Showing 93001 words to 96000 words out of 131003 words

Chapter 32 - DAUDAR GORA BOOK 2 PDF COMPLETE BY bilyn Abdull .txt

19 Jul 2024

31088

cikin gashinta. Ɗan kwantar da ita yay da ga zaman karkacewar da tayi, ya miƙe ya ɗauko ɗaya da ga cikin wayoyinsa. Gabanta ya sake zuwa ya dirƙusa ɗin dai maimakon zama da ya saba yi, ita inba a gaban UBANGIJINSA ba yayin bauta masa bata taɓa ganinsa durƙushe haka gaban wani ba. Duk da bawai yayi wani durƙuso bane na ƙasƙanci. Hasalima yanda yay ɗin sai ya ƙawatar irin masoyi a gaban masoyiyyarsa ɗin nan da suke cikin tsananin shauƙi ma juna. Contact ɗinsa ya shiga sannan ya miƙa mata wayar. Karɓa tai tana sake kumbura fuskar nan da tai jazur duk a suntume musamman idanunta. Kalmarsa ta zai ƙara ne ya sata danne hawayen tilas badan ta gaji da kukan ba. Number Mammy ta lalubo, taja wasu sakkani kamar mai tunani ko tsoron kiran sannan tai dialing. Bugu biyu zuwa na uku kuwa aka ɗaga. Da sauri ta rumtse idanunta hawayen da take riƙewa na ɓulɓulowa. Da ga can jin anyi shiru Malikat Haseenat da ta ɗauka wayar kasancewar Daneen Ammarah ta shiga wajenta sanar mata Malikat Bushirat babu lafiya tace ta haɗa mata ruwan wanka shine ta bar wayar gefenta, ita kuma ganin number Tajwar Eshaan yasa ta ɗauka da tunanin ko shima zancen Malikat Bushirat ɗin ne. Amma sai kuma taji anyi shiru ga kuma kamar ana jan ajiyar zuciyar kuka da ake ƙoƙarin dannewa yana son fita.
“Assalamu alaikum”.
Ta faɗa a nutse cike da dattakonta. Kamar an ƙwalama Iffah farantin silver saman kai da sauri ta ɗauke wayar a kunnenta ta miƙa masa kukan da take dannewa na kufce mata. Bashi da zaɓin amsar wayar shi ya kai nasa kunnen, tunda har aka riga aka ɗaga bashi da hurumin cewa zai yanke sai ya sakata a tashin hankali. Wayar ya kai kunnensa yana mikewa da yin sallama cikin sassanyar muryar nan tasa mai cike da nutsuwa da kame kai. Malikat Haseenat ta lumshe idanu da sakin ajiyar zuciya ta amsa masa. Cikin mamaki yace, “Jaddah ke ce? Ina Mammyn?”.
“Tana haɗamin ruwan wanka ne. Ina fatan lafiya dai ko naji kamar ana kuka da farko?”.
Ji yay duk yama kasa cewa komai, a karo na farko na rayuwarsa yaji yana jin nauyin kakar tasa. Amma sai ya daure da ƙyar acan ƙasan maƙoshi ya furta, “Fhareedah ce Jaddah. Dama muna buƙatar Mammyn ne anan”.
Malikat Haseenat tsohuwar ƙwarai mai ran ƙarfe da cikar kamala. Sai kawai ta saki murmushi batare da ta nuna ma ta fahimcesa ba tace, “Oh to bara ta fito sai a sanar mata”.
“Uhum”.
Ya faɗa ciki-ciki. Bata sake cewa komai ba itama ta yanke wayar... Nannauyan numfashi ya sauke yana ɗan murza goshinsa. Sai kuma ya kalli Iffah da ta rufe idanu hawaye na cigaba da tsiyaya. Shi kam yama rasa gane kan wannan kuka, amma ya fahimci harda shagwaɓa da ragwantakar tsiya sai shegen tsiwa bakinta babu mai iya kadata a zance. Amma gashi a ɗan tabatan da yay da bai wuce ko ƙwayar zarra da ga abinda ke tattare da shi ba ya sauke take wannan rakin. Lallai ashe akwai aiki gabansa dan ba'a fara komai ba wannan sharar gona ce. (🚴🚴Taɓɗi).
Tashi yay ya yaye bedsheet ɗin gadon dan yayi ma kansa alkawarin gyara sirrinsa da kansa. Gudun karma ya barsu a gani closed dinsa ya wuce da su ya adana. Sai kuma yama ga su bar ɗakin kawai, dan haka ya zo ya ɗauketa zuwa ɗakin kusa da wannan ɗin ya rufe wannan...


