Showing 24001 words to 27000 words out of 142577 words

Chapter 9 - WANI SALO BOOK COMPLETED by Sa'adatu Alkali D-Tsafe.txt


Ammina munyi kewar ki."
Kanshi ta shafa cikin kula da k'aunar irin ta uwa da d'anta tace.
"Allah ya muku albarka."

"Ameeen ya rabbi Habibi Ammin mu."

Inna dake cikin d'akin ne ta fito jin muryan jikan nata da kuma k'amshin turaren babban jikan
nata,
cikin sauri ta fito,
tana zuwa ta kalli Usman yadda yake zuba yarinta a gaban mahaifiyar tashi ,
dariya tayi sosai tace.
"Shin wai kaika kam Usmanu baka ganin ka girma ne gankafa tsoho da kai."

Kallon ta yayi cikin dariya yace.
"D'a baya girma a gaban iyayen shi,
na rasa d'umin jikin Abba na tun ina da shekara d'aya kinga ko dukda haka Hamma Umar na
ya zame min madadin Abba na."

Murmushi sukayi dukan su,
dai-dai lokacin kuwa Hamma Umar yayi sallama cikin sanyi,
fuska a sake Inna ta amsa mai gami da cewa.
"Umaru sanda kafi mata yanga Umaru kafi k'arfin kabi mace sai dai ta bika Umaru sanda mai
k'amshin al'miski Umar mai yawan kyauta da tausayi."

Murmushi yayi cikin sanyi yace.
"Bakya gajiya da surutu ne ke kam?."

"Ya zanyi in gani ance ma kowa irin Kane mai tsadan magana."

Kallon ta ya d'an yi cikin sanyi yace.
"Allah ko Ammin Inna ce ta b'ata miki yaro da surutu kinga Usman ko duk surutun ta ya d'auka."

"Ehh d'in na b'atashin."

Shi kuwa Usman dariya kawai yake dan yasan dama za'a rina,
itako Ammi murmushi kawai takeyi tana kallon fuskar d'an nata,
shi kuwa Hamma Umar a hankalin ya matso gaban Ammin nashi cikin girmamawa da tsananin
k'aunarta ya durk'usa a gabanta guiwa bibbiyu cikin sunkuyar da kai ya cire hular kanshi,
ya k'ara matsota tare da sunkuyar da kanshi.
a hankali Ammi ta d'ago hannun ta cikin sanyi ta dafe tsakiyar kan nashi sannan ta kalleshi cikin
kula tace.
"Allah yayi muku albarka rabbi ya karemin ku aduk inda kuke Allah ya tsare min imanin ku."

a hankali ya d'ago hannayen shi duka biyu ya dafe hannun ta dake tsakiyar kanshi cikin sanyi
yace.
"Amin Amin Ameeen ya rabbil izzati ,
Ammi Allah ya kare mana ke."
"Amin Amin"
tace sannan ya koma ya zauna gabanta ya tonk'oshe k'afafun shi yana fuskantar ta,
shi kuwa Usman yana konce kanshi na kan cinyarta shima yana fuskantar d'an uwan nashi.

Wannan shine d'abi'a ko once al'adarsu Hamma Umar muddin suka zo gunta.

Ita kuwa Inna sai murmushi take tana kallon d'iyar tata da yaranta,
itako Ammi ajiyan zuciya ta sauk'e cikin sanyi tace.
"Farouq ya jikin d'an uwanka?."

kai ya d'an d'ago ya kalleta a hankali yace.

"Ammi da sauk'i sai dai Usman sam baya son bin dokan likita komai ya samu ci yakeyi yayita
d'ure-d'ure kuma yasan zuciyar sa nada rauni Ammi kiyi mishi fad'a bana son abinda zai cutar
dashi."
ya karishe maganar cikin raunin murya

Hannu Ammi tasa ta kamo kunne Usman d'in cikin hukuntawa tace.
"Baka ji ko?."
k'ara ya d'an saki cikin d'an yarfa hannu yace.
"Kai Ammi ninefa banda lafiyar amman kuma wai sai Hamma Umar zaki tabbaya ya jikina d'in,
shiko ya fiye tsare-tsare."

Dariya Inna tayi tace.
"Baka dai ji shiyasa."
.dai-dai lokacin yayan Ammin nasu ya shigo shima dariya yakeyi d'an yana matukar k'aunar
yaran k'anwar tasu.

