Showing 3001 words to 6000 words out of 22575 words

Chapter 2 - SARKIN SADAUKAI Complete by Mansur Usman Sufi .txt

gangancin shiga bukkkar ba.
Dakarun dake tsaitsaye suna jiran fitowar yan uwan su sai kawai suka ga ana wurgo gawarwakin dakarun daga cikin bukkkar.
Al'amarin da ya fusata sauran dakarun kenan suka dunga kunna izuwa ciki,
Amma sai yazamana gawarwakin su ake ta jefowa waje koda ihu basa yi an yi masu yankan rago
Kafin wani lokaci fiye da rabin dakarun sun sheka barzahu.
Ko da ganin hakan sai Sarkin yaƙi lahmar ya fusata ainun ya tako da kafafafunshi har izuwa bakin kofar bukkkar yana mai dakawa sau ran dakarun tsawa dakarun suka ja da baya,
Sannan ya yunƙura da nufin ya kunna kai izuwa cikin bukkkar,
Kwatsam bazato babu tsammani sai kawai ya ji an gabza mashi wawan naushi a fuska saboda karfin naushin sai da ya yi sama tamkar an janye shi da ƙugiya sannan daga bisani ya faɗo ƙasa tim!.
Kafin ya yi wani yunƙuri kawai a kaga wani kyakkyawan saurayi ya yi fitar burgu daga cikin bukkkar kafadarshi rataye da wani ƙaramin yaro.
Sa'adda dakarun suka yi arba da saurayin sai kuwa suka ce dawa Allah ya haɗa mu
Kawai sai suka zare makaman su suka rufa mashi baya suna ihu da kururuwa mai firgitar wa,
Ko da ganin hakan sai saurayin ya falfala da azababban gudu izuwa cikin dajin.
Nan fa dakarun suka dunga kai mashi hare-hare ta ko ina amma sai yazamana saurayin ya na tsira,
Duk yawan kibbau ɗin da su ke harba mashi sai yazamana yana zille masu cikin gwanintar yaƙi
A na cikin wannan hali ne saurayin ya ɓace musu ya shige cikin duhuwa.
Wannan shi ne dalilin daya sanya waɗannan dakaru ke biye da wannan saurayi mai ɗauke da ƙaramin yaro, domin su hallaka sa.




******
Lokacin da sarkin yaƙi ya yi arba da idanun mahayin sai yaji zuciyarshi
ta buga da ƙarfi abinda ya faɗo mashi a zuciya shine ko da cewar bai ga
fuskar mahayin ba amma yaji a jikinshi cewa tabbas ya taɓa ganin fuskar mahayin sai dai abin tambaya a nan shine a ina
ya taɓa ganin mahahin kuma mace ce ko namiji amsar tambayoyin
da sarkin yaƙi ya kasa bawa kanshi kenan kawai sai ya daga takubbanshi
sama ya falfala da azababban gudu izuwa kan mahayin yana kwarara ihu.
Ko da ganin hakan sai mahayin ya dako wawan tsalle daga inda yake ya kaiwa sarkin yaƙi lahmar wawan sara da takobinshi da nufin tsinke mashi wuya cikin zafin nama sarkin yaƙi yasanya takobinshi ya kare saran sannan suka ruguntsume da
masifaffan yaƙi suka wanzu suna kaiwa juna sara da suka cikin matuƙar zafin nama juriya da bajinta ta gaban kwatance
Wohoho! tabbas jarumtaka da sadaukantaka baiwa ce daga Allah komai hassadar mutum idan ya ga yadda gwanayen biyu ke tsallakewa
miyagun hare-haren
juna dola ne ya jinjina masu ya tabbatar da cewa sun cika GWARAZAN JIYA.
A zahiri ga wanda ya ke kallon yadda artabun ke wakana zai fahimci cewa sarkin yaƙi ya fi mahayin karfin damtse sai dai mahayin ya fi shi sanin salon yaƙi nanfa yazamana cewa jaruman biyu har daka tsalle su ke yi suna kaiwa juna hari.
