Showing 51001 words to 54000 words out of 142577 words
Chapter 18 - WANI SALO BOOK COMPLETED by Sa'adatu Alkali D-Tsafe.txt
kanshi yana kad'a hannun
tare da zaro harshen yana kad'awa Ummul cikin tsokana yace.
"Bana gaya mikiba yanzu ke ba y'ar gida nan bane yanzu dagani sai Nenne na."
ya k'arishe maganar yana rawa,
Usman ne ya d'an roggoshi keyarshi yace.
"Aliyu wato kaine d'an tada zaune tsaye ko."
ita kuwa kuka tasa tana cewa.
"Ya Usman ba kaga Aliyu ba."
Murmushi yayi yace.
"Muna sonki Ummul d'in mu ke y'ar gidan nance har Abadan."
K'ollah ta zubda tare da cewa.
"ya Usman kai kad'ai kake sona, nima ina sonka."
Ido ya lumshe sannan yace.
"Allah ya d'aiyiba."
murmushi sukayi dukan su,
shi kuwa Hamma Umar hannun Usman ya jawo ya d'an sunkuyo kanshi a hankali yace.
"Ka kula da kanka d'an uwana ina son ka ina tsoron abinda zai cutar da kai."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Nayi lafiya fa."
Haka sukayi sallama suka tafi,
Ita kuwa suna fita harabar gidan ta bud'e sabon shafin kuka,
sunyi tafiya mai d'an nisa,
Hamma Umar yana tuk'in hankalin shi na cikin tunanin halin da k'anin shi ke ciki,
kamar a mafarki yaji Ummul tasa hannunta ta d'amk'o........
By
*GARKUWAR FULANI*
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 2⃣0⃣
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
*H*annun ta tasa ta damk'o siterin ta rink'a juyashi tare da murza shi da k'arfi tana.
"Allah ka tsaya ni in sauk'a ehe,
ni bazan koma gidan kaba ka sauk'e ni a nan zan tafi gidan Anty Halima."
murza kan motar take da k'arfin ta,
tuni motar ta fara yawo a tsakiyar titi ga ababen hawa dake ta gaban su da bayan su da gefe,
gaba d'aya motar kanta ya kufce,
a firgice yace.
Innalillahi Ummul kin san abinda kikeyi kuwa?."
fizge hannayen ta yayi da k'arfi cikin tashin hankali ganin ya nufi kan wani mai a dai-dai ta yana
k'ok'arin hawa kanshi ita kuwa tak'i sakewa sai murzawa take tana.
"Ka sauk'e ni a nan bazan koma gidan kaba bana sonka na tsaneka."
Ido ya zaro cikin tashin hankali ganin saura k'iris ya taka wani mai reke da yake gefen titin gaba
d'aya mutanen wurin sai rik'e kai sukayi suna.
"Innalillahi subahanallahi."
shi kuwa Hamma Umar cikin firgici da tsoron ganin zata sashin kisan kai gaba d'aya jikin shi sai
rawa yake yi,
cikin b'acin rai ya fizge hannayen ta sannan ya tura ta jikin sit d'in ta koma ta bugi jikin marfin
motar sannan ta sake tasowa tana k'ok'arin sake rik'e kan motar,
tsawa ya buga mata cikin zafin rai ya ware tafin hannun shi ya zuba mata mari d'aya wanda
saida taga taurari na yawa a sararin samaniya kunnen ta saida ya bada sautin kiuuuu sannan ta
kuma jin yayi dum lokaci d'aya zanen yatsun shi suka taso a farar fatarta tuni fuskar tayi jazir
gaba d'aya ta rasa ina take dan marin ya gigitata, shi kuwa da k'er ya samu ya tsaida motar jikin shi na rawa zuciyar shi cike da tsoron karta sashi
kisan kai yayi parking a gefen titin cikin sauri ya fito ya nufi gun mai reken da mai a daidaitan
hak'uri ya rink'a basu,
da sun hatsala amman ganin yadda yake basu hak'uri yasa sukace.
"ba komai Allah ya tsare gaba a rink'a kula."