Bayan sun gaggaisa ne,
sukaci gaba da hira,
Usman yana zaune gefen Ammin su yana bare banana yana mik'a mata tanaci inya bata d'aya
sai ya kuma bawa Inna sannan ya mik'a wa kawun nasu pilet d'in,
shi kuwa Hamma Umar zaune yake kusa da Ammin nashi yana rik'e da hannun ta yana yanke
mata farce,
abinda tunda Umar ya girma shike yanke mata farce,
yakan shirya sam musamman dan yaje ya yanke mata farce kuma hakan shike yankewa
Usman ma fartatunshi.

Suna cikin hiran kawun nasu ya d'an yi gyaran murya cikin sanyi yace.
"Umar kwana ki su Abban ku sunzo sun min baya nin batun auren ka da d'iyar Abban naki,
mun tattauna maganar kuma yadda sukayi yayi dai-dai,
toh shekara jiya sunzo sun shaida min asabar mai zuwa za'a d'aura auren sun kuma cemin sun
gama komai za'a fara bikin nanda kwana 3 ,
toh Amman duk da sunce sun gama komai mukuwa mun had'a kayan lefen ,
yanzu haka Antyn ku sun tafi kai lefen ne shiyasa kukaji gidan shiru."

Kai ya d'an d'ago ya kalli kawun nasu da Ammin shi sannan ya kalli Inna da Usman a hankali
yace.
"Dama nazone in shaida muku batun,
ashe Abba har yazo."
sai ya juya gun Ammin shi murya can k'asa yace.
"Ammi ban nemi auren nan ba su Abba bani kawai sukayi shiyasa baki tab'a jin na miki zancen
ba ko Usman ban gaya mishi ba dan nima a satin daya wucene suka gaya min,

amman Ammi ya kika gani kina son abin ko a barshi?."

Murmushi tayi tare da shafa kanshi cikin kula tace.
"INA so Farouq ina al'fahari da wannan had'in fatana Allah ya baka ikon rik'e amanar da suka
baka ka kular musu da d'iyarsu fiye da yadda suka kula da kai da d'an uwanka."

Cikin rauni yace.
"Insha Allah Ammi yadda kikace haka za'ayi."

Shi kuwa Usman murmushi ya rink'a yi cikin jin dad'i da wani yanayin da zuciyarsa keyi ya kalli
Hamma Umar d'in yace.
"Ko zakayi zurfin ciki ga kowa a duniya ni ban canccanci kayi zurfin ciki a gareni ba."

Kan Usman d'in ya dafa cikin sanyi yace.
"Ba wani abu nawa wanda zan boye maka a duniya,
Abba ne ya hanani in gayawa kowa shiyasa B'iyaye na ka gafar ceni."

Rik'e hannu Hamman nashi yayi cikin happy yace.
"A duniya zanyi fushi da kowa amman banda kai da Ammin mu ina farin ciki in nagan ka cikin
farin ciki."

Murmushi yayi sannan ya kalli kawun nashi cikin sanyi yace.
"Kawun in nayi Aure zan d'auki Ammi na da Usman su koma gidana nima na samu ladan
mahaifiya ta da k'anina."

Kai kawun ya juya mishi alamar a,a sannan yace.
"Banzan hanaka ba Umar amman kaga auren naku kamar auren cushene akayiwa yarinyar nan
dan haka sai kaga ya yana yin zaman naku zai kasan ce."

cikin sauri Ammi tace.
"A duk inda kake kana samun ladana ni kam d'an uwanka kuma ai kaine jigonsa,
nima zan kula da tawa mahaifiyar."

Shiru kawai yayi dan shi kam a ranshi ya kudurta yana son mahaifiyar shi ta kasance kusa
dasu.

Daga nan sukaci gaba da hirarsu,
haka suka wuni cikin farin ciki,
sai dare suka tafi.

A gida kula Ummul tunda matan su Kawun suka kawo kayan auren,
yayin da su Mama matar Daddy da Anty Halima da k'annen Nenne suka tarbi bak'in Ummul ta
shige d'akin Hajjajo ta rink'a wani irin kuka ,

haka ta wuni kuka baci ba sha ta k'aura cewa kowa ta k'aura cewa komai gani take duk ba
masoyan ta bane .

