Showing 21001 words to 23304 words out of 23304 words

Chapter 8 - BASMA by Ummu Maher (miss green).txt

21 Jun 2024

4457

anya kuwa agidansu ake wannan toya wainar.


Sosai ya yi namijin ƙoƙari wajen raba wannan gawurtattan faɗan,ai kuwa yana rabawa Hajiya Saratu ta fashe da kuka don tabbas yau tasha duka a hannun Hajiya Aisha.


"Wallahi wannan matar so take ta kasheni ni da ƴaƴa na abubakar shigowa kawai sukayi suka fara dukanmu kamar sun samu jakai,wallahi bazan yarda ba sai an ƙwatomin ƴanci na".


kallon mahaifiyar ta sa ya yi ya girgiza kai sannan ya ce"Umma tabbas aƙwai abinda ya faru har hakan ta kasance,tunda na ke a gidannan ban taɓa ganin Mama ta yi magana akan duk abinda su Salimat da maryam suke mata ba,uwa uba abinda sukewa Basma amman yarinyar nan ban taɓa ganin ta ɗaga idanu ta kalli abinda suke mata ba ballanta ma har ta iya ramawa."
"To dan ubanka rama mata zakayi ko me?shege wanda bai damu da ƴan uwansa ba,daman ina lura da yadda ka ke wani shsshigewa wannan shaiɗaniyar wannan kurmar,ai ko na yi hauka bazan yadda ka ɗakki mana ire iren ƴan giya ba tanbaɗaɗɗu,kun ɗauka bamu san abinda ubanta ya ke ba?to ko yanzu mutum idan yaje borno ya ce akaisa gidan Abdu ɗan caca,mai mata mai harka da gudu za a kaika gidansa don haka wallahi bazan taɓa yadda in haɗa jinina da gurɓatacciyar zuri'a ba".


ko kafin Hajiya Sara ta rufe bakinta mama ta ce"oho ai mahaifinta ne ya ke yi ba ita bace takeyi ba to alhamdulillah,kuma mu haryanzu bamu taɓa haɗa Allah da wani ba,ke kuwa ko yanzu idan akaje unguwarku,aka tambayi inane gidan karuwai za a nuna gidan ubanki kinga kuwa mu gidanmu bashi da wannan sunan,don haka idan zakiyi magana ki dinga taunata tunda kema baki san abinda za a mayar miki ba".mama tana faɗar wannan maganar taja hannuna muka fita daga farlon".
Tsabar haushi Abubakar ko tsayawa baiyi ba da sauri ya fito daga ɗakin ya tafi wajen aikinsa,don yau yana jin zuciyarsa babu daɗi,tabbas idan mutum ya yi dacen uwa tagari to fa tabbas ya godewa Allah don mace tagari itace tushen al'umma.




"Wallahi Umma bazan yadda da wannan cin mutuncin da Basma ta yi min ba,jiba fa yadda ta fasamin bakina sau jini ya ke".tana faɗar hakan ta fashe da kuka sosai.


Zagaye kawai Hajiya Saratu take aɗakin na ta tunanin kawai abinda xa ta yiwa Hajiya Aisha kawai take,tabbas a wannan karan ba za ta yadda ba dole sai Aisha ta ɗanɗana kuɗarta akan abinda ƴar ƙanwarta ta yi mata wato Basma.


Mayafinta ta ɗauka ta fito tana harar ɗakin Hajiya Aisha tana ce wa aranta in kinsan wata ai baki san wata ba,don saina ɗauki mummunan mataki akanki da wannab shegiyar kurmar.








****


"Wai Ahmad wannan wani irin rayuwa ne akawo maka mata yau ƙwana ɗai ɗai har ƙwana 30 amman baka taɓa shiga ɗakinta ba,kasan laifinka awajen Allah kuwa"?.




mahaifiyar ta sa ya yi sosai sannan ya ce"Hajiya nima kaina ban san abinda ya ke damuna ba ni dai nasan tunda na rasa Basma sai na ke jin kamar na rasa komai na wa. . .."


tun kafin ya ƙarasa da sauri ta katsesa wajen ce wa"wato akan wannan shegiyar kurmar yarinyar ne ka ke wulaƙanta min ƴar ƙanwata?to tabbas idan bata yi da wasa ba saina saka an kullemin shegiya ta rasa me fito da ita daman bata da galihu,ni za ta cinyewa ɗa saboda tsabar maita na cinta,to wallahi ka fi ƙarfinta shegiya karuwa kawai."


jin maganar mahaifiyar ta sa ya yi kamar ta buga masa wata guduma akansa,gwara ta gaya masa duk maganar da za ta faɗa masa akan ta faɗawa Basma baiwar Allah wacce bata ma san abinda ke faruwa ba.






