Showing 6001 words to 9000 words out of 35109 words

Chapter 3 - AFIF BOOK COMPLETE DOCUMENT Writing by oum yasmeen.txt

birnin zaki ce ya san message d'in mai mahimmanci ne ga abinda a ka ce.


*"Assalam! Yayana da fatan ka na lafiya? Dan Allah ka dawo gida koda kuwa na lokaci kad'an ne Abie ba lafiya bai san waye a kansa ba Yaya ko so ka ke sai ya mutu ka zo mana ta'aziya?"*


Ya karanta sak'on ya fi sau goma tuni ya fad'a duniyar tunani kar yarasa Abie kamar yadda ya rasa Jiddah wannan fa mahaifin da ya tsaya masa a rayuwa ne. Duk matsayin daya kai to Abie ne ya tsaya mai mahaifin da ba shi da kamar sa kowa ya guje shi amma ban da Abie tuni idonsa ya canza launi ya koma ja tumble din daya zuba wine a cikin sa yayi jifa da shi tuni wani memory ya dawo mai Jiddah ce take mai gizo ta ce


*"My man ka ga abin da Abie ya kawo min a matsayin gift din birthday dinka my Man Abi ya na son ka yana son farin cikinka dama nima Daddy zai so nawa farin cikin my Man Daddina barazana ne ga rayuwarmu domin na ji..."*


Tuni ya tako ya rufe mata baki ya ce.


"jiddah Daddinki ya na son ki Jiddah kar na ƙara jin wata mummunar kalma ta fito daga bak'in ki kin ji my lovely wife."


Wani dogon numfashi ta saki ta ce.


"My m'Man ina ji a jikina ba zan yi tsawon rayuwa ba dan Allah my Man idan ka yi aure ka sawa ƴarka sunana."


Hancinta ya ja ya ce.


"Kar na k'ara jin wannan zancan Jiddah kowacce mace da ki ka gani in cikinta ya tsufa ji ta ke duniyar ta fita a ranta kiyi addu'a Allah ya saukeki lafiya kin ji my Jiddana."


Numfashi ta furzar tuni ta shiga tunani dama za ta iya tsayar da su Daddy ta game da abin da suke shirin aikatawa? Dama za ta iya gano inda dodon tsafinsu ya ke ta ruguzashi wannan wanne irin uba ne? Wanda ya fifita son Duniya a kan Lahirarsa? Duk wani sace-sace da safarar miyagun ƙwayoyi shi ne a kan gaba duk wani safarar mata zuwa ƙasar waje Daddy ne wasu zafafan hawaye suka zubo mata "Da ana canza Uba da na canza nawa."


"Jiddah my Jiddah!" Ina ba ta san ya na yi ba sai da ta girg za ta sannan ta dago idanunta cike da hawaye.


Afif cikin sigar lallashi tamkar ba muskilin mutumin nan ba ne d'an boko wanda karatun Addini da na zamani ya ratsa shi wanda ƴan mata suke rububinsa wanda magana ma da k'yar ya ke yin ta Ya ce


"My lovely wife ki daina kuka in sha Allah ba abin da zai faru duk da nayi dake ki fad'a min damuwarki kin ƙi ya ki ke so na yi da raina? Jiddah ke ce mace ta farko da na fara so Jiddah idan na rasa ki dai-dai ne da rasa raina." Rungume ta yayi tamkar za'a k'wace masa ita a daren ranar aka kai ta Aliyu Mansur hospital domin jini ya b'alle mata za ta haihu ba wanda ya yarda ya shiga d'akin shi yake duba ta sai dai me?


Dubawa ya yi bai ga allurar da zai yi mata ta tsayar da jinin da take zubarwa fito wa ya yi ya kira wata nurse ta dauko mai allurar ya yi mata rubutu da ta je pharmacy ta d'auko masa.

Cikin ikon Allah ta haifi ƴarta mace mai kama da mahaifinta sai dai ta d'auko chocolate colour d'in Jiddah daga gani ba fara ba ce.


Cikin farinciki Afif ya ce.


"Jiddah kin ga kyautar da ubangiji ya yi mana." Ya sa hannu ya d'auke ta ta na cikin kayan sanyi masu kyau ya yi mata huduba.


Murmushi tayi ta ce.


"Na gani ina cike da farinciki ni na haifawa gwarzon jarumi Ƴa gaskiya yau rana ce ta musamman a rayuwata."


Afif ya ce.


