Showing 87001 words to 90000 words out of 142577 words
Chapter 30 - WANI SALO BOOK COMPLETED by Sa'adatu Alkali D-Tsafe.txt
da k'arfi ta
zazzaro ido tana waige-waige kamar me neman wani abu,
dakyar ya Usman ya kamo kanta da hannu biyu ya kwantar da ita a kan cinyar shi dan
yadda take fisge-fisge Ammi bazata iya control enta ba,
ita kuwa Ammin sai shafa bayanta takeyi a hankali kwalla cike a idon ta tana furta,
"hasbunallahu wa ni'imal wakil".
Shiko ya Usman yana ruggume da ita a jikin shi gaba d'aya jikin nashi sai kerma yake a karo na
forko da yaji rauni da tausayin kanshi da kanshi ga taussyin halin rayuwar da Ummul ke ciki a
zahiri yasan kuka rahama ne in dai da k'una a zuci amman shi kuka ya k'aura cewa rayuwarsa
tunda Hamma enshi ya bar duniya baya gane halin rayuwar da yake ciki dazaran k'unan rai da
k'uncin rayuwar sun tokare mai zuciya sai yayi ta aman jini yana murza kai da k'irji inko dere
yayi sai ya tashi ya kwana nafilfili da nemawa d'an uwanshi rahamar Allah a hakan ne Adam ya
gano wani abu daya shiga rayuwar Usman da zaran ya kad'aice sai ya rink'a juya kai yana
mirgina kan nashi kan kafad'un shi kamar yadda yayi tayi lokacin daya zauna gaban gawar
Hamma Umar abin a hankali ya zamewa Usman wani narkarwa ciwo mai zafi a ranshi da
rayuwarshi da zaran ya tuno yadda yaga gawar d'an uwanshi sai kawai yayi ta juya kai jiki na
rawa hakan yasa yanzu da zaran hankalin shi ya tashi ko ranshi ya baci sai ya rink'a wannan
abun,
so yanzuma da Ummul take ta fisge-fisge da gurnani yana ruggume da ita duk da ba wanda
yake gane me take fad'a hakan yasa sai ya rink'a juya kai yana murza k'afafunshi dan zafin da
zuciyarshi ke mishi,
ita kuwa Ummul sai gurnanin takeyi Ammi kuwa duk sai zuciyarta ta d'anyace ta tasasu a gaba
ta kife kanta tana kuka mai cike da dafi a zuciya,
Ya Adam ne ya k'araso cikin d'akin da sauri ya d'ago Ya Usman wanda ya kife kai a
kan bakin gado yana jan numfashi da a wahalce,
Abba da yanzu ya iso da su Nenne da Hajjajo da su ya Sadik sai Aliyu suka shigo saboda jiyo
k'arar da Ummul tayine,
cikin karfin hali Abba yace,
"Adam, d'aukemin Usman daga nan".
Usman najin haka cikin rawar murya da juya kai ya fara magana,
"Abba ku kyaleni dan Allah kubarni inkula da amanar d'an uwana ku barni in kula da
amanar da Hamma na ya barmin".
sai kuma yasa hannu biyu ya rik'e kanshi yana juya kan a wahale yana k'ollah murya na
rawa yace,
"Nanne ina zankai Ummul ? mezan mata ta sami sauki? Ammi ina soro kar d'an d'an
uwana ya cutu ya zanyi na kare mutunci da lafiyar Iyalan Hamma na?".
sai kuma ya kife kai ya saki wani irin kuka mai k'arya zuciyar mai sauraro kuka yake har
numfashin sa na cizga duk jikin shi sai b'ari yakeyi tamkar mazari,
Aliyu ne ya dafa kafad'ar shi cikin matsanancin kuka yace, "ya Usman tashi muje muyi
nafila muroka mata sauki,
Hamma Umar yace min duk damuwa tanada magani a gun Allah, kutashi muyi musu
addu'a zata samu sauk'i kullum Hamma Umar nace min Aliyu duk tsanani yana tare da sauki,
nasha in sameshi yana kuka in nace mishi Hamma Umar me yasa ka kuka? sai yace min Aliyu
Usman baida lfy ina kukane wa ubangijina ina nemawa Usman lafiya a gun mai bada lafiyar,
dan haka muma muje mu nemawa Ummul lafiya a gun mahaliccinmu".
Yana kaiwa nan yaja hannun ya Usman suka fice suka nufi part insu al'wala sukayi
sannan su fara nafilfili tare da karatun qura'an,
haka kowa na gidan yai alwala suka dukufa nemawa Ummul sauki gurin Allah,
Ammi kuwa na rungume da Ummul tana shafa bayanta a hankali tana tofa mata
addu'o 'i har tasami bacci wanda takan razana duk mintina kad'an.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya cikin rashin wal-wala da kuncin zuciya yayinda
kowanne ke buya yayi kuka san ranshi daga Abba, Hajjajo, Nanne, Adam, Sadiq, Aliyu,
wanda b'angaren Ya Usman kuwa abun sai rahamar Allah kullum yana cikin aman jini ba
k'ak'k'autawa kuma yanzu ya samu sauk'i yana iya kuka hakan yasa da zaran ya fara kuka
kuma sai tari sai aman,
Ammi kuwa tamik'a lamuran ga Allah tadage wajen kula da Ummul wadda tazamo
tamkar mutum mutumi duk da ansami cigaba a yanayin ta takan d'an sha tea duk da
sai Ