Showing 9001 words to 12000 words out of 35109 words

Chapter 4 - AFIF BOOK COMPLETE DOCUMENT Writing by oum yasmeen.txt

saboda dad'in dataji k'intab'a mata inda yake mata k'aik'ayi har ihun dad'i ta saki,


Inna hadiza tace.


"Wallahi kuwa basmah ashe ga abinda takeyi shiya duk tabi tafiki komai bara malam yadawo dole gobe hajiya tatafi da ita can k'arta je tasa momana abin kunya k'insa k'auye ba'a raina abin fada, tana fadar haka ta zoba aguje domin cikinta ya murd'a ai suk'ai karo da tsahare cikin fusata ta finciko tsahare tayi baya da ita ta wad'i ganin haka tsahare ta d'auki iccan data gama dukan zarah ta buga mata agadan baya ganin ta tsuguna yasa tsahare ta shiga bayi tabarta dafe da k'ai


Inna hadiza tace.


Wllh tsahare kika fito saina zaune ki yasin sai kin gwammace kid'a da karatu,


"To, to balama uwar tunɓele tunkiya baki da saiti saidai a saita ki


ki kenan koda yaushe cikin fad'a yawa k'arya.


Inna hadiza ta juyo tace.


" yanzu magen juidah ni kake fadawa haka?"


"To, k'arya nayi miki ashe halinki bazai sauyaba keki nan koda yaushe cikin fad'a to yasin na dawo zangyara miki zama yakadai rigarsa yayi d'akin su, yabar inna hadiza da sakakk'en baki


K'ahuru ne ya shigo a guje yana cewa.


" wannan wacce irin musiba ce abu yak'i k'arewa yau nayi bayan gida yafi sau biyar Allah kaduba ni"


Inna hadiza tace.


"Ya dai duba mu inkana addu'a k'ai kad'ai Allah ba amsawa zaiba


Cikin fad'a yace.


Nasako dake dazu wanne rashin mutunci ne bakiyi manaba nida d'an uwana ak'an abin duniya dan haka yasin da mu kike zance shegiya kawe


"ganin tsahare tafito yayi fit yashiga


"cikin azabar ciwan ciki inna hadiza tace,


"Wallahi bara malam yadawo sai kunbar gidan nan tunda sokuke in mutu jikake tsuuuuu tasaki ak'asa ,


" basmah datake nesa taga abinda ya faru tasaki wata irin dariya harda ruke ciki yayin da zara take kwance cikin halin zugi domin sosai kirjinta yake mata ciwo




_______________________




*Addis Ababa Ethiopia*








Sanye yake da shadda gizner fara kal ya sanya hula bak'a yana sanyi da agogo Rolex watch kallo d'aya zakai wa agogon hannun sa kasan zallar gold ne k'asunbar sa sai shek'i take takalmin kafar sama baki ne wadda ake sawa taken sauciki hannusa yaduba yaga lokacin tashin su ya kusa yace.

"Kabir yice ko ba afad'awa yanjarida zuwana ba ko ?"


Kabir yace gaskia bani da masaniya amma k'aima k'anka kasani tayaya zaka zo birrin xaki al'ummar gari sukasa sani k'aine fa maijiran gado yauwa gaskia waddah ya kamaka Wotan nur bayan ta girma aka had'a da naka wadda kuk'ai tare da jiddah yayi kyau sosae yawa daman tare akayi su


"Afif yana jinsa yayi masa banza domin ya tambata yabiyewa kabir saiya sa sa ciwan baki anyi mutum ba gajiya ,


" ganin hak'an yasa kabir shiru da bak'insa har suka iso Addis Ababa airport har ciki akashi ga dasu cikin izzah ya fito daga cikin wata hadaddiyar mota hakama kabir yafito sai da akagama bincik'ensu aka tambatar cewa bizar su Afif beyarda ba ya shiga jirgi da mutane ba domin inwani besan Saba wani yasan sa private jet ya hauwa kuma awaje na musam ma akasa shi ..


mujallar da aka kawo mai ya fara dubawa kamar da gasama yad'aga ya d'aga wata mujallar ranar tambas rubutn ya dau hankalin sa inda akayi rubutu da manyan baki asama kamar haka,


*A YAU NE ZA'A CIGABA DA SAURARON SHARI'AR ALHAJI YUNUS SALIS MAI DALA*


inda ake zargin sa da safarar miyagun kwayoyi da safarar kananun yara kowa yasan alhaji yunus wadda akeyiwa lak'abi da mai dala sirikin Dr aliyu mansur aliyu zaki wato d'aga sark'in birnin zaki


Juya jaridar yake ko abinda yad'ai yana muradin samune tambas zai sawa sirik'ina ido zaimai kwantan b'auna yanzu bazai sa baki ashari'ar sa domin akwai takunsak'a tsakanin su musam man hark'ar kasuwancin sa shi baya matsawa al'umma komai nasa mai arahane tun kafin jiddah ta mutu ya nemi suhada hannu farashin su yazamo daya,


"Whiskey irin lemuk'an nan masu kama da giya ya tsiyaya yasha yasaki tattausan murmushi wadda balalle wadda yake kusa dashi yagane mai yake nufi ba ahankali ya furta yanzu wasan zai fara"


"Ahankali jirgin ke saukowa kasa ya dora'a babban filin tashi da sauka na malam aliyu mai zaki dake babban birnin zaki Masha Allah gaskia ta hadu wato komai na birnin zaki da banyake,


" ahankali yake saukowa tamk'ar mai tausayin k'asa a hankali yake k'arewa komai kallo tambas shekara shidda ba wasa ba komai ya canza a sanin daya yimai ya yarda da maganar bahaushe da yake cewa kowa yab'ar gida yab'arsa,


"Tuni wani memory baya ya dawo mai lokacin da had'a kayan sa bayan mutuwar jidda yab'ar k'asar gabaki daya yanzu ma in banda ance mai abie ba lafiya ba zaizo ba
Yazu kuma ya dawo ba dan yako maba sai dan yayi shirin rayuwar gaba insha Allah mak'iya sun daina cin galaba ak'ansa"


Sai yanzu yake ganin wautar sa da yabar gida da tuni komai yazo k'arshe yanzu zai sanyawa kowa ido domin binciko wanda ya kashe jidda da makuma wanda yake da sahannu acik'in kisan ba kowa ne yasan aik'in sa na boye sai Allah sai abie sai kuma shi domin ko kabir besa niba


Da sauri kabir ya dafa kafad'ar sa ya ce.


"Baba fa yaxu yana jiran ka tunanin mai kake haka ?"


Facemask ya d'auko yasa domin yasan za'a iya gane sa har yan jaridu suzo cik'in izza da k'aisata yake tafiya kallo daya zakai mai yashe da shid'in jinin sarauta ne gaban wata hadadd'iyar mota bak'a hulik harta glass d'inta bak'ine motar k'irar Benz ce cikin sauri driver motar ya fito ya zube a kasa yana ta mai kirari


"Afif hannu ya d'a gamai ya ce.


" Baba dan Allah kad'ai na d'ur kusa min ni da kai duk daya muke a wajan Allah ko bakomai ka haifini mai zaisa ka dinga zubewa a gabana tashi dan Allah yasa hannu ya d'aga shi "


Baba ya share kwallal data taro a idon sa ya ce.


"Aliyu nagodae tambas halinka mai kyau ne sa b'anin yan uwanka baka hulak'an ta da adam kana tausayawa nak'asa da kai ba abin da zan iyasa saka maka da shi ina godiya ko bana yima ka aiki kana biyana allah ya tsare ka ya kareka"


Ahankali ya bud'ai baki tamk'ar mai ciwan baki ya ce.


"Baba lokaci na tafiya muje a sibitin da ka kwantar da abie"


Baba ya ce.


"Gaskiya bazaka sami da mar mai martaba ba domin dr uzairu ya hana ganin sa yace yana buk'atar hutu"


Cikin kad'uwa afif ya ce


"Maisa za asa dr uzairu ya duba shi bayan ansan zai iya cutar dashi dole ne yau Inga abie inma manyan masarauta sun hana adawo dashi asibiti na ni zan kula dashi kuma zanyi binki can wanda yasa masa guba a cikin a bincin sa


Baba ya ce.


