Showing 30001 words to 33000 words out of 35109 words
Chapter 11 - AFIF BOOK COMPLETE DOCUMENT Writing by oum yasmeen.txt
in koma ɗakina ƙar wannan mai baƙin halin ta ga nazo shashin ki tayi tunanin wani abu muke kullawa ,
"gaskiya kam"
jeki tashi tayi tana sanye dariga da wando sun ɗa meta sosai har ana gano undis ɗinta ta fita ga wani uban ta kalli mai tsini taci gashin doki sai taunar chingum take yawa karuwa
Wannan kena
Alhmdllh zara ke ce kike magana kai Allah na gode maka addu'a bata waɗuwa kasa banza
Cikin muryar mara lafiya tace
Inna ruwa zan sha
"To, zarah ta bara in kawo miki malam zo kaga zarah tana iya magana da sauri tsohon ya shigo fari tas yace
"Allah kaine abin godiya dauko mata rubutun nan ta ƙara sha ,
"To malam bata tayi tasha cikin rashin ƙwarin jiki ta tashi ta dafa bango ,
Inna tace
Zarah zaki iya tafiya
Kai ta ɗaga mata ban daki ta shiga tayi futsari ta fito
Washe gari
bayan sallar magariba ansha ruwa limamin masallacin sarki ya sanar da daurin auran Aliyu mansur Aliyu da zarah yusif mai taba tuni sanar war tafara amsa kuwa akunnan afif haka cikin masarautar daidai da zubewar hanal..
duk kan wani firgici gimbiya rumaisa ta shiga ga hanal a kwance ba ta motsi wannan wanne irin tashin hankaline da sauri ta dauki wayar ta dake kan stool number anni ta shiga nemo wa
gumi duk ya wanke ta sai tayi rashin sa'a akashe girgiza kanta tashiga yi tace
" ina bazata yihuba wato kenan mai martaba ya shammace su ko de gaskiyar gimbiya zaliha ne da take faɗa mata tana zargin sarki zai bawa aliyu kujerar sa wallahi dole ɗana ne zai hau kujerar birnin zaki ba wani can ba ita yanzu bata wannan yarinyar ta dan ta take wannan fa auran da hikima aka yi shi ƙara neman lahin kilishi tayi tana ta bugawa,
amma anki dauka baki ciki ne ya ishe ta ga shi yanzu dare ne ba damar fita bata san lokacin da tayi cilli da wayar ta ba wannan jarabar ta ishe ta tabbas mamy ta shamma ce su amma yanzu aini yin fadan zai kama wallahi sai nasa mamy kinyi kuka da idon ki a birki ce zaliha ta shigo tace
Maman faisal kinji a bin da yanzu na ji to wallahi ki maza ki tawo mu tafi dole yanzu muyi fitar sirri muje gun hajja domin itace maganin matsalar mu
masu karatu daman hajja na nan muje zuwa ai wannan fadan ƙar shene
"hmmm wato anty zaliha duk aikin da hajja tayi mana ya tashi a banza,
wannan shegen ya dawo gashi auran da muka sa shi yaƙi yi yau Allah ya warga za shirin mu ki duba fa ki gani muka sa anni ta tsane shi bata kaunar ta ganshi to wallahi haka zamu sa al'umma ta tsane shi mayafinta ta dauko tace
"zo muje turusss suka yi ganin faisal yana tsaye yana kuka gaban tane ya waɗi domin tasan faisal masoyin mamy ne baya ƙaunar wani abu ya taɓa a halin mamy cikin ƙarfin hali tace
"Faisal lafiya ka ke kuka yawa wanda a kai maka mutuwa ?"
Faisal ya ɗago ya kalleta hawaye na zuba a idanuwansa yace
"Mama me isa zaki sa yaya a cikin damuwa wato duk abin da ke faruwa ku ne sila mama wallahi anty zaliha dan buƙatar kan ta ce yasa ta haɗa kai da ke ba ƙaunar ki take ba mama kiyi wa Allah da manzon sa ƙar ki je gun boka baki san irin masifar da take cikin zuwa gun boka ba mama dan Allah ƙar kije saboda ina jiye miki kunyar lahira domin gwara ta duniya ,
"da kata min faisal wallahi fita ko in tsine maka ,
Al ni kinga nayi shiru wato daman rashin kunyar ka ta kai ka ?