*Miss green ce*
[08/08, 14:12] Miss Green🍀: *🍏Basma🍏*






📝By Ummu maher(miss green🍀






35🟢36






. . .kusan mintina talatin kenan Sarauniya jidda tana kan yarima Abeed tan kallon ikon Allah tunani kawai ya ke tunda ya zauna kusan ma za ta iya cewa harda hawaye.a hankali ta kira sunansa ta ce"yarima me ya sameka haka ka ƙwana biyu sam mun kasa gane kanka,hatta matanka ma sunce ka yi musu tawaye ba sa ganinka ƙwata ƙwata idan aƙwai abinda ya ke damunka ne ka faɗa min don Allah".?

Ta faɗi hakan kamar za ta yi kuka,duk taurin rai irin na Sarauniya jidda amman matuƙar taga Abeed a wani hali to fa sai kaga ta zama kamar wata hauka sabon kamu.


"Kai na ke sauraro Abeed".kai tsaye ta faɗi hakan tana wara idanuwanta akansa,sun kuyar da kansa ya yi a duk tsawon shekarunsa a duniya bai taɓa jin mahaifiyarsa ta faɗi sunansa kai tsaye ba,saboda sunan mahaifinta ne sarkin sudan.


Kunya kawai ya keji akan abinda zai fito daga bakinsa ya furtawa mahaifiyarsa akan mace ya shiga wannan halin macen dama bai san yanzu a inda take ba?ko rufe idanuwansa ya yi to fa fuskar Basma kawai ya ke gani,ya rasa wani irin mugun so ya ke mata hakan da haryanzu aikinsa ma yana barazanar tsayawa cak,saboda tsabar tunanin Basma.


"Yanzu Yarima ban isa ka gayamin abinda ke damunka ba?shikkenan babu komai amman na tabbatar da Fulani ce waccen munafukar kishiyar tawa da ta fini awajenka yo da yanzu tuni ka faɗa mata tunda ita ce tayo min naƙudarka ai dole ma ka faɗa ."tana faɗar hakan ta kama hanya za ta tafi.


Da sauri ya tashi ya ruƙo hannun mahaifiyarta sa duka guda biyu bai san lokacinda ya rungumeta baki ɗaya ba,ya fashe da kuka sosai kamar wanda akace masa iyayensa duka sun mutu.


Sosai jikin Sarauniya jidda ya yi sanyi tabbas abinda za kaga ya sa Yarima kuka to fa wannan abin ba ƙaramin abu bane,a hankali ta zaunar dashi cikin tausayi irin na ɗa da uwa ta kalleshi a hankali kamar ɗan ƙaramin yaro ta ce"yauwa ɗana yanzu gaya min me ke damunka ƙwana biyu da har ka kulle kanka kai ɗaya a ɗaki ka ƙauracewa matanka"?.


tabbas yana son gayawa mahaifiyarsa gaskiya kuma baya son ɓoye mata komai a hankali ya buɗe bakinsa ya faɗa komai duk jikinsa a sanyaye ga wata irin muguwar kunyar mahaifiyarsa daya ke ji.


A zafafe ta tashi ta ce"daman akan wata ƴar iska ne ka saka kanka acikin wannan halin?ita ƴar uban waye a duk faɗin ƙasar nan da za ta saka ɗana mafi soyuwa a raina cikin matsala har haka?Abeed ka daina cin abinci ka daina gayu,wajen aikinka ka daina zuwa?ka ƙauracewa matanka?duk a dalilin wannan fitinanniyar yarinyar?wata ƙila ma mayya ce ta kama maka kuruwa to wallahi bazai taɓa yiyuwa ba sai na ɗauki mummunan mataki akanta.shegiya wata ƙila ma ƴar matsiyata ce".tana faɗar hakan fuuu ta fita daga ɗakin ba tare da ta sake ko da kallon inda ɗan na ta yake ba.
Wasu zafafan hawaye suka taho kamar an buɗe fanfo ya rasa yaya zaiyi da rayuwarsa tun daga ranar da yaga wannan yarinyar shikkenan ya shiga wani matsanancin hali.








