Showing 1 words to 3000 words out of 22575 words
Chapter 1 - SARKIN SADAUKAI Complete by Mansur Usman Sufi .txt
SARKIN SADAUKAI 1
Littafi na ɗaya 1
Sarkin marubuta yaƙi
MANSUR USMAN SUFI
Wthapp number & call
08137237071
Saurayi ne kyakkyawa na gaban kwatance mai kimanin shekaru ashirin da ɗoriya sanye da tufafi na fatu riga da wando tun daga sama har ƙasa, gashin kanshi ya zubo izuwa bisa kafaɗunshi har yana ɗauke da wani yaro mai shekaru goma a Kafaɗarshi,
Yana faman tsala gudu babu sassauci a cikin wani ƙasaitaccen daji ma'abocin dogayen bishiyu, Duwatsu, Ƙoramu,da kwazazzabai, Saboda ƙarfin gudun da ya ke yi har tsallake ƙananan duwatsu ya ke yi.
ko da ya shafe sa'a ɗaya yana gudun sai ƙarfin gudun nashi ya ragu ainun gajiya ta fara ka mashi.
kwatsam bazato babu tsammani sai ya ga waɗansu irin masifaffun kibbau na sauka a dajin tamkar ruwan su ake daga sama.
ko da ganin hakan sai ya shiga amfani da hikimar shi ya na zillewa kibbau ɗin cikin Matuƙar zafin nama naban al'ajabi tamkar ɗaukewar ruwan sama a ka daina harbo kibban.
ko da ganin hakan sai saurayin ya nufi wata sarƙakiya mai cike da duhuwa a dajin ya sauke yaron daga Kafaɗarshi ya sayan shi cikin duhuwar ta yadda babu wanda zai iya ganinshi sannan ya juya ya yi kamar taku huɗu daga inda ya ke
sannan ya ja ya tsaya yana mai jiran yaga abinda zai faru yana waige waige-waige da dube-dube.
kwatsam sai ga waɗansu irin girda girɗa-girɗan dakaru masu kirar samudawa Masu tarin yawa suna fitowa daga duhuwar dajin.
Dakarun suna da girma tamkar toron giwa suna shirye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matuƙar kwarjini daban tsoro fuskokin su a sanye su ke cikin hulunan ƙarfe
idanuwan su kadai a ke gani a hannayen su suna rike da miyagun makamai dangin su gatari, Takobi, Sungumi da Majaujawa.
kafin saurayin yayi wani Yunƙuri dakarun sun rugo izuwa gare shi suna ihu da kururuwa mai firgitarwa ana haduwa a ka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar kwarjini, a na cikin wannan yaƙi ne wani badakaren ya shammaci saurayin ya gabza mashi naushi a fuska ya bazar dashi a kasa
Kawai sai shugaban dakarun ya uwarci wasu dakaru suka duba cikin duhuwar dajin sai gasu sun fito da yaron da saurayin ya ɓoye, kawai sai shugaban ya cillawa badakaren dake rike da yaron wata wuka ya riƙe shi kuma ya ɗora kaifinta wukar a kan wuyan yaron domin
ya yi mashi yankan Rago wani barde dake kusa da shi ya a jiye wani farin kasko domin jinin
yaron ya zuba a cikin shi.
Kafin badakare ya yanka wuyan yaron da KAIFIN TAKOBIn shi
kwatsam! bazato babu tsammani sai wani mahayi ya yi fitar burgu daga cikin duhuwar dajin a bisan wani ingarman Doki Fari Sol!.
kafin badakaren ya yi wani yunƙuri
mahayin ya zare wata sharbebiyar takobi a gadon bayanshi ya sare ma shi wuya kan shi ya yi fitar burgu, Gangar jikin ta faɗi ƙasa rikica.
Sa'adda sarkin yaƙi lahmar yayi arba da gawar badakaren sai ya dakawa sauran dakarun tsawa yana mai yi musu nuni da su farma mahayin a lokaci guda dakarun sukayi
ɗauki kan shi, A na haɗuwa da juna aka kacame da azababban yaƙi mai matuƙar muni ban tsoro daban al'ajabi.
