Showing 21001 words to 22575 words out of 22575 words

Chapter 8 - SARKIN SADAUKAI Complete by Mansur Usman Sufi .txt

gobe ya keto Ina tsaye a bakin kofar Darul-arzik,
Daga wannan batu boka Jadwar yayi bankwana da sarauniya Nuwairat ya fice daga turakar.
Kamar yadda sarauniya Nuwairat ta faɗa haka al'amarin yaksance wato tun sulesainin dare ta kammala haɗa rundunar mayakan ta,
Su ka ɗauki hanyar zuwa birnin Darul-arzik, tun kafin hudowar rana suka isa kofar birnin,
Lokacin da isa sai boka Jadwar ya dubi sarauniya Nuwairat cikin ladabi yace"ya shugabata ina ganin zai yi kyau mu jira anan har izuwa lokacin da za'a buɗe kofar birnin,
Koda jin wannan batu sai sarauniya Nuwairat ta fusata ainun ta dube sa tace "wannan wata irin maganar banza ce kake yi
Tabbas yanzu batare da ɓata lokaci zamu karya kofar birnin mu afka musu da yaƙi,
Dajin hakan sai boka Jadwar yace"ya shugabata tuba nakeyi Amma kiyi sani cewa bakomai bakomai ne yasanya na faɗi hakan ba sai domin cewa idan har mu ka afka birnin zai zamo cewa tamkar harin bazato mu ka kawo musu,
Tabbas dole ne a samu waɗanda zasu yi gudun tsira daga cikin al'ummar birnin wata ƙila a samu rashin Sa'a a cikin masu gudun tsirar har da budurwar da muke nema,
Koda jin wannan ƙarin bayani daga bakin boka Jadwar sai sarauniya Nuwairat tayi ajiyar zuciya sannan ta dube sa tace"tabbas zancen ka dutse ne ya abin dogaro na tabbas na yi maka mummunar fahimta,
Kamar yadda boka Jadwar ya bada shawara haka al'amarin ya kasance sai aka jira dakarun birnin Darul-arzik suka fito,
Sannan aka shiga fafata yaƙi, kasancewar masu iya magana na cewa karfin yawa yafi Sarkin Karfi dai yazamana cewa dakarun Nuwairat sun samu nasara akan dakarun birnin Darul-arzik,
Kamai rashin imanin mutum idan yaga yadda gawarwakin ƙananan yara da tsofaffi mata suka cika Birnin dole ne ya zubar da hawayen tausayi,
Batare da bata lokaci ba aka ribace waɗansu yan mata guda biyar dasu kaɗai suka rayu daga cikin
Jama'ar birnin,
Bayan an kwashe dukiyoyin birnin a matsayin ganimar yaƙi
Sai aka ɗauki hanya domin komawa izuwa birnin Garul-mausul,
Tare da waɗannan kyawawan yan mata guda biyar da suka tsira daga cikin jama'ar birnin Darul-arzik,
Inda a lokacin da aka isa birnin ne aka tafi dasu izuwa wani gida na musamman,
A daren ranar da aka kawo su ne su kayi yunkurin tserewa daga hannun dakarun masu tsaron su bayan sun hallaka dakarun ta hanyar yi musu kisan gilla,
Bisa wannan dalili ya sanya boka Jadwar da sarauniya Nuwairat suka shiga farautar su a cikin daji har suka turo musu waɗannan miyagun halittu domin su hallaka su,
Wannan shi ne dalilin da ya baro da waɗannan yan mata guda biyar daga birnin Garul-mausul kuma suke gudun tsira domin kada waɗannan halittu su hallaka su,
Lokacin da zaratan yan matan huɗu suka ci-gaba da falfala azababban gudu domin tsira da rayukan su daga miyagun halittun da suka turo su,
Sai suka shafe tsawon daƙiƙa Ɗari biyu suna wannan tsere a dai dai wannan lokaci ne halittun suka karfin gudun su ya fara raguwa saboda tsananin zafin rana da kishi ruwa da suka addabe su,
Wannan shi ne abinda ya bawa halittun samun nasarar hallaka yan matan uku
Ta hanyar farke cikin su suka cinye kayan cikin,