Cikin abinda baifi mintuna goma ba sai ga kira da ga amintaccensa. Bayan gaisuwa da yay masa cike da tsantsar girmamawa ya nema wa su Daneen Ammarah iso. Duk da yaji mamakin jin kamar su biyu ake nufi kai tsaye ya bada umarnin ya shigo da su room 3. Karo na farko kenan bayan ita da ke matsayin matarsa da wani zai shigo jerin bedrooms ɗin sa na saman nan gaba ɗaya. Dan ko su matansa da duk aka kawo nan suka rasa ransu a hawa na huɗu ake ajiyesu. Iffah ce ta farko da ta taɓa hawowa hawan ƙarshen nan.
Ba shi kawai ba, hatta da Iffah da tayo gayyar sai da ta daburce da jin sautin muryar Malikat Haseenat na sallama. Amma jarumin naku sai yay ɗam da fuska daɗa duniya bai aikata komai ba babu alamar ko gezau tattare da shi. Sai dai kasancewar sa mutum mai tsananin kunya sai ya kasa yarda ya haɗa ido da Malikat Haseenat ɗin. Dan ita kaɗai ta shigo Daneen Ammarah na falo ta kasa shigowa. Bata san dalili ba kawai taji bazata iya ba, dan zuwan ma sai da Mammah ta tilasta mata harma yanda ta nuna ya bama Malikat Haseenat ɗin mamaki matuƙa dan kunya ce a bayyane kamar wadda zatai gamo da surukinta.
A hankali ta cigaba da gara kekenta cikin ɗakin idanunta na yawo kan Tajwar Eshaan da tun kallo guda da yay mata bai sake ba da Iffah da ke duƙunƙune a gado cikin bargon da ta sashi ya lulluɓa mata saboda rawar sanyi da takeyi. A gaban Iffahn ta dakata, a hankali cikin dattakonta da ƙasaita ta kira sunanta da kai hannu ta janye bargon data lulluɓe har kanta da shi. Ɗan zabura Iffah tayi, sai kuma tai saurin maida kanta tana hawaye. Tausayi yarinyar ta bata, dan duk wanda ya kalleta yasan tana cikin wani halli. Batace komai ba ta juya kallonta ga Tajwar Eshaan da ke ɗan satar kallonsu...
“Barka da safiya Jaddah”.
Ya faɗa a taƙaice yana wani ƙara fuskewa abinsa. Itama sai tai kamar bata fahimci komai ba ta ce, “Barkan ka dai. Mike damunta haka jikinta zafi zau ga fuska duk ta kumbura idanu sun ɗashe yarinya duk ta fita a hayyacinta”.
Wayyo shikam ina ƙasa ya ɓuya ciki ko zai kuɓuta da ga bata amsar da bai ma san ta ina zai fara ba. Amma sai ya dake yana ƙara ɗan kauda kai gefe tsahon sakkani kamar bazaice komai ba. Sai kuma ya motsa lips a hankali a gaɓar da ma ta gama fidda rai da samun amsa.
“Ta girma ne”.
Kallonsa kawai Malikat Haseenat keyi, da jinjina murɗaɗɗen hali irin nashi mai cike da shegen miskilancin tsiya. Sai kuma ta janye a hankali ta maida kan Iffah dake raira kuka a hankali. “Niger (Sweetheart)” ta kirata a hankali. Da ƙyar Iffah ta iya amsa mata murya a ɗashe.
“Daure ki tashi zaune muga”.
Kwatanta tashin tai har sau biyu amma ta kasa, sai ma wani wahallen kuka da take saki saboda yanda zafi mai azaba ke ratsata. Ta shiga jujjuya kai da faɗin, “Jaddah bazan iya ba. Zafi kamar zan mutu”.
Idanu ya lumshe a hankali. Ji yake kukanta na wani irin sukar masa zuciya. Itama kanta malikat Haseenat ɗin wani irin tausayin Iffah'r ne ke ratsata. Ita tasan ba lalaci bane ko raki kawai. Dan zuri'ar su Tajwar Eshaan ɗin fitinannun mutane ne da indai mace taje hannunsu basa iya mata ta sauƙi. Shiyyasa mafi yawansu basa iya zama da mace ɗaya, sannan suna aure da wuri gudun faɗawa halakar zina duk da akwai bijirarru a cikinsu da kan ringa aikatawar. Amma ita a karan kanta ta daɗe tana mamaki akan Tajwar Eshaan da ya nuna baya buƙatar aure tun a shekaru fara girmansa, hakama yanda ya kai har shekarun da aka masa auren fari na sata jin waswasin ko yana neman matan banza ne ko baida isasshen lafiya. Dan tasan duk wanda ya kasance jinin zuri'ar wannan daula baya iya kauda kai ga mace irin hakan da ya nuna shi.........✍️