Nan take ƙarar karafniyar Ƙarafa ta cika dodan kunne, Ihu da kururuwar mazaje ta cika dajin gaba ɗaya,
Duk wajen da Mahayin ya sanya a gaba sai dai kaga mazaje na zubewa ƙasa matattu tamkar ana sassabe a gonar
auduga, Dakarun suna kai mashi miyagun hare-hare cikin matukar zafin nama, sa'adda wannan yaro yaji wajen
ya kacame da artabu sai kawai ya Durƙusa ƙasa ya kama rarrafe ya ɓoye a bayan wani dutse.
kafin shuɗewar Daƙiƙa
saba'in mahayin ya hallaka fiye da kaso shida bisa goma na dakarun, Al'amarin da ya yi matuƙar firgita sauran dakarun kenan
suka fara ƙoƙarin cika wandonsu da iska, Shi kuwa sarkin yaƙi ko da ya ga irin muguwar ɓarnar da mahayin ya yi mashi sai
ya fusata ainun.
Duk wannan fafatawa da a keyi saurayin da ke Ƙoƙarin ceto rayuwar yaron yana kwance magashiyan
yana kallon abin da ke wakana tsakanin mahayin dasu sarkin yaki zuciyarshi cike da matuƙar mamaki yana mai cewa acikin ranshi.
Ya a ka yi wannan mahayi yasan cewa ina cikin bukatar taimako?,
Amsar tambayar da ya kasa bawa kan shi kenan, Lokacin da sarkin yaƙi yaga cewa mahayin ya kusa ƙarar da dakarunshi sai kawai ya dako wawan tsalle daga inda yake tsaye
tamkar an harbo shi daga cikin baka yana saman ya zare waɗansu zaratan takubba a gadon bayanshi ya dira a kusa da in da mahayin ya ke a lokacin da sauran dakarun su ka ja da baya a ka fara kallon-kallo tsakanin su.
Abin tambaya a nan shi ne daga ina wannan saurayi da yaron suka fito?.
Kuma mene ne dalilin da ya sanya waɗannan dakarun ke farautar rayukan su.
Dalilin hakan kuwa shi ne :-
*****
Fiye da shekaru dubu biyu da arba'in da huɗu a yammacin gaɓar tekun Bahar-maliya an yi wata ƙasaitacciyyar ƙasa da a ke yiwa laƙabi da zawatul-ifdal.
Kasar madinatul-ifdal ta bunƙasa a arzikin noma da kiwo gami kasuwanci, Daɗin daɗawa kuma sun tara ZARATAN MAYAKA masu juriya a filin yaƙi.
Sarkin da ke mulkin ƙasar yakasance gawurtaccen jarumin Matsafi, shekarun shi hamsin da ɗoriya,
A na yi mashi laƙabi da Shazwan ibn zamaran,
Sarki Shazwan yana da matar aure guda ɗaya jal wacce ta haifa mashi 'ya guda ɗaya mai suna sulairat.
Gimbiya sulairat takasance kyakkyawar gaske da labarin kyawun ta ya yaɗu a nahiyar baki ɗayarsu.
Ta gaji mahaifinta sarki Shazwan a fagen sadaukantaka da ilimin tsafi.
Mutanen ƙasar madinatul-ifdal suna zaune lafiya babu tashe-tashen hankula sai dai kash! akwai wata matsala guɗa ɗaya da take ci musu tuwo a kwarya.
Wannan matsala ita ce bayyanar wata GOBARAR DAJI duk bayan wata shida a shekara sau biyu take zuwa.
Gobarar ta na samuwa ne daga wani daji da ke maƙwaɓtaka da kasar.
Duk sa'adda da annobar ta bayyana tana haddasa hasarar rayukan jama'a dukiyoyin su
haɗu da rushewar gine-gine.
Bokayen nahiyar gami da masu bincike sun ce GOBARAR DAJIn na bayyana ne sakamakon waɗansu hatsabiban aljanu,
Wasu kuma su ka ce wani shuumin boka ne ke haddasa GOBARAR DAJI ma'ana dai babu matsaya guda ɗaya ingantacciya game da annobar.
Sa'adda Sarki Shazwan ya ga cewa wannan annoba taƙi ƙarewa kuma ya ziyarci manyan bokaye amma babu wata mafita.
Sai kawai ya yanke shawarar ya tara gaba ɗaya bokayen shi, Kowannen su ya shiga gudanar da bincike na tsawon mako biyu domin nemo bakin zaren.
A ranar da mako biyu ya cika ne bokayen suka hallara a wani daƙin sirri bisa jagorancin shugaban bokayen wani dattijo ma'abocin kwarjini mai suna Dargas ibn Aumal.
Sa'adda Sarki Shazwan ya ga cewa daƙin taron yayi shuru,
Sai kawai ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗar baki ya yi gyaran murya yace "yaku waɗannan bokaye masana ilimin tsafi shin ina sakamakon da binciken ya baku?. Game da mafitar abin da ya taramu a nan ?.