Wohoho! tashin hankali ba a
sa mashi rana,GOBARAR ANNOBA kuwa idan ta taso babu mai ɗauke ta face Ubangiji,
Nanfa yazamana cewa ba iya bishiyoyi da duwatsun da ke dajin ba hatta sauran dakarun
suna cikin matukar tashin hankali domin bishiyun da ke karairayewa
sakamakon artabun jaruman biyu suna yunƙurin murƙushe su ba shiri suka shiga guje-guje gami da ifice-ifice a na cikin wannan artabu ne
wani tunani ya faɗowa mahayin,Tunanin kuwa shine matuƙar a ka cigaba da wannan artabu wannan jarumi dake kwance magashiyan.
zai iya rasa rayuwarshi, koda gama tunanin hakan sai kawai ya shammaci sarkin yaƙi ya gabzamashi wawan naushi a kirji saboda karyfin naushin sai da ya yi katantanwa a sama sau huɗu sannan ya kife a ƙasa.
Kafin yayi yunkurin miƙewa tsaye mahayin ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya rikiɗa izuwa wata baƙar guguwa ya tashi izuwa
sama ya keta gajimare ya bace bat!.
Sarkin yaƙi ya miƙe tsaye zumbur
kawai sai ya ga wajen wayam babu mahayin, Saurayin da wannan karamin yar, Cikin matuƙar takaici ya taƙarƙare ya kwarara wawan ihu a cikin wannan hali ne kwatsam!
sai sarki shazwan, Sarkin bokaye Dargaz,waziri Rufyanda waɗansu zaratan dakaru suka rugo izuwa wajen a bisa dawakai suka yi turjiya,
Sarki Shazwan ya kama linzamin dokin shi ya sauko ƙasa, Sarkin bokaye, Waziri, da sauran dakaru suka yi koyi dashi.
Sa'adda Sarkin yaƙi lahmar ya yi arba dasu sarki shazwan sai hankulansu suka ɗugumzuma cikin matukar razani ya sunkiyar da kansa kasa na alamun jin kunya a matsayin sa na dirkar birnin madinatul-aɗfal wanda matukar ji da akansa a fagen jarumtaka,
Amma ace bakon jarumi ya gagare sa tabbas wannan bakaramin abin kunya bane,
Cikin alamun sanyin jiki ya tunkari inda su sarki shazwan suke tsaye,
Tun kafin yace wani abu abu sarki shazwan ya dube sa cikin alamun tsananin fushi ya ce dashi,
"Yakai dirkar birnin madinatul-aɗfal kayi sani cewa haƙika ka tafka babban kuskure da har ka bari wannan bakon jarumi ya tserar da rayuwar wannan yaro da saurayin da muke farauta,
Yayin da sarki shazwan yazo nan azancen sa sai ya mayar da dubansa ga boka Dargas yace dashi
"Ya abin alfaharin birnin madinatul-aɗfal ina so yanzu ka gudanar da bincike bisa halarar tsafinka Domin ka gano mini shin wane ne wannan mahayi da ya ceci rayuwar yaron da muke farauta sannan a halin yanzu suna in ne
Koda jin wannan batu daga bakin sarki shazwan sai sarkin bokaye ya zira hannun sa ɗaya cikin aljihun rigar sa ya ɗauke wani ɗan madaidaicin madubin tsafi da girman sa bai huce faɗin tafin hannu ba,
Ya shafe sa da hannun sa na hagu yana mai karanto waɗansu dalasiman tsafi ya shiga gudanar da bincike,
Sannan daga bisani ya ɗago da kansa cikin ladabi da girmamawa yayi gyaran murya sannan ya kawo gwaron numfashi ya ajiye cikin kakkausar murya yace"ya shugabana hakika mahayin da ya ceci rayuwar wannan yaro da muke farauta ya cika hatsabibi kodai wanda yasan sirrin mu ko kuma wani makusancin mu domin duk kokarin na gano sa abin ya faskara,
Sai dai na gano cewa a halin yanzu suna gab da shiga gidan tsira wanda da zai sun shiga cimmusu abu ne mai matukar wahala.
