Showing 6001 words to 9000 words out of 22575 words

Chapter 3 - SARKIN SADAUKAI Complete by Mansur Usman Sufi .txt

mai taushi wanda idan mutum ya taka shi sai yaji tamkar kafar sa zata nutse a cikinsu saboda haushi.
A ɓangaren yamma na fadar aka kirke wata ƙasaitacciyar karagar mulki da aka sana'an ta ta da zallar mulmulallan jauhari aka yi mata feshi da farin ruwan zinare mai fatsi - fatsi, tana sheƙi da ɗaukar idanun duk mai kallon ta,
Zaune a bisa karagar mulkin wani shirgegen mutum ne fari,mai tarin saje da ƙasumba kirar samudawan farko, yana da mitsitsin kai mai ɗauke da yan mitsi-mitsin idanu jajaye da faffafɗan hanci mai manyan kofofi tare da wani tafkeken baki tamkar kofar gari,. Cikin sa rundememe ne tamkar an kifa masa kwarya,
A jikin sa yana sanye da wata doguwar koriyar alkyabba da aka yi mata cin baki da zaren Lu'u'lu'u
Takalmin dake ƙafarsa yakasance mai ban sha'awa domin idan ka kalle sa sai kaga yana canza launi lokaci - zuwa - lokaci, sanye a kansa akwai lambu na sarauta,
Tabbas wannan mutum ya cika mai kwarjini kuma mai ban tsoro, domin komai dakewar jarumi idan yayi arba dashi dole ne tsoro ya ɗarsu a zuciyar sa,
Kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci cewa yakasance gwarzon mayaki mai tarwatsa maza a filin daga,
Ba wani bane wannan mutum ba face sarki uslaim ibn kahmar,
Sarki uslaim yakasance gawurtaccen mayaki kuma mashahurin attajiri ya hau karagar mulkin kasar Baharen tun da yana da shekaru sha biyar a duniya,
A rayuwar sarki uslaim babu wani abu najin daɗin rayuwa daya rasa domin a kullum yana samun kuɗin shiga da adadin su yakai dinare miliyan ɗari,
Batun dabbobin ni'ima kuma yana da sama da miliyan dubu, ballantana gonaki da kadarori,
Duk wannan abubuwan More rayuwa daya tara bai hana sa jin kamar ya hallaka kansa ba saboda baƙin ciki,
Bakomai ne ya haddasa masa hakan ba sai domin duk sa'adda ya tuna cewa 'yar sa daya fi so fiye da komai bata tare dashi,
Dalilin rabuwar sarki uslaim da yarsa gimbiya zarifakuwa shine kamar haka ,
Wata rana gimbiya zarifa na zaune a cikin turakar ta, Turakar ta ƙawatu ainun da nau'ikan kayan ƙawa da alatun jin daɗin duniya,
A wannan lokaci dare ya tsala yayi duhu dunɗum babu abinda kunne keji face kukan gyare da haushin karnuka,
Tana cikin wannan haline sai kawai taji kukan jariri ya cika bangaren Turakar baki ɗaya,
Al'marin da yayi matukar bata mamaki kenan kuma ya ɗaure mata kai domin a iya sanin ta a gaba ɗaya gidan sarautar babu wacce ke ɗauke tsohon ciki,ko mai shayarwa tsakanin kuyangi da barorin gidan,
Abin tambaya anan shine daga ina wannan kukan jariri yake,
Amsar tambayoyin da gimbiya ta kasa bawa kanta kenan
Abu kamar wasa sai gimbiya zarifa tafi sautin kukan jaririn yana ƙaruwa,nan take taji zuciyar ta bazata iya jurewa ba sai taje ta ceci wannan jariri gama tunanin hakan keda wuya sai kawai ta miƙe tsaye ta nufi kofar fita daga Turakar,ta tura kofar ta fita
Ai kuwa sai taga dakarun dake tsaron wajen sun kamu da barci mai nauyi,