*LITATTAFAN DAI SUNE KAMAR HAKA*


*DAUDAR GORA Billyn abdul*


*KI KULANI hafsat xoxo*


*A RUBUCE TAKE Huguma*


*RUMBUN K'AYA Hafsat rano*


*IDON NERA Mamuh ghee*




_LITTAFI DAYA: 400_
_LITTAFI BIYU: 600_
_LITTAFI UKU: 800_
_LITTAFI HUDU :1000_
_LITTAFI BIYAR: 1200_


_KUDIN TALLATA MAKU HAJOJIN KU KUWA SUN KASHI KASO 4:_


_TALLA A DUKKANIN SHAFUKAN MU DA KE MANHAJAR YOUTUBE, FACEBOOK, TELEGRAM, WATTPAD, INSTAGRAM, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES. YA KAMA :25,000(DUBU ASHIRIN DA BIYAR)_


_TALLA NA IYA SAMAN SHAFI DAYA NA BOOK DAYA: 1000 1K_


_TALLAN TSAKIYAR SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA: YA KAMA 800_


_TALLAN KARSHEN SHAFI NA BOOK DAYA RANA DAYA. YA KAMA NERA 500_


_ZAFAFA BIYAR 2023!! ZAFAFA PAID BOOKS!! LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_


ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN


MARYAM SANI
ACCESS BANK
0022419171


SAI A TURA SHAIDAR BIYAN


09033181070


IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA


09166221261


*ƳAN ƘASAR NIGER🇮🇳. ZAKU TURA KATIN AIRTEL TA WANNAN NUMBER WAYAR KAI TSAYE KUMA*


+227 96 09 67 63


Books biyar 1250CFA
Books hudu 1050CFA
Books uku 850CFA
Books biyu 650CFA
Bookk daya 450CFA


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.


MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏽_*[5/31, 7:48 PM] +234 703 445 5862: 𝐓𝐲𝐩𝐢𝐧𝐠📲




✨𝕯𝕬𝖀Ɗ𝕬𝕽 𝕲𝕺𝕽𝕬✨
(𝕮𝖎𝖐𝖎 𝖐𝖆 𝖘𝖍𝖆𝖙𝖆)






𝓑𝓲𝓵𝔂𝓷 𝓐𝓫𝓭𝓾𝓵𝓵 𝓬𝓮🤙🏻


Book two(46)