Ya zamana cewa sauran budurwa guda ɗaya wacce har yanzu take falfala gudun babu ƙaƙƙautawa
Sa'adda budurwar taga cewa miyagun halittun sun kusa cimma ta kuma an kashe gaba sauran Yan uwan ta matan,
Kawai sai taja ta tsaya daga gudun da take yi ta fuskanci halittun batare da ta riƙe wani makami a hannun ta ba,
Hawaye na zuba daga idanun ta, koda halittun suka ga cewa tayi yi gaba da gaba
Sai kawai suka diro daga sararin samaniya suna masu yi mata ƙawanya suna dalalar da wani irin yawu daga bakunan su,
Daga can sai halittun su kayi kukan kura suka afkawa
Kyakkyawar budurwar da azababban yaƙi mai matukar muni da ban tsoro suna kai ma ta miyagun hare hare da fuka -fukan,bakunan su da faratan hannayen su masu kaifi tamkar takobi, da nufin yi masa kisan gilla,
Budurwar ta wanzu tana kai cewa da zillewa hare- haren miyagun halittun cikin gwanin ta da kwarewar yaƙi,
Duk Sa'adda ɗaya daga cikin halittun ya kai ma ta hari idan budurwar ta goce sai kaga duk abin da harin ya taɓa ya tarwatse koda kuwa dutse ne
Koda hassadar Mutum idan yaga yadda budurwar take zillewa hare haren miyagun halittun dole ne ya jinjina mata ya tabbatar dacewa ta cika Basadaukiya mace mai kamar maza,
Su kansu halittun sai da suka cika da matukar mamaki da al'ajabi,
Domin a wannan karon ne suka taɓa fafata yaƙi da wata bil'adama da suka shafe tsawon Sa'a batare da sun samu nasarar hallaka ta ba,
Ana cikin wannan artabu ne wani daga cikin halittun ya kai wa budurwar wani wawan hari da fuka -fukan sa,bisa Sa'a sai ya make ta faɗi ƙasa jini na zuba daga hancin ta da baki,
Kuma numfashin ta na fita sama sama, koda samun wannan nasara,
Sai halittun suka yunkura izuwa kan ta suna wani irin gurnani da dalalar da yawu daga bakunan su domin su yi fata fata da sassan jikin ta,
Kwatsam bazato babu tsammani sai kyakkyawar budurwar taga halittun sun kurma ihu sannan su faɗi ƙasa suna shure shuren mutuwa,
Al'amarin da yayi matukar bawa budurwar mamaki kenan, tace a cikin ranta shin kowane ya hallaka waɗannan halittu,
Amsar tambayar data kasa bawa kanta kenan
Kawai sai ta yunkura ta miƙe zaune da ƙyar,
Ai kuwa sai tayi arba wani narkeken baƙin aljani dauke da waɗansu jarumai guda uku mace ɗaya namiji ɗaya sai karamin yaro
Tsaye daf da inda take zaune,
Budurwar ta ƙura musu idanu ko kiftawa bata yi
Ba wa su bane Waɗannan mutane ba face su jaruma Husnaila,
Koda su sunaila suka lura da halin da budurwar ke ciki sai ta durfafi inda take domin ta bata taimakon gaggawa,
Yayin da ta isa sai sunaila ta firo wata jakar fata a gadon bayan ta ɗauko wani ƙyalle ta shiga goge mata jinin dake zuba a bakinta da hancin ta,
Bayan ta kammala ne ta ɗauki wani garin magani daga cikin jakar ta haɗa a cikin wani kofi na azurfa bayan ta zuba ruwa ta cakuɗa sai ta kafa budurwar a baki ta shanye,
Koda kammala shanye ruwan maganin nan take budurwar taji ƙarfi a jikin ta har ta iya muƙewa tsaye
Batare da wani ɓata lokaci ba sunaila da saurayi Hizmal suka yi wa budurwar jagora har bisa kan Aljani Marhutul-Azab suka ɗora bisa gadon bayan sa
Bayan kowa ya hau sai Marhutul-Azab ya sake yunkurawa ya tashi izuwa sararin samaniya ya shiga keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Bayan tafiyar su saurayi Hizmal tare da wannan budurwa da suka ceci rayuwar ta.
