Showing 57001 words to 60000 words out of 131003 words

Chapter 20 - DAUDAR GORA BOOK 2 PDF COMPLETE BY bilyn Abdull .txt

19 Jul 2024

31126

matuƙa garesa. Kallonta yake cikin ido a wani irin yanayin da ke neman sarƙe fitar numfashinsa. Muryarsa a wani irin sanyaye ya furta, “Sune suka baki guba ki bani?”.
Shiru kamar bazatace komai ba, sai kuma ta ɗago ta ɗan kallesa. (To Miya rage kuma? Ai bataga amfanin cigaba da ɓoye masa ba) dan haka kai tsaye kawai ta jinjina masa kanta. “Ni nasan baka buƙatar sai na maimaita komai, domin ban ɓoye komai a zamana gidan nan ga Ajmaal ba, hatta randa nake neman dafin macizai ido rufe na sanar masa, shiyyasa har yanzu zuciyata taƙi daina mamakin miyasa kasha madarar tunda har kaga saƙon kuma...”
Wani murmushi ne ya nema suɓuce masa a hankali, sai dai bai yarda ya bayyana akan fuskarsa ba ya hadiye kayansa yana mai lumshe idanunsa da launinsu ya canja baki ɗaya. Kamar bazai tanka ba sai kuma ya sake buɗe idanunsa ya sauke a kanta cikin wani irin kasalallen kallo da ya tilastata rissinar da nata.
“A ranar banga saƙonki ba dan bana cikin ƙasar nan”.
Ɗagowa tai da sauri ta dubesa. Idanunta a ware cikin rawar harshe ta ce, “Kamar ya baka cikin ƙasar nan? Bayan matarka an mata kisan gilla a tsakanin, hakama tsohon da kowa ke tabbatar da jayayyar da yay da kai ce tasa ka ɓaddashi. Kana nufin kuma da gaske kai ne Ajmaal ɗin dai?”.
Idanunsa ya lumshe ya buɗe a hankali, sai kuma ya miƙe a nutse zuwa gabanta, binsa take ita dai da idanunta da ke a waje gaba ɗaya kamar zasu faɗo har ya kai zaune a kujerar kusa da ita. Zamansa ya maida kafa ɗaya kan ɗaya idanun nan nasa masu kaifi shanye a kanta. Itama ta kasa daina kallonsa, dan gaba ɗaya kamar a rikice ma take. “Duk matar da aka kawo Masarautar nan da sunan tawa ni ke kaɗai na taɓa gani da idanuna, babu wacce ta taɓa rasa ranta ina a cikin masarautar nan kuma. Zaki san Ajmaal kamar yanda kike buƙata domin ina son muyi aiki tare”. Ya ɗan yi murmushin da ya nema ɗauke duka numfashinta batare da ya jira amasawarta ba ya cigaba, “Ki ɗauka anan tare kike da Ajmaal ba Shahan-shan Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ba. Mi kike son sani?”.
Da ƙyar ta iya haɗiye yawu da rawar jikinta, dan itakam kallon komai take kamar a mafarki. Hasalima ya ƙara birkitar mata da kai ne. Cikin rawar murya kamar mai in ina ta ce, “Cafa kai baka taɓa ganin fuskar su ba, suna mutuwa kuma baka cikin masarauta? Taya hankali zai ɗauki wannan maganar?”.
“Ta yanda ya ɗauki zaman Tajwar Eshaan tare da ke anan babu wani shamaki mai shari'a”. Ya faɗa a hankali kamar ba daga shi kalaman suka fito ba. Yawu ta haɗiye da ƙyar tana ɗan tura baki jin ya kirata mai shari'a, sam zuciyarta tama ƙi yarda da wancan zancen nasa, “Ya akai ka zama abokin Sir Fawzan?”. Ta faɗa a hankali tamkar mai tsoron wani ya jita. Shiru babu alamar zai amsa mata idonsa na kallon ƙasa, dan dauriya kawai yake da surutun nan, da alama ita kuma kamar ma yanzu ya fara mata daɗi. Ya ɗan ja numfashi ya fesar a hankali, “A baɗini Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed abokin kowa ne a ƙasar ruman da sunan Ajmaal, dan haka shima Fawzan ya shigo ne kamar yanda kowa ke shigowa, a taƙaice dai na haɗu da shi ne a ƙasar Cuba, lokaci ina wani couse, abinda ya fara haɗamu so bawai sai an maimaita faɗarsa bane, kawai dai sanda nasan shi ɗan ƙasata ne naji farin ciki, na kuma nuna masa cewa nima asalina ɗan canne...”
Yanda yake maganar da ɗaɗɗaya kuma kamar da ƙyar sai taji ya bata tausayi da dariya, ta daɗe da fahimtar magana abune mai wahalar gaske a gareshi. Kamar ko yasan mi take tunanin, sai gani tai ya miƙa mata waya yana ɗan murza goshinsa da ke sarawa. “Mu cigaba a rubuce kaina yana ciwo”.
Dariya abun ya bata, tai murmushi idonta a kan wayar da yake miƙo matan. Kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa a zuciyarta tana faɗin (Miskilanci ma ai cuta ce gaskiya), a zahiri kam sai ta ɗan taɓe baki tana rubuta, “Miyasa randa na haɗu da kai a Eira garden ban ganku tare ba?, bayan kuma shi ya kirani ne dan na haɗu da Ajmaal?” ta mika masa wayar. Rubutun kawai ya tsirama ido harta fara ƙosawa, dan bashi da alamar zai bata amsa. Sai da ya gama shan ƙamshinsa sannan ya amsa a rubucen shima. “Dama banyi niyyar mu haɗun ba, dan ina son na fara sanin waye ke”.
Sosai ta waro idanu tana kallonsa lokacin da ta gama karantawa. Bama ta san bakinta ya suɓuce wajen faɗin, “Saboda mi to?”. Shiru yay kawai ya tsira mata idanu, sai kuma ya ɗago a hankali ya zare wayar daga cikin hanunta.
“Saboda yamun bayanin manufarki da kai tsaye ni ta shafa batare da shima ya san hakan ba” ta karanta. Sake kallonsa tai mamaki na bayyana a fuskarta. Nan ɗin ma bakinta ne ya suɓuce wajen faɗin, “Anya mutumin nan bada saka hanunka aka kawoni gidan nan ba?”.
Wani irin lumshe idanu yay cike da salo ya sake buɗewa a kanta, sai kuma ya saki wani makirin murmushi yana kauda kansa.
“Ka amsa min Please”.
Ta faɗa tana matsowa karshen kujeran da ya maida zaman nasu gab har ƙafanta na gogan nashi. Nan ma babu alamar zai tanka matan tsahon wasu sakkani, kafin ya fiskanceta da kyau kaifafan idanunsa a kanta. “Idan na matso da makashina kusa da ni sai ya zama laifi?”.
Zumbur ta miƙa tafukan hannayenta duk biyu akan fuskarta ta furta, “Ya arrahaman ka kasheni, wlhy ka gama dani. Na shiga uku ni Fhareedah wace irin MAKAUNIYAR ƘADDARA ce kuma wannan ɗin?”. Yanda take kaikawo da sambatun jikinta na rawa kaɗan ya rage ya kwashe da dariya. Amma ya danne da ƙyar, sai dai duk da haka sai da ya kauda kansa gefe yana murmushi. A mamakinsa sai yaji kawai ta fita a wajen da ɗan gudu-gudu. Sosai ya zaro idanunsa, sai kuma kawai ya saki murmushi mai faɗin da har haƙoransa na bayyana a bazata. Murmushin yake shi kaɗai yana faman kare baki idanunsa akan hanyar da tabi.....