" To, shiga sukayi da gashi har kabir baba ya tuk'asu afif ya zaro wayar sa yana dan nawa da alama abu yake mai amfani wayar sa tayi ringing har sau ukku sannan ya d'aga yace,


"Yau ina so arabawa ma muk'ata kayan cikin store gobe insha Allah kayan dana yi order zasu zo amma iya kayan abinci ban da nasawa "


Cikin ladabi mutumin dayake waya dashi ya ce.


"To, oga angama


Be jira maganar ya k'arasa mai ya kashe wayar


"Gaban wani tamfatsaesan asibiti suka nufa yagaji da had'uwa abin sai wanda yaga ni gaba ki daya an zane shi da dagi (wato zannan sarauta)
a gaban asibitin anyi rubutu da manyan baki an rubuta,




*SAIFULLAH ABDULHAKIM MAI ZAKI INTERNATIONAL HOSPITAL*


Wannan asibiti mallak'in masarauta ne tun farkon kafa masarautar aka samar dashi domin duba sarki da ahalin sa masarautar wannan k'arni kowanne sarki inyazo sai ya gyarashi alokacin mulkin sarki aliyu a ka rushe shi yama ginin bulu da bulu yayi musu abubuwa na ban mamaki yasamar da makarantu da da asibitoci yayi musu wutar su tak'an su shiyasa awannan gari basu da tsara wajan cigaba sarki saifullah shiya fara gina asibitin yasa sunan sa yakuma mallakawa masarautar ,


"Asalin su yan k'asar Ethiopia ne awasi yanki da ake kira *TETHYAN*
al'ummar wannan yakin suna rayuwa kamar dabbobi basu yarda dawani addini ba ko addinin Christan basayi basu dawani tufafi sai ganye yankin tethyan yaki ne mai sahara sarki saifullah iyayan sa shika dai suka haifi shi sai yan uwan baban sa suna da yawa sosai kwasam sai adalin sarkin kasar masar ya turo malame domin ayi musu wa'azi "


Sun sha wahala sosai saidai wasu da ga cikin su sun musulim ta saboda azabar da kafirawan wannan k'arni suke musu yasa suka bar k'asar baki daya tafiya suke sugaji suyada zango wasu acikin su in wahala tayi yawa wasu suka mutu k'alilan ne suka rayu inda suka sami daji mal yalwar ruwa da bishiyoyi suka yada zango masu maharba in suka zo harbin su kan yada zango haka birnin zaki ya kafu da akai shawara yaka mata asamar da sarki agarin alokacin saifullah yana da mata Khadijah sai su kaga yaba da hali mai kyau suka nadashi zamo shine sarkin su a inda aka samo garkon garin su Zara ayi da al'umma taki yawa wasu hausa wa ma suka tattaro suka dawo garin musam man fatake yayin da wasu larabawa suka kawo musu tallafi a haka suka sami ci gaban kwastsam wata rana khadijah ta haihu ta haifi danta na miji akasa mai abdullhakim ya maida sunan baban sa watan abdullhakim daya mahaifinsa ya mutu mutuwar ta gir giza sa.


Nan fa yan uwan mahaifin sa wa yanda sukayi ragowa suka shiga a zabtar da shi sai suka shiga fada ala dule saiya sauka da ka kan mulki sauran yarukan dake garin suma suka ce sai ya sauka ya zamo duk shekara ukku za adinga nadin sa masarauta al'umma gari kuwa suka ce basu yarda ba a yayin fad'an ne aka kashe mahaifiyar sa saida yayi sati baya sanin wani a k'ansa abdullhakim yana da shekaru takwas aduniya.


"Khadijah tak'ara haihuwa ta haifi d'anta namiji yasa masa Ahmad sosai yayi murna da sa muwar wannan da bayan Ahmad khadijah ta haifi d'anta namiji a kasa masa aliyu wato kak'an afifi sarki saifullah yana da shekara dari da tatin ya mutu yayi daya yi duguwar jinya wasu na ganin cewa jifansa akai hadinga aman jini"


Saifullah ya dubu khadijah ya ce.