Batare da fargabar komai ba ta cigaba da durfafar inda take jin kukan
Amma abu kamar wasa sai gashi ta har ta fice daga lambun shaƙatawar ta batare da taga inda jaririn yake ba,
Haka dai ta cigaba da tafiya zuciyar ta cike da matukar mamaki da al'ajabi, kawai sai ta ƙara azama domin ta isa inda wata farar kwalba take mai haske,
Yayin da yazamana saura taku goma tsakanin ta da kwalbar ba sai taga cewa wannan kwalba na ɗauke da wani koren ruwa mai yauƙin gaske kuma kukan daga cikin ta yake fitowa,
Al'amarin da ya yi matukar ɗaure mata kai kenan tace a cikin ran ta ya akayi kukan jariri ke fito daga cikin ta kuma wane ne ya ajiye kwalbar,
Haƙiƙa al'amari ne na sihiri, yanzu zan buɗe kwalbar domin naga mene ne a ciki domin dai masu iya magana na cewa da a baka labari gwara ka bayar,
Koda kamma ayyana hakan sai kawai ta ɗauki kwalbar ta buɗe murfinta,
Kaico! Hakika rashin sani yafi dare duhu, inda ace zarifa tasan abinda zai faru da bata yi gangancin bude kwalbar ba ,
Domin koda buɗewar ta sai wannan koren ruwa ya rikiɗa izuwa wani narkeken baƙin aljani mai matukar muni ban tsoro daban al'ajabi, gaba ɗaya jikin sa cike yake da gashi, yana ɗauke da manyan fuka-fukai,
Koda gimbiya zarifa tayi arba da aljanin sai ta ɗimauce ta buɗi baki da nufin ta kurma wawan ihu amma kafin takai ga aikata hakan aljanin ya busa mata wata iska daga bakin sa take barci mai nauyi ya ɗauke ta,
Kawai sai ya suret ta ya luluƙa izuwa sararin samaniya ya ɓace ɓat a cikin gajimare,
Tun kafin ƙetowar alfijir gaba ɗaya gidan sarautar ya hautsine da gujegujen jama'a bisa jin labarin ɓatan gimbiya zarifa,
Abangaren sarki uslaim kuwa lokacin da labarin ya riske sa sai ya haukace ya kama kashe kuyangi da barorin sa,
Al'amarin da ya sanya gidan sarautar ya hautsine kenan kowa ya shiga gudun ceton rayuwarsa,
A cikin wannan haline bokan masarautar ya bayyana ga sarki uslaim a lokacin da yake kai komo a Turakar gimbiya zarifa hannunsa riƙe da takobin sa na digar da jini, fuskar sa a murtuke babu annuri tamkar an aiko masa da sakon Mutuwa,
Koda sarki uslaim yayi arba da boka ƙarzum sai ya bude sa cikin matukar fushi da bai taɓa yin kamar sa ba yace "yakai ƙarzum shin wane shirmen banza kake yi har wani ya shigo gidan sarauta ta sace gimbiya, yi maza ka gano mini wane ne shi kuma ina ya kai ta,
Na rantse da darajar iyaye na sai na yi masa kisa mafi muni da ba'a taɓa yiwa wata halitta ba,
Koda jin wannan batu daga bakin sarki uslaim sai boka ƙarzum ya zube ƙasa ya kwashi gaisuwa cikin ladabi cikin kakkausar murya yace"ya shugabana kayi sani cewa zuwa inda gimbiya zarifa take a halin yanzu dai -dai yake da mutum ya sayi ajalinsa da kuɗin sa bakowa bane ya ɗauke ta ba face Sarkin bokayen duniya wanda a halin yanzu babu mashahurin matsayi kamar sa walau mutum ko aljan,
Ya shugabana kayi sani cewa duk faɗin duniya babu mahalukin da isa yaje inda gimbiya take har ya ceto ta face wani mutum guda ɗaya hal! Wannan mutum kuwa ba wani bane face.