Haka tayi ta kuka har dare,
Anty Halima ce ta shigo tare da Ya Usman cikin takaici tace.
"Ummul kiji tsoron Allah ki tausayawa kanki yanzu wannan kukan maganin me zai miki?."

Kuka ta k'ara sakewa cikin dashewar murya tace.
"Anty kiji yadda Hamma Umar yake harkokin sa shi ko a jikin sa ni aka cusawa bak'in ciki,
na tsani Hamma Umar bana sonshi ko a matsayin d'an uwa bare abokin rayuwa."

Tsaki Anty Halima taja sannan ta juya ta fice tana cewa.
"Tunda bakya jin magana kiyi duk yadda kike so,
Aure ne dai saura kwana 6 nima daga gobe zanzo su Anty Shuwa kuwa suma gobe zasu zo
dan su fara shirya ki."

Tana kaiwa nan ta fice abinta,
ita kuwa Ummul sai hawaye,
Ya Usman ne ya matsota cikin sanyi yace.
"Kiyi hak'uri kibar kukan Ummul kina soyamin zuciya da kukan ki,
Ummul ko so kike zuciyata ta fashe."

Shiru tayi cikin tausaya mishi baki na rawa tace.
"Ya Usman kasha maganin ka."

Murya a raunane yace.
" ko nasha maganin
ba zaiyi aiki ba in har baki bar kukan nan ba."

Cikin tsoron halin da zai iya kasan cewa,
tasa hannun ta share hawaye ta,
murya na tace.

"Nayi shiru ya Usman."

"Toh" yace sannan ya kamo hannun ta suka fito parlour abinci ya bata ta d'an ci .

Haka abu yake tafiya ba mai iya lallashin Ummul sai Usman kuma ba wanda take saurarawa sai
shi bata cin abinci Sai in ya Usman d'in nata ne matsamata bata shiri da kowa sai shi shiko
Usman shi kad'ai yasan cikin halin da yake rayuwa yana boye sirrinshi a zuciyar shi,
abinda bamu saniba shin zuciyar Usman zata iya jurewa kuwa? .

Yau talata tun da sassafe gidan su yake cike tib da bak'in haka yasa Ummul ta takure kanta

cikin d'akin Hajjajo akan gadon ta mai rumfa,
ko k'awayen ta tak'i su ganta,
tana konce a hankali taji k'amshin turaren Hamma Umar d'in a take taji wani irin tsanarsa na
ratsata,
shi kuwa kai tsaye bak'in gadon ya nufa yana zuwa ya tura hannu shi a k'asan.....


By
*GARKUWAR FULANI*
*RUBUTACCEN AL,AMARI*

page 1⃣1⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*








*Zan abbato mutanen sokkoto su y'an kwaraine basu da tsoggoma idan kaje ka sanya fad'a
musu zasu rik'eka da kyau harda lallamah k'warai-k'warai na gane duniya mai sonka shike yi
maka hiddima masoya na na sokkoto kun gaman gata gaisheku �nakeyi domin
kuke raba gardama sokkotawa ina al'fahari daku domin baku da hassada a zuk'atan ku
shiyasa na sadaukar da wannan shafi gareku sokkotawa*











*Ha*nnushi ya tura kasan pillow dake gefen ta da niyar zai jawo laptop d'in shi daya bari a
wurin,
lalubawa yakeyi aman baiji inda laptop d'in yakeba dan d'akin yana da duhu gashi kan gadone
mai rumfa duk yasha gyara da shimfid'a da labulaye sai ya k'ara duhun,