Sai sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka bayyana a wajen,
Sa'adda Nuwairat da Jadwar suka yi arba da gawarwakin halittun sai suka cika da matukar baƙin ciki maral misaltuwa su shiga kallon alamun takun sawayen inda aljani Marhutul-Azab ya sauka,
Cikin hanzari boka Jadwar ya buɗe bakin sa sannan ya runtse idanun sa ya karanto dalasiman tsafi yana Gama rufe bakin sa sai yayi nuna da hannun sa ga wata bishaya dake fuskantar inda suke tsaye sai ga hoton dukkanin abinda yafaru tsakanin budurwar da su saurayi Hizmal ya bayyana a jikin bishiyar tun daga farko har ƙarshe,
Cikin alamun tsananin takaici sarauniya Nuwairat ta dubi boka Jadwar tace "ya dodon bokaye shin yanzu Mene ne mafita
Haƙiƙa idanuwa basu taɓa rintsawa ba matsawar budurwa NIHLA tana numfashi a doran ƙasa
Kuma bazan taɓa koma izuwa ƙasa ta har sai yaga na hallaka ta na mallaki SARKIN SADAUKAI Hibairu amatsayin abokin rayuwa ta,
Koda jin wannan batu daga bakin Nuwairat sai boka Jadwar yayi shiru Sannan daga bisani ya buɗi baki yace"Ya shugaba ta tabbas nayi matuƙar baƙin ciki da bamu riski waɗannan jarumai ba da su ka samu nasarar ceton rayuwar budurwa Nihla ba,
Domin kuwa sune suke ɗauke da yaro Humair makaho wanda shine kaɗai ya iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI a kaf fadin duniya,
Sannan aljanin dake ɗauke da su kuwa shine ke dauke da taswirar fadar Sarkin bokaye,
Haƙiƙa bakamar asarar mukayi ba da mun riske su shi kenan burin mu ya cika na duniya baki ɗaya,
Yanzu abinda kawai za su muyi shine mu bazama farautar su domin mu cimma su,
Sai dai kuma ya shugabata wani hanzari ba gudu ba
Yanzu gashi zamu yi wannan tafiya kuma bakiyi sallama da jama'ar ki ba,
Koda jin wannan tambaya sai Nuwairat tace "nasan da hakan abinda nake buƙata kawai shine ka tashi Manzo na sihiri ya tafi izuwa Birni na domin ya sanar da jama'a ta labarin tafiya ta,
Koda jin wannan umarni sai boka Jadwar ya sake buɗurwar baki ya karanto waɗansu dalasiman tsafi sai ga wani saurayi ya bayyana a wajen,
Bayan Jadwar ya sanar da saurayin duk abinda ke wakana sai Saurayin na sihiri ya ɓace ɓat,
Sannan boka Jadwar ya karanta wadansu dalasiman a karo na uku take wata dardumar sihiri ta bayyana a wajen,
Ba tare da wani jinkiri ba sarauniya Nuwairat da boka Jadwar suka hau bisa kan Dardumar
Take Dardumar sihirin ta tashi sama a cikin iska ta shiga keta gajimare cikin matsanancin gudu tamkar giftawar tauraruwa mai wutsiya,
Hakika boka Jadwar yayi shura a fagen ilimin tsafi
Wannan shi ne abinda ya faru da budurwa Nihla da sarauniya Nuwairat ke son ta hallaka bayan ta kashe baki daya mutanen birnin su,
Da kuma abinda ya wakana tsakanin ta dasu saurayi Hizmal akan hanyar su ta sada yaro Humair makaho da SARKIN SADAUKAI Hibairu,
Mu haɗu a
GOGA SHA FAMA littafi na 1 Domin jin
cigaban wannan kayataccen labari,
Daga mai ɗebe miki kewa a kullum da ko yaushe

Mansur Usman Sufi
Sarkin marubutan yaƙi

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login