.Shiru Malikat Haseenat tai kawai tana kallon Iffah da ta koma ta kwanta hanunta ta riko cike da lallashi ta ce, "To ya isa haka kukan kinji yarinyar albarka.
ALLAH yay miki albarka. Ya jaddada rahama a gareki da yalivataccen farin ciki na har abada. ALLAH ya sa ki cigaba da zama haske mai haskaka wannan zuri'a".
A saman lips ya amsa da Amin. Yayinda Malikat Haseenat tal amfani da wavarta tal kiran Daneen Ammarah. Wani irin yamm ya dinga ji a jikinsa jin Mammah na bada imarnin Daneen Aminarah ta shigo. Sai yaji kamar kasancewar su a waje guda yau wani abu ne mai girman gaske. Da kyar ya iya dauriyar cigaba da tsaiwa a inda yake har ta shigo dakin. Itama vanda take yi din kamar wadda ta daburce. Sam taki varda ta dub inda yake kamar yau ne rana na farko da suka kasance karkashin inuwa daya. Koda ya daisheta kamar yanda ya saba cike da jarumtar danne nasa vanayin shima a hankali ta amsa masa batare da ta dubesa ba.
Ita dai Mamma hankallnta nakan Iffah ne bata san mima sukeyi ba. Sai da taji tsaiwar Daneen Ammarah kusa da ita ne ta dago. Daneen Ammarah da idanunta ke akan Iffah wani irin tashin hankaline ke kokarin mamaye fuskarta amma tana dannesa. Muryarta a dan sassauce ta furta, "Mike damunta haka?".
"Danki ne".
Malikat Haseenat ta bata amsa a dunkule. Ta fahimta dan haka bata sake magana ba sai da Malikat Haseenat ta ce, "Kamamun ita ta tashi zaune da kyau. Sai ki sake hadamun ruwan dumi da wadan nan torerrukon". Kai kaval Daneon Ammaiati ta limina ra Mammah, ta matsa ta kama iffah ta tayar, kuka take sosai tana rirriketa amma Malikat Haseenat ta ce mata ta barta so take ta zauna din sosai. Ba vanda zatai haka ta zaunar da ita ta zame jkinta batare da ta sake varda la kalla sashen da Tawar Eshaan ya ke ba ta wuce bathroom abinta. Shima sai kawai yaji zaman dakin bazal wu mesa ba. Dan haka va fito abinsa yana mai satar kalion Iffah da ke kuka da mutsu-mutsun kasa zama da kyau. Kai tsaye Gym dinisa ya nufa. Jallabivar fikinsa ya zame ya canja da sport wears va shiga motsa iiki da zafi-zafi kamar wanda ale tunzurawa....
*Da kvar lifah Ta va kai kanta bavi da namaken Daneen Ammarah. Ashe dazu ba karamin taimako vake mate ba da yake daukar ta a komai. Sonai hankalin Malikat Haseenat da ita kanta Daneen Ammarah din ya sake tashi da yanda tariya ma ta gagari Iffan A bayin ma duk yanda taso gamin ta nutsu a cikin ruwan ta kasa zama. Sai faman rirriketa take da magyar "Mamy dan ALLAH ki fiddani, why da ciwo sosai" Kwantar da kanta Mamy tai akan Kafarta tana shafa kanta cike da lallashi dan tana zaune ne a bakin kwamin. "Yi hakuri to ba'a magana a bayi zai daina".
"Mamy bazai daina ba karawa yakeyi".
Dauriya kawai Daneen Ammarah keyi, amma j take kamar tai kuka. Ta fahimci dole Iffah taji ciwo ne, civo kuma bawai karami ba. Ita kam takan rasa miyasa maza basu da tausavine sam. A shekarun Iffah bai kamata namiji yay mata irin wanna zuwan na lokaci guda ba. Duk da tasan su waye mazan ahalin nan nasu akan mace, balle kuma shi da ya kasance tsahon shekaru ma babu mace, ko da ya samesu kuma ita dai Iffah'r ce ta farko dama take hasashen ya kusanta kenan ko yaya. Tunda kaf varan randa aka kavosu garesa washe gari ake zuwa a dauki gawarsu sun rasa ransu. Daga Iffah tai da ga ruwan, ta daure fuska sosai babu alamar wasa tattare da ita, "Ki tsaya a duba ko kinji ciwo ne a wajen, dan wannan zafin da kike ta ambata dole zai kasance akwai damuwa Ibnati. Idan kuma aka bar mace da irin matsalar nan yana lalatata koma ya taba mata brain. Ko kina so ki samu matsala a brain din ki?".
Da sauri Iffah ta jinjina mata kai alamar 'a tana hawaye. Daneen Ammarah ta hadive murmushin da ke taso mata dan ta mata hakane dan ta tsoratar da ita dama kawai. Ai ko sai gashi ta yarda ta duba cikin sauki amma fa ta boye fuska cikin tafukan hanunnta, wani irin matsanancin kunyar Mamyn a ratsa bargo da jinin jikinta. Amma sai take jin inba itan ba bazata taba iya nunama wani ba sai ko Ummu ko su Arfa da suna raye.
