Showing 18001 words to 21000 words out of 22575 words

Chapter 7 - SARKIN SADAUKAI Complete by Mansur Usman Sufi .txt

jaruma Hushriba tayi gyaran murya tace
"Yakai sarki shazwan kayi sani cewa babban muhimmin abinda ya kawo ni wannan ƙasa taka kuma har na ceci rayuwar al'ummar kasar ka daga ANNOBAR GOBARAR DAJI
Shine yaro Humair da kuke nema domin ku yanka da ku bayar da jinin sa ga abin Bautar ku domin kare kanku daga GOBARAR DAJI
A halin yanzu ni ma shi na fito farauta domin na cika burina na mallakar tsumin tsafi dake fadar Sarkin bokaye,
Hakan kuma ba zai tabbata ba face na sadu da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI na bayyana masa buƙata ta ta zuwa fadar Sarkin bokaye domin ya samo mini tsumin tsafi
Yaro Humair shine kaɗai yasan Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI
Kun ga kenan a halin yanzu ina matukar kaunar ganin Yaro Humair makaho a raye saɓanin ku da kuke yunkurin hallaka sa,
Hanyar da zaku kawar da wannan guguwar annoba kuwa shine,
A halin yanzu saura kwanaki ɗari uku da sittin da uku SARKIN SADAUKAI HUBAIRU ya kammala bawa tsuntsun tsafin sa horan yaƙi domin ya samu nasarar fito wa daga dajin Baitul-shamshan ya bayyana a wannan duniya tamu
Ya kai wannan sarki kayi sani cewa kasar ka ce ta farko da SARKIN SADAUKAI zai fara bajewa daga doran ƙasa,
Kuma yaro Humair ne kaɗai ne zai iya magana da Yaren Hibairu SARKIN SADAUKAI har ya fahimci hanyar da zai roƙar muku alfarma a wajen sa,
Kaga kenan a halin yanzu idan ma kun mallaki yaro Humair kun yanka sa kun bayar da jinin sa ga abin Bautar ku
Dai -dai da kun dabawa kanku wuƙa domin dazarar SARKIN SADAUKAI ya fito daga dajin Baitul-shamshan zai baje Birnin ka baki ɗaya babu wata halitta mai rai da zai bari ta cigaba da numfashi,
Sa'adda jaruma Hushriba tazo dai- dai nan a jawabin ta sai hankalin gaba ɗaya jama'ar dake cikin turakar ya dugunzuma ainun
Kuma ɗakin yayi shiru tamkar Mutuwa ta gifta,
Sai daga bisani Hushriba ta cigaba da cewa "A halin yanzu zama bai same mu ba,
Dole mu sake bazama farautar yaro Humair makaho domin ya zamo cewa mun mallake sa,
Domin hakan ne kawai zai sanya dukkan mu mu kai ga cika burikan mu, 08137237071
Wani abu da baku sani ba shine wannan mahayi da ceci rayuwar yaro Humair da saurayi Hizmal ba wani ba ne face yar uwa ta gimbiya Sunaila,
Nasan cewa ko wace yar uwa ta kuma nasan hanyar da zan rabata da yaro Humair
Lokacin da gimbiya Hushriba ta sake zuwa nan azancen ta sai kowa ya cika da matukar farin ciki gami da mamaki,
Hushriba tayi ajiyar zuciya ta ɗora da cewa "A daren yau nake so kayi umarni ga dukkan al'ummar wannan birni da su hallara a fada a lokacin da zamu tafi izuwa farautar yaro Humair domin masu iya magana na cewa da zafi-zafi akan daki ƙarfe,
Tabbas a lokacin da jama'a suka hallara zai basu wani sinadaran tsafi da zasu nasu kariya daga GOBARAR DAJI har zuwa lokacin da zamu dawo daga abin da muka fita farauta,
Koda jin wannan batu daga bakin Hushriba sai sarki shazwan ya cika da matukar farin ciki maral misaltuwa,
Nan take batare da wani ɓata lokaci ya umarci shamaki ya sanar da zagi cewa sarki yana son ganin kowa a fada kuma ba'a ɗauke wa kowa ba koda jariri ne sabuwar haihuwa,
Bayan sarki shazwan yayi wannan umarni nan take ya sallami su waziri Rufyan domin kowa yaje ya kammala shiri kuma yayi bankwana da iyalan sa,
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin jaruma Hushriba da su sarki shazwan.