Ba ke kad'ai ba har da ni bari na d'auko wayata na bugawa Abie na baro ta a office" ya mika mata Ƴar.


Girgiza kai ta yi ta ce.


"Ka je da ita zan shiga toilet kuma na ga ma'aikatanka suna so su gan ta ka ga sai ka nuna musu ko?"


"To, shikenan na tafi yau Abie zai ji labari mai daɗi."


"Kai ta daga masa ya fita cikin nutsuwa ta mik'e tanufi toilet ta tsugunna tana fitsari. Kamar daga sama ta ji ana cewa to yanzu zabmu gudanar da aikinmu ya zama dole mu kasheta saboda ta san komai na mu cikin razani Jidda ta fito abguje dai-dai da shigowar wani matashi bak'i ko fusk'arsa ba ta iya gani ya caka mata wuka ya fita a guje wata ƙara ta saki wacce ta dinga amsa kuwwa a cikin asibitin a guje ya jefar da wayar hannunsa in da Kabir ya rufa masa baya tuni ta yi k'asa hannu ta d'ago mai duk jini ta ce "A...l..iy...uu" ta fad'a a rarrabe.


Tun da take a rayuwarsa bai raba jin Jiddah ta kira sunansa ba k'arasawa wajenta ya yi ya rik'o ta ya yi da karfi ya na rik'e da Nur a hannunsa.


AFIF ya ce.


"Jiddah don Allah kar ki tafi ki bar ni Jiddah! Jiddah!! Waye yayi min yankan ƙaunar nan ya ke k'ok'arin raba ni da ke? Jiddah ki fad'a min abin da ki ke b'oye min."


Cikin zafin ciwo ta ce.


"Sssss aaaa ne dddddda wwww aa zzzzz iiii." Kwata-kwata ya kasa gane abin da take nufi domin ji ya yi bakinta ya na ambato Kalmar shahada idanunta ya yi sama.


Cikin d'imaucewa ya ce.


"Jiddah! Jiddah!! Jidddddah!!! Shikenan Kabir sun raba ni da ita sun kashe ta sai da na ce ta fad'amin waye wanda ya ke mata barazana tak'i."


Cikin sauri ya dafa kujerun dinning table domin komai ya dawo mai sabo fil a ransa.


Cikin sauri Kabir ya k'araso inda ya ke ya rik'e shi ya ce.


"Ina ka ke ajiye inhaler dinka?"


Nuni ya yi masa da cikin aljihunsa domin ba zai iya d'aukowa ba cikin sauri Kabir ya sa hannu ya d'auko ya zura masa a bakinsa da sauri ya rik'e ya na zuk'a.




*__________________*




ƘAUYEN GARKUN


Inna Hadiza ta ce.


"Malam gaskiya zaman mu da Zahra ba zai yiwu ba, domin cutar nan fa ana d'auka ka san inda zaka kai ta ko kuma Hajiya Zaliha wacce take kai Yara aikatau ta dauk'eta ta samo mana kud'in aurar da Auta. Kai ka ga yanzu ba abinda ka ke siyarwa kuma biki yana k'ara towa."


Shiru ya yi ya na jin abin da ta ke fad'a can ya ja numfashi ya ce.


"To ke ki ka raine ta ba ni da ja a maganarki jiya ma d'an'uwana Manu ya same ni da maganar idan ba zan samo mata inda za ta zauna ba, zai je wajen Mai gari a raba gado ina na kud'in tan ge wurina kinbga fad'uwa ta zo dai-dai da zama ko?"


Inna Hadiza ta ce.


"To ka ga Wallahi munfi k'arfin zama da Zahra tun muna ganin tana sane take yi ashe cuta ce yanzu fa a garin nan ba'a siyan komai ina d'ora mata ka ga me ne amfanin idan ba ta je birni ta yi mana aikatau ba Hajiya ta fad'a min kud'in shekara za'a bani ka ga sai mu gyara gidan nan ko?"


"A'a ki ce harkar ta samu ce."


"Sosai ma Malam za'a bani dubu dari uku fa."


"Dan Allah matar rufin asiri ko har Basma za mu tura?"


Tuni annurin fuskarta ya d'auke ta ce.


Malam wanne irin zance ka ke? Idan ta tafi wa zan gani na ji dad'i? Duk fa na aurar da yan uwanta."
To fa! Jama'a wannan wanne irin rashin imani ne ita ba ta so ta rabu da 'yarta amma tana so ta tura marainiyar Allah._


Malam Yusifa ya ce.


