Showing 72001 words to 75000 words out of 131003 words
Chapter 25 - DAUDAR GORA BOOK 2 PDF COMPLETE BY bilyn Abdull .txt
Zamansu sam babu daɗi a tsahon shekara bakwai da suka kasance tare, dan sai tayi da gaske yake haɗa shimfiɗa da ita. Farin ciki kam babu tsakaninsu, dan ko murmushi sai dai taga yanayi amma ba ita ba har ALLAH ya ɗauke abinsa. Bayan barinsa duniya ta koma cikinsu Miran Arshaan a dalilin jin sirrinsu da tayi, a nan ne itama take sanar da su burinta na rama duk abinda Tajwar Haysam yay mata akan Tajwar Eshaan. Daga nanne kuma Miran Jasim ya koma nemanta, a ɓoye kuma tana tarayya da Miran Arshaan shima. Wannan kenan ALLAH yasa dai kun gane dan nidai na zayyano babu ruwana🥱).
★... MALIKAT BUSHIRAT ★....
Tunda ta shigo sashen nata ta zube tama kasa motsawa. Babu abinda ke mata zuwa da dawowa sai fuskar yarinyar da abinda ta gano a cikin idanunta. Tabbas anzo wajen, kuma lallai anzo gaɓar. Gaɓar da a farko ba ita tai hasashen zuwa ba. Wai ita, ita Malikat Bushirat, mahaifiyar Shahan-shan mai mulkin karagar ikon ƙasar ruman baki ɗaya, yarinya ƙarama, ƴar talakawa ta kalla tsabar idanunta, ta sanar mata _inma ta kasheta ta kashe maciji ne bata sare kansa ba, ko bata numfashi, ruhinta zai dawo bibiyar fansar ruhin ƴan uwanta_. Kai kai kai, wannan wace irin rana ce, wace rana ce haka tazo gareta? Itace fa, ita ɗin nan dai, tauraruwar taurari, farin wata fitilar samaniya, rana mai rabama kowa aiki, taiku mai ruwan ban mamaki, zakanyar da ba'ai mata wargi, buhun ƙayar da ba'ai masa danni, mace mai kamar maza kwarine babu. Bahun barkono ba'ai masa shiƙa. Kokino ba giyar yaro ba sai dai manya karami yasha ya kwana a jeji. Giwa taku da ga nesa isharar yara, ƙarfe baka karyuwa sai da wuta, MALIKAT matar Shahan-shan uwar Shahan-shan ƴar asali jinin asali. Takai zaune daɓas jin hajijiya na neman zubar da ita. A hankali ɗakin ya shiga juya mata, sai kawai ta lumshe idanun ko hakan zai bata salamar da take buƙata.....
★★.. SHAHAN-SHAN ★★...
Bayan ta gama zayyane masa birkitattun zantukanta guduwa tai tabar ɗakin, har yayi yinƙurin bin bayanta ya fasa. Amma ko sau ɗaya bai rintsa ba, saboda yanda kalaman nata masu tsananin saka ruɗani ke masa kai kawo. Zai iya rantsuwar wani mahaluki bai taɓa bashi tsoro na gaskiya ba kamarta, tabbas yana buƙatar sake sanin ainahin wacece yarinyar nan bayan sanin da ta sanar masa a baya. A hankali tambarin nan ya sake masa flash a cikin idanunsa, tare da kalamanta akan bashi madara da cewar ita ke amfani da su ba sukeyi da ita ba, ita ta kawo kanta nan bashi ya kawota ba, sai kawai yaji zuciyarsa na wani irin rawa, ga kansa da ke masa sarawar ciwo tun a dare da ta barsa.
Da ƙyar ya iya ajiye komai a gefe ya tashi zuwa bathroom, sai da ya fara wanka sannan ya fito yay nafila ya ƙarasa da shirin fita massalaci.
★....
