Showing 9001 words to 12000 words out of 22575 words
Chapter 4 - SARKIN SADAUKAI Complete by Mansur Usman Sufi .txt
tafkeken baki tamkar kofar gari, yana da faffaɗan kirji tamkar faranti,
A kwiɓin hannayen sa biyu yana maƙale da waɗansu fuka-fukai guda biyu daga kasan gadon bayan sa yana sanye da wata irin murtukekiyar jela irin ta kifi,
Sanye a ƙugun sa yana sanye da bante na fatar damisa mai ɗauke da guraye da layu na tsafi, a tsakiyar kansa yana ɗauke da manyan ƙaho guda biyu irin na ɓauna,
Tabbas wannan mutum ya cika abin tsoro domin babu wani mutum da zai yi arba dashi face ya ɗimauce,
Sa'adda Abidatul-auliya tayi arba da mutum sai jikin ta yakama kyar ma tamkar mazari har tana sakin fitsari a wando saboda tsananin tsoro da razani,
Yayin da mutumin yaga halin da Abidatul-auliya ta shiga sai ya takarkare ya bushe da dariya mugunta,mai kama da kukan baƙi sai daga bisani ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da Sakon mutuwa sannan ya buɗi baki cikin kakkausar murya yace "yake wannan bil'adama kiyi sani cewa kin aikata mini laifi wanda ahalin yanzu babu wani mahaluki da ya taɓa yi mini shi kisani cewa wannan ƙorama da kika yi mini fitsari a ciki ba ruwa bane face JININ SARAKAI na baƙaƙen aljanun duniya na shafe tsawon shekaru dubu arba'in ina sihirce wannan jini domin in samu nasarar mallakar gaba ɗaya sarakunan ma'ana na zamo SARKIN SARAKAI na aljanu,
A yau ne zan kammala wannan aiki nawa sai gashin kin wargatsa mini wannan buri na wa a cikin Abin da bai gaza daƙiƙa goma ba wanda na shafe tsawon shekaru dubu arba'in,
Lokacin da mutumin yazo nan azancen sa sai hawayen baƙin ciki suka zubo masa,
Sannan daga bisani ya cigaba da cewa "Na rantse da rayuwar mahaifina sai na yanke mini hukuncin da har abada bazaki taɓa mantawa da ni ba
Koda gama faɗin hakan sai mutum ya a nuna Abidatul-auliya da ɗan yatsan sa na hagu take wani irin koren haske yayi fitar burgu daga gare sa ya shiga jikin Abidatul-auliya
Nan take taji wani irin tsananin zafi a tsagin jikin ta na hagu tamkar ana ƙonata da wuta,
Nan fa ta fara ihu da kururuwar neman taimako
Sannan daga bisani mutumin ya ɗauke hannun sa na dubi Abidatul-auliya yace "yake wannan bil'adama kiyi sani cewa har abada baza'a taɓa samun magani lalurar ki ba domin nemo maganin dai dai yake da barkewar YAKIN DUNIYA na uku,
Koda mutumin yazo nan a zancen sa take ya bace bat tamkar bai taɓa wanzu wa ba.
Adai-dai wannan lokaci ne Abidatul-auliya tajiyo karar takun sawayen dawakai da haniniyar su,
Ai kuwa koda ta duba sai tayi arba da dakarun masarauta su kimanin dubu biyu sun durfofi inda take, da zuwa su ka ɗauke ta batare da ɓata lokaci ba, suka juya suka nufi hanyar da zata kai su birnin Tehran,
Tun daga wannan rana tsagin jikin Abidatul-auliya ya kamu da ciwon kuturta,
Kuma sai dare yake yi mata raɗaɗi, sarki ya nemi bokaye da matsafa a sirrance akan su gano masa maganin cutar dake damun gimbiya amma abu yaci tura , domin duk bokan da yajewa da maganar sai yace masa shima bai san maganin lalurar ba,
Har sarki ya mutu aka ɗora Abidatul-auliya akan karagar mulki amma ba'a gano maganin cutar ba,
Kuma yazamana cewa gaba ɗaya birnin Tehran babu wanda yasan cewa Abidatul-auliya na ɗauke da wannan cuta ta kuturta, hatta dakarun da suka ɗauko ta daga cikin wannan daji a lokacin da al'amarin yafaru,
Tun daga ranar da wannan abu yafaru bata ƙara bari wani mahaluki yaga jikin ta koda kuwa hannayen ta da kafafunta face fuskar ta kaɗai, ko wanka da kwalliya zata yi da kanta take yi bata bari kuyangi su yi mata,
Wata rana Abidatul-auliya na zaune acikin Turakar ta bisa ƙasaitacciyar kujera ta tafka uban tagumi, a wannan lokaci dare ya tsala kuma yayi duhu dunɗum babu abinda kunne keji face haushin karnuka da kukan gyare tsilli-tsilli.