Jarumi Hibairu wanda ake yiwa laƙabi da SARKIN SADAUKAI na duniya
Bincike ya tabbatar da cewa ahalin yanzu babu gwarzon mayaki kamar sa,
Domin an ce yana iya gudun Sa'a goma ɗauke da zakanya a kafadar sa batare da ya gaji ba,
Kuma duk girman zaki idan suka bangaji kirjin juna sai dai zakin ya faɗi ƙasa,
Duk abin da bokaye zasu faɗa game da SARKIN SADAUKAI sai dai su faɗa kawai amma yace yadda ake tsammani,
A wannan lokaci Hibairu na rayuwa ne a cikin daji da ake kira da suna Baitul-shamshan,
Bai taɓa ganin bil'adama face dabbobi da aljan,
Bazai taɓa fitowa daga cikin dajin Baitul-shamshan face a ranar da ya kammala bawa tsuntsun tsafin sa horan yaƙi,tare kammala karance sirrikan dake jikin ZOBEN SHIRIN sa
Tabbas tunkarar Hibairu da buƙatar ceto rayuwar gimbiya zarifa a can fadar Sarkin bokaye dai dai yake neman jaki mai ƙawo,
Ko kuma nace maka dai dai yake da mutum ya siyi ajalinsa da kuɗin sa, domin Hibairu yana magana ne da wani yare guda ɗaya dashi ne kaɗai ya iya shi a duniya domin mahaifiyar sa ta rasu bayan dakika goma da Haihuwarsa,
Sa'adda boka ƙarzum yazo dai dai nan ajawabin sa sai idanun idanun sarki uslaim suka zazzaro kuma hankalin sa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe,
Ya dubi boka ƙarzum tamkar zai fashe da kuka yace
"Ya samanin ilimin tsafi yanzu mene ne mafita, tabbas zan iya bayar da komai da na mallaka domin ceto gimbiya ?
Da jin wannan batu sai boka ƙarzum yayi shiru yana mai dogon nazari gami da sunkiyar da kansa ƙasa,
Daga bisani ya ɗago da kansa sama ya dubi sarki uslaim sannan yaja dogon numfashi yayi ajiyar zuciya yace "ya shugabana kayi sani cewa mafita ɗaya ce in cigaba da gudanar da bincike bisa halarar tsafi na domin gano yaushe ne jarumi Hibairu zai fito daga dajin Baitul-shamshan da kuma hanyar da zamu bi mu bayyana masa buƙatar mu,
Lokacin da boka ƙarzum yazo dai dai nan zancen sa sai zuciyar sarki uslaim ta ɗan samu nutsuwa,
Daga wannan furuci boka ƙarzum ya ɓace ɓat tamkar bai taɓa wanzuwa ba ,
Wannan shi ne dalilin daya sanya sarki uslaim ke zubar da hawaye a kullum
Tun da daga wannan rana sarki uslaim yakasance cikin shirin zuwa dajin Baitul-shamshan domin saduwa da jarumi Hibairu SARKIN SADAUKAI
Haka dai sarki uslaim ya cigaba da tafiyar da sha'anin mulkin sa kamar yadda ya saba,
Lokacin da aka kacame da azababban yaƙi tsakanin su saurayi Huzmal da zakin sihiri a cikin gidan tsira a bakin kofar shiga ta uku
Yazamana cewa saurayi Huzmal da mahayin na kaiwa zakin hare hare cikin matukar zafin nama juriya da bajinta,
Shi kuwa zakin ya wanzu yana mai kai musu hare tamkar wani ifritu,
Nan fa su Huzmal suka fahimci cewa tabbas yau sun gamu da gamon su
Ana cikin wannan fafatawa ne zakin ya shammaci mahayin ya yakushe sa da faratan sa a cinyar sa ta hagu
Take inda ya yakushe san ya haddasa wani lafcecen rauni jini yayi feshi yayi tsartuwa