"Toh nagode."
yace dasu sannan ya koma cikin motar ya shiga ya zauna fuska a tsuke tamkar bai tab'a dariya
ba,
jan motar yayi da gudu ya kama hanyar damaturun,
ita kuwa tunda ya zabga mata marin ta kife kanta kan cinyoyin ta ta rink'a kuka mai cike da
takaici,
bai kulata ba,
ita kuwa kukan taci gaba dayi tana sheshshek'a,
a haka har suka isa cikin damaturu a inda suna shiga hadari na tashi iska mai sanyi ya rink'a
busawa tako ina sai walkiya ake da d'an rugugi alamu irin hadarin karshen damuna ce,
suna isa yayi parking sannan ya koma ya zauna ya jingunu da jikin kujerar yana jin yadda take
kuka,
a zahiri mamaki yake irin tsanar da Ummul ke mishi sannan itace da laifi itace da kuka kuma
har cikin ranshi yaji zafin marin da yamata,
ajiyan zuciya ya sauk'e sannan yasa hannu ya d'an dagota ya jingina ta da jikin shi hannun ta
ya kamo cikin sanyi ya cusa hannun kan k'irjin shi sai kuma ya kalleta a hankali yace.
"Kiji yadda kikasa zuciya ta bugawa dan tsoron karki sani nayi kisan kai Ummul nine ba kyaso
amman k'iyeyyar har tana k'ok'arin saki in kashe wasu a banza."
sai kuma yayi shiru sannan yasa tafin hannun shi yana shafa fuskar ta a hankali yace.
"Kukan ki nasa zuciya ta tayi nauyi sabida sai inga kamar na k'asa rik'e amanar dana d'auka ne
kiyi hak'uri ki gafar ceni banyi niyar tab'a lafiyar jikin kiba."
tureshi ta rink'a yi tana janye hannun ta,
shi kuwa rik'e hannun yayi a hankali ya bud'e d'an durowan gaban motar wani d'an k'ara min
kontena ya d'auko bud'e wa yayi sannan ya d'auko wani zoben Diamonds sai shek'i yakeyi
tamkar tauraro yatsarta ya d'an d'ago a hankali ya zira mata zoben cikin sanyi yace.
"Kinyi kyau matata yatsarki ta haska zoben."
fizge hannun tayi dai-dai lokacin da ruwan sama ya fara sauk'a ,
bud'e motar tayi ta fice cikin kuka ta koma can tsakiyar harabar gidan ta tsaya tana kuka,
ganin haka ya fito ya rufe motar cikin sauri yaje gabanta hannun ta ya rik'o tare da cewa.
"Kiyi hak'uri zomu shiga cikin gida kar ruwan ya tab'a mu,
kinsan ni bana son ruwan sama ya tab'a ni zai sani zazzab'i."
cogewa tayi fir tak'i shiga daya kamo hannun ta sai ta dasa mai ihu,
ganin haka ya rufe gidan sannan ya wuce ya shiga cikin gida a zaton shi ko zataji tsoro ta
biyoshi,
Abu kamar wasa ya shiga,
ita kuwa sai tsuguna wa tayi a wurin ruwan yana ta sauk'a a kanta duk ta jik'e tayi jilik sai d'iga
takeyi ga tsawa da walkiya da akeyi,
parlour ya fito rik'e da leima ya nufi gunta,
yana zuwa ya jawota jikin shi cikin rawan sanyi yace.
"Khairi kiyi hak'uri mu shiga cikin gida kar mura ta kamaki d'an Allah mushiga ciki bana so
ruwan ya tab'ani."
Jin haka ta fizgota leimar ta cillata gefe haka ko iska ya debeta yayi woje da ita,
shi kuwa da sauri ya d'ago hular rigar shi da take konce a kafad'an shi ya rufe tsakiyar kanshi
dan in ruwan sama ya bugi kanshi yana sashi zazzab'i da ciwon kai mai tsananin,
hannun shi kuwa ya hard'e a k'irjin shi tuni ya jik'e cikin rawan sanyi da karkarwa ya jawota jikin
shi a hankali yace.
"Toh aikin rama mu tafi cikin gida kiyi hak'uri k'anwata."
cikin kuka tace.