Ka rutsa iyayan ka kana fada musu baƙaƙen maganganu komai muna yi dan kuji daɗi ne da badan ina son mahaifiyar ku ba to ni da ban haifa ba in ƙƴaleta zanyi taje tayi fadan ita kade ita kuma wannan banzar kƴale ta mu tafi in tagaji ta tashi
"cikin kunar rai ya fita domin wallahi yana ji ajikin sa komai ya kusan rugujewa domin zakaran da Allah ya nufa da cara kona muzuru ana shawo sai yayi
"sosai duniyar ke juya mai wannan wanne irin tashin hankaline girgiza kansa yashiga yi tuni wata murya tashiga yimai amsa kowa tana kuka kamar muryar jidda amma ba tata bace domin yanzu wacce take gaban sa ta kasa kama da jiddar sa ko daman ba jidda yake gani ba tace
"Habibty na yau ni zaka tuzar ta ko ? yau ni kayiwa kishiya ?"
Afusa ce ya tashi zaune yana karantu ayatul kursuiyyu abakin sa domi n shi kan sa lamarin tsoro yake basa cikin ƙarfin hali yace
"ke ba jidda na bace bazaki taɓa kama da jiddana ba wallahi ki fita daga rayuwata kina tsohuwa kina faɗamin ke zan wa kishiya ,
Hhhh wato ka fara fahimtar koni wace ko to yau zanyi ajalin ka
Ƙarya kike wallahi ubangijina ne kade zai iya yin ajalina bake ba mashirika duk suffar da zaki juye min wallahi bazaki ban tsoroba domin zuciyar aliyu ta jan zaki ce kuma wallahi sai na kawo ƙarshan ki
"tuni ɗakin yayi wani irin baƙi idanunta yayi ja gawani irin hayaƙi da ke tashi a jikin ta fusƙarta tayi wani rin ƙato faratan ta dugaye ta sheƙe da wata dariya tace
"a yanzu faɗan zai fara jariri tun kana yaro nake fakon rayuwar ka a yau zan maka kisan gilla kamar yar da uban san duniya yayiwa ƴar sa hhhhhh
"Wallahi ƙarya kike wa yakashe min mata? ,
na sani bazan fadaba kuma kai ma yau inda taje zaka je bara in fada maka na dade ina yimaka siffa irin ta matar ka saboda kai idanuwanka sun makance ka kasa ganewa sani akai na kashe matar ka saboda ta san sirrin mu yau kai ma zaka fita tuni ta dauki wata huƙa zata daɓa mai ya kauce .
'cikin ƙarfin zuciya da na addu'ar dake bakin sa ya warci huƙar dake hannun sa ya daɓa mata a ciki tuni tayi wani irin zubewa a ƙasa halittar ta ta zama biyu rabi mutum rabe aljan tayi koƙarin dan na lahiyar jikin ta ta kasa ɓacewa tuni haske ya gauraye ɗakin waya ya dauko ya fara laliban lahiyin shugaban gidan yarin gida mai kan zaki
"salama yayi ya cikin girmamawa ya amsa yace ranka yadaɗe shugaban masu gida "
yauwa ina buƙatar yan sanda mata da maza su zo shashina har da kai
"an gama oga gamu nan zuwa cikin lokaci kalilan jiniya ta gauraye masarauta kowa ya fito yaga wa akazo kamawa
shashin uban masu gida aka nufa tuni zuciyoyin maƙiya yayi haske domin suna gani wayan nan jami'an tsaro shi suka zo kamawa tuni gun ya cika yan sanda mata ne biyu sai maza shidda suka shiga yana zaune yayin da tsohuwar matar ta na kwance ta zama halitta biyu amma za a iya gane ta sallama sukayi ya amsa ya basu damar shigowa
"gata nan ku dauke ta ku tafi da ita dakin ajiya zan zo zanyi binki can ta sannan kafin na zo ku tabbata kun bata tsaro ban yar ba kowa ya ganta
Cikin mamaki suka dauke ta domin sungane wace ita shuganban gidan yari yace
"okay sir angama ....