Lokacin da aljani Darmanu ya tsala da azababban gudu a sararin samaniya ɗauke da sarki Uslaim,boka ƙarzum,da dakarun rakiya domin rabi sahun aljani Marhutul-Azab dake ɗauke da yaro Humair,saurayi Hizmal da sunaila domin ya cimmu su,
Sai Darmanu ibn kauƙas ya wanzu yana tsala Azababban gudu babu sassauci yana keta gajimare,
Ana cikin wannan tafiya ne sai yazamana cewa rana ta kwalle tayi tsananin zafi,
Don haka sai boka ƙarzum ya umarci Aljani Darmanu da ya yada zango,
Koda jin wannan umarni sai Darmanu ya saki fuka- fukan ya sauka ƙasa luuuh!
Ya sauƙa a bisa turba, inda ya saukan ya kasance daji ne mai yalwar duwatsu, koramu haɗe kwazazzabai,
Har wasu daga cikin tawagar rakiya sun yunkura zasu sakko daga kan Aljani Darmanu sai boka ƙarzum ya daka musu tsawa yana mai nuna cewa su dakata,
Kawai sai ya dubi gabas,yamma,kudu da arewa,
Sannan ya juya ya dubi Sarki uslaim cikin ladabi yace
"Ya shugaba na wannan daji jikina bai kwanta da shi ba, da alamu akwai wani tarko mai cutar wa, ina ganin zai fi kyau mu sake cigaba da tafiya har sai mun samu waje mai cikekken tsaro sannan sai mu haɗa zangon,
Kafin boka ƙarzum ya gama rufe bakin sa sai kawai akaga waɗansu waɗansu ayarin gwaggwan birrai na fito wa daga kowace kusurwa a dajin waɗansu na dirowa daga saman bishiyoyin dajin waɗansu daga cikin ƙarƙashin ƙasa,
Kafin kace me yarin birran sun yi musu ƙawanya
Su dai birran suna da girma tamkar toran Giwa munin fuskokin su kuwa ya huce misali,gaba ɗaya jikin su cike yake da gashi buzu-buzu babu kyan gani gaba ɗayan su na shanye cikin sulken yaƙi nau'i daban -daban tamkar sun kasance bil'adama,
A hannayen su kuwa suna dauke da miyagun makamai masu barazana da dukkan wata halitta mai numfashi.