Sa'adda da boka dargas yazo yazo nan ajawabin sa sai takaici da bakin ciki suka mamaye zuciyar sarki shazwan ya dubi Sarkin bokaye yace "Ai sai kayi maza ka kai mu inda suke domin mu riske su cikin hanzari kafin su kai ga shiga gidan tsira,
Kafin sarki yagama rufe bakin sa Sarkin bokaye ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya nuna Sarki shazwan,waziri Rufyan da sauran dakarun da hannun sa na hagu take suka zama wani farin haske,
Hasken ya dunƙule a waje guda, sannan ya tashi zuwa sararin samaniya ya ɓace cikin gajimare
**** ***** ****
Al'amarin wannan mahayi da ya ceci rayuwar wannan saurayi da makahon Yaron nan kuwa ,
Bayan ya karanto dalasiman tsafi sun ɓace ɓat basu bayyana a ko ina ba sai a cikin wani daji ma'abocin kwarjini daban tsoro,
Dajin yana ɗauke da gajerun bishiyoyi masu yawa da duwatsu,koramu haɗe da kwazazzabai,
Kallo ɗaya mutum zai yiwa dajin ya fahimci cewa baza,a rasa wani abu mai cutarwa a cikin sa ba
Koda bayyanar su sai mahayin ya zira hannun sa a aljihu ya ɗauko wata yar siririyar kwalba dake ɗauke da wani koren ruwa ya buɗe murfinta kawai sai ya miƙa wa saurayin yana mai umartar sa da ya shanye ruwan.
Batare da fargabar komai ba ya karɓa ya kafa a baki ya kwankwaɗe ruwan,
Faruwar hakan keda wuya sai ya ji gaba ɗaya ƙarfin jikin sa ya dawo tamkar babu wani rauni a jikin sa.
Kawai sai ya miƙe tsaye zumbur ya na mai duban mahayin cike da matukar mamaki.
Mahayin ya katse shirun da ya wanzu ta hanyar buɗar baki yayi gyaran murya cikin tattausan murya yace"
Yakai mafarauci Huzmal kayi sani cewa nasan cewa a halin yanzu zuciyar cike take da tambayoyi agareni
Shin wane ne ni kuma me yasa na ceci rayuwar yaro Humair,
Saboda haka ahalin yanzu ba lokacin da zan amsa maka tambayoyin ba ne saboda gagarumin aikin dake gaban mu na tseratar da Yaro Humair,
Sa'adda saurayi Huzmal yaji wannan batu sai ya cika da matukar mamaki
Abu na farko da ya faɗo masa arai shine
Shin ya akayi mahayin ya san sunan sa , sannan ya kasa tantance Muryar mahayin mace ce ko namiji,
Abin tambaya ma ana shine shin mene ne kudirin mahayin na ceton rayuwar mu?
Amsar tambayoyin da saurayi Huzmal ya kasa bawa kansa kenan,
Mahayin ya katse shirun da ya wanzu akaro na biyu ta hanyar buɗar baki ya karanto waɗansu dalasiman tsafi ya nuna wata bishiya dake gaban sa akaro na biyu,
Yana gama rufe bakin sa sai ga photon su sarki shazwan ya bayyana a jikin bishiyar suna tafiya a cikin gajimare cikin matukar sauri tamkar sun kasance aljanu ba bil'adama ba.
Koda ganin Hoton sai mahayin ya sake karanta waɗansu dalasiman tsafi take su duka ukun suka ɓace ɓat basu bayyana a ko ina ba sai gaban wani kasaitaccen gida a cikin dajin,
Gaba ɗaya ginin gidan an yi shi ne da zallar duwatsun wuta masu kwarin gaske,
Yana ɗauke da tagogi barkatai ,da kofa guda ɗaya hal!
Wanda aka sana'anta ta da zallar mulmulallan bakin karfen jauhari,
Wacce inda za'a sanya karti majiya karfi mutum hamsin bazasu iya ture ta ba,
Cikin azama mahayin ya durfafi kofar gidan yana rike da makahon Yaro Humair a hannun sa, saurayi Huzmal na biye dashi,
Yayin da aka isa daf da kofar gidan aka mahayin ya sanya hannun sa ɗaya ya shafi ginin gidan take wani rubutu da akayi shi da zallar zinare ya bayyana a wajen,
Kawai sai mahayin ya karanta rubutun yana gama rufe bakin sa sai kofar gidan tayi wani irin ƙara da ya cika dajin baki ɗaya,
Daga can sai kofar ta buɗe kanta,batare da wani jinkiri ba mahayin ya riƙe hannun yaro Humair ya kunna kai izuwa ciki,
Saurayi Huzmal ya mara masa baya, su na shiga sai kofar ta mayar da kanta ta rufe ruf kamar bata taɓa wanzuwa ba.