Ita kuwa Ummul tana ganin shi dan ita ta dad'e a d'akin so duhun yabi idonta shi kuma yanzu ya
shigo d'akin shiyasa yake ganin duhun sosai,
tab'e fuska tayi cikin ko in kula tasa hannu ta turo laptop d'in nashi k'asa dai-dai sautin kan
yatsunshi ta turo shi,
shi ko da sauri ya sunkuya da nufin yasa hannu ya taro laptop d'in kar ya kai k'asa gudun karta
lalace,
amman ina cikin rashin sa'a ta fad'o kan yatsunshi tsinin aggil d'in jikin marfinta ya caki kan
farcen babbar yatsarsa,
cakar da a take farcen ya tsage lokaci d'aya jini ya fara zuba a take k'afar ta fara wani irin b'ari
dan azabar daya ratsashi gaba d'aya yatsar kuma sai motsi take kamar zata fice a jikin shi,
cikin wani irin azaba dayaji ya ziyarci k'ahon zuciyarshi ya dafe kanshi da k'arfi hannun shi sai
rawa suke gaba d'aya jijiyoyin kanshi suka taso ida nunshi sukayi jazir ya kasa magana sai
harshen shi ya d'an zaro ya rink'a d'an kad'awa yana furza numfashi tuni zufa ta keto mai ta
sashoshin jikin sa, harshen yake d'an kad'awa yana fidda sautin.
"Shihhhhhhhh ahhhhshhhhhh."
Sai kuma k'afar tashi daya d'an d'ago yana yarfawa,
Ita kuwa Ummul sai murmushi mugunta ta rink'a yi tanaji dariya nason kufce mata murmushin
takeyi tuk'uru cikin jin dad'in azabtar dashi da tayi sai wani kad'a kai takeyi tana magana a
ranta.
"Kad'an ma kaji Hamma Umar wannan shine makullin wahalar da zakasha a hannun na,
kaida azabtuwa kun kullah,
Sai kayi kuka cur-cur da hawaye ka sai ka gommace kid'i da karatu sai ka sakeni saki mafi muni
wanda zan haramta maka har sai inna nasake wani auren an sakeni."

Kai ta jinjina taci gaba da maganar zuciyar da bata saniba na yanzun ya fito fili cewa take.
"Tabbacin da nake dashi ko ince yak'ini na sani Mustapha bazai sakeni ba har Abadan zamu
rayu tare."

Da sauri Hamma Umar d'in ya bud'e idanun shi daya rumtse jin sautin Ummul d'in kan gadon ya
tsurawa ido cikin wore idanun shi ,
fuskar ta ya tsare da ido cikin zafin nama ya mik'a hannushi kan gadon,
ita kuwa ganin haka tayi wani irin dira daga kan gadon a guje tayi woje a parlour ta samu ya
Usman da su Hajjajo da Inna tare da Anty Halima da Anty Shuwa k'anwar Nenne,
cikin rawan jiki ta koma gefen ya Usman ta zauna cikin tura baki da tsuke fuska,
Anty Halima ce ta kalleta cikin tuhuma tace.
"Me kika aikata? kika fito a guje haka?."
fuska ta k'ara tsukewa sannan ta kalli Anty Shuwa dake ta danna mata harara cikin son yin kuka
tace.
"Nayi ai ban sani bane."
Hajjajo ta bud'e baki zatayi magana kenan sai kuma tayi shiru ganin Hamma Umar d'in d'aya
fito cikin d'akin nata ,
tafiya yake yana d'ingisa k'afar tashi duk inda ya taka sai jini dake zuba gaba d'aya jijiyoyin

kanshi sun taso kanshi a k'asa yake tafiya hannushi rik'e da laptop d'in nashi yayinda d'aya
hannun kuma yake rik'e da iPhone d'in shi,
Ya Usman ne da Anty Halima sukayi kanshi da sauri cikin rawan baki Ya Usman yace.
"Hamma Umar me ya fasama yatsa yaushe ya fashe kalli yadda jiki ke zubafa."
Anty Halima kuwa gaba d'aya jikin ta rawa yake ganin duk jini ya wonke mai k'afarsa cikin sanyi
murya na rawa tace
"Hamma Umar a tsaida jinin nan mana ya dena zuba."

kai ya gyad'a musu cikin jarumta da dauriya ya nufi hanyar fita yana ce musu .
"Ba komai fa."
har yake bak'in k'ofar fita,
Hajjajo da Inna sukayi kanshi da sauri cikin kula da tsananin k'aunar jikan nasu suka kalleshi,
kusan a tare suke magana.
"Kai Farouq me ya fasama k'afar?
kayi magana kayi shiru ?."
kai ya jinjina a hankali yace.
"Tuntub'e nayi."
fad'in haka da yayi ne yasa suka rink'a jeromai "sannu-sannu Amman kaji azaba kam ai abinda
ya fasa farce ba k'ara min abu bane."