Saɓanin shi kaɗan ita Iffah tana baro ɗakin zubewa tai a inda ta shigo sai barci, takai tsahon awa uku tana barcin kafin ta farka a firgice. Ta jiƙe sharkaf da zufa bata wasa ba, ga mummunan mafarkin da tai na mata matuƙar kai kawo, dole ta dangantashi da mummuna, dan yau ne karo na farko data farayinsa. Addu'a ta shigayi kamar yanda kaka ya gargaɗeta a duk sanda tai irin mafarkin, sai da ta samu ƴar nutsuwa sannan ta miƙe. Bathroom ta shiga ta wanke fuskarta, tsaye tai a gaban mirror tana kallon kanta, sai ta dinga hango kamar duhu-duhu ta bayanta, babu alamar zata tsorata, sai ma sake ƙurama mirror ɗin ido tayi, amma a ranta addu'oi take karantawa. Dishi-dishin ta cigaba da kallon abun, sai kuma ya shiga bajewa kamar wani hayaƙi ya fara ɓacewa. Juyowa tai a hankali, abin mamaki sai ko gashi a zahiri hayaƙin yana bajewa cikin ƴan sakkani ya ƙarasa ɓacewa ɓat. Ajiyar zuciya mai nauyi ta ja ta fesar, cikin halin ko'in kila kuma sai ta ɗage kafaɗa da sake juyawa ga mirror ɗin tana kai hanunta ta baya ta ɗan shafo gefen kafaɗarta ta dama, zuciyarta na raya mata ta ɗaga rigar ta gani, wata kuma na ture mata tunanin da cewar mafarki fa ba gaskiya bane. Rashin matsaya ya sata ajiye komai gefe ta ɗaura alwala ta fito. Nafila tayi kusan awa ɗaya harda karatun Alkur'ani duk da batai mai yawa ba ta koma gado ta kwanta. Maimakon barci sai abinda ya faru tsakaninta da Malikat Bushirat ɗazun ya shiga dawo mata a rai, tasan ta shaƙeta, bata tashi tsintar kanta ba sai a jikin Shahan-shan tana haɓo. Ya taimaketa ya tsaya har tai wanka ya bata kayansa ta saka ya bata shayi, da ga shan shayin ne bata tashi tsintar kantaba sai yanzu a ɗakin nan da ta farka da ga mummunan mafarkin nan. Ya akai ta shanye shayin daya bata da yanda tazo nan ɗakin bata sani ba..........✍️
_🚴Tofa wata jiƙaƙƙiya, Shahan-shan kayi takanka Iffah dai da alama ba.... (🥱Bara dai na gimtse bakina)_
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN
MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171
SAI A TURA SHAIDAR BIYAN
09033181070
IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA
09166221261
*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*
+227 96 09 67 63
Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA
KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.
MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*
[5/31, 7:48 PM] +234 703 445 5862: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲
✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)
𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻
𝕭𝖔𝖔𝖐 𝖙𝖜𝖔 (36)
.........Yana cikin Gym ɗinsa tun barowarsa masallaci sallar asuba yana motsa jiki amintaccensa ya isar da saƙon neman iso da ga Sayeed Fayzul-haq. Sayeed Fayzul-haq shima amintacce ne a garesa yanzu, dan haka ya bada izinin shigowar tasa. Kallo ɗaya Sayeed ya masa ya duƙar da kai, dan yau motsa jikin yake ko riga babu, dogon wando ne kawai bai sa rigar ba, sai ƙaramin towel dake saman kafaɗarsa ya taimaka wajen rufe jikin nasa. Batare da ya daina abinda yake ba balle kallon Sayeed ɗin cikin ƙasaitar nan tasa da zafin da Iffah ta haɗa masa a daren jiya muryar ta sake komawa ƙasa ya furta, “Akwai wata damuwa ne?”.
Sayeed Fayzul-haq yay saurin sake risinawa cike da girmamawa yace, “Eh to badai mai yawa bace. Tun a daren jiya naso sanar da kai sai kuma na fasa dan nasan ka shiga barci. Akan Miran Jasim ne da iyalinsa......” nan ya zayyane masa komai a nutse.
Ɗan murmushi yayi a karo na farko batare da ya ce komai ba har tsawon wani lokaci da Sayeed ya fidda ran cewar tasa ma. Machine ɗin da yake kai ya kashe, ya sakko yana jan towel dake a kafaɗarsa rataya ya shiga tsane wuyansa zuwa fuska. Zufa yake sosai kamar wanda yay wanka. Zama yay a kujera, da sauri Sayeed Fayzul-haq ya ɗan zuba ruwa a kofi ya miƙa masa. Baiyi musu ba ya amsa, sai dai kurɓa huɗu yay ya ajiye dan bai damu da shan ruwa ba idan ya gama motsa jiki, yafi son shan shayinsa na ƙa'ida.
A fisge kamar an masa dole ya ce, “Mi Doctors ɗin sukace akan jikin nata?”.
Yasan Matar Miran Jasim ɗin daya daka yake magana, “Ya shugaban sun tabbatar da taji ciwo musamman a ƙashin bayanta da ya taka. Wannan shine result ɗin binciken nasu.” ya faɗa yana miƙa masa takardun dake hannunsa. Amsa yay batare da ya duba ba ya ajiye gefensa. Hakan ya tabbatar ma da Sayeed ɗin yana buƙatar lokaci, dan shima tunda ya shigo ya fahimci yau ƴan miskilancin ne da mulki a kusa. Dan haka ya rissina ya masa sallama. “Afito lafiya”.
Idanunsa kawai ya lumshe batare da ya tanka ba. Shiru yayi a gurin kamar mai nazari, idanunsa ƙyam akan file ɗin.....
★★....