Abidatul-auliya na cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai wani kyakkyawan tsuntsu ya bayyana agare ta a cikin iska yana mai ƙura mata idanu,
Koda tayi arba da tsuntsun take ta dawo cikin hayyacin ta daga duniyar tunanin da ta shiga zuciyar ta cike da matukar mamaki da al'ajabi
Bisa mamaki sai Abidatul-auliya taji tsuntsun ya bushe da dariya tamkar yakasance bil'adama sannan daga bisani ya fara magana cikin murya mai ɗan karan daɗi tamkar ana busa sarewa
Yana mai cewa"Barka da warhaka ya sarauniyar kyawawan duniya Abidatul-auliya bintu shafwaz,
Ya ke wannan sarauniya mai daraja nasan cewa a halin yanzu zuciyar ki cike take da matukar mamakin yadda akayi nake magana alhalin nakasance tsuntsun ba bil'adama ba,
Tabbas ni bil'adama ne kamar ki sai dai na boye miki siffa ta ne saboda waɗansu muhimman dalilai,
Ya ke wannan sarauniya kiyi sani cewa bakomai ne yakawo ni gareki ba sai domin na taimaka miki wajen samun maganin lalurar da ta addabeki atsagin jikin ki na hagu tsawon shekaru masu yawa,
Koda jin wannan batu sai Abidatul-auliya ta dubi tsuntsun cike da mamaki tace"Kace mini kai bil'adama ne to shin wane ne kai? Kuma mene ne ribarka idan ka taimake ni na samu maganin lalura ta?
Koda jin waɗannan tambayoyi sai tsuntsun yayi ajiyar zuciya sannan yayi gyaran murya yace"Haba ranki ya daɗe me kike ci ne na baka na zuba ai cikin bayanin dazan yi miki za kiji duka amsar tambayoyin ki amma tun da kina buƙatar su bari na fara sanar dake.
Da farko ni suna na shubairu ibn mauzur mahaifina mashahurin boka ne da yayi shura a yankin nahiyar larabawa,
Duk cikin ya'yan mahaifin mu ni ne kaɗai na gaje shi tun banfi shekara goma sha biyar ba da rasuwar sa,
Game da amsar tambayar ki ta biyu kuwa zakiji amsar acikin bayanin da zan yi miki,
Binciken da na gudanar bisa halarar tsafi na ya tabbatar mini dacewa tun mahaifin ki yana raye ya ziyarci bokaye da dama domin samo maganin lalurar ki amma abu ya ci tura,
Yake wannan sarauniya mai daraja kiyi sani cewa har abada bazaki taɓa warkewa daga wannan lalura taki ba face kin sha wani tsumin tsafi dake ajiye a cikin wata salka a fadar Sarkin bokayen duniya,
Bincike ya kara tabbatar mini da cewa babu wani mahaluki da ya isa yaje fadar Sarkin bokaye ya ɗauko tsumin tsafi face wani hatsabibi kuma taƙadirin jarumi da ake yiwa laƙabi da SARKIN SADAUKAI,
Hibairu wani irin mutum ne da yake rayuwa ta daban domin ya taso ne a cikin dabbobi da aljanu tun yana jariri, bai taɓa ganin wani bil'adama ba ballantana ya iya Yaren su,
An kira sa ne da SARKIN SADAUKAI saboda tsanin jarumtakar sa ya huce hankali,
Bazai taɓa fitowa daga dajin Baitul-shamshan ba face ya kammala karanta waɗansu dalasiman tsafi dake jikin wani ZOBEN SHIRI dake hannun sa wanda adadin sirrikan tsafin shine adadin dabbobin dake cikin dajin,
Game da amsar tambayar ki ta uku kuwa akan mene ne riba ta idan na taimaka miki wajen samun maganin lalurar ki shine
Sai domin na gano cewa kece kaɗai wacce zata taimaka mini wajen biyan tawa Bukatar,
Kamar yadda kike ɗauke da lalurar tsagin jiki
Ni ma ina da irin ta sak amma a tsagin dama kuma na samu tawa lalurar ne alokacin da nake fafata artabu da yan uwana a ƙoƙarin su na rabani da muhimman sirrikan tsafin mahaifin mu,
Bisa wannan dalili ne yasan ya nake so mu haɗa karfi da karfe domin mu sadu da sadauki Hibairu a lokacin da zai fito daga dajin Baitul-shamshan domin mu bayyana masa buƙatar mu ta zuwan sa fadar Sarkin bokaye,
Koda tsuntsun ya zo nan azancen sa sai kawai ya rikiɗa izuwa wani zabgegen kyakkyawan saurayi ba ya sanye da riga ko wando face bantai na fatar damisa da ya rufe al'aurar sa zuwa kwaurin sa,