Kafin shudewar wata rabin sa'a zakin ya samu nasarar yiwa Huzmal da mahayin miyagun raunuka sama da ashirin,
Duk wannan artabu da ake yi wannan yaro makaho na goye a gadon bayan saurayi Huzmal yana jin duk abinda ke wakana ,
Ana cikin wannan gumurzu ne kwatsam bazato babu tsammani sai akaji kofa ta biyu ta buɗe dake bayan su,
Sai suka yi arba da su sarki shazwan, kafin ɗaya daga cikin su yayi yunkuri boka Dargas ya cire wani dogo mashi a damtsen sa mai tsawo kaifi da jinin tsiya ya cillawa saurayi Huzmal da nufin yayi masa kisan farat ɗaya ya hallaka shi,
Cikin wani irin bakin zafin nama Huzmal ya wurkila ya zamewa harin
Bisa rashin Sa'a sai mashin ya soke ɗaya daga cikin idanun zakin
Take zakin ya kama kururuwa,sannan ya rikiɗa izuwa wata bukatar haske take kubar ta tashi sama cikin iska ta shiga izuwa mazaunin da ke jikin kofar ta murɗa kanta. Har sau uku kawai sai ta buɗe
Cikin matukar farin ciki saurayi Huzmal goye da yaro Humair makaho da mahayin suka kunna kai izuwa ciki
Kafin sarki shazwan waziri Rufyan Sarkin yaƙi,da Sarkin bokaye da sauran tawagar su suyi wani yunkuri, kofar ta sake rufe kanta ruf , wannan farar kuba ta sake rikiɗa izuwa wannan kwarangwal ɗin zaki kamar yadda yake a ɗazu..
Sa'adda su saurayi Huzmal suka shige izuwa cikin kofa ta huɗu,
Sai suka tsinci kansu a cikin wani katon fili mai yalwa,
A yammacin filin akwai waɗansu ɗaku na guda biyar,
Ginin ɗakunan an yi sune da manyan duwatsun wuta masu kwarin gaske, kofofin su kuma an yi sune da mulmulallan jan karfe, inda za'a sanya karti majiya karfi mutum hamsin bazasu iya ture ɗaya daga cikin kofofin ba,
A kofar ɗaki na farko an ajiye wani ƙatuwar akwatu ta baƙin ƙarfe,
Ɗaki na biyu kuwa an ajiye waɗansu akwushi guda huɗu, kowane akwushi na ɗauke da ruwa garai-garai kuma ya bambanta da ɗayan wato wani fari,baki,shuɗi da ja,
Kofar ɗauki na uku kuwa yana ɗauke da waɗansu kwalabe da girman su bai huce na gwanda ba,
Suna da ɗauke da wani koren ruwa a cikin su
Kofar daƙi na huɗu da na biyar kuwa an ajiye waɗansu gumaka na waɗansu irin tsuntsaye masu ban tsoro,
Idan mai kallo ya ɗaga kan sa sama izuwa saman kowace kofa ɗakin zai yi arba da waɗansu alluna masu ɗauke da rubutu da aka sassaƙa su da wani itace bishiya,
Lokacin da saurayi Hizmal dake goye da yaro Humair makaho da mahayin sukayi arba da waɗannan ɗakuna biyar sai suka cika da matukar mamaki,
Kuma ya dugunzuma ainun suka kama kalle-kalle da dube dube domin su gano wane ɗaki ne daga cikin ɗakunan biyar ɗin su shiga ga domin isa gidan tsira,
Tsawon daƙiƙa Ɗari da Hamsin ɗayan su bai ce uffan ba, sai daga bisani saurayi Hizmal yayi gyaran murya sannan ya kawo gwaron numfashi ya buɗi baki ya dubi mahayin cikin alamun tsananin damuwa gami da tashin hankali yace yace"ya abokina shin yanzu wane ɗaki Yakamata shiga daga cikin ɗakunan biyar domin mu shiga izuwa gidan tsira tabbas hankali na a tashe yake tunda idan mu kayi rashin Sa'a a karon farko bamu shiga izuwa ɗakin da zamu tsira ba,