****


"Basma jiya munyi waya da mahaifinki ya ce yana son ganinki kije maiduguri,to ni dai ina tunanin tura ki wannan garin musamman ma gidan mahaifinki daba saitine dashi ba".


kallon mama na yi na yi wani murmushi har ɗan dimfil ɗina ya lotsa mai matuƙar ƙaramin ƙyau tabbas addu'ar dana daɗe ina yi ce akan mahaifina yanzu gashi Allah ya amsa min hankalinsa yanzu ya dawo kaina.


Wannan murmushin dana yi shine ya tabbatarwa da mama ce wa tabbas inason ganin mahaifin na wa,don haka ba za taɓa iya raba ɗa da uba ba,don haka abinda yanzu kawao yafi shine ta ƙaleta taje ko da sati biyu ne ta yi kafin lokacin bikinta.


Da daddare Aliyu yazo,nasha adona da wani sabon less ɗina ni daman gani da cikar halitta sosai shiyasa ma ban cika saka mayafiba don tabbas zan haɗa babban go slow idan har na fito haka.


Ta kuramin Hafsat ta yi dole na na saka mayafin pink colour ruwan less ɗin,na yi irin ɗaurin zahra buhari,ban saka komai ba daga hoda sai ƙwalli sai lipstick,idanuwan nan nawa kamar na mage sai sheƙi suke,fata ta mai ƙyau da haske sai walƙiya take,ƙyau tsantsa irin na shuwa arab,ga kuma jinin fulanin asali duk sai ya haɗu ya bada wani irin colour mai masifar ƙyau.


"Wow gaskiya Basma kinyi ƙyau sosai kamar na saceki wallahi".cewar Hafsat wacce take gogemin takalmina high hill wai adole shi zan saka,ga shi kuma siket ne duk sai na jini a matse.


Babu yadda zanyi don idan naƙi sakawa nasan halin mitar Hafsat don haka na karɓa na saka duk ina jin jikina kamar kowa kallona ya ke.


A hankali na ke takuna mai matuƙar ɗaukar hankali,sai ka rantse koyamin tafiyar akayi amman babu ko ɗaya,kawai dai halitta ta ce hakan muka haɗu da maryam a kan hanya haushi kamar ya kashe ta ta bugeni ta wuce.


Nima ko kallonta banyi ba na yi wucewa ta saboda bana son abinda zai ƙara haɗani dasu,don tun dukan dana yi wa Salimat yanzu na karɓarwa kaina ƴanci don ko gani na ta yi canja hanya take.
tun daga nesa ya kafamin idanuwansa kamar zai cinyeni,a kunyace na ƙarasa kusa dashi na gaishesa,amman sai da na yi gaisuwar tafi sau biyu sannan ya dawo cikin hayyacinsa,ya shafa gashin kansa ya kalleni sosai sannan ya ce"gaskiya Basma Allah ya tsaraki sosai yadda ki ka san wata tauraruwa,a gaskiya na yi dacen matar aure,ga addini,ga kunya,ga ƙyau,ga ladabi da biyayya,gaskiya na zama autan mata wallahi.


Ƴar dariya na yi cikin kunya na juyar da fuskara gefe ya ce"au rowar ganin ƙyaƙƙyawar fuskar taki ki ke? gaskiya ni dai ki juyo idan baki juyo ba kuka zanyi".ya faɗi hakan cikin shagwaɓa kamar wani yaron goye.


Hirarmu mai daɗi muka fara anan ne na ke sanar dashi tafiya ta maiduguri,wani irin faɗuwar gaba yaji ya kalleni idanuwansa taf da hawaye ya ce"yansu Basma sai ki kama hanya ki tafi har maiduguri ai is too easy wallahi yadda rayuwar nan ta zama wata iri"?.ya faɗi hakan yana kallon na sosai kamar zai cinye ni.


Tausayi sosai ya bani don daman nasan dole za'ayi haka,amman babu yadda zanyi don bana son dama ta ta kufcemin addu'ar dana daɗe inayi akan mahaifina Allah amsa,nuna masa na yi babu yadda zanyi ne kuma ba daɗewa zanyi ba.


Ranar har ganin mama Aliyu ya yi akan maganar mama ta rarrashesa sosai ta nuna masa muhimmancin hakan tunda yanzu na kusa aure.


Babu yadda ya iya dole ya haƙura ya cigaba da yimin addu'ar fatan zuwa lafiya da dawowa lafiya.








*****
"Yarima aƙwai hanyoyi da dama da za'a gane wannan yarinyar a duk inda take,sai dai inason ka ƙwantar da hankalinka don Allah,ka rage wannan tunanin ka ji".