Sa'adda sarauniya Abidatul-auliya tayi arba da saurayin nan take taji zuciyar ta buga da karfi kuma tsikar jikin ta ta tashi,
Bakomai ne yasanya sarauniya Abidatul-auliya taji zuciyar ta ta buga da karfi ba sai domin tunda take a rayuwar ta bata taɓa ganin wani ɗa namiji mai kwarjini da kyan diri tamkar saurayin ba,
Abinda yasanya tsikar jikin ta ta tashi kuwa shine Yayin da ta kalli saurayin sai taga barin jikin sa na dama na zubar da wani ruwan mugunya na kuturta,
Daga can sai saurayin ya sake rikiɗa izuwa wannan kyakkyawan tsuntsu ya buɗe baki a karo na uku yace "Na barki lafiya ya sarauniyar kyawawa sai mun sake saduwa a ranar da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI zai kammala karanta ɗalasiman tsafin dake jikin ZOBEN SHIRI a dajin Baitul-shamshan,
Koda gama faɗin hakan sai ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba,
Nan take sarauniya Abidatul-auliya ta cika da matukar farin ciki maral misaltuwa yazamana cewa a kullum idan dare ya tsala sai ta zauna a wannan baraba ta Turakar ta koda wannan tsuntsun zai sake bayyana gareta wato shubairu ɗan boka mauzur
Wannan shi ne abinda ya faru da sarauniya Abidatul-auliya ya birnin Tehran dake yammacin duniya.
3
Kwatsam bazato babu tsammani sai saurayi Hizmal da mahayin suka ji ƙarar alamun zare sakatun wannan ƙofa daga ciki,
Daga bisani sai ƙofar ta bude sai ga wani irin haske da kamshi mai nan sha'awa ya ratso daga ciki
Cikin matukar farin ciki maral misaltuwa mahayin ya kunna kai izuwa ciki saurayi Hizmal yayi koyi dashi goye da yaro Humair a gadon bayan sa,
Su na kammala shiga sai ƙofar ta mayar da kanta ta rufe ruf!.
Adai dai wannan lokaci ne sarki shazwan waziri Rufyan Sarkin bokaye da sauran tawagar su suka bayyana a wajen bayan buɗewar ƙofa ta huɗu,
Sa'adda suka bayyana sai sarkin bokaye ya dubi sarki shazwan cikin matukar takaici yace"ya shugaba na haƙiƙa munyi babban rashi da har mu kayi kuskure su saurayi Hizmal suka ƙetare kofa ta biyar suka shiga izuwa gidan tsira
Bisa tsarin wannan gida babu wanda ke da ikon shiga cikin gidan tsira matukar akwai wanda ya ƙetare kofa ta biyar har sai nan da kwanaki uku,
Koda jin wannan batu daga bakin Sarkin bokaye Dargas sai kowa ya cika da matukar takaici, shi kuwa Sarki shazwan saboda matukar takaici bai san sa'adda ya takarkare ya kurma wawan ihu ba wanda ya firgita duk wata halitta dake wajen har da boka Dargas,
Sai Daga bisani ne ya turɓune fuska tamkar an aiko masa da wasikar mutuwa ya dubi Sarkin bokaye a lokacin da idanuwan sa suka kaɗa su kayi jawur tamkar garwashin wuta cikin kakkausar murya yace"ya Sarkin bokaye ina so kayi ma za ka gudanar da bincike gano mini shin mene ne abin da ke faruwa a birni na,
Koda jin wannan umarni daga bakin sarki shazwan sai idanun Sarkin bokaye suka zazzaro su dube sa cikin ladabi yace"ya shugaba na shin ka manta ne cewa abisa ƙa'ida da dokar wannan gida sihiri baya tasiri,
Idan kuwa har ka naso na gudanar da binciken dole sai dai mu koma da baya,
Sai dai ina da wata shawara,shawarar kuwa ita ce mu kasu guda biyu kaso na farko su jira anan har zuwa nan da kwanaki uku domin su samu damar shiga izuwa kofa ta biyar su cimma su saurayi Hizmal,
Ni kuma da wasu zamu koma izuwa birnin mu domin mu kai ɗauki jikina ya bani cewa tabbas bayan tafiyar mu wani mummunan al'amari ya faru sai dai bazan iya sanin ko mene ne ba tunda bani da halin gudanar da bincike,
Yayin da sarki shazwan yaji wannan shawara daga Sarkin bokaye sai yayi shiru yana nazari Daga bisani kuma ya dubesa yace"Ka kawo shawara mai kyau saboda ka tafi kai da sauran Yan uwan ka bokaye mutum biyar,tare da waziri Rufyan
Ni kuma da Sarkin yaƙi zamu zauna nan mu jira cikar kwanaki uku domin mu cimma su saurayi Hizmal.