"Nasan daga wannan rashin lafiyar bazan ta shiba ya ku ya'yana ina yi muku nasiya da ku hadai kan ku dana ya'yan ku ku zama tsin tsiya ma daurin ki d'aya ke hajarah kece karama ina yimiki nasiya daki bi yan uwanki
duk abinda yan uwana zasu yi muku ku kauda idon ku nasan mahaifina ya fad'an min kafin ya mutu cewa yayi mafarki k'an ya'yana da jiko kina zasu rabu ba ak'an komai zasu raba k'an suba sai akan mulki kuma sannan in kukai hakuri kune zaku dinga mulkin birnin zaki iya Sani na naba ku ilimin addini nawaba turawan kasar asi damar zuwa wannan k'asa koya wa al'ummata karatun zamani alhmdllh kun iya nasamar da makarantun addini dana zamani ko bayan raina ban yarda asibitin dana gina kusa shi agado ba nayi ne domin al'ummar garin nan k'arku yarda ahad'a hannu da ku wajan cutar da yan uwan ku k'ar ku bawa yan uwana da mar kud'a kai da su ku cutar da d'ayan ku"


Cikin kuka suk'ada baki suka ce insha Allah zamu kiyaye


"A yau na kasan ce me farinciki saboda duk kan wani nauyi na al'umma na sauke ina kuma da d'ai godaiwa Allah da yasa k'asar birnin zaki ta zamo laular Muslim ci a nayi yarnan ban bar muku komai ba sai zinare
daya shima na gada daga gun mahaifina sai kuma ilimin dana bar muku kuyi ko k'ari ku rek'e sana'ar ku ta fitar da kayan masarufi kuna k'ai wa wasu k'asa shan dama garu ruwa makotan mu .


magana ce ta kak'are mai ganin haka suka rudai sukai kan sa Kalmar shahada itace zancan sa na k'arshe aduniya wani ihu hajara ta saki nan ta rumgume mama tana kuka bayan arba'in baffanin sa zoka zo domin a shawarta wanda zai maye gurbin sarki tuni suka manta da na shiyar mahaifin su ban da Ali haka kuwa ta faru anyi riki ci daga k'arshe abdulhakim ya hau kujerar mulki bayan ya mutu Ahmad ya hau kujerar mulki haka akazo ka'n sarki aliyu


*sarki aliyu*




Yanada mata ukku matar sa ta farko itace hajiya asma'u wacce ake kira anni tana da ya'ya uku akwai alhaji mansur sai alhaji Ibrahim sai gimbiya sauda sai matar sa ta biyu itace hajiya maimunatu tana da y'aya biyu akwai gimbiya sumayyah sai alhaji Adam sai matar sa ta ukku itace hajiya rafi'a ita Allah be nata haihuwa ba duka matan suna auran manyan mutane basu yarda dawani bare ba ba d'an cikin zuri'ar su ba lokacin da alhaji mansur xai aure mamy kaf cikin su ba Wanda ya yarda sai sarki aliyu ran anni ya kai mutuk'ar baci da jin hukuncin da mai martaba ya yanke"

Cikin fusata take tafiya bata damuwa da irin kallon da hadimai ke mata da kuma baya alkabbarta harta na hardai ta isa shashin sarki inda yake hutawa sai dai ranar bara ranar girkin ta bace ta hajiya maimuna ce iso ta nai ma


Mai tsaron kofar yace.


"Ranki ya dai dai bara inje in isar da sak'on ki ,


Zuciyarta wani irin tafasa take ta d'a k'anta domin bazata tab'a lamunta ba d'anta ya aure shuwah kuma domin kowa ya sani su mallake maza suke sai abin da suka ce musu hak'an ma abin kunya ne a cikin kishiyoyi ta kuma uban ta ma balarabe ne babarta ce shuwa tana cikin tunanin zuci


Ya zo ya zube a gaban ta ya ce


"Ranki ya da dai na isarwa da jakadiya sak'on ki kuma ta fad'a mai ya baki iso "