Lokacin da su saurayi Huzmal suka shiga cikin wannan kofa sai suka tsinci kansu a gaban wata kofar wacce ta nunka ta baya nauyi da fadi
A gefe guda an ajiye wani teburin azurfa mai tsawon kamu huɗu,
Teburin yana ɗauke da waɗansu manyan kubobi guda biyar da akayi su da zallar karfen jauhari suna sheki da ɗaukar idanu
Komai kallon ƙurillar mutum bazai iya tantance kubobin ba
Yayin da suka yi arba da su sai mahayin ya ɗaga kansa izuwa saman kofar take yayi arba da wani allon karfe da akayi rubutu a jikin sa da tawagar Za'afaran kamar haka,
Yakai ma'abocin wannan gida kayi sani cewa wannan kubobi guda biyar dake ajiye a kan wannan teburi a cikin su ne zaka samu mabuɗin wannan kofa ta biyu,
sai dai fa ina so kayi sani cewa matsawar ka ɗauki mabuɗin da bashi ne na kofar ba zaka faɗa izuwa cikin musiɓa maimakon shiga izuwa gidan tsira,
Sa'adda mahayin yazo nan zancen sa sai hankalin sa ya dugunzuma ainun
Abinda ya dugunzuma hankalin sa shine idan har yace zai tsaya bincika wacce ainihin Mabudin kofar su sarki shazwan zasu iya cimmusu,
Haka kuma idan ya sanya kubar da ba itace mabuɗin kofar ba zasu halaka baki ɗaya,
Wani abu daya kara dagula masa lissafi shine shirin tsafi baya taɓa tasiri a wajen
Sa'adda mahayin yazo nan a tunanin sa sai hankalin ya dugunzuma ainun ya ƙurawa kubobin idanu yana nazarin su domin ya gane wacce ce mabuɗin kofar
Sai da ya shafe tsawon dakika arba'in yana nazarin batare da ya gane wacce ce mabuɗin kofar daga cikin kubobin ba,
Ana cikin wannan hali ne sai aka ji wani Irin ƙara ya cika wajen baki ɗaya, cikin hanzari suka waiga domin suga ko mene ne aikuwa sai suka ga ashe wannan kofa ta farko ce ke yin ƙaran alamar cewa zata buɗe wani ya shigo cikin gidan,
Saboda matukar razani mahayin bai san sa'adda ya miƙa hannun sa bisa teburin azurfar ba ya ɗauki ɗaya daga cikin kubobin ya zira ta a cikin wani kwaroron rami dake tsakiyar kofar ya shiga murɗawa da dukkan karfin sa domin ya buɗe kofar,
Shiru ka ke ji tsawon dakika hamsin babu alamun buɗewar kofar,
Kawai sai aka ji kofar dake bayan su ta buɗe sai ga su Sarki shazwan sun bayyana
Da yake daga inda su sarki shazwan ke tsaye zuwa inda su Huzmal suke akwai tazara mai yawa sai su sarki shazwan suka falfalo da azababban gudu izuwa kansu suna masu zare makaman yaƙin su.
Sa'adda mahayin yayi arba da su sarki shazwan suka ya sake ɗimauce wa ya cigaba da murɗa kubar iyakar karfin damtsen sa har gumi ya fara keto masa,
Shi kuwa saurayi Huzmal sai ya ɗauki Yaro Humair ya goya sa a gadon bayan sa domin ya ga abinda zai faru har kwallar takaici ta zubo masa,
Har yazamana tazarar dake tsakanin su dasu sarki shazwan bai huce taku goma ba amma babu alamun kofar za ta buɗe,
Ana cikin wannan hali ne kwatsam bazato babu tsammani sai aka ji kofar tayi kara ta buɗe,
Cikin hanzari mahayin ya kunna kai izuwa ciki tare da saurayi Huzmal dake goye da yaro Humair a gadon bayan sa,
Har Sarkin yaƙi lahmar ya dako tsalle ya saka kafar sa a kofar sai wata irin gagarumar iska ta cimimiyosa tayi wurgi dashi sai da yayi katantanwa a sama sau hudu sannan ta fyaɗashi da ƙasa,
Sannan kofar ta mayar da kanta ta rufe ruf!
Cikin matukar takaici Sarkin yaƙi lahmar ya mike tsaye, sarki shazwan, waziri Rufyan, Sarkin bokaye na cizon yatsa cike da takaici.