Su tsoppin sun yarda Amman Anty Halima da Anty Shuwa kam sun gane sarai Ummul ce taji
mai ciwon dan ganin yadda take zare ido da alamun rashin gaskiya Ita,
kuwa Ummul har cikin ranta take jin dad'in ciwon da taji mishi,
a wani sashin zuciyar ta kuwa tana mamakin yadda Hamma Umar d'in ya rufa mata asiri yak'i
cewa Ita ta fasa mishi k'afar,
dan ta tabbaya d'aya fad'a Ita kuwa da ta shiga 9 nema ba 3 ba.

shi kuwa Hamma Umar ko inda take bai kallah ba ya fice yana d'ingisa k'afar,
ya Usman kuwa karb'a laptop d'in Hamman nashi yayi ya rik'e cikin raunin fuskar sa kamar zaiyi
kuka dan tausayawa d'an uwan nashi,
har zasu fita ya juyo ya kalli Ummul d'in cikin raunin da yanayin tuhuma dan ya gane itace silar
ciwon Hamman nashi,
itama kallon shi takeyi cikin sanyi ta rumtse idonta,
shi kuwa juyawa sukayi suka tafi.

Suna zuwa part d'in su Hamm Umar d'in yayiwa yatsar tashi dressing sannan yawa kanshi
allurar ya kuma sha magani.

Ita kuwa Ummul suna fita Anty Shuwa da Anty Halima suka jata d'akin dake gefen na Hajjajo
suka rink'a yi mata gyare-gyare tare da tsumata da irin tsumukansu na shuwa'arab ,
Anty Shuwa ce ta b'alle marfin wani roba sannan ta jijjiga tare da mik'ewa Ummul d'in cikin
tsuke fuska tace.
"Karb'a ki shanye yanzu ki bani robar."

Kai Ummul d'in ta karya cikin kuka da gajiya da d'ure-d'uren da suke mata tace.
"Ni dai amai nakeji dan Allah a barni hakanan."

A fad'ace Anty Shuwa tace .
"Sai kinsha muguwar banza yadda kike mishi mugunta haka zai rama kiji tsoron mutumin da
baya magana inya tashi ramawa zaki yabbawa aya zakinta."
kai Halima ta jinjina sannan tace .
"Gaya mata dai Anty wallahi wata rana zakiyi nadama abinda kikewa Hamma Umar d'in."

Haka suka rink'a yi mata fad'a da nasiha sunayi suna tsumata tare da dilketa da murjeta.

Haka nan kullum Sai sun murjeta sun tsumata,
ta fito tayi rasa sai wani shek'i take tamkar tarwad'a fatar jikinta kuma tamkar auduga komai
nata yasha gyara sai wani k'amshin mai sanyi take fiddawa ko wucewa tayi k'amshin ta sai ya
ratsa wurin
gashin kanta kuwa ba'a maganar gyaran d'aya sha, an gyareshi gyara na mussamman k'afafun
ta da hannayen ta kuwa an musu zanen Lalle na mu samman komai na Ummul ya fito rasa ta
fito a shuwa'arab d'in sak.


A gefen ago Hamma Umar kuwa ,
komai Ya Usman ne yake gudanarwa gaba d'aya ya gayyato abokon Hamma Umar d'in nashi ...

Yau ta kama Jumma haji babbar rana Wanda ya kasance gobe asabar ne za'ayi d'aurin aure
Ummul da Hamma Umar .

Toh a rayuwar shuwa'arab akwai wata al'adar da sukeyi a duk lokacin da zasuyi bikin su ,
suna yin wannan al'adar tasune kamar gone za'a d'aura aure ,
kuma wannan al'adar tasu tana kunshe da wata al'adar kuwa Wanda a halin gaskiya a yanzu
haka gaba d'aya shuwa'arab sunbar yin wannan al'adar ta biyun na farin dai sunyi Amman na
biyun kam ,
a shuwa'arab d'in ma na zamanin yanzu da yawa basuma san al'adar ba dan tuni anbar yin
al'adar duk da dai a zamanin da d'in ma a cikin aggwaye 100 da wuya a samu aggwaye 5 masu
yin wannan al'adar domain al'adace mai nuni da d'auka alk'awari da kuma rik'o da amana suna
kiran al'adar da sunan *Nad'in uwar gida*
So shiyasa aggwayen yanzu basa wannan al'adar ta biyun kenan fa,
Amman na farin kam har yanzu shuwa'arab sunyi kuma in an gama na farinne akeyin na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login