"Ban rama ba kam,
kuma bazan shiga gidan kaba sai in zan rama marin da kayi min."
murya na rawan sanyi yace.
"Na yarda mu shiga saiki rama."
baki ta tura sannan tace "toh."
hannun ta yaja suka shiga cikin gidan ,
suna shiga d'akin ta ya nufa da ita,
a gaban mirror ya tsaya da ita,
cikin rawan sanyi ya cire mata mayafin nata sannan ya zuge zip d'in rigar ta yasa hannu zai cire
mata rigar tayi maza a juya tana hararan shi tana cewa.
"Ka barni in cire abina da kaina ."
"Na barki nima bari inje in cire nawa."
sai kuma ya bud'e durowa ya zaro mata riga da wondo wondon iya guiwa sai rigar mai d'an
fad'in wuya ta yadda kafad'an ta yake fita inya ta saka kayane mai tashi da sulbi,
kan gado ya ajiye mata sannan ya fita ya koma bedroom d'in shi,
yana shiga ya canza kayan shi sannan ya fito ya nufi kitchen tea ya dafa musu mai zafi wai
maganin sanyin,
d'akin shi ya koma da niyar d'auko woyarshi yana rik'e da cups d'in yana juyowa da nufin zai fita
kenan ya ganta tsaye a bak'in k'ofar shigowan fuska a had'e tace.
"Zan rama fa ehe."
Ido ya tsura mata cikin mamaki ajiye cups d'in yayi kan mirror sannan ya juyo a hankali yace.
"Toh zoki rama."
shigo wa tayi ta tsaya a gaban shi ta d'an d'ago kanta tana kallon fuskar shi,
shi kuwa kollon d'an tsawonta yake tunda ko fuskarsa in zata kalla sai ta daga wuya da kai,
kuma wai shine tana ikirarin tazo ta rama marin daya mata,
cikin ranshi kuwa jira yake yaga iya rashin kunyarta zata mareshin neko k'ak'a,
ganin tana ta d'ago wuya da k'afafun ta dan ta isoshi tsawo ta kasa,
sai ya d'an rok'ofo kanshi ya sunkuyar dai-dai tsawonta cikin rumtse ido yace.
"Rama."
fuskar shi ta tsurawa ido ta d'ago hannun zata yarfa mai marin sai kuma tayi maza tayi k'asa da
hannun sai hawaye car-car a idanun ta,
shi kuwa jin shirun ne sai ya bud'e idanun shi ganin tana kallon fuskar shi tana kuka yasa ya
d'an yi murmushi cikin kula ya jawota jikin shi ya ruggume ta kanshi ya sunkuyar dai-dai kan
hab'arta daya maran a hankali ya rink'a fese mata iskan bak'in shi mai sanyi sannan yasa tafin
hannun shi yana share mata k'ollah, ita kuwa cikin kuka tace.
"Ni dai sai na rama amman ba, a fuskar kaba."
murmushi yayi a ranshi yace.
"Gaskiyar bahaushe wata fuskar tafi k'arfin mari."
fahimtar da yayi bazata iya ramawan bane,
sai ya mik'o mata cup d'in tea shima ya d'auki d'ayan ya fara sha yana lumshe ido cikin lallashi
yace.
"Kisha tea sai na goyeki a madadin marin."
ajiye cup d'in tayi tace ita bazata shaba kuma shima ya ajiye sai ya goye tan,
murmushi yayi ya ajiye cup d'in yana jin sanyi na ratsashi,
tsakiyar d'akin ya dawo kan carpet ya durk'usa ya mik'e tsawonshi kamar mai konciya sai kuma
ya d'an taso ya k'afa hannun shi a k'asa sannan ya mik'e tsawonshi ,
cikin sanyi yace.
"Toh zoki hau."
murmushi mugunta tayi dan tanaga bazai iya d'aukar nauyin taba,
da sauri ta matso ta zauna a tsakiyar bayan shi sannan ta tonk'oshe k'afafun ta ta d'an ware
hannun ta sannan ta had'a yatsun ta haka tana ta murmushi mugunta ,
dai-dai lokacin woyarshi ta rink'a suwa ita kuwa sai gyad'a kai take tana lumshe ido,
yana kallon ta duk abin da takeyi,
a haka har
zuwa wani d'an lokaci sannan ya manna jikin shi kan carpet d'in ya kwanta yana maida
numfashi,
itako murmushi tayi sannan ta mik'e zata tafi,
sai ya rik'o hannun ta ya fizgota jikin shi ya matseta gam cikin maida numfashi yace.