*Bazan taɓa mantawa dake maman hibba duk abin da nazama kece sula Allah ya raya su hibba wallahi bazan taɓa biyan kiba 💯*
takun ƙarshe
sosai mutane suka girgiza da ganin wacce aka fito da ita kowa da abinda ke faɗi yayi da ita tana jan mayafin ta tana rufe fusƙar ta a yau iya to zarta ta tozarta ga muni da tayi a idon mutane
_to jama'a wannan ya ishe ku hankali ita duniya ba ma tabbata bace duk irin abin da mutun zai aikata ya fara dubar Allah me bayansa zai ka sance ƙar kaga ubangiji ya ƙyale ka to talala yayi maka akwai ranar kamu_
"in giza ta cikin mota sukayi motocin ta suka fara tafiya tuni kowa ya watsai yayi da aka dinga gutsiri tsoma acikin gidan masarauta kowa da abinda yake faɗi
Wannan kenan
hajiya rumaisa kinga hajja shiru bata dawoba tun muna jin muryarta muna ganin abin da takeyi kinga bama jin komai bama ganin komai sai baƙi
hmmm zaliha kina ganina nifa tunda nasa kullin da hajja ta bani bana gani ke kuma sai wari kike
"da sauri hajiya zaliha ta tashi domin wasu irin ƙurajene suka feso mata take ga wasu tsutsotsi da suke fitowa ta gabanta,
ihu tasa tana fusge fusge tana cisgar naman jikin ta a haka su mai dala suka shigo cikin gidan domin hajja tace musu yau a kwai taro me zasu tarar
"uzairu wa nake gani kamar hajiya rumaisa da zaliha daman suna cikin gungiyar mu?"
nima mamakin da nake kenan me ya kawo su nan
to ina hajja taje wata ƙara sukaji tuni su wajan goma suka cure waje ɗaya
duk wata tukunyar tsafin gidan waɗowa take tana fashewa haka wayan da akasa a kwalba domin sun kasa yan kuwa duk sun fashe mutanan da aka kama suna guduwa sukuwa sun kasa ɗaga ƙafa
"ai basu ga tashin hankali ba sai da uwar tsafin nasu tayi wani irin ihu tace,
A yau zan bar muku gidan ku sannan ko wanne sai na dau fansar abin da yayi min domin kunmin alkawari za ku kawo min jinin jinjiri ba ku cikan ba sannan ko wanne da irin baƙar cutar da zan same
hhhhhhhhh ɗiiiif kake ji basa jin komai basa gani domin ko wanne abu na gidan rugujewa yake yana waɗuwa
Anan mai girma gwamna ya mutuwar hulaƙanci harshansa duk ya zazzago
Sukuwa su rumaisa da zaliha da rarrafe suka bar gidan domin sun kasa tafiya kuka rumaisa take tana kin cuceni hajiya zaliha wayyo Allah bana gani
*(ina sanar da masoyana sabon littafina KIN CU CE NI)*
Wata dariya ta rushe da ita tace
Alhakin gimbiya asiya ne yake bin mu
"wallahi kin zalin ceni kin sani amatsala sai da nace miki bazan ba kika ce we gimbiya asiya zata ƙwace mana miji sai mun tashi tsaye akanta ,
Hmm ki atunanin ki ni masoyiyar kice tab kina ruwa yarda ban haifa ba wallahi kima baza kiji daɗin nake ƴa'ƴan ba
Kuka rumaisa ta rushe da shi tana ta kaicin rayuwar da kishiyar ta ta sata acikin sosai hajiya zaliha ke burgima tana neman dauki jikinta duk ya farfashe ga wasu irin ƙuraje dake zubda ruwa yawa ba yar gayun nan ba
Allah kayi mana kyakkyawan ƙarshe
Wannan kenan
Ƙauyan garkun 🛖🛖
inna hadiza tana zaune yayin da ta zuba ta gumi domin yau wa'aɗin malam ya cika yace mata inbata fito mai da zarah ba to wallahi sai yayi mata hulaƙancin da bata taɓa zataba
inna hindatu ta tawo tana waƙar habaici tace
duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa kan doka ita rayuwa juyi juyi ce yau da kai ake gobe da wanin ka
Afusace inna hadiza tace
Ke tsaya kiji da abin da ke damun ki duk kin haifar mana yan daba
a hayye rasss au allah yo gwarani na haifa kefa inna ce basma yar yaya babba ce kin cuceta kin gurɓa ta bata rayuwar ƴa ga lawandi mai kifi ya sake ta da tsohon ciki
Tsahare ta fito tace
"ai hindatu daka ta kiji duk lalacewar ya'yan malam to inna hadiza ce kinga ajiyar tuƙunyar da ta ajiye a daƙin inna mai taba da yake tunda ta mutu ba shiga ake ba ,
"ke tsahare daman duk abin da su jagwa keyi sanadin inna hadizane ?"