Lokacin da aka fara kallon- kallo tsakanin ayarin gwaggwan birrai da su sarki uslaim,
Sai aka shafe tsawon daƙiƙa goma a cikin wannan hali,
Sai daga bisani ne su sarki uslaim suka yi wuf suka zare makaman yaƙin su,
A lokacin da ayarin gwaggwan birran su kayi kukan kura suka yi ɗauki kansu,
Lokacin da aka haɗu da juna nan take waje ya kare da azababban yaƙi,
Bangarorin biyu suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta
Ana fara wannan artabu ne fa su sarki uslaim suka fara gane kuren su
Domin duk inda ɗaya daga cikin gwaggwan birran ya sanya a gaba sai dai kaga dakarun rakiya na zube wa ƙasa matattu,
Wani abu da ya ɗaurewa su sarki uslaim kai kuma ya basu mamaki shine yadda akayi makaman su suka kasa yin nasara akan gwaggwan birran
Abangaren boka ƙarzum kuwa ya wanzu a tsakiyar birran tamkar wani ifritu,
Sai dai aka shafe tsawon Sa'a ɗaya ana wannan fafatawa ɗaya daga cikin su sarki uslaim bai samu nasarar koda hallaka gwaggwan birran ba,
Al'amarin da yayi matukar dugunzuma hankalin su kenan suka shiga damuwa ainun bisa ganin cewa
Tabbas wankin hula zai kaisu dare,
Sa'adda boka ƙarzum yaga cewa idan aka cigaba da wannan yaƙi a haka zasu rasa rayukan su baki ɗaya sai kawai ya shiga amfani da karfin sihirin tsafi domin ya ga ya ragargaji birran,
Amma sai abu ya ci tira,ya zama na cewa yayi amfani da sirrikan tsafi fiye da dubu biyu amma basa tasiri akan birran,
Abangaren sarki uslaim kuwa lokacin da ya zurfafa izuwa cikin Kogin tunani domin samun mafita,
Koda samun mafitar sai sarki uslaim yayi wuf ya mayar da takobin sa izuwa cikin kube,
Cikin wani irin baƙin zafin zafi ya suri wani reshen bishiya dake wajen ya shammaci wani gwaggwan biri ya maka masa akai,
Bisa mamaki sarki uslaim yaga gwaggwan birin ya kurma ihu ya faɗi a ƙasa magashiyan,
Koda ganin hakan sai sarki uslaim ya zage karfin sa ya shiga yaƙar gwaggwan birran da wannan reshen bishiya,
Duk inda ya sanya a gaba sai kaga birran na zubewa kasa magashiyan, wasu sun sheƙa barzahu,
Koda ganin yadda sarki uslaim ke samun nasara akan birran sai suka yanyame sa tamkar yadda dandazon kudaje ke yanyame kwallon mangwaro,
Domin a tarihin su babu wata halitta da taɓa yi musu barnar da sarki uslaim yake yi musu,
Sa'adda su boka ƙarzum suka hango Yadda sarki uslaim ke samun nasara akan gwaggwan birran,
Sai kawai su kayi koyi dasu suka shiga ɗaukar rassan bishiyoyin dajin suka shiga dukan birran,
Wohoho! Kaico haƙiƙa masu iya magana sunyi gaskiya da su ka ce inda babu ƙasa nan ake gardamar kokowa, kuma idan rawa ta kiɗa ya canza dole ne rawa ta canza,
Nan fa yazamana cewa filin yaƙin ya hautsine da ƙarar karafniyar ƙarafa da ihu haɗe da kururuwar birran,
Ƙura ta turnuƙe sararin samaniya, bishiyoyi suka dunga rangaji suna faɗuwa ƙasa,
Duwatsu kuwa suna karo da juna suna bindiga suna farfashewa,
Abangaren aljani Darmanu ibn kauƙas kuwa ya wanzu a tsakiyar birran tamkar GOBARAR DAJI domin duk inda ya kai damƙa da hannun sa sai kaga ya cafko birrai guda biyu ya ɗaga su sama ya maka kansu a jikin duwatsu sun faɗi ƙasa matattu,
Lokacin da gwaggwan birran suka ga cewa bala'i yakai ba'a'i sai suka fara kokarin tserewa,
Amma sai da su sarki uslaim suka dunga binsu a baya suka ƙure musu gudu suna rafkewa,
Kafin shuɗwar Sa'a ɗaya su sarki uslaim sun samu nasarar hallaka ayarin gwaggwan birran,