Makarar da tai ya ja mata yin salla ba'a kan lokaci ba, ga jikinta na mata ciwo sosai tako ina har tana jin buƙatar ɗan motsashi ko zata samu sassauci. Gym ɗin da ta gono ranar a leƙe-leƙenta ta tuna. Yanda ya ƙayatu ya sake zaburar da ita ta miƙe tana murmushi. Fitowa tai da ga ɗakin data kwanan batare data damu da rashin ganin Tajwar Eshaan ɗin ba kasancewar tasan ɗakin barci dama ai sai wanda ya zaɓa. Ɗakin jiya ta koma, ta buɗe kayan da tai online shopping ɗin nan da har yanzu suna a jakar da aka kawosu. Pink kayan training ɗin nan na Company Adidas da suka ɗauka hankalinta tun a waccan ranar ta ciro ta fara kimtsawa. Tsaf ta fito cikinsu kamar wata babyn roba, bata damuba da yanda rigar ta tsaya mata iya kan ciki har ana ganin jikinta, hakama wandon ya matuƙar kama jikin nata. Kayan sun fidda mata ainahin shape ɗin ta masha ALLAH. Duk da tasan babu kowa da zai ganta sai da ta ɗaura after dress a sama. Cikin ranta take addu'ar ALLAH ya sa dai yana can sama yana motsa nasa jikin dan tasan dai da wahala ace ya fita iyanzu.
Ganin hadiminsa a ƙofar Gym ɗin da yay saurin zubewa yana gaisheta bai sa takawo a ranta yana ciki ba, dan idanunta sun rufe da son zuwa ta ɗana machines ɗin nan masu ƙyau. Cikin sassanyar muryarta tai sallama tana shigowa kanta tsaye. Kamar wanda aka farkar da ga barci ya buɗe idanunsa da ke a lumshe. Sai dai kuma bai motsa ba ya kai dubansa ga ƙofar shigowar inda yaji muryar tata ta gefen ido. Mamaki ne ya kamashi dan baiyi zaton tama san da Gym ɗin ba, ganin kamar bata lura da shi ba ya sake lafewa yana kallon ikon ALLAH.
Da ƙyar ya iya riƙe numfashinsa yana lumshe idanu da buɗewa lokacin data gama yaye after dress ɗin data ɗoro saman kayan training ɗin ta ajiye kan wani machine. Tun da ga saman gashin kanta dake ɗaure da ribbon a tsakkiya yana lilo har zuwa takalma ɗin ƙafarta yabi da kallon nan nasa na ƙasan ido. Idanun ya sake lumshewa yana ambaton sunan ALLAH, dan yau ne karan farko da ya taɓa ganinta a ainahinta kamar haka, dan kayan sun lafe mata da ƙyau da fidda ainahin surarta fiye da jiya da ya ganta da towel.
Oho ita dai bata san yana yi ba, sai ma faman kokawar yanda zata kunna machine ɗin data hau take yi. Hararar Machine ɗin tayi tana ɗan diddira ƙafa na haushi. Ya ɗan murmusa yana kauda kansa. Kusan sakkani ashirin ya miƙe a hankali yana ajiye towel ɗin hannunsa. Tana ɗan duƙe da cigaba da ƙoƙarin son kunnawar taji ɗumin mutum a bayanta. A zabure ta ɗago gabanta na faɗuwa, jikinsa ta jingina kasancewar tsaye yake bayanta daf da ita sosai, shigewar idanunsu cikin na juna ya sake ruɗar da ita ta janye jikinta da sauri tai baya sai ta koma tana fuskantarsa. Kif-kif ta farayi da idanunta daka ganta kasan a ruɗe take, dan cikin sarƙewar harshe ta furta, “Good morning”.
Ɗauke kansa yay cike da basarwa ya ɗan sake matsowa batare da ya amsa gaisuwar datai masan ba, idanunta ta rumtse da sauri ta sake juyawa a yanda take farko ta bashi baya. Kallon bayan nata ya sake ɗan yi ya kauda idanun, kaɗan ya motsa lips ɗinsa murya can ƙasan maƙoshi cikin kunnenta ya ce, “Bissmillah” yana kai hannu ya kunna mata tare da jan jikinsa baya duk a lokaci guda. Ji take inama ƙasa ta buɗe ta shige ciki kawai ta huta. Tayi dana sanin shigowa Gym ɗin nan a zuciyarta yafi sau dubu. Jin machine ɗin na neman zubar da ita ƙasa yasa dole ta fara ɗan yin gudun, sai kuma ta sauke nannauyar ajiyar zuciya hangosa ya juya mata baya ta cikin mirrorn da aka zagaye Gym ɗin gaba ɗaya. Yanzu kam ya saka riga, duk da haka ta kasa sakewa, kaɗan-kaɗan sai ta kai dubanta kansa da ga inda yaken gaban teburin wasan basket ball dan shima game ne mafi soyuwa a ransa bayan wasan polo da ƙwallon ƙafa.