Ko da jin wannan batu sai bokayen su ka yi shiru wannan ya kalli waccan aka rasa wanda zai ce uffan a cikin su,
Daga can sai sarkin bokaye Dargas ibn Aumal ya Miƙe tsaye ya fuskanci sarki sannan yayi gyaran murya gami da gyara riƙon kwagirin dake hannunshi cikin murya irin ta Hamshaƙan Matsafa ya ce
"Ya shugabana zance mafi rinjaye da bincike ya tabbatar mana shine
Babu wani matsafi ko wasu miyagun aljanu dake haddasa GOBARAR DAJI face wani hatsabibin jarumi ɗan baiwa mai tattare da abubuwan al'ajabi a halin yanzu babu wani GWARZON MAYAKI kamarshi a wannan nahiya ana yi mashi laƙabi da HUBAIRU IBN MURRASU ma'ana SARKIN SADAUKAI,
HUBAIRU ya na rayuwa ne a cikin daji ba shi da abokin mu'amala da ya huce aljanu da dabbobi tun yana jariri mahaifiyarshi ta rasu bayan ta haifeshi a cikin dajin.
Wannan dalili ne yasanya gaba ɗaya ɗabi'un shi irin na dabbobi ne yana da jarumtaka domin komai girman bishiya idan ya naushe ta take zata jijjigo har jijiyar ta ta faɗi ƙasa.
Yana iya saɓa Zaki da Damisa a kafadarshi ya yi gudun rabin Sa'a batare da ya gaji ba.
Komai tsananin yawan abokan gaba a cikin abinda bai gaza daƙika ɗari biyu ba yana iya ƙarar da su,
Wani abin mamaki ga HUBAIRU shi ne shekarun shi basu haura sha bakwai ba da Haihuwa.
GOBARAR DAJIn kuwa tana Bayyana ne a lokacin da Hubairu ke bawa wani tsuntsun tsafin shi horon yaki,
Horan yaƙin da Hubairu ke bawa kan shi yana yi ne kawai domin kare martabar dabbobin dake dajin domin a Fahimtar shi sune zuri'ar shi,
Domin bai taɓa ganin wani bil'adama a rayuwarshi ba.
Sa'adda shugaban bokaye Dargas yazo nan ajawabin shi sai sarki Shazwan ya cika da matukar al'ajabi.
Dargas yaci gaba da cewa bincike ya tabbatar da cewa SARKIN SADAUKAI zai fitowa sarari a wannan nahiya zai shigo cikin 'yan uwan shi bil'adama.
Amma sai bayan ya kammala bawa tsuntsun tsafin na shi horon yaƙi,
Tare da kammala karanta waɗansu dalasiman tsafi dake jikin wani zoben sihiri dake sanye a hannun shi na hagu,
Adadin sirrikan tsafin dake jikin zoben shine iya adadin dabbobin dake dajin.
Bincike bai bayyana a yaushe ne zai kammala karanta sirrikan tsafin ba
Sai dai akwai hanya guda ɗaya da zamu bi wajen kawo karshen GOBARAR DAJI hanyar kuwa ita ce.
Wajibi ne a yanka yaro makawo kuma Maraya, Za a yi amfani da jinin shi ne wajen zubawa a cikin rijiyar bauta da ke tsakiyar birnin mu.
Wannan shi ne Abin da mafi yawan binciken sauran yan uwa na bokaye ya tabbatar.
Sa'adda sarkin bokaye yazo dai dai nan a zancen shi sai sarki Shazwan ya cika da matuƙar farin ciki maral-musaltuwa amma sai ya dubi boka Dargas a lokacin da ya koma bisa kujerar shi ya zauna yace buɗi baki ya ce dashi
"Yakai masanin ilimin tsafi naji dukkan bayanin ka sai dai ina da tambaya guda biyu.
Da farko ina so nasan a ina zamu samu yaro makaho kuma maraya?,
Sannan ta Wace hanya zamu tsira daga sharrin SARKIN SADAUKAI a lokacin da zai fito daga dajin Baitul-shamshan?.
Ko da jin wannan tambaya sai sarkin bokaye yayi shiru yana mai zurfafa cikin kogin tunani,
Daga can ya cigaba da cewa
"Ya shugabana a halin yanzu yaron da za a yanka yana cikin dajin kasar ka tare da wani jarumi da ya ke kula da Rayuwar shu tun bayan rasuwar mahaifan shi,
Game da amsar tambayarka ta biyu kuwa bayani ne mai tsawo da yake buƙatar bincike da dogon nazari,
Yanzu dai abinda yafi muhimmanci da zamu gabatar shine farautar yaro makaho domin magance GOBABR DAJI
dake tunkaro mu nan da mako shida, kasan masu iya magana na cewa idan duka yayi yawa na kai a ke karewa.