Eh ita ta kaisu gun boka akan ita bata haifaba farfaɗiyar da zara kiyi ita ce tayi mata asiri a yanzu zan fasa tukunyar
dan Allah tsahare ki tausayamin wallahi malam yace in ta fashe ni zan fara hauka kuma cikina yayi girma ki tausaya min
innar su jagwa tace wallahi ko tsahare bata fasaba ni sai na fasa ashe daman duk ke ki ka tarwatsa mana gida aka ɗinga ƙwatance damu a garinnan
dan girman Allah ƙarki fasa
ai kuwa tuni inna hindatu tayi cilli da tuƙunya jikake
jifff a ƙasa tuni wani ƙaton miciji ya fito ya fasa ƙansa yayo gun inna hadiza malam da su ƙarangiya suna tsaye suna kallon iƙon Allah
"cikin ɗacin rai malam yace
"hadiza na sake ki saki ukku ki tattara ki barmin gida yanzu kuma wallahi sai na miƙaki gun hukuma ki fito min da ƴata ke da dillaliya
Wani ihu tasa domin ƙumurcin micijin nan ya kanannaɗe mata ahannu tuni fatar jikinta ta koma ta miciji tace
dan girman Allah malam kai haƙuri ka temakeni ƙar ka sakeni dan Allah ka mai da ni ɗakina wallahi na tuba na daina nayi na dama
Kifitarmin daga gida ………✍🏼
*AFIF*
Oum yasmeen
*My first novel is return black*
_the writer of BINTA YAR JAGALIYA_
https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k
*____________________________________*
*____________________________________*
Chapter 79-80
*☆☆︎*
*☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆*
"Dan Allah malam kai haƙuri ,
kai Duna jeka ka kirawo min su Aisha da rabi yau sai sun san komai game da ke
Duna wata shewa ya saki daman kunsan akwai yar tsama tsakanin su da inna hadiza yace
"To, bara in tafi ,
"Magen juyda yace,
da kata duna malam daka bari gobe aje yau dare yayi sannan mazan su sun dawo ko
hakane wallahi raina yake aɓace ni yanzu babban tashin hankalina shine ina zarah take marainiyar Allah hadiza kin cuceni
" sosai inna larai take kuka tace ;
wallahi hadiza kin cuceni kin rabani da ƴa'ƴana kin tarwa tsamin yarana daga mai shayeshaye sai dan daudo Allah ya isa tsakani na dake
toni kowa ya watsai yayi da malam da duna suna ta jefo da kayan inna hadiza daman komai yayi farko zaiyi ƙarshe
wannan kenan
zama yayi ya zuba ta gumi wai yau shi aka daurawa aure ajiyar zuciya yayi ya tashi yace
"Allah isa hakane mafi alkhairi ya bamu zaman lafiya ,
nikuwa nace amin
'shiga ɗaki yayi kai tsaye ban ɗaki ya nufa inda yayi alwala ya dauki al qur'ani mai girma ya fara karantawa
wannan kenan
yau zarah an daura miki aure kinyi dacan miji na kera sa'a Allah ya baku zaman lafiya
ƙasa tayi da idanuwanta domin wata irinyar kunyace ta kamata wai yau ita akai wa aure kuma dan sarki sosai zuciyarta ke wani irin bugu anya ba mafarki take ba anya idanuwanta biyu tashi tayi cikin sanyin murya tace
"inna zan kwanta baki da wani abu da zanmiki ?"
