Showing 33001 words to 35109 words out of 35109 words
Chapter 12 - AFIF BOOK COMPLETE DOCUMENT Writing by oum yasmeen.txt
labarin abin da ya faru tsakanin shi da hajja
"sosai ta shiga firgici daman hajja ba zuciya ɗaya take zaune da muba cikin da shashshiyar murya tace,
afif komai ya zo ƙarshe insha allah sannan kafin zara ta tare inaso nan da jibi kuje da ita taga ahalinta .
ƙasa yayi da kai yace
yarda kikace haka za ai
wannan kenan
washe gari
tuni kowa ya shirya domin zaman shari'a da yake ta cikin gida ce gashi kuma jiya da daddare an kama su hajiya rumaisa da su mai dala tuni wajan ya dau shiru sakamaƙon shi gowar sarki zama yayi a ƙojerar da aka tana darmai
"tuni suka tashi suka gaidashi kowa ya zauna ana surutu ƙasa ƙasa ,
idanun mutane suna bakin ƙofa domin aga wa za'a shigo dashi harta mamy da ƴa'ƴanta suna gujerun gaba ,
zaru idanuwa tayi domin ganin anshigo da su mai dala harda ƙishiyoyin ta duk abin da su rumaisa suka zama bata kasa gane suba bare anni da kilishi da suke aminansu suma zaro idanuwa sukai
gyaran murya sarki yayi yayin da zuciyar sa take a toshe domin yau ita ce rana mafi mune a rayuwar sa matan sa har biyu a wannan bada ƙalal gwara zaliha bata haifa da shiba
amma rumaisa uwar ƴa'ƴan sa ce ɗaga ido yayi suka haɗa da faisal wanda yake kuka idanuwan sa sunyi jajir abin ka da farar fata tunjiya da yadawo daga gidan yari yake kuka har iyanzu kau da kai yayi domin dole ya yanke mata hukunci akan abin da suka aikata cikin nutsuwa da ƙwarjini yayi addu'ar buɗe taro yace
alhmdllh yau Allah ya toni asirin duk wani gurɓatatce dake masarautar nan sannan ajiya Allah yayiwa gwamna rasuwa dukda yanzu haka gawarshi tana asubiti ana binkice
"sannan kai mai dala zanso ka faɗawa mutane abin da kuka aikata ,
Shiru yayi sai can yayi ƙasa da kansa domin san duniya ya ƙaishi da kashe yarsa ta cikin sa buɗa maki yayi yace
nida uzairu da hajiya hajiya zaliha da hajja mu muka tora a kashe *JIDDAH* amma abin mamaki kafin wanda muka tora ya kasheta sai mukaji mutuwar t…………✍🏼
*topa ku biyoni domin jin yarda zata kaya kafin irufe littafin afif gobene ƙarshe tsawan wata biyar ina rubuta littafin nan ina roƙon ubangiji duk wani kurakuran danayi aciki ya yafemin sannan ku biyoni a labarina na RASHIN SANI*
{♥︎‿♥︎}
*AFIF*
Oum yasmeen
*My first novel is return black*
_the writer of BINTA YAR JAGALIYA_
https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k
*____________________________________*
*____________________________________*
Chapter 81-82
*☆☆︎*
*☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆*
*AFIF*
*🅃🄰🄺🅄🄽 🄺🄰🅁🅂🄷🄴*
""Amma wallahi ba ni na kasheta ba abin da nasan inayi safarar yara ƙanana shine abin da nake ,
"shiru gun yayi domin jin mai sarkin zace ,
Saida ya nisa sannan yace
"a cikin ku wa ya kashe min mahaifi ?"
tuni su waziri da uwantale babar waziri suka fara muzurai
"wannan kuma uzairu ya fini sanin komain domin da shi aka haɗa baki saboda shine likita me kula da mai martaba Allah ya jiƙanshi da rahama ,
"Uzairu we hakane ?"
eh amma wallahi ni abin da san na aikata nayi koƙari in mai allura bata yuhuba hajja ce ta bashi guba abincin da ta kawo sannan sanƙira da uwantale su sukai kaiwa aliyu guba sha shin sa ana zatan mamy ce ta bashi
"tuni aka tuso ƙiyar uwan tale da sanƙira da waziri ,
Haɗa baki sukai suka ce sun aika ta sai aka dawo kan hajiya zaliha tuni daman tana ta tonawa kanta asiri da abin da ta aikata ganin basu wahalal da shari'a ba aka yankewa su uwan tale huƙuncin rataya ranar sallah a idon
mutane domin izina ga al'umma hajiya rumaisa kuma da zaliha huƙuncin ashekara ashirin agidan yari har su mai dala duba da irin ɓarnar da suka aikata suma ratayesu za ai shi kuma za abada gawar gwamna abinne ta saboda an gano ba wanda ya kashe shi doka guduma akai fadawa suka kare sarki domin antashi da shari'a
da gudu faisal ya rungumai afif yana kuka yace
"Dan allah ka yafewa mama ko zata sami salama arayuwar ta,.