"An gaya miki ni dokine da zan goyeki a banza,
nima saina samu maganin sanyin da kika samin."
Baki ta tura tace.
"Toh ai ba ladan mari bane,
kuma ni bani da
maganin sanyi."
"Kina dashi mana."
"Toh ina yake?."
hanun shi ya cusa cikin jikin ta tare da lumshe ido yace.
"D'umin jikin kine kawai zai cire min wannan sanyin inba hakaba zai sani zazzab'i."
tureshi tayi ta mik'e sai kuma ta d'an yi k'ara jin yadda yake murza hannun shi a kan k'irjin ta,
murmushi yayi ya mik'a hannun kan gado ya jawo blanket sannan ya jawota jikin shi kan carpet
d'in ya kuma rufesu da blanket d'in,
hannun shi yasa yana shafa cikin ta a hankali yace.
"Ina son Baby daga gareni Khairi kiyi Addu'a Allah yasa yau nayi ajiya a nan."
tureshi takeyi shiko sai murzata yakeyi a hankali yace.
"Kiyi hak'uri in kasance dake."
Cikin fad'a tace.
"Bana so."
da sauri yace.
"Karya ne kina so kam."
hawaye ta fara zubdawa tana jin yadda yake murzata da juyata,
ita kuwa,
tureshi take d'an yi duk da yau yana binta a hankali ba zafi sosai,
amman sai kuka takeyi cikin raki tana cewa.
"Bana sonka na tsaneka."
duk da yana cikin duniyar nitsuwa Amman yaji zafin kalamta gare shi,
a ranshi yake fad'in.
"Ko cikin yanayin da ma'aurata suke ruggume juna dayin musayan kalaman soyayya shi a cikin
yanayin ma Ummul tureshi take a madadin ta mak'ale shi sannan kalaman k'iyeyya take fad'a
mishi a madadin na soyayya kuma kuka take na jin tsanarshi a madadin tayi kukan gamsuwa,
haka ya zame jikin shi ya konta gefe sannan ya jawota ya ruggume ta da k'arfi yana fidda
nannauyan numfashin a hankali yace.
" wata rana zaki soni Khairi ,
fatana Allah yasa jinin na ya gauraye da naki,
ki haifarmin d'ana nasan shi kam zai soni."
manne wa tayi a jikin shi dan ya gajiyar da ita ga kasala daya k'ara rufeta numfashi ta rink'a
maidawa a hankali,
cikin ranta kuwa fad'i take.
"Tabbas in nayi garaje Hamma Umar zai d'irka min ciki ya barni da matsala."
a haka da wannan tunanin tayi bacci a jikin shi,
shi kuwa ruggume ta yayi har saida yaji baccin ta yayi nisa sannan ya mai data kan gado shi
kuma ya gyara wurin yaje yayi wonka yayi al'wala yazo yayi ta nafilfilin daya saba da karatu
qura'an,
sai k'arfe 2:30 ya konta ruggume da ita.
Washe gari da safe bayan ya gaba komai ya shirya ya fita,
yana fita itama ta fita kai tsaye kemis na bayan layinsu taje k'wayoyin family planning ta seyo
tazo ta boye wanda kullum sai tasha,
acewarta bazata haihu dashiba in yana son haihuwa ya saketa ya auro wata.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya kullum sai tasha maganin a boye duk da ba wani bashi kanta
takeyi ba,
bayan ta fara shan maganin da kwana goma kawai ranan ya shiga ya samu tasha maganin
kenan tana rik'e da sachet d'in,
sosai Ummul taji tsoro da mamakin yadda Hamma Umar d'in ya birkice mata tamkar zaiyi hauka
bata tab'a ganin baccin ranshi kamar na wannan ranar ba,
ya rink'a surface mata fad'a daga karshe ya kwashesu yace zai kai ya nunawa Abba ,
ganin haka tayi ta kuka tana bashi hak'uri tare da cewa bazata sake shaba,
ganin yadda ta nuna bazata kuma ba yaji dad'i ya yarda ya barta bayan yayi ta mata nasiha.