★★..... ★....




A yanda hadiman leƙen asirin nata suka shigo yasa ta bama duk sauran hadiman dake zagaye da ita umarnin barinta. Jikkunansu har rawa suke suka fice, a yanda ta zuba musu ido yasa bama su tsaya wani jan jeni ba suka shiga sanar mata komai dan sun san bata buƙatar jan zance da tsaho.
“ALLAH ya ƙara miki lafiya mai amfani uwargida shugabar matan wannan daula. A yau Malikat Bushirat ta baƙunci Uwar masu gida. A yanzu haka ma suna a garden ɗin ta tare har da Daneen...”
Wani irin kallo take watsa musu da kai tsaye suka fahimci manufarta. Sake gurfana sukai a gabanta cike da girmamawa. “Kamar yanda ki ka fi buƙata mun kasance da su a wajen muma, duk da kaɗan ya rage Daneen ta ganemu”.
Fuska ta yatsine alamar ba wannan take son ji ba. Fahimtar hakan ya sakasu cigaba da faɗin, “Sun tattauna abubuwa da yawa, sai dai gaba ɗaya a dunƙule sun ta'allaƙa ne a neman afuwar Uwar masu gida da Malikat tayi. Ta faɗi maganganu masu yawa itama na nuna fushi, sai dai da ga karshe ta sakko harta yafe mata abubuwan da suka farun da dorawa da bata shawara game da al'amarin Zawjata-almilk. Da ga ƙarshen zancen sun kuma dai ya ƙare akan son ƙarin auren Shugaban wannan daula....”
A karan farko Malikat Ashwaq ta miƙe zaune sosai tana kallonsu. “Sai me ya faru?”. Ta faɗa kamar idanun nata zasu faɗo a kansu.
“Babu alamar dai Uwar masu gida ta bada goyon baya, daga hakanne kuma Daneen ta fahimci motsin mu a wajen iyakar abinda muka ji kenan”.
Hannu kawai ta ɗaga musu alamar suje. Suna ficewa itama ta miƙe, da ƴar sassarfa ta bar falon hutawar tata zuwa ɗakin barcinta mafi zama sirri gareta har kafafunta na neman harɗewa........✍️