Wllh ban ruƙe mama ba Allah ya yafe mana
"ameen,
Wanann kenan
Tuni su anty aisha da rabi suka hallara sai kuka suke jin abin da malam yake ce musu
Malam yace
" a yau zaki barmin gida tunda bana ku bane ,
sosai take rawa tana juyi su kuwa rufa'i tun da a ka fasa randa suka shiryu yanzu haka suna zuwa daukan karatu
a guje inna hadiza ta fita yayin da suka kusa karo da Duna a ƙofar gida
''shima ya shigo a guje domin ya faɗa musu wani albishir tuni ƙiɗan algaita ya fara ra tsosu da kuma jiniya bigeta yayi ya shige ,
yayi da ta dakata domin ganin wasu masu kayan sarauta
"inna inna wallahi dan sarkine ya shigo garin nan kuma nan gidan suke nema yanxunnan lawandi yake faɗamin ,
dafa girji tayi tace
Mun shiga ukku allah isa ba ƙarangiya aka biyo ba
"uhmmm ni menayi da za abiyoni bayan sun tabbatar bani da laifi har yanzu dai wannan cutar taki tana nan baki ga abin da ya sami yar uwarki ba ,
"Bana son rashin mutunci wllh kakiyaye ni manu kana jinsa ko ?"
Ya isa dan allah ku dakata yawa wasu yara ni yanxu wallahi na shiryu barar da nake na a dena sana'a zan nema
Malam yace
"Alhamdullahi na jidaɗi daka shiryu manu yanzu in anjima kai wanka kazo mutafi gun yansanda kai ƙara domin wallahi ba zan yarda ba sai anne momin ya'ta kasa ƙara sawa yayi dukansu suka tashi domin ganin wacce ta ke shugowa duk da hutu da jin daɗi ya game jikin ta ta koma yawa balarabiya cikin tantama malam yace
"zara keece?"
Eh nice malam sai ta rushe da kuka da sauri hindatu da larai suka matso kusa da ita wani sassanyan ƙamshi ke fitowa a jikin ta ga suttura ta alfarma
"Zara ke kika zama haka hindatu ɗauko min ta barma ,
"TO, to yaya da sauri ta tafi dauko ta barma da wowa tayi ta shinfiɗa misu suka zana ,
duka sun sandare cikin kuka ta fara basu labari ba wanda beji tausayin taba
"dan girman Allah zara ki yafe mini
Wallahi malam ba abin da kaimin inma akwai na yafe tuni suka nemi afuwar juna basma kuwa saboda kunya kasa motsi tayi inama ita aka tura aikatau
"malam tare dashi muke ,
To to shigo da shi
To tace ta tashi a sanyaye ta daɗe a soro domin bata san yarda zata faɗamai ba candai tayi kundunbala ta nufi inda motarsa take yana cikin ya zuba mata
"idanuwa Allah yana gani besan irin son da yakewa zara ba yana jinta a jinin jikina ,
Cikin sanyin murya mai daɗi tace
Yace ka shigo
"okay muje tayi haka zata fara tafiya ya ruƙo hannunta sosai ta fara ƙoƙarin ƙwacewa amma ina ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba,
Haka ta haƙura suka jera tare sai suka zama taurari tuni kowa ya fito domin gida gida duna yake bi yana zara ta dawo tana auran dan gidan sarki
"da sukaje cikin shagwaɓa da bata santayi ba tace
Dan Allah ka sakini
banza yayi mata tabbas mamy uwace ta gari haka ya aiyana a zuciyarsa
"har suka shiga cikin gida har ƙasa ya durƙuwa ya gaidasu ,
a tabarma ya zauna sunyi mamaki yana jikan sarki dan gidan sarki amma ba ƙemƙƴami ya zauna a wannan gidan nasa
"hindatu jeki ki gyara ɗakin iya su zauna domin dare ya kusayi basa koma a yauba ga inaso ta zaga dangin mahaifiyar ta ,
to malam
Saurin kallon sa tayi irin hutu da jindaɗi da yatashi da shi bata tunanin zai iya zama anan
na gama malam
Zara kaishi ɗakin kafin ku tafi
To tace iya gyara ya sha gyara ga yar katifa ansa sai ƙamshin turaran huta yake ajiye wayoyinsa yayi ya zauna janyo ta yayi yace
"zauna muyi jira ki bani labarin garin nan,
Lamgwabar dakai tayi kamar baby tace
to ka bari sai ansha ruwa sai inbaka yanzu nagaji
uhm mijinki kike cewa kin gaji
wata kunya ce ta rufeta ta rufe fusƙarta da ta fukan hannayan ta sun sha jan lalle
Zuba mata ido yayi yace
"au kinyi lalle ko ki nunamin mugani ?"