To babu makawa abokan gabar mu zasu iya cimma mana har su samu nasara akan mu,
Koda jin wannan batu daga bakin saurayi Hizmal sai mahayin yayi shiru yana mai sunkiyar da kansa ƙasa yana mai zurfafa cikin Kogin tunani,
Sai da ya shafe tsawon daƙiƙa hamsin a cikin wannan hali sannan ya ɗago da kansa sama ya dubi Hizmal sa idanunsa waɗanda su kaɗai Hizmal ɗin ke iya gani ya buɗi baki yace"yakai Hizmal kayi sani cewa a iya tsawon rayuwa ta babu abinda zan sanya a gaba face na cimma nasara akansa,
Naji a jikana cewa wancan ɗauki na biyu shine ɗakin da zamu samu tsira,
Koda jin wannan batu daga bakin mahayin sai Hizmal ya gyaɗa kai alamar gamsuwa, kawai sai mahayin ya shige gaba, saurayi Hizmal na biye dashi a Baya goye da yaro Humair,
Suka durfafi kofar wannan ɗaki na biyu, da isar su daf da kofar sai suka shiga nazarin waɗannan akwushi masu ɗauke da ruwa kala- kala a cikin su.
Daga can sai mahayin ya dubi saurayi Hizmal yace"ya Hizmal ina ganin wannan koren ruwa dake cikin akwushi shine zamu ɗauka mu zuba a cikin wannan mazirari dake jikin kofar sannan ta buɗe,
Koda gama faɗin hakan sai Mahayin ya tsugunna a ƙasa da nufin ya ɗauki wannan akwushi mai ɗauke da jan ruwa a cikin sa,
Sai kawai a kaji yaro Humair yayi magana akaro na farko da fara wannan tafiya,
Al'amarin da sanya mahayin ya fa sa ɗaukar akwushi kenan domin yaji me yaro Humair makaho zai ce.
Yaro ya buɗi baki cikin murya mai daɗi Yace"yaku yan uwana kuyi sani cewa duk da kasancewar bana iya gani da idanuna na kasance makaho amma na fahimci cewa wannan ruwa ja dake cikin akwushi ba shi ne mabuɗin kofar ba domin kuwa duk inda ja yake tashin hankali ne da rashin zaman lafiya,
Ina ganin akwushi mai ɗauke da farin ruwa shine mabuɗin kofar domin duk inda farin abu yake akwai zaman lafiya da kuma alkairi,
Sa'adda mahayin da saurayi Hizmal suka ji wannan batu daga bakin yaro Humair sai suka cika da matukar mamaki da al'ajabi bisa wannan fasaha d hikima da yayi ,
Batare da wani ɓata lokaci ba Mahayin ya sake tsugunnawa aƙasa ya ɗauki akwushi mai ɗauke da farin ya zuba a cikin wannan mazirari dake jikin kofar,
















A Birnin Tehran anyi wata gawurtacciyar sarauniya,kuma Basadaukiya da ake yiwa laƙabi da Abidatul-auliya,
Abidatul-auliya takasance kyakkyawa tagaban kwatance da bokaye da su hasashe suka tabbatar dacewa,
A wannan KARSHEN ƘARNI babu wata mai kyan diri da sura tamkar ta,domin labarin kyawun ta ya bazu a ko ina a duniya,
Daɗin daɗawa kuma ta shahara ainun a fagen sanin alƙalumman sihiri,
Tun sarauniya Abidatul-auliya tana da shekara sha huɗu a duniya ta hau karagar mulkin birnin Tehran,kuma a halin yanzu tana da shekaru talatin cif, amma bata taɓa yin soyayya da wani ɗa namiji ba ballantana tayi maganar aure,
Sautari manyan sarakuna, bokaye, attajirai kan bijiro da bukatar soyayyar su ga sarauniya Abidatul-auliya amma basa samun nasara,