Toh fa bayan sunyi haka da kwana biyu ta lallab'a taje wani prvt hospital ta shirga k'ariyar ta
kan cewa da yardar mijin ta suko tunda aikin kud'i ne ba wani dogon bincike suka sa mata y'ar
robarnan da ake tsawa a hannu suka d'inke mata,
suka amshi kud'insu ko a jikin su,
koda ta dawo haka tayi ta wasan b'uya da Hamma Umar d'in har saida wurin d'inkin ya worke
ras ta yadda bazai ganeba,
shi kuwa kullum addu'ar shi Allah ya bawa Ummul d'in ciki yanaga duk abin nata zai ragu inta
fara haihuwa dashi.
Yau Saturday tun safe Hamma Umar baije ko inaba yana gida ko parlour bai fitoba yana d'akin
shi ,
dan ya fara gajiya da azabtar dashi da Ummul keyi,
ita kuwa Ummul tun safe ta shirya a nufinta in taga ya fito zai tafi potaskum zatace zata bishi,
ganin shiru-shiru bai fito bane har bayan sallan la'asar saita fito a hankali ta nufi d'akin nashi,
a hankali tayi sallama tare da tura k'ofar ta shiga,
kan gadon ta hoggoshi yana kwance yayi rigingine ida nunshi a lumshe ba komai a jikin shi sai
towel dake d'aure a k'ugunshi alamun daga wonka ya fito,
shiru bai amsa sallamar taba,
shigowa tayi cikin d'aga k'afafun ta a hankali bak'in gadon taje ta tsaya tana son ta tasheshi ta
rasa ya zatayi ta tasheshin gashi gaba d'aya ganin surar jikin shi na bata tsoro,
a hankali ta durk'usa a bakin gadon cikin kauda fuska ta fara magana.
"Hamma! Hamma! Hamma ka tashi mana."
yana jinta yayi shiru kamar maiyin bacci a ranshi kuwa farin ciki yake da shigowar ta d'akin
nashi,
ita kuwa tashi tayi ta zauna gefen shi a bakin gadon a hankali tace.
"Hamma yau bazaki je gida bane? Hama weekand d'in ma baza'a fitaba ni ina son zuwa inga
Nenne na."
murmushi ya d'an yi gano yawo take son fita shiyasa take wani yin ladabin kura ga mai akuya,
mik'a yayi a hankali sannan yasa hannu ya jawota kan k'irjin shi hannun shi yasa ya rink'a shafa
bayan ta a hankali yace.
"Zamuje mana in kina so."
Mutsumutsu ta rink'a yi cikin had'e fuska tace.
"Ehh ina so mana ka tashi mu tafi."
towel d'in nashi ya rink'a murzawa tare da jawo blanket ya rufe su sannan ya k'ara jawota jikin
shi a hankali yace.
"Bazan iya tuk'in ba sai an bani maganin."
hannu tasa tana ture hannu shi da yaketa b'alle boturan gaban rigar ta mai dogon hannu wai
duk dan ta boye tabon abin family planning d'in ne,
shi kuwa ido a rufe ya zare rigar tata,
sannan ya kuma rink'a shafa wutanta ido a lumshe a hankali har ya isa kan damtsen hannun ta
da akasawa robar,
ido ya bud'e jin kamar d'an k'urji a cikin hannun nata gashi da alamun kamar tabo,
da sauri ya tashi zaune cikin hamzari ya d'ago ta ya manna ta a k'irjin shi sannan yasa hannu ya
kamo hannun nata ya d'an daga,
da sauri ya tureta cikin wani irin yanayi ya kafa mata.
By
*GARKUWAR FULANI*
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 2⃣1⃣
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
*I*do ya tsura mata yana k'ok'arin k'ara jawo hannun nata,
ita kuwa da sauri ta janye hannun gaba d'aya har jikin ta na rawa sai ta konta a kife ta cusa
hannayen nata k'asan k'irjinta ta konta kan hannayen tayi luf