Koda jin wannan umarni daga bakin sarki shazwan sai sarkin bokaye ya juya da baya ya shige izuwa cikin wannan kofa ta huɗu da suka fito waziri tare da bokaye biyar suka mara masa baya,
Suka bar su sarki shazwan a tsaitsaye cirko cirko fuskokin su cike da matukar damuwa,
Wannan shi ne abinda ya faru da su sarki shazwan da su saurayi Hizmal a cikin gidan tsira,
****. *****. *****
Daji ne ma'abocin kwarjini,da ban tsoro, ya tara bishiyoyi, duwatsu,koramu haɗe da kwazazzabai,gami da manyan tsaunuka,
Komai rashin tsoron Mutum idan ya yaga yadda dajin yakasance dole ya razana,
Domin da gani dole ne a samu miyagun dabbobi ko aljanu a cikin sa,
Tsananin shirun da ya wanzu a wajen ya ishi ya firgita Mutum
Sai dai abinda zai bawa mai kallo mamaki shine duk yadda dajin ya tara wadannan abubuwan ban tsoro amma sai gashi wani bil'adama ya wanzu a cikin sa amma babu alamun tsoro ko razani a tare dashi
Kyakkyawan saurayi ne ɗan kimanin shekaru sha biyar yana sanye da bante iya gwiwar sa, babu riga a jikin sa, https://youtu.be/tsdKzDyEuVk
Hakan ne abinda ya bayyana surar jikin sa ta jarumtaka , jikin sa a murɗe yake tamkar na ƙarfe,yana da faffaɗan kirji tamkar duwatsu aka cuccusa masa a ciki,gashin kansa baƙi ne siɗik mai kyalli ya zuba akan fuskar sa da kirjin sa,
Kafar sa ko takalmi babu, a hannun sa yana riƙe da wani dogon mashi mai baki tamkar zarto mai kaifi tamkar takobi,
Kallo ɗaya za ka yiwa saurayin ka fahimci cewa yana da karfi na Allah ya isa,
Tafiya yake a dajin cikin ƙasaita yana mai ratsa duwatsu koramu da sarƙaƙiyar duhuwar bishiyoyi tamkar yana cikin turakar sa,
Yana cikin wannan tafiya ne ya jiyo alamun motsi a bayan,. Koda ya waiga bayan sa sai yayi arba da wata zakanya da mijin ta suna tsere cikin nishaɗi,
Idan namijin ya ba wa macen tazara sai macen ta zage damtse ta tsere masa, ta mai yimasa gurnani dake nuna cewa ta samu nasara ,
Sa'adda saurayin yaga abinda zakanyar da mijin ta ke yi sai ya kalle su yayi murmushi har suka zo suka gifta ta gaban sa suna matsanancin gudu suka yi nisa sosai har yazama dakyar yake iya hangosu.
Sai kawai shima ya takarkare ya falfala da azababban gudun mai ban al'ajabi daban mamaki,
Domin ƙorama, duwatsu da bishiyoyi basa tsaida sa,
Duk faɗin ƙarama tsallake ta yake yi.
A wasu lokutan sai kaga ya daga tsalle sama yana yana mai rike rassan bishiyoyi tamkar wani ɗan biri,
A wasu lokutan ma idan yaga bishiya zatayi masa waigi sai kaga ya sanya hannun sa ɗaya ya naushe ta ta faɗi ƙasa ya bi ta kanta ya huce,
Cikin Abinda bai gaza daƙiƙa goma sha biyar ba sai gashi ya dira a can gaba ɗaya inda zakunan suke,
Ya yin da su kayi arbda da saurayin sai suka ja suka suka tsaya cak,
A kayi kallon kallo sai bisani sai zakanyar da mijin ta suka dako sufa izuwa kan saurayin yayin da suka hada kirji da juna sai su duka biyun suka faɗi ƙasa tim,.