Rasama abin cewa Daneen Ammarah tayi, sai kawai ta mike jiki a sable cike da tausayin Iffah. Tabbas dolene ta dinga kuka, a hakan ma sai taga dauriyarta, dan in har watace tofa sai duk masarautar nan sun fahimci halin da ake ciki. Fitowa tai ta samu Malikat Haseenat da ke zaman jiran fitowarsu. "Mammah akwai matsala fa gaskiya, dole a nema likita dan varinvar nan taji ciwo bana wasa ba' Idanu Malikat Haseenat ta dan lumshe tare da budewa a lokaci guda. Dama ita ta fahimci hakan ai tun sanda tasa Iffah zama, ta kuma yi hakanne dama danta fahimta. Amma saboda ta sake tabbatarwar tasa Daneen Ammarah din sake taimaka mata, turarrukan data bada a saka mata in har Iffahn taji ciwo mai yawa to bazata iya zama ba daman.
"Ammarah wanna sirrine mai girma na shugaban daular ruman. Bazal yiu ya fita ba kema kin san bama zai yarda ba. Dole ke zaki bata kulawar da ta dace".
"Hakane Mammah, amma nina dauka shekaru rabona da yin wani abu a matsayin likita. Kar'a samu kuskure".
"Baza'a samu ba insha ALLAHU Ammarah. Na sanki akan komai shiyyasa nake alfahari da ke".
Da kyar Daneen Ammarah ta iva hadiye kukan da ke taso mata. Dan in har aka tuna mata ita din kwararrivar likitace a baya yakan sosa mata wani wani bangare na rayuwarta data shude da bata son tinawa.
Dan tamkar fami akan gyanbon da tasan har gaban abada bazai taba ya warke ba a zuciyarta ne.
Muryarta na dan rawa ta ce, "Zanje clinic na samo kayan aiki". Da ga haka ta fice. Da kallo Malikat Haseenat ta bita zuciyarta itama na raunana. Tana son Ammarah, matukar so da duk a cikin yayanta sai dai a bio bavanta. Sai dal tana dannewa da nuna iya tausayinta kawai gudun karta raba kan zuri'arta da kanta…... Tsaf Daneen Ammarah taima Iffah da ke kuka na fitar hankali dinkin, wai dan a ta mata allurar kashe radadi fa kafin ma ta tabata. Ana kammalawa ta dinga rawar sanyi na zazzabi kanta kam ai kamar zai fashe da ciwo. Malikat Haseenat ta tafi domin basu waje, sai dai ta aiko da lafiyayyen farfesu na musamman da wani irin kunun madara mai zafi shima na musamman. Sai tarin was sirrika da Iffah zata dinga amfani da su vain sit bath da zai taimaka mata warkewa da wuri da kuma wanda zata sha dan tasan in dai wannan yakinne kam Iffah yanzu ta farashi. Dan in ma fitinar ce shi kam kamar yacema kowa bai iyaba a ahalin nasa. Gashi yana dage-dagen wadan nan shegunan karafunan abu goma da goma.
Daneen Ammarah sai da ta tabbatar ta gyara toilet din akin tsaf duk da bawani datti tunda ba'a nan suka kwana ba. Bata canja mata rigar Tajwar Eshaan din da har yau take jikinta ba duk da ta mata girma da tsaho, dan ko'a wajen gashin dama sakata tai ta nannade kawai. Zaunar da ita tai kan filos masu taushi amma ta kasa zama da kyau sai da ta karkace.
Bata hanata ba ta zuba mata madarar da ke ta turiri tare da farfesun naman tsuntsaven da ke ta tashin kamshi.
"Mamy na koshi bakina daci barci zanyi".
"A'a Ibnati daure kinji, idan kika sha madaran nan kikaci wanna naman sai na karasa miki dayan alluran ki kwanta barci har sai sanda kukaso tashi kinji. Bakiji jikinki yayi zafi ba sosai. Haba diyar albarka haihuwar alkairi".
Da wannan lallabawar Iffah ta fara shan madarar a hankali, Daneen Ammarah a bata farfesun da kanta cike da kulawa. A haka Tajwar Eshaan ya shigo dakin da sallama va samesu. A cikin kwalliya ya ke tsaf ta alfarma ga ban kamshinsa da ya cika ko'ina na dakin, a takaice dai a Shahan-shan din sa yake. Cikin dakewar nan tasa mai bove duk wani sirrin zucivarsa da ainahinsa yake. Idanunsa sakaye da eyeglasses.
Ya wani kara kyau da cikar kamala ga wani kwarjini mai kara yalwata haibarsa ga mai kallo. Daka gansa kasan shi dinne dai daya tilo Shahan-shan din kasar ruman mai rumawa da kasar ruman. Sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login