Al'amarin da yayi matukar ɗaure mane ma auren nata mamaki kenan,
Su ka ce aransu anya kuwa sarauniya Abidatul-auliya tana da cikakkiyar lafiya,
Ya za'ace mace takai waɗannan shekaru masu yawa batare da tana son wani ɗa namiji ballantana ta buƙaci namiji a kusa da ita,
Bisa hakan yasanya boka suka shiga gudanar da bincike domin su gano dalilin faruwa hakan
Amma haka suka gama binciken su babu wani cikekken bayani daga gare su,
Abinda basu sani ba shine bakomai ne yasanya sarauniya Abidatul-auliya bata soyayya ba ko batun aure ba sai domin wata matsananciyar lalura da ta addabeta tsawon shekaru masu yawa tun kafin ta hau karagar mulki,
Wannan lalura dake addabar ta Ita ce tsagin jikin ta na hagu yana ɗauke ne da kuturta kowane dare Abidatul-auliya bata iya barci saboda raɗaɗin da kuturtar ke yi mata
Ta samu wannan lalura ne tun tana da shekaru goma sha biyu a duniya wata rana ta shiga izuwa dajin dake makwabtaka da birnin Tehran domin yin farauta,
Abidatul-auliya na tafe bisa kan ingarman doki ja sanye cikin gagarumar shigar yaƙi mai matukar kwarjini daban tsoro,a gadon bayan ta tana rataye da waɗansu zaratan takubba masu kaifi da tsinin tsiya,. Ta wanzu tana tsala Azababban gudu a cikin dajin ma'abocin dogayen bishiyoyi duwatsu,da koramu,
Sai da ta shafe tsawon Sa'a ɗaya tana tsala Azababban gudu batare da haɗu da wani abu mai cutarwa ba, hatta kukan yan kananan tsuntsaye bata ji, al'marin da yayi matukar ɗaure mata kai kenan kuma ya bata mamaki
Domin tunda take fita farauta hakan bai taɓa faruwa ba,
Tana cikin wannan hali ne sai wani tunani ya faɗo mata tunanin kuwa shine anya kuwa bawai gudun da take yi bane abisa dakin ta shine ya sanya namun dajin suka gudu,
Koda tazo nan a tunanin ta sai kawai ta cigaba da sassarfa ,
Abu kamar wasa sa gashi ta shafe wata sa'a ɗaya batare da taji motsin komai ba,
A dai dai lokacin yaki bawali don haka sai taja linzamin domin ta ta tsaya cak!
Sannan ta kama ta sakko kawi sai ta durfafi wata ƙorama mai ɗauke da ruwa garai-garai gwanin ban sha'awa don haka sai ya tsugunna a gefen tayi bawalin,. Sannan ta sanya hannun ta da nufin ta ɗebo ruwan ƙoramar amma sai ta lura cewa fitsarin da tayi ya shiga cikin ƙoramar ya canza launin ruwan,
Sannu a hankali sai kalar ruwan ƙoramar ya canza launi izuwa ja,
Kwatsam bazato babu tsammani sai Abidatul-auliya ta ji an dakamata tsawa mai ban tsoro
Saboda matukar razana bata san sa'adda ta kife a ƙasa ba tana baƙi gami numfarfashi, kuma hantar cikin ta kaɗa tsoro Yakamata ainun,
Daga bisani sai taga wani mutum tsoho tukuf ya bayyana a tsakiyar ƙaramar tamkar yana tsaye ne akan turba,
Mutumin yakasance dogo tamkar bishiyar turare, gashin kansa da gemun sa farare ne solko ɗigon baƙi babu, idanuwan sa jajayene tamkar garwashin wuta, hancin a taɓe yake tamkar ba dashi yake shaƙar numfashi ba, yana da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login