_Tofa, Malikat Ashwaq yaya dai🥱🏃_





*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*




_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
[5/31, 7:46 PM] +234 703 445 5862: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)






𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻






𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (30)




..........“Ƙoƙarin kare kai bashi zai fidda kowanne mu ba, duk da bazai yiwu ace dukanmu anan ne muka aikata ɗin ba, sai dai dole duk ma wanda ya aikata a cikinmun yake dai. Shin wace irin rayuwa ce muke son ta cigaba da yaɗuwa a wannan zuri'ar tamu ne bayan kasancewar mu jini ɗaya?. Shin mi muke nema wanda UBANGIJI baiyi mana shi ba? Mi muke buƙata da ga siffofin shugaba na gari da ALLAH bai azurta bawan ALLAHn nan da shi ba da a kullum muke son nuna bore da hukuncin ALLAH? Ni na rasa gane mi duk mai ƙoƙarin assasa fitine-finen nan ke buƙata ba ko san zuwa. Shin mulkin yake so ne? Ko kuwa rayuwar wannan bawan ALLAH da'a kullum alkairinsa ke zagaye da mu..” takaici ya saka hawaye ziraro masa. Handkherciff yasa ya share tare da sake dubansu ya cigaba da faɗin, “Shike nan babu mai hana koma waye yin yanda ya ke so, sai dai ya sani a duk randa yazo hanunmu wlhy ko shi waye a cikinmu sai yayi dana sani da nadamar kasancewarsa cikin zuri'ar mu. Sannan tarihi zai masa tanadin da bazai taɓa goge sunansa ba a matsayin azzalumi mai fuska biyu a cikin zuri'ar mu. Wannan faɗan ba nashi bane namu ne, dan mu nan da mu akeyi ba da shi ba, dan haka duk wanda ya shirya bismillah muma mun shirya”.
A zahirance duk nuna goyon baya a kan maganarsa sukai, sai dai a ransu ji suke kamar su shaƙo wuyan Sayeed Tasadduq-Husain ɗin. Yasan da hakan, shiyyasa ko kallo babu wanda ya ishesa a cikinsu, ya kuma ci dubu sai ceto. Miran Arshaan da gaba ɗaya ya ke jin kamar ya danne Sayeed Tasadduq-Husain a wajen ya masa yankan rago ya taushi zuciyarsa da ƙyar, dan wannan wata dama ce a garesa, rashin ganin Miran Jasim a wajen yay masa da ɗi, dan haka ya miƙe cike da dakewa da tsan-tsar iya makirci shima ya fuskancesu ya zuba kausasan kalamai, da ga ƙarshe ya rufe da faɗin, “In ma tsoro da kunya sun hana duk ma wanda ya aikata ɗin zuwa nan batare da mun farga ba to na tabbata akwai mabiyansa da irinsa anan ɗin, sai su isar da saƙonmu na tabbatar da duk randa mutum yazo hanunmu sai ya yabama aya zaƙinta a wannan masarauta kamar yanda Sayeed Tasadduq-Husain ya faɗa”.
Kalamansa kam tabbas sun saka wasu fara hasaso abinda yake son dama ai hasashen, sai dai babu wanda ya furta a zahirance aka cigaba da tattaunawa.