A sannanne ƙura ta lafa kuma kowa ya dawo cikin hayyacin sa,
A sannanne sarki uslaim ya lura da irin muguwar barnar da ayarin gwaggwan birran sukayi musu,
A kalla sun kashe dakarun rakiya mutum ɗari biyar
Batare da bata lokaci ba a kasa shiga kwashe gawarwakin tare da duba lafiyar waɗanda suka samu raunuka,
Aka kafa tantuna domin a yada zango, kuma kuyangi suka shiga hidimar dafa abin kalaci,
Wannan shi ne abin da ya faru da sarki uslaim da tawagar sa akan hanyar sa ta farautar yaro Humair,
*****
Zaratan ƴan mata ne su biyar, kyawawa na gaban kwatance, waɗanda kallo ɗaya zasu iya ɗimauta zuciyar duk wani ɗa namiji,
Ke ta faman falfala azababban gudu bisa duga-dugan su tamakar zasu fice daga duniyar,
Suna gudun abisa cikin kasaitaccen daji mai ɗauke da manyan bishiyoyi, duwatsu, koramu haɗe kwazazzabai,
Kallo ɗaya zaka yi wa yan matan ka fahimci cewa sun kasance ma'abota bota rayuwa a cikin daji
Saboda tufafin da ke sanye a cikin su yakasance an sana'anta sa ne da fatar damisa,kafafun su ko takalmi babu,
Duk sa'adda da yan matan suka ɗaya ɗaga kawunan su izuwa sama sai kaga sun sake zage damtse sun ƙara karfin gudun su fiye da ɗazu suna cikin wannan gudu ne sai kawai suka ji an suri ɗaya daga cikin su an yi sama da ita,
Nan fa suka tsaya cak suna haƙi da numfarfashi, tamkar ran su zai fita,
Hawaye na zubo wa daga idanun su, su ka shiga dube- dube da kalle-kalle suna masu kwalawa yar uwar tasu kira tare da kiran su nan ta,
Daga can kwatsam sai suka an jefo da gangan jikin ta babu kai,
Nan fa sauran Yan matan suka sake ɗimauce wa suka sake falfawa izuwa cikin daji domin tsira da rayukan su,
Komai rashin imanin mutum idan yaga yadda yan matan ke gudun tsira dole ne ya zubar da hawaye.
Su dai waɗannan yan mata bakomai ne ke biye dasu ba face waɗansu miyagun halittu masu ɗauke da siffa irin ta ƙurar
Kuma yan matan sun fito ne daga wani birni da ake yiwa laƙabi da Garul- mausul ,
Birnin Garul-mausul ya kasance kasaitaccen birni da ya shahara ainun a fagen kasuwanci,noma da kiwo
Daɗin daɗawa kuma sun tara zaratan Jarumai masu juriya a filin daga,
Sarauniya Nuwairat bintu Darhaz ita ce ke rike da Sarautar birnin
Nuwairat takasance kyakkyawa tagaban kwatance wanda labarin tsananin kyawun ta ya watsu a ko ina a sassan duniya,
Mace ce mai matsakaicin kaurin jiki, ba doguwa ba ce ba gajere ba,fatar jikin ta wankar tarwaɗa mai sheƙi da taushi tamkar ta jariri sabuwar haihuwa,
Tana da dara-daran idanuwa farare ƙal, masu haske tamakar tatacciyar madarar shanu, kwayar cikin su takasance baƙa sidiƙ,tamkar an ɗiga tawada,
Hancinta dogo mai lankwasa da kyau, a ƙasan sa an tsaga wani ɗan madaidaicin baki da laɓɓansa suka kasance jajur, haƙoran sa cikin su masu haske da sheƙi,
Wuyan ta dogo mai kyau tamkar na barewa, kirjinta kuwa a cike yake kuma a tsaye ƙyam bai ranƙwafa ba tamkar nunanniyar gwanda,
Cikin ta a shafe yake tamkar bata taɓa cin komai ba,
Ƙugun ta a tsuƙe yake daga gaba,
Daga baya kuma yayi tudu sosai, tamakar idan aka ɗora tuffa zata zauna akan kai saboda tudu su,
Tana da sharɓa sharɓan Cinyoyi masu ɗaukar hankali, yatsun kafafun ta da hannaye sun kasance zarara masu ban sha'awa,
Gashin kan ta baƙi siɗiƙ mai kyalli da sheƙi tamkar gilashi ya zuba izuwa kan kwankwason ta.