"Kuma fa hakane, Lawandi ma ba zai ji dad'i ba ba ya ganinta ko?"


"Shi yasa na ke son ka ka na da fahimta." Kafin ta k'arasa ta jiyo sallama, da sauri tabtashi ta fita ta tare kofa ta ce.


"Wa na kama? Wallahi Duna sai ka biya ni ashirin d'ita ko in tona maka asiri." wata dariya duna yayi yace.


Inna hadiza kenan wllh Allah yayi miki jarabar san kud'i yawa kuturwa ko kuma ma ince kin dorawa k'anki inbanda San kud'i irin naki ko yar alkunyar nan ke bakya yi




Inna hadiza tace .


"Wallahi duna kaban kud'i na komai zaka fada daga baya kenan amma katsaya kana yimin wani shirman banza da hofi dawasu kafafuwanka yawa kwarashi"


Cikin fusata duna yace.




"Iyee inna hadiza ni kike fadawa waka to na cinye bazan bayar ba yasin kuma kin iya suya hhhhhh,




"Yana fadan haka ya buga tsalle saka makon wata cabka da inna hadiza ta kaiwa huyan sa zata damko shi"




Kai kai mai zangani hadiza kahu manu yace.


"wato d'an nawa guda d'aya dana mallaka aduniya kikewa haka ?"


inna hadiza tace.


"Kaga manu ina mutuntaka kafita a sabgata tun kafin inyi k'asak'asa dakai "




Wani ashar mai maiko kahu manu yace.


Daman hadiza yar gidan makaho ni kike fadawa haka shegiya yar jagora to wllh anbuga dani anbarni ko yanzu allura ta tonu garma kin manta abinda naji kuna fada keda mai Kai yara aikatau ko ma ince safara domin karu.........✍️


*AFIF*






Oum yasmeen






*My first novel is return black*




_the writer of BINTA YAR JAGALIYA_


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


*____________________________________*


*____________________________________*




Chapter 41-50






*POV MANU*






Kafin ya karasa tace.


dan girman Allah manu Kai hakuri ka rufan asiri badai ashirin bace na bar masa


"cikin hanzari duna ya dawo inda suke yace


Babana mai kake fadane haka dan Allah nima ku gutsuramin abinda kuke fada inji ?"


Kahu manu yace .


"Jakar ubanka nace duna yaushe zaka daina munafurci iyeeee ?"


To wllh hutar munafukai daban take yasin babbakar tsirai za aimaka kai kabi duniya asannu roko hannun sa yayi suka shiga cikin gida mai zasu tar matar nura takama zarah tana duka


ganin haka kahu manu yace.


Kee ramatu wallahi kikeyayi su *aljani canya*


tuni yarufe bak'insa yace


"insuka nuna miki kalar su kyayi bayani yasin duk son da nura gake miki guduwa zaiyi yabar ki ya Allah k'ar ka k'ara nunamin wannan rana danayi gamo yashige yanufi ya shashin sa,


"Jin hakan yasa ramatu jikinta yayi sanyi ko dai gaskia ne abinda baraka take fada mata domin ita ranar bata nan tatafi unguwa "


Duna yace.


"wallahi yau kika sata tayi aljanu sai k'in sani laikawa yayi yaga uban baya nan yayi gaba tafiya yake yana waka dawani wadda yake son basma domin ita Zara ko wanka inna hadiza bata barinta yi yanxu haka shaka'ar ta goma sha biyu amma Allah yayi mata girman jiki bata da kiba haka kuma baza akirata kajerah ba domin ita tsaka kaki ce


Duna yace.


" lawandi lawandi bani kifi


Cike da hadarai lawandi yace.


"Wekai duna wanne irin baki ne da kai kullum sai ka cimin kifi ko gajiya bakayi ?"


Duna yace .


"To bani zanci ba surikin kane bashi da lafiya har zakai min rashin arzuki




"Wanne surikina domin danxu naga malam ya shige?"


Duna yace




"To, Rufa'i ne bashi da lafiya bani zanci ba "


Lawandi yace.


"To,bara inbaka k'ulin d'ari biyu amma wallahi duna k'ar inji k'ar in gani d'an wallahi duna naji ance baka bashi ba zanma hulak'ancin da baka zato dan yawo agarin nan sai ya ga'gareka ai kana jina ko ?"


Duna yace.


