maganar kamar saukar aradu,nan da nan idanuwa na sukayi jawur kamar gauta,na juyo na kallesu tsaf hawaye sun fara taruwa i danuwa na,da gudu na shiga cikin gidan ina rufe bakina da hijabina,ina jin zuciyata kamar za ta fito.


Tabbas rashin ji a rayuwa ba ƙaramin abu bane,tabbas yau da ace ina iya mayar magana to babu abinda zaisa ƙinƙi mayarwa da su Salimat magana.


Mama tana zaune a farlo na faɗa kanta ina kuka sosai,hankalinta atashe ta ɗago fuska ta tana kallon cikin idanuwa na yadda sukayi jawur kamar gauta cikin alhinin ganina a haka ta ce"Basma me ya faru?me ya sameki?".kukan har yanzu na ke ba tare dana ba ta amsa ba,koda da maganar kuramen ne.


Hafsat ma da ta gama waya yanzu da munir jin kuka cikin tashin hankali ta fito ta ɗagoni ta rungumeni tana tambayata lafiya"?.


ban iya ba ta amsa ba ta zaunar dani a hamkali akan kujera ta ɗakko biro da takadda ta ce"Basma don Allah ki yi haƙuri ki tsayar da kukan ki faɗamin me ya faru?".


Karɓar abin rubutun na yi hannuwa na suna kakkarwa na fara rubutun cikin kuka hawaye na yana ɗigowa kan takaddar.mama sai kallona take tana tausayina har cikin ranta.
Da sauri Hafsat ta karɓa ta fara karantawa,zuciyarta har tafarfasa take wajen karantawa ta tashi da sauri xa ta fita,na ruƙo hannayenta duka biyu ina kuka ina girgiza mata kai.


Ko kallon inda na ke bata yi,mama ma da sauri ta amshi takaddar tana karantawa itama zuciyarta tafarfasa kawai take don abinda su Salimat sukewa Basma ya yiwa yawa.


Bankaɗa labulen ɗakin Hajiya Sara Hafsat ta yi,ko sallama bata yi musu ba tana shiga ta shaƙo wuyan maryam ta yarfa mata maruka har biyu,da sauri Hajiya Sara ta tashu tana ce wa"na shiga uku na Hafsat baki da hankaline zaki shigo mana ɗaki kamar mahaukaciya ki riƙe wuyan ƴa ta kina duka kamar wata zautatta?to wallahi idan ma munafukar uwarki ce ta aikoki ma ɗan banzan duka zaki sha wallahi".tana faɗar hakan tana ƙoƙarin cire ni daga jikin Maryam.


Alokacin mama da Basma suka shigo ɗakin,faɗa sosai akayi don mama da Hajiya sara suma danban sukayi sosai,Salimat ta shaƙoni sosai har sai da na fara ganin wasu taurari,ban san sanda wani ƙarfi yazomin ba na shaƙeta nima na zauna kan ruwan cikinta na hau dokanta kamar Allah ya aikoni.


Nan da nan bakinta ya fashe har ya ta fara zubar da jini a bakinta,muna cikin hakan ne Yaya Abubakar ya shigo,sosai ya yi mamakin abinda ke faruwa har yana tunanin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login