Sa'adda su saurayi Huzmal suka samu nasarar shiga cikin wannan kofa sai suka tsinci kansu a cikin wani makeken falo mai ɗauke da kayan ƙawa da alatun jin daɗin rayuwar duniya,
Daga can bangon yamma a falon akwai kofa guda ɗaya hal,
A gefen kofar an ajiye wani kwarangwal ɗin murgunejen zaki amma an cire kasusuwan sa an ajiye su acikin kaskon tsafi
A gefen kaskon an ajiye wata jimammiyar fatar damisa mai ɗauke da wani jan rubutu,
Koda saurayin Yayi arba da abubuwan sai ya taka da kafafun sa ya durfafi inda suke yana mai yafito saurayi Huzmal da hannu yana mai nuna ya biyo bayan sa,
Yayin da aka isa sai wannan mahayi ya ɗauki wannan jemammiyar fata mai ɗauke da jan rubutu ya shiga karantawa a fili Huzmal na saurare,
Yakai ma'abocin wannan gida kayi sani cewa wannan ita ce kofa ta uku daga cikin kofofi biyar na wannan gida,
Bazaka taɓa samun nasarar shiga cikin ta ba face ka ɗauki wannan kasusuwan ƙafafuwan zaki ka sanya a jikin kwarangwal ɗin inda mazaunin su yake,take zasu rikiɗa izuwa Mabudin kofar,
Idan kuwa ka sanya ƙasusuwan ba a mazaunin su ba take ruhin zakin zai dawo jikin sa ya hallaka ka,
Sa'adda mahayin yazo nan a karatun taswirar sai idanun saurayi Huzmal suka zazzaro ya dubi mahayin cikin alamun tsananin damuwa tamkar zai fashe da kuka yace "yakai wannan jarumi shin yanzu taya ya zamu iya sanin ina ne zamu sanya ƙasusuwan zakin har ya rikiɗa izuwa Mabudin kofar batare da mun halaka ba.
Ka sani cewa ahalin yanzu abokan gabar mu suna biye damu kuma tabbas suna son su cimma na,
Koda jin wannan batu sai mahayin ya sunkiyar da kansa ƙasa yana mai nazari Daga can sai ya ɗago da kansa yaja gworon numfashi yai ajiyar zuciya yayi gyaran murya yace"yakai Huzmal ina so ka kwantar da hankalinka domin ina da yaƙinin zamu iya buɗe wannan kofa,
Koda yake cewar a halin yanzu abokan gabar mu zasu iya cimma na anan,kai dai kawai ka zuba idanun kaga abinda zai faru,








































2












Koda ganin hakan sai mahayin ya sanya hannun sa ya ɗauko wannan kasusuwan zaki yana nazarin su har tsawon dakika arba'in
Daga can sai ya sanya kashi ɗaya a jikin kafafun zakin take ƙashin ya fara motsawa wani irin haske naban al'ajabi ya gauraye sassan jikin sa,
Koda ganin hakan sai mahayin da saurayi Huzmal suka ja da baya a tsorace
Sannu a hankali kwarangwal ɗin ya dunga sauya launi har ya dawo izuwa cikakkiyar halittar sa ta zaki,
Kawai sai ya takarkare ya kurma wawan ihu kai ko ganin girman zakin ya isa ya tsorata mutum,
Kafin ɗaya daga cikin su yayi wani yunkuri zakin ya dako suma izuwa inda suke,
Koda ganin hakan sai saurayi Huzmal ya yi koyi dashi suka tari zakin aka ruguntsume da azababban yaƙi mai ban tsoro,
sakamakon saukar ruwan sama a daren jiya,
Hakan ne yasan ya tun da duku- dukun safiya mutane ficewa daga cikin gidaddajin su su ka tafi izuwa kasuwa domin tallata hajar su,
Manoma suka fita gona domin yin noma, babban abinda ya kara sanya mutane farin ciki shine yadda garin yayi lullumi saboda Rashin fitowar rana,
A wannan lokaci fadar kasar ta cika ta batse da al'umma babu masaka tsinke yara, da manya maza da mata
Gaba ɗaya ginin fadar an yi shine da waɗansu irin duwatsu na zubar daju da yakutu, fadar ta ƙawatu da nau'ikan kayan kawa da alatun jin daɗin duniya har da ma abinda idanu basu taba gani ba,
Shimfidar fadar anyi tane da wani koren kilishi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login