Wohoho! Haƙiƙa duk in da kyawu yake idan aka zo kan sarauniya Nuwairat to batu ya ƙare.
Gawurtacciyar Basadaukiya ce mace mai kamar maza, daɗin daɗawa kuma takasance azzaluma tagaban kwatance,
Tsananin zalunci Nuwairat ya huce tunanin bil'adama
Domin kowa bata kyale ba babba da yaro,
Wani abu da yake tayar da hankalin jama'a shi ne yadda aka yi sihirin tsafi kowane iri baya tasiri akan ta,
Kuma babu wani al'marin da zata sanya a gaba face ta cimma nasara akan sa,
Duk wata ƙasa da Nuwairat ta sanya a gaba sai taga bayan ta,
Ta cinye mutanen kasar da yaƙi sun zamo ganima gare ta,
Bisa wannan dalili yasanya ta zamo gagarabadau kuma kadangaren bakin tulu a tsakanin sarakuna bokaye da matsafa,
Duk saurayin da ya bayyana soyayyar sa ga sarauniya Nuwairat baya taɓa samun nasara,
Da yawa daga cikin su ma sun rasa rayukansu bisa bakin cikin rasa Nuwairat a matsayin abokiyar rayuwar su.
Bisa al'adar sarauniya Nuwairat duk shekara tana yin hawa na musamman da kan ta,
Ta kai mamayar bazato da rundunar mayakan ta,
Kwatsam a kashe garin ranar da Nuwairat zata yi wannan fita yaki ne,
Ta yi wani mafarki da ya firgita ta ya hana ta sukuni,
Ba wani abu ta gani har ya hana ta barci ba face surar wani kyakkyawan saurayi,
Wanda tun da take a rayuwar ta bata taɓa ganin bil'adama mai kyawu tamkar sa ba,
Tun a daren sarauniya Nuwairat ta ƙasa rintsawa bisa yadda zuciyar ta kamu da matukar kaunar saurayin da ta gani a Cikin barcin ta,
A lokacin tashi Manzo ta aika aka kirawo mata bokan masarauta mai suna jadwar ibn zairum,
Lokacin da boka Jadwar ya bayyana a gaban sarauniya Nuwairat a Turakar ta barci sai ya zaɓe ƙasa ya kwashi gaisuwa a gare ta,
Sannan daga bisani ya ɗago da kan sa sama,
Saadda yayi arba da halin da sarauniya Nuwairat ke ciki sai ya ɗimauce dakyar ya samu sake sunkiyar da kan sa ƙasa a karo na biyu amma sai jikin ya kama kyarma,
Ba a Kowa ne hali boka Jadwar yaga Nuwairat ba har ya ɗimauce face bisa arba da yayi zahirin kyakkyawar surar ta bayyana a fili
Domin a wannan lokaci ne tana sanye ne da rigar barci shara-shara wacce bata kai ƙwaurin ta, kuma bata rufe rabin kirjin ba, hasken fitilun dake turakar ya kara bayyana kyakkyawar surar ta ya mace dake cikin rigar barcin shara-shara.