Bata tsaya Jin mai zai ce ba ta shiga cikin haddan floor ya gaji da had'uwa ga wani ni imtatcan kamshi da ke ta shi hajiya maimuna tana zaune a a kai Royal chair mai launin c green an k'awata ta da adon flower milk da yarfin golding tana taka Turkey carpet k'a fa fuwanta na nitsaiwa saboda taushin sa bata biya ta kan hajiya maimuna ba ta nufi d'akin kai tsayai sa munsa tayi ya ki shingid'a yana jan carbi dana kare mai kallo dadtijo ne domin ba za a kirashi tsoho ba fatarsa chocolate color ce irin ta yan ethiopia wato shi ba fari ba shi ba baki ba yana da manyan idanuwa fuskar shi cike da k'a sun ba haka da yake ya cire rawani kan shi yana da yalwar gashi duk da furfura ta kusan cike k'an sa da sauri na sun ku yar da k'ai saboda da guwar da yayi ya amsa sallamar hajiya anni tambas Allah yayi mai kwar jini ya cika sunan na sa da ake ce wa ali


Samun gu tayi ta zauna ta rusunar da kai tace.


"Barka da hutawa an samai ka lafiya ba tajira amsa warsa ba ta ciga ba domin kusan halin su daya da afif akwai alamun da zai maka kasan cewa yana tare da kai in ko kuma ya amsa ran ka ya dai adalin shugaba na ji maganar da kayi na cewa ka tura hakimai su tambayo auran mansur Allah ya k'ara maka ni san kwana ba we zan ja da maganar ka ba aa ka duba ka gani kaf ahalin mai zaki ba su tab'a auran bare ba in kayi haka zai iya budai kofa ga yan baya suk'i jinin su su auro bare ya sarkin birnin zaki ka duba magana ta shine d'an ka na fari ba wataran shi zai zama sark'in garin nan ,


Shiru yayi yana sauraran ta kamar ba zai magana ba sai ya ce.


"Ni shugaba ne dole inyi adalci a k'an dauyin da Allah ya dora min mu da su duk al'umma daya ne kuma mu musulmene dan haka aure ba fashi nan da sati mai zowa za a daura aure ki shirya amsar sirik'ar ki zaki iya ta fita "


Mamaki ne ya kusan kashe ta a zaune mai isa yana da kafiya in yace eh to babu mai juya ta ta koma aa cikin kunar rai ta tashi muryar ta na rawa tace,


"Na barka lafiya fucewa tayi ranta in yayi dubu ya b'aci dariyar da maimuna ta saki ce ta sa ta dawo hayya cin ta bata Kula ta ba ta huce domin a yanzu bata da lokacin hajiya maimuna amma a juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe tasa k'afa ta futa direct shashin ta ta huce tana zuwa ta d'auki waya ta shiga kira har ta kusa yanke wa aka dauka aka ce


"Hajiya anni barka da rana
ina toilet ne shiya ban d'auka da huri ba ina fatan lafiya ?"


Kilishi ina ba tun lafiya mahaifin ku ya dage sai wannan yarinyar ta shigo gidan nan ina cik'in ma tsala


"Anni kuma duk abin da malam ya ce a yi k'in yi kuwa ?"


Kilishi na daina kashe kud'i na agun malamai kina ga wancan karon da muka je cewa yayi asiri ko tsafi ba zai tab'a cin sa ba na barwa Allah komai ita ma ance ta na da addu'a kullum sai tayi azk'ar tun da ya dage sai ya aure ta to nan da wata hud'u da auran su zai auri yar gid'an hajiya aina'u aminiyata..........✍🏼


*AFIF*






Oum yasmeen






*My first novel is return black*




_the writer of BINTA YAR JAGALIYA_


https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k


*____________________________________*


*____________________________________*




Chapter 51-60






" Anni anya kuwa zai yarda ya aure ta kin san halin yaya fa ,




Tsaki tayi tace




"Barni da shi sai ya aure ta kamar yadda mahaifin sa ya yarda ya aure zab'in sa nima sai ya aure nawa yarinyar nan zaliha tana da k'irki ga tarbiya"
Hmm anni kenan kamar ba kisan wace mahaifiyar ta ba kuma fa kinsan tare mukai makaranta da dai kin zab'a mai wata da yafi amma wallahi anni


Ai kafin ta k'arasa abin da tayi niyar fad'a tace ,






"Kilishi yimin shiru in ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login