ɗagawa fulani kai ya yi alamar zai daina,yana son matar sosai don tana fahimtarsa aduk halin daya shiga,amman ya rasa me yasa mahaifiyarsa ba ta nuna kulawarta aduk wata damuwarsa,damuwarta dai ita ce damuwa, ko da ma cen Sarauniya jidda macece mai son kanta sosai balle yanzu da ta ƙara bunƙasa.




Ranar yana ɓangarensa ya fito daga wanka kenan ɗaure da tawul,sai ga fulani ta shigo ɗakin suka gaisa ta ce"yauwa ka yi sauri ka shirya k yi baƙi"?.ɗan murmushi ya yi sannan ya ce "to".


yana gama shiryawa cikin kayan meetings ɗinsa coart ce fara da kuma wando baƙi,ya riƙe necktail ɗin a hannu ba tare daya saka ba.wani irin ƙyau ya yi sosai kamar ka sacesa.


Gaisawa sukayi da mutanen sannan fulani ta gabatar dasu"waɗanan masu zane ne na kawo maka daga ƙasashe da dama duk irun zanen da mutum ya ke so suna zana wa,wala na mutum ko na wani abin daban".


kallonta ya yi sosai sannan ya matsa kusa da masu zanen ya rufe idanuwansa ya fara siffanta musu yadda Basma take.


Su kuwa suna ta baje fasaharsu kamar ba gobe,suna gamawa ya buɗe fuskarsa sosai akan zanen,na farko sam baiyi kama da fuskar Basma ba,amman na biyun yana ɗora idanuwansa kan hoton yaga Basma ras acikin hoton kamar za ta yi magana.




Da sauri ya rungume Fulani yana nuna mata zanen wanda ya yi dai dai da hoton fuskar Basma,ai kuwa a ranar Fulani ta baza hotunan sosai.


"Hmm Batul wannan yarinyar fa da ake cigiya na santa".inji cewar Hajiya Tani.


"Ai kuwa Tani wannan yarinyar duk wanda ya nemo duk inda take to tabbas babu shi babu talauci".ƴar dariya Hajiya Tani ta yi sannan ta tashi ta ce "to ni bari in tafi amman gobe zanzo".bata jira abinda Batul zata ce ba ta fita da saurinta.




A gidansa ta samesa ko sallama bata yi ba,mahaifin Basma ya ɗago ƙyawawan idanuwansa ya kalleta sannan ya ce"Tani ban hanaki zuwa gidannan ba"?.bata kula saba again sai kawai ta fara gaya masa ai ana neman ƴarsa Basma a masarautar ƙaisa.




Da sauri ya tashi ya kalleta sannan ya yi wata dariya ya ce"tabbas talaucin dana ke ciki a yanzu yazo ƙarshe,ashe yarinyar dana ke wulaƙantawa ita ce silar arziƙina?Allah na gode maka.




Har masarautar ƙaisa yaje tafiyar ƙwana har uku a mota,yana zuwa ya shine mahaifin yarinyar nan da ake nema,ai kuwa babu ɓata lokaci aka kaisa ɓangaren Fulani don ta ce bata yi shamaki da duk wanda zaizo akan maganar wannan yarinyar ba.




Sosai ta yi murna amnan cikin lokaci ƙanƙani ta haɗe fuska ta tashi tana zagaye a ɗakin ta kallesa sosai,sannan ta ɗakko wani ɗan ƙaramin aƙwati.ta wannan aƙwatin kuɗine acikinsa ayanzu ba anjima ba za'a ɗaurawa ƴarka aure da kuma ɗana Yarima."


kamar saukar aradu haka yaji maganar amman cikin dakiya ya amsa mata da to,ai kuwa a ranar aka ɗaura wannan auren,babu sanin ango da amarya,kai hatta Sarauniya Jidda babu saninta a ciki.








*Caɓɓijan ana wata ga wata kun san ba ƙaramin bidiri za a yi a wannan littafin ba*


*tabbas aƙwai chaƙwakiya sosai acikinsa*




*ku biyoni don jin yadda littafi na ukunsa dana huɗunsa zai kasance*




insha Allah anan zan tsaya a free page,zan fara payment kada ki bari a baki labari wannan littafin ban zafafa kuɗinsa ba akan farashi mai rahusa 200 wato naira ɗari biyu ne kacal complete ɗinsa katin mtn ki ta acc.


Duk mai son cigabansa wato complete ya yi min magana ta wannan number👇🏻👇🏻👇🏻




07068606171
Ummu maher(miss green)


amman ta whatsapp zakayi min magana.






*Miss green ce*

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login