ina ni ina sa matar uban masu gida aiki soki ke a aiko da fadawa su kamani jeki ki kwanta yarnan Allah yayi miki albarka
Amin tace ta shiga ɗaki ta haye gado
"assalamu alaikun "
amsawa tayi tana faɗaɗa fara'arta tace
hajiya asiya yau kece ashashin nawa kode suruƙarki ki kazo gani
gyara zama tayi tace
"ehto hakane gobe insha Allah inaso ta tare a shashina domin na dauko masu gyarata sannan akwai malamin da zai dinga zuwa koya mata karatu tunda kinga zumi ya kusan fita ranar ɗaya ga sallah bayan an sauko daga edi zata tare
"masha Allah allah ya dafa mana ,
Amin inna kinji ankama hajja ashashin aliyu ko kina da masaniyar zancan ɗazu baiwata razeena take faɗamin wallahi hankalina ya tashi shi kuma be futoba balle aga lafiya yake ko ba lafiya ba ?"
ki ja danki ajikin ki kisan damuwarsa ki zama abokiyar shawararsa
ayya kuwa zan iya wallahi inna ganshi zuciya wani irin bakinci ki take tayi kamar zata fashe
"ki tafi da addu'a abakin ki insha Allah maƙiya sun dina tasiri a kanki da dan ki ,
cikin ƙarfin gwuiwar da inna ta bata ta tashi ta fita ta ƙofar sirri iya tsawan shekarun datayi a gidan sarauta bata taɓa kai kanta shashinasaba tafiya take cikin izza da isa ta ƴaƴan sarakai
saida tazo dai dai ƙofar tasa gabanta ya dinga waɗuwa addu'a tashiga karantowa aikuwa duhun da hayaƙin da take gani tuni ya baje
"masu tsaronsa ne suka zo suka tsaya abakin gate ɗin ganin ko wacece yasa suka matsa gabaki ɗayansu sukai ƙasa da kai lamar girmamawa sa ƙafarta ta dama ta fara shiga sai datayi
"tafiya mai nisa sannan ta isa kofar da zata sadata da wajan nasa sallama tayi ta tora kofar ,
jiyo kira'ar karatun al qur'ani tayi toni ta gane inda bedroom ɗinsa take shiga tayi be sani ba ta sami arm chair ɗin sa ta zauna ,
"gyaran murya tayi dan ya ji yo,
"da sauri ya jiyo domin yasa shi ka ɗene zaro indo yayi domin iya bazata ya shigeta anya kuwa mamy yake gani ?''
cikin farinciki daya kasa ɓoyiwa a zuciyar ta tace
ka idar da karatunka sai muyi magana
kamar wani raƙumi da akala ya gyaɗa mata kai
"sallama yayi ya fara karanto addu'o'i sanna
suka shafa tare juyowa yayi ya tsura mata ido baya ko kibtawa yana so ya gano me yakawo mamy cikin daran nan
katsai shirun tayi da
"aliyu nazo inji gaskiyar abinda ya faru kai da hajja sannan a yau zan roƙi alfarma dan girma Allah da manzon sa ƙar ka duba shekarun baya abin da ya faru kaddara ce wacce zamuce ta rigayi fata ka ruƙe zarah amana ƙar ka cutar da ita
sosai hawaye ke zuba a idanun ta ita tasan irin raɗaɗin da zuciyarta kayi ayau duk wani baƙin ciki na shekara da shekaru yake ta sowa bayan ta binneshi dan ta data haifa da cikin ta ta hufintar da rayuwar shi ta barshi tun yana yaro besan daɗin uwa ba ,
rar rafowa yayi inda take ya ruƙe mata hannaye cikin muryar kuka idanuwansa sun kaɗa sunyi ja yace
"Wallahi mamy dai dai da rana ɗaya ban taɓa ruƙe kiba a zuciyata kawe dai wasu lokutan zuciyata namin zafi na rashin madafa bango abin jin gina abbie ya taka rawar gani arayuwata kabir mamy aminin ƙwaraine
"rungumaishi tayi suka fashe da kuka ba me rarrashin wani cikin kuka tace ,
Allah yayi maka albarka
Ameen yace ya fara bata