Amma saurayin ko da ƙafarsa bata motsa ba ballantana yayi gezau,
Sai da akayi haka har sau goma, koda zakunan suka ga cewa sun kasa samun nasara sai kawai suka risina da kawunan su ƙasa suka durƙusa alamun dake nuna cewa sunyi MUBAYA'A ga saurayin,
Ba wani bane wannan saurayi ba face jarumi Hibairu wato SARKIN SADAUKAI.
Yayin da Hibairu yaga zakunan sun risina agareshi sai kawai ya juya ya cigaba da tafiya a dajin hannun sa riƙe da wannan mashi mai baki biyu,
Wannan shi ne abinda ya faru da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI a cikin dajin Baitul-shamshan.
Al'amarin su saurayi Hizmal kuwa sa'adda suka samu nasarar shiga izuwa gidan tsira sai suka tsinci kan su a cikin wani kasaitaccen gida da aka kawata sa da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin duniya, gaba ɗaya ginin gidan anyi sane da zallar duwatsun zubar daju yana sheƙi da walwali, ko ina an kawatashi da furanni da furanni da shuke-shuke gwanin ban sha'awa.
Gidan yana ɗauke da manyan falo guda arba'in kowanne na ɗauke da kayan alatun jin daɗin duniya daya bambanta da ɗayan,
Haƙiƙa babu wani Basarake ko attajiri da zai tsinci kansa a cikin gidan face ya raina kansa ya tabbatar dacewa ya shiga cikin maƙurar aljannar duniya,
Bayan su saurayi Hizmal sun sauka a cikin wata ƙasaitacciyar turaka sai kowa ya shiga kimtsa cikin sa bayan an kammala an samu nutsuwa ne sai Hizmal yayi gyaran murya sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye ya dubi mahayin nan yace"ya kai wannan jarumi ma'abocin karfin damtse lokaci yayi da ya kamata ka bani amsar tambayoyin da nayi maka a baya,
Koda jin wannan batu sai Mahayin ya ɗora hannun sa a kansa ya cire rawanin sa fuskar sa ta bayyana a fili ƙarara,
Sa'adda saurayi Hizmal yayi arba da fuskar mahayin sai ya cika da matukar al'ajabi da mamaki,
Bakomai ne ya basa mamaki ba sai bisa ganin cewa mahayin yakasance tsaleliyar kyakkyawar budurwa,
A iya tsawon rayuwarsa bai taɓa ganin mace mai kyan diri tamkar mahayin ba,
A karon farko Hizmal yaji soyayyar ya mace ta shiga zuciyar sa,
Kyakkyawar budurwar ta jefi Hizmal da wani irin kayataccen murmushi mai ɗauke da alamar tambaya,
Sannan ta buɗi baki cikin zazzakar murya mai daɗi tamkar sarewa tace"yakai Hizmal a yanzu na bayyana maka wace ce ni
Yanzu kuma zan sanar dakai dalilin da ya sanya taimaka maka wajen ceton rayuwar yaro Humair,
Da farko dai suna na Husnaila bintu ishwar, mahaifina ƙasurgumin matsafi ne kuma ƙasaitaccen sarki da yayi shura a yankin ƙasashen yamma ta tsakiya,
Dalilin rabuwa da mahaifina da ƙasar mu kuwa shine ,
****. *****. *****
Kimanin shekaru arba'in bayan shuɗewar KARSHEN ƘARNI na shida da yin YAKIN DUNIYA na biyu,
An yi wata ƙasaitacciyar ƙasa da ake yiwa laƙabi da Baitul-Mausul,
Ƙasar Baitul-Mausul ta bunƙasa a harkar kasuwanci,noma da kiwo daɗin daɗawa sun tara zaratan Jarumai masu juriya a filin daga,
Sarautar ƙasar na karkashin mahaifina sarki ishwar,
Sarki ishwar yakasance gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin daga, ya na da tarin dukiya,gami da sanin ilimin tsafi,
Mutum adali mai tausayin talakawan sa, bisa wannan dalili ne yasan ya jama'a ke matukar kaunar sa da yi masa biyayya,
Kuma sarakunan dake nahiyar suke shakkar sa basa yunkurin kawo masa farmaki,
Mahaifina yana da matan aure guda huɗu kuma dukkanninsu sun haifa masa ya'ya
Yarima ubaiyu shine babba, sannan