"Yasin bazan k'ar b'a ba tunda ka mai dani maha'inci mara rok'on amana yabuga ko dadd'iyar rigarsa yayi gaba




Jiyayi tamk'ar sauk'ar arado yaji ana cewa *ya aki ya aki*


" cike da murna ya juyo yace .


"Magen judah Kai nake gani ?"


Cikin muryar ustazai yace.


"Wato ainiyin yau na dura a garin nan zaman sa'audiyyyah ya ishan ya waladon ina laraba tayi aure bayan tafiyata?"


Duna yace.


"magen juda ina tsarabar mu ina kallo kallan danace ka tawomin dashi yo bayan katafi tayi aure yanxuma wata mai kamawa za aibikin yar mijinta ya naganka da ga Kai sai jallabiya ?"


Tuni ya fara tunani k'ar shegan yaron nan ya gane korushi akai yasami abin tsokana tuni wata dabara ta wado mai


"Magen judah yace.


" inna sami lokaci zanje birrin ZAKI inyi canjin *riyal* baban kallo kallo zanbaka Kai har yanzu baka rabu da sha shanci ba shige mutafi kai min shara


"Bintalo bintalo masoyiya bintalo ma Lodi (my love) cikin fusata magen juda ya kaiwa rigarsa cabka tuni ta yake


" yasin inayardar inyi yawo agarin nan ba k'afa yanxu magen juda ni zakaiwa haka agaban masoyiyata ?"


Yasin duna kafita a idona kud'in dazan baka na fasa aikafin yak'arasa jikake kiyyyyyy ya yagamai ya fita aguje


Magen juda


"Cikin Kin hanzari ya juyo yace.


" d'ahuru k'arangiya kuma kundawo?"


Su Dahuru yace.


Duka suka amsa da eh wallahi yau aka sako ni ajirgi aka dawo dani

K'arangiya yace.


"Nikuma yau na fito daga k'urkukun masarautar ZAKI SBD Ana zargina da sa guba


Duka suka rumgume juna sukace yau sai gidan mai taba tuni suka runguda Kai sukayi gaba wani ihu suka zuba tuni kowa na gidan ya fito Dan ganin maike faruwa


" inna hadiza tace.


Ana wata ga wata yau kowa na garin nan nan sai yasan najadun tsofaffi sundawo to wllh yan kajina da dabbobi na ayirdin ku wallahi


Magen Judah yace.




"Keeeeeeban za kazar matsiyata we harni shi afada wa nama shida yake sa'audiyyyah ,




Cikin fusata tace




"Owo dai bamu ga alama ba ,






K'ahuru yace






Nida naje Makkah aikatau harni zaki fada haka


Tsahare tace.


Jibeku Dan Allah kunyi kallal dukiya ko jindadi kai dakatashi da wowa saika dawo da riga ayage


Shikuwa k'arangiya yarantsai saiyasa kowa na gidan gudawa domin da maganin daya kwana biyu beyi bahaya ba aka bashi a asibitin masarautar ZAKI shi zai xoba musu a nono da fu'ar daya kawo musu




" k'arangiya yace.


"yaya babba bara inshiga d'akin ki indauko roba inzuba tsarabar nonan dana kawo muku ko inzaki iya shiga kid'auko min inzuma ?"


Cikin jindad'i ya girmamata ta d'auko kujera yar tsuguno tazauna tuni tsahare ta washe hak'ora yawa mai shirin shan jini


"Inna hadiza tace


"Da tun farko kafad'an ba tafiyar ku d'aya da su k'ahuru ba jeka kad'auko"


gefan zaninta ta kwance tashare hawaye tace.


"Allah sarki inna mai gasarah dama kina raye kiga abinda k'arangiya yayi mana kullum so kike su shiryu yau Allah yayi shiryuwar k'arangiya tsahare kiduba fa kigani ko wayancan da suka dawo daga saudiya gari mai daraja garin annabi Muhammad *( S.A.W )* basu kawo mana komai ba anyakuwa ba kuro su akai ba

Tak'ara fyece majina tace.


" k'arangiya Allah yayimaka albarka inna saka albarka kamar inna mai gasara ce tasa maka SBD kaf cikin kishiyoyina inna mai gasara tafi sona
kai kanin mijina ne ko bahaka ba aminiyata tsahare ?"


Cikin jindadi tsahare tace.


"Ehwllh yaya duk tafi San mu akan su larai "


*Ta gyara mata zancan nata*


k'arangiya yace.