Ya yin da boka Dargas yazo dai-dai nan a zancen shi, Sai sarki Shazwan ya cika da matukar farin ciki.
Take bokayen suka yi bankwana su ka rabu a kan cewa zasu sake gudanar da bincike a karo na biyu a kan gano mafita game da SARKIN SADAUKAI, Sannan suka ɓace cikin alkalumman sihiri.
Sai sarki Shazwan ya shafi wani kambun a damtsen shi da hannunshi na hagu ya ɓace bat tamkar bai taɓa wanzu wa ba,
Bai bayyana a ko ina ba sai a cikin turakar shi.
Koda bayyanar shi sai ya ƙwallawa wata kuyangar shi kira,
Kuyangar ta bayyana a gareshi ta zube ƙasa ta kwashi gaisuwa cikin girmamawa.
Sarki Shazwan ya dube ta ya ce. "ya Sunaila ina so ki tafi izuwa gidan Sarkin yaƙi ki sanar masa cewa ina son ganin shi yanzu cikin gaggawa.
Ko da jin wannan batu daga bakin sarki Shazwan sai kuyanga Sunaila ta sake risina wa ta ce "An gama ya shugaba na,
Tana gama faɗin hakan sai ta miƙe tsaye ta fice daga turakar da sauri,
Kawai sai sarki Shazwan ya dunga kai komo a cikin turakar ya kasa zaune ya kasa tsaye.
Yana cikin wannan hali ne Sarkin yaƙi ya bayyana a gare shi ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin ladabi,
Sannan ya buɗi baki ya ce "Gani gare ka ya shugabana me ka ke da buƙata?
Sarki Shazwan yayi gyaran murya sannan ya ce
"Yakai Sarkin yaƙi lahmar kayi sani cewa ban kirawo ka nan ba sai domin ina so ka tafi zuwa dajin dake ƙasa ta ka farauto mini wani yaro makaho ɗan shekara biyar.
Farautar yaron shine zai tseratar da rayuwar gaba ɗaya al'ummar birnin mu daga GOBARAR DAJI,
Zaɓi biyu gareka kodai ka kawo mini yaron a raye ko kuma ka yankashi ka kawo mini jinin shi.
Ko da jin wannan umarni sai sarkin yaƙi lahmar ya ce "An gama ya shugabana cikin wannan zaɓi biyu da ka bani Dole ne ɗaya yakasance.
Ko da gama faɗin sai sarkin yaƙi ya Miƙe tsaye ya nufi kofar fita daga turakar.
Kallo ɗaya zaka yi wa sarkin yaƙi ka fahimci cewa ya cika mai karfi na Allah na isa,
Duk da kasancewar shi saurayi amma yana da ƙirar samudawan farko, Ya tara Ƙwanji mai cike da curin tsoka tamkar duwatsu aka cusa ma shi a ciki ya na da doguwar fuska mai kyawu da kwarjini ƙasumba da gemu Baƙaƙe sidik.
Idan ka ɗauke sarki da gimbiya a gaba ɗaya Birnin Madinatul-ifdal babu gwazon mayaƙi tamkar shi
Kuma ya gaji sarautar ne a wajen mahaifin shi ma'ana sarautar ta su gado ce.
Ko da ficewar Sarkin yaƙi lahmar sai ya ɗebi dakarun yaƙi guda dubu bisa dawakai suka fice daga cikin birnin madinatul-ifdal.
Sa'adda su ka fice sai suka nausawa cikin daji suna lafiya cikin hanzari, Yar gajeriyar tafiya su ka yi su ka fara hango wata ƙaramar bukka a dajin guda ɗaya jal.
Don haka sai suka kasu huɗu, waɗansu su ka yi bangaren Yamma,kudu,gabas wasu arewa, suna masu yiwa bukkar Ƙawanya.
Cikin hanzari Sarkin yaƙi ya umarci waɗansu dakaru Mutum ɗari domin su shiga bukkar su buɗe su fito da a binda ke cikin ta.
Ya yin da dakarun suka zo dai dai bukkkar sai suka kewaye ta waɗansu mutum ashirin daga cikin su suka kunna kai izuwa ciki.
Kaico Haƙiƙa rashin sani yafi dare duhu domin inda waɗannan dakaru sun san abin da zai biyo baya da basuyi