Cikin alamun matukar damuwa sarauniya Nuwairat ta dubi boka Jadwar cikin sanyayyar murya mai ɗauke da damuwa tace"ya abin dogaro na shin ina dalilin wannan kyarma taka da kuma sunkiyar da kanka ƙasa batare da ka dube ni ba?,
Koda jin wannan tambaya sai boka Jadwar ya buɗi baki Muryar na rawa yace "Ya shugaba ta na rantse da kyawun surar ki,
Bazan iya kallon ki a cikin wannan yanayi ba koda kuwa na daƙiƙa goma ne domin,
Domin kallon kyakkyawar surar ki zai iya sanya wa na manta da kai na da ma dukkanin sirrikan tsafi na,
Koda jin amsar waɗannan tambayoyi daga bakin boka Jadwar,
Sai a sannanne ta lura cewa ashe rigar barci a jikin ta kawai sai tayi wuf ta janyo wani mayafi na alhariri ta rufe jikin ta,
Sannan ta sake duban boka Jadwar ta buɗi baki a karo na biyu ta buɗi baki da nufin ta ce wani abu amma sai boka Jadwar ya ɗaga ma ta hannu yana mai nuna cewa ta dakata,
Sannan yayi gyaran murya a karo na biyu cikin kakkausar murya yace"ya shugaba ta ba sai kin wahalar da kanki wajen sanar da ni abin da kika gani a cikin mafarkin ki ba, hakika duk na gani a cikin madubin tsafi na kuma nayi bincike,
Ya sarauniyar kyawawan duniya kiyi sani cewa haƙiƙa kin faɗa tarko mai wahalar fita,
Domin saurayin da kika gani a cikin mafarkin har kika kamu da soyayyar sa ba wani ba ne face
Wani hatsabibin jarumi da ake kira da suna Hibairu wato SARKIN SADAUKAI na duniya,
Hibairu wani irin mutum ne daya rayu a cikin daji da dabbobi da aljanu bai iya kowane irin yare ba,
A halin yanzu ba zai fito daga daga cikin dajin Baitul-shamshan da yake zaune a cikin sa ba face ya kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI a ranar da zai bayyana a wannan duniya ta mu zai yaƙi biladama ne domin ya kare martabar dabbobi,
Babu wani mahaluki da zai iya magana da Hibairu har ya fahimci Yaren sa face wani yaro makaho mai suna Humair,
Wani abin baƙin ciki da na gani a cikin madubin tsafi na shine akwai wata budurwa guda ɗaya wacce ita ce mace ta farko da SARKIN SADAUKAI zai fara yin arba da ita a cikin dukkan biladama,
Don haka ita ce wacce HUBAIRU zai kamu da ƙaunar ta fiye da komai a rayuwar sa,
Saboda tasirin cewa ita ce jinsin mace ta farko daya fara gani a rayuwar sa,
Sa'adda boka Jadwar yazo nan azancen sa sai sarauniya Nuwairat ta cika da matukar al'ajabi,
Amma sai ta dube da cikin alamun matukar damuwa tace "shin wace ce wannan budurwa da zata fara saduwa da SARKIN SADAUKAI,
Hakika duk inda take sai na farauto ta na hallaka ta domin ya zamo cewa nice mace ta farko da sarkin sadaukai zai fara arba da ita,
Har ya kamu da tsananin kaunata,. Boka Jadwar ya yi ajiyar zuciya a dai dai lokacin da zufa ta keto masa.
Ya dubi Nuwairat cikin alamun tsananin damuwa yace"ya shugabata kiyi sani cewa haƙiƙa farautar wannan budurwa abu ne mai matukar wahalar gaske,
Domin lokacin da matasa Cikin halarar tsafi domin na gano birnin da budurwar take sai na sha bakar wahala har da na su ma sau arba'in
Sannan na gano birnin , ana kiran sa da suna Darul-arzik,
Yana ne sa kaɗan da birnin ki. Abinda na fahimta kawai shine tabbas mutanen birnin Darul-arzik sun kasance hatsabiban mutane masu ƙarfin sihirin tsafi tunda dai gashi tsawon shekaru kina kai farmaki izuwa kasashe da bira ne amma ba ki iya gano wannan birni na Darul-arzik ba.
Sa'adda boka Jadwar ya zo nan a jawabin sa sai sarauniya Nuwairat ta cika matukar farin ciki maral misaltuwa ta dui Jadwar tace "Babu ruwa na da hatsabibancin su tabbas na gano wannan budurwa na hallaka ta
Shin ka manta ne cewa babu wani al'amari dazan sanya a gaba face na samu nasara akan sa
Tabbas ina so ne alfijir ɗin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login