Ya ɗauka tsahon lokaci da su a falon suna tattaunawar, dan suna fitowa da ga zaman ma masallaci suka zarce sallar la'asar. Bayan an idar ya koma sashensa. Bai nema Iffah ba yanzun kam. Dan yana buƙatar ɗan hutawa saboda yau zai ɗanyi fitar dare ta sirri zuwa cikin gari. Sai dai koda ya shiga ɗakin ma sai yaji baida buƙatar kwanciyar saboda ransa a matuƙar ɓace ya ke har yanzun. Tashi yay ya canja kayansa cikin wasu fararen wando da riga tas na kamfanin *Nike* da sukai masa matuƙar ƙyau duk da ya sane badan kwalliya ba. Takalma ya ɗaura a ƙafarsa baƙaƙe ya ɗauka p-cap a hannu ya fito cikin takun nan nasa mai tabbatar da shi ɗinne dai ko da ga nesa. Cikin sauri amintaccensa ya miƙe ƙansa rissine, ba sai yace masa ga abinda yake buƙata ba, kai tsaye ya fahimci inda suka dosa. Kafin ya ƙaraso gareshi yay saurin ɗaga waya yay kiran sarkin barga. Ana ɗagawa yay saurin bashi umarnin shirya dokin amana da kowa ya san in ba shi ba Shahan-shan ɗin baya hawan kowanne doki a gidan. Wayar ya katse dan dai-dai da isowar Tajwar Eshaan ɗin, ganin ya nufi elevator batare da ko kallon inda yake yayi ba shima ya zabura. Cikin sauri ya danna floor 1 bayan ƙofar ta maida kanta ta zuge.
Suna fitowa da ga lift ɗin ɓoyayyar hanyar da zata fiddasu batare da ko hadiman ƙasan sungansu ba ya nufa, amintaccensa biye da shi. A wani ƙaton fili suka fito, an gyara wajen da wani irin farin yashi mai matuƙar ɗaukar idon mai kallo da birgewa. Kasancewar ruwan saman da aka sha sai wajen ya sake bada wani yanayi mai matuƙar daɗi ga sassanyar iskar da bishiyoyin da aka ƙawata wajen na dabino na bayarwa. Da ga ɗan nesa da su Sarkin barga ke riƙe da ƙyaƙyƙyawan farin dokin da shi da kansa ya raɗa ma abinsa suna da ƙyautar ALLAH. Kamar yanda ɗabi'ar dokin take suna fitowa yay wata irin haniniya da girgiza kai kace ƙamshin Tajwar Eshaan ɗin yake ji ya shaida kasancewar sa a waje. Da wani irin gudun bajinta ya nufosu, yana isowa gabansa yay wata irin ƙwafutar ƙasa yay girgiza da haniniya, har gashin saman kansa zuwa wuya na wani tarwatsewa da haɗe kansa waje guda. A hankali Tajwar Eshaan ya lumshe idanunsa yana sakin sassanyan murmushi da mutane kan jima basu gani tare da shi ba sannan ya kai hannu ya shafi fuskar dokin yana masa magana ƙasa-ƙasa da ko Sarkin barga da amintaccen hadiminsa dake tsaye gefe kawuna a risine basa iya jinsa. Cikin wani irin salon da ke tabbatar da ƙwarewarsa a iya sarrafa dokin ya damƙi linzamin sa cikin action mai matuƙar ɗaukar hankali da bajinta ya ɗane saman sa. Cikin tabbatar da ƙwarewar da dokin ya samu a hanunsa yay wata irin haniniya da ƙwafutar ƙasa ya ɗiba hanya tamkar a filin polo. Rere suka fara ɗan gaske da sauran dokunan huɗu da aka sakakarma linzami batare da kowa a kansu ba. Duk wanda ya ga yanda yake sarrafa dokin basai an faɗaba ya san shi ɗin ƙwarren ɗan wasan polo ne kuma jarumin gaske. Dan cikin ƙanƙanin lokaci yay ma sauran dokunan da babu kowa ɗin fintinkau, har ya sake dawowa ya koma sannan su suka iso. Kaida gani kasan yana nishaɗi da wasan matuƙa. Sosai su sarkin barga ke murmushi da jinjina jarumta irin ta gwarzon Sarkin nasu. Ko'a cikin dubu shi ɗin na dabanne da kai tsaye za'a nuna a shaida. Dan suna da tabbacin da a lokacin yaƙi ne yazo babu abinda zai hana ya zama babban jarumin da tararsa a filin daga abin tsoro ne. Ya ɗauka tsahon lokaci yana wasan dokin har sai da yaji ya gamsu jininsa ya tashi fiye ma da yanda yake buƙata sannan yaja linzamin dokin ya dire bisa ƙasa cike da bajinta yana sauke numfashi ɗaya-ɗaya. Da sauri amintaccensa ya matsa garesa hannunsa ɗauke da ƙyaƙyƙyawan tray mai ɗauke da gorar ruwa da glass cup. Goran ruwan ya ɗauka batare da ya haɗa da cup ɗin ba, ya ɓalle murfin ya kai bakinsa. Yasha kusan fin rabi sannan ya juyo ya juye sauran akan fuskar dokin nasa yana ɗan murmushi. Haniniya dokin yayi mai nuni da isharar jin daɗin kasancewarsa da adalin ubangidan nasa. Shima sai ya kai hannu ya share masa ruwan yana murmushi. Ƙaramin towel Sarkin barga ya miƙo masa da sauri, bai musaba ya amsa ya goge hannunsa da wuyansa sannan ya kai shi ga fuskar dokin shima ya share masa ruwan da ƙyau. Yanda yake ma dokin da kansa dolene ka tabbatar akwai matuƙar shaƙuwa a tsakaninsu mai birgewa da ƙayatarwa. (Ko dabba ma ta san me bata kulawa da nuna ƙauna kenan☺️😘)


★★...... ★.... ★...


Karo na biyu kenan da ta sake dawowa ɗakin ta samesa yana kai kawo rai a ɓace. So take taji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login