"Yaya bara indauko roba "


Inna hadiza tace.


"Kawo jak'ar ka in ruk'ema kaji dad'in d'auko wa




" hava yaya ni na isa inbaki arok'o aa bana so inga k'in wahala bara inje da ita uwar gida sarautar mata inna tsahare ina huni mun same ku lfy ?"


kanfa inna hadiza dana tsahare ji suke kansu zai fashe Saboda jisuke har hayak'i yake saboda girma har ruge rugen ammsawa suke laira da hindatu kowa ancika anyi fam SBD bak'inciki


Cikin daki kowa roba ya dauko ya b'allo magani guda hudu ya zuba ko shi likita cewa yayi yasha rabi SBD in mutum yafara bahaya ba control yajuye nono tas ya juya saida yaga yanar ke sannan yane mo suga acikin jak'arsa
cike da farincikin nasara ya fiyo ya dure mata agaban ta

Tuni inna hadiza ta washe hak'ora wadda duk goro ya cinye su tace.


"Allah yayi baka albarka k'arangiya saidai bani da kud'in suga


Har'arta k'arangiya yayi dayake san zuciya ya rufe musu ido basu gani ba yace.


" k'arki damu nasa ga ludayi ki bawa kowa kishanye ragowar


Magen judah yace.


Haba k'arangiya gamu yan uwanka kasan munyini bamuci ba shine kake bata


Wata kwafa k'ahuru yayi yace.


"Niban san lokacin da k'arangiya yazama haka ba


cikin tsawa inna hadiza tace


"zoka ku sha tunkafin inshanye ,


" ganin k'arsuyi asara yasa suka k'arba dayake suna shiri da tsahare ta zuba mata mai yawa yauwah auta Allah yayi rabon baza asha bakeba ungo sha ki barmin ragowar


"To, innata k'arb'a tayi tasha


" inna hadiza dadi yayi dadi batasan lokacin da ta zauna ak'asaba tashanye tas tace bara in kwanta kafin sallal la'asar

"To, yaya tsahare tace.
Nima kwanciya zanyi kafin manu yadawo sukuwa surik'an larah wato baraka da ramatu tunda aka basu suka shige shashin su hakama su hindatu kamar daga sama inna hadiza taji cikinta na murdawa aguje ta fito saidai mai tana zuwa bak'in bayi d'insu ta tarar da lahi tace.




*Hausawa sun ce 👉👇*


*maganin biri dan katan uwa*








"Kai magen juidah waye ab'and'ak'in nan?"


ai ba bak'in mgn domin shiyasan halin dayake ciki,

"Cikin daga muryah tsahare dake band'aki tace.


Yaya nashiga ukku bazan iya tashiba shikkenan na rasa k'afa yaya zoki d'auke ni inna hadiza kowa tuni tasaki abunta a k'asa su larai da hindatu abun naso bek'ai na hadiza da tsahare ba


"Suna cik'in binlahin nan sai ga zarah ta shigo k'anta dauke da icce mai yawa ta kalli basma tace.


Dan Allah basma zoki sauke min


" cikin halin sangarta da kuma na ha'ula'in datake ciki tace.


Weke zarah wacce irin mara zuciya ce nace kifita a harka ta naga alama so kike ki shafa min cutar nan take to ta Allah bataki ba shegiya wane besan mae kike ba yarinya batakai takawo ba amma jibeki koni dana girmeki k'in fini komai to kisan dasani wallahi kika d'auko mana abin kunya sai mun muki duk'an daba mutab'a yimiki ba kafin ak'ai ki gun maigari ya koreki ,,


"Jin hak'an keda huya inna hadiza wanke k'afarta da jikin ta tafito dayake kaf cikin su ba waddah yayi mata alfarma tace,,


" basma ashe bani kadai nake zargin yarinyar nan ba janyo zarah tayi yawa tasami buhun kayan wanki ta mare ta dan ubanki wake tattab'eki a garin nan ?"


Allah sarki zarah batasan mai suke nufiba cikin rawar murya tace.


"Wallahi ba inda nake zowa inna kihi hakuri "


Inna hadiza ta k'ara buga mata kai a garo ta damko gaban rigarta cike da mugunta ta murdai mata kirjinta wata irin k'ara tasaki saboda wani irin zafi dataji bashiri ta saki fitsari,


Basmah tace.


"Innata kinga abinda nake fad'a miki ko to gashinan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login