ta shi tayi zata gudu domin bazata iya wannan sabuwar rayuwar da daddy nur ya tsuro mata da ita
ƙafa yasa aikuwa ta harɗe ta waɗo jikin sa cikin soyayya wacce bata ɓoyuwa a fusƙar sa yace
"au ni kike gudu ? hmmm yarinya dan dai azumi muke da yau na cire miki kunyar ki "
Ƙasa tayi da kyakkyawan idanuwan ta ta fara wasa da hannun ta cikin siririyar muryarta kamar sarewa tace
"Dan Allah daddy nur kai haƙuri kaga a gidan mu nake ,
Tabbas yarda tayi tasiri a jikin sa kallo ta yake yawa wata yar baby lalle aure ni'ima ce da shi
cikin salon tsokana ya ja mata kumatu yace
"uhmm daddy nur sauran ƴa'ƴan da zamu haifa fa kinsan fa ina so muhaifi ƴaƴa masu yawa kinsa nifa ba rago bane ?"
da sauri ta ɗago ta kalle shi
ɗaga mata gira yayi yace
ta shi kije nima akwai aikin da zanyi a garin nan
cikin sauri ta tashi tace
"To, daddy nurr
uhmm momy ɗin nur
Rufe fuska tayi
Tana dariya ta futa
da sauri saude ta sha gaban ta tace
"iyee ahe daman gaskia duna yake faɗamin kin koma balarabiya ''
Cikin mamaki ganin irin ramar da saude tayi ga wani uban goyo da tayi duk ta fita hayyacinta ta ce
Saude
"Zarah kin ga yarda na koma ko ?…… "
kamar ƙadangaruwa ta gyaɗa mata kai tace
"zo muje mu zauna "
cikin yaƙe duk fusƙar ta ta muzan ta tace
"to,
duk da irin tsamin da take bugawa haka zara ta haƙura suka shiga ɗakin inna hindatu tuni hira ta ɓarke tsakanin su
Zara bayan tafiyar ki mama tayi min auran dole bana sonshi haka na haƙura kinga dan mu
Dasauri zara ta kunto shi a baya tace
masha Allah kuna kama saude
dariya tayi tace
"dan Allah ki roƙar mana mijin ki ya bashi aiki a company ɗin sa "
a jiyar zuciya ta saki tace
"To, saude zan tambaye shi
tare da saude suka zaga dangin mahaifiyar ta domin aliyu yace bashi da lokaci bayan ta dawo daga zaga dangi ta huce taga ana ta gine gine
tuni suka shiga mamaki suda saude wata mahaukaciya ce ta taso tana rawa tace
La kamar zarah malam
Kuka zara tasa tace
"eh inna nice haka kika koma ?"
Hhhh haka boka ya mayarda ni
Ganin tana nema ta dukesu yasa suka ruga aguje sai da suka zo wajan gida suka nutsu zara ta kalli saude tace
"saude rayuwa ba tabbas ,
alla ka samu dace
"Amin saude"
to bayan sun koma masarauta ranar sallah aka kai zara gidan ta tasha kuka dangin mahaifiyarta sun nuna mata so
Zarah da afif sun shinfiɗa rayuwa mai kyau abin sha'awa tuni ta matsamai sai ya dawo da nur duk da mamy taƙi
haka ta matsa mata saida ta basu domin ita tayi alƙawarin baza wahalal da dan wani ba domin taga izina duk da tana fama da laulahi haka ta jure zarah ta haifi dan ta namiji yaci sunan yusif ana cemai Imam sosai anni tayi dana sani haka su hanal yanzu hanal ta aure kabir suna zaune cikin kwanciyar hankali tare da matarsa da ya'yansa ita dai likitoci sunyi binkice bazata taɓa haihuwa ba saboda mahaifarta ta lalace haka take kula da ya'yansa saboda matarsa aikitake...
*Bayan shekara hudu*
zara ta ƙara haifan yan biyu duka mata aka sa sunan mahaifiyar ta da anni ana ce musu
afura da afreen bayan su tace hutawa zatayi
"nikuwa nace banga laifin kiba ƴa'ƴa har ukku a shekara hudu"
tuni rayuwar su ta canza ya samawa kauyan garkun abubuwan jin daɗi har da makarantu yayi musu ya gyara gidan su zara ya koma na bulo ya samarwa su duna aiki
Yanzu shine sarkin garin abdul gwamna sosai suka samarwa da birnin zaki ci gaba zara ta zama yar boko ga ilimin addini
Cikin takunsa na izza ya matso bakin kofa ya dubi zara cikin so da kauna yace
"hayaty mu rufe ƙofar mu nagaji da oum yasmeen ta ɗibar mana labari tana bazawa a duniya "
rugumai shi tayi tayi mai kiss a kumatu tace
"gaskiya kama daddy nur mungaji ,
duka yaran suka matso suka rumgumai su suna dariya
Alhmdllh Alhmdllh
Ya ubangiji duk kan wasu kura kuraina ka yafe min a yau na kawo karshan littafin AFIF
Ina godiya ga kungiyar
*KING AND QUEEN WRITING CHAMBER*
Sai
*AMINCIN WRITING ASSOCIATION*
Mu haɗo a littafina na gamaba
Zaku iya samin audio na wannan littafin akan wannan number 09061890481