Duk abinda take yana hankalice da ita sarai, amma ya fuske domin bata damar motsa jikin yanda ya kamata. Cikar mintuna ashirin da hawanta machine ɗin ya ajiye ɗan abin 🎾 wasan basket ball ɗin ya nufeta. Ta gabanta ya zagayo, idanunta a rufe da alama hakan yafi mata daɗi ko ta rufene dan shi oho. Da haƙori ya danne lips ɗinsa yana kauda idanunsa da ga inda suka sauka, kashe machine ɗin ya sata buɗe ido da sauri, dan duk da taji ƙamshinsa ya sake kusanto ta batai zaton shi ɗin bane ba. Kamar zata fasa kuka ta duƙar da kanta da sauri tana tura baki gaba.
Lips ɗin nata ya ɗan zubama idanu, sai kuma ya janye yana ƙoƙarin barin wajen da faɗin, “Next..” a hankali. Wani irin kwarjini da shakkarsa takeji, sai taji bazata iya masa musu ba sam. After dress ɗinta ta ɗauka tana maidawa jikinta tana nufarsa inda yake gaban wani machine ɗin. Komai baice mata ba akan after dress ɗin, ya nuna mata yanda zatai da hannu ya bar wajen. Yanzu ma tanayi tana satar kallonsa, ji take rigar na neman taɗeta amma ta fuske sai ɗan tattarota da tai a hannu ta cigaba da yi da sauri-sauri dan ya fara mata daɗi. Yanda ya basar da ita baya kallon ko inda take sai take jin ƙarin ƙaimi...
“Wayyo ALLAH na!”.
Siririyar muryarta ta ratsa kunensa a bazata, dan basket ball ɗin da yake ta fara janye hankalinsa shima ba kallonta ya ke ba. Tsabar ƙasaita ta zame masa jiki a hankali ya juyo duk da zuciyarsa na wani irin harbawa da sauri-sauri, ganinta a ƙasa wanwar ya sashi nufarta da ƴar sassarfar da bata canja komai a takun nutsuwarsa ba. Itako ganin yanda yake tafiya kamar ma bai ga faɗuwar da tai ba sai kawai ta fashe da kukan da ita kanta tasan na taɓara ne, dan koda ta faɗi ba wani ta bugu bane sai dai tanajin zafi a ƙafarta da ƙugunta sosai gaskiya. Kaifafan idanunsa ya sauke a kan hanunnta dake dafe da ƙugun nata, ɗayan kuma a agarar ƙafarta madaidaiciya fara sol.
“What is Happening?”.
Ya faɗa da ƙyar fuskar nan babu alamar fara'a tattare da shi balle nuna alhini, a can ƙasan ransa kam zafi yake ji a jikinsa shima kamar yanda ya fahimci tana ji. Wani kukan taɓara-taɓara ta sake fashe masa da shi tana nuna masa agarar ƙafarta da faɗin, “Shikenan ƙafana ya cire, ni dai ka kiramin Mamy da Jaddah wayyo ni Ummu, Iyyani ƙafana ya karye Hanash Akhi”.
(Stubborn girl) ya faɗa a zuciyarsa idanunsa na wani shanyewa a kanta. A zahiri kam yi yay kamar zai share sai kuma ya kai duƙe gabanta a hankali. Maimakon duba ƙafar da take faman riƙewa cak ya ɗagata a wajen. Babu shiri tai saurin saƙalo hanunnta a wuyansa jin kamar zata faɗi tana waro manyan idanunta. Fahimtar magana zatai ya kauda idanunsa, a can ƙasan maƙoshi kamar an masa dole ya furta,
“Ban son surutu..”
Takaici kamar zai shaƙe Iffah ta cuna bakin nan gaba ta kauda kanta gefe itama lips dinta na motsawa da alama magana take wadda ba'aji. Ganin inda ya nufa da ita ta ɗan sauke ajiyar zuciya a ɓoye, yana sauketa a gadon ta yunƙura zata tashi, maidata yay ya kwantar yana watsa mata shegen kallon nan nasa na ƙasan ido da Iffah ta kasa gano fassararsa har yanzu, ba zato taji ya ture hanunta da ke dafe da ƙugunta dan anan tamafi jin zafin faɗuwar ya maye gurbinsa da nashi........✍️
_🥱To kuma dai, Ni na gaji da wagga lalata ta Iffah. Anya bazan koma team Shanshani ba😒😬🚴._
*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*
*DAUDAR GORA Billyn abdul*
*KI KULANI hafsat xoxo*
*A RUBUCE TAKE Huguma*
*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*
*IDON NERA Mamuh ghee*
_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_
_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_
_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_
_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_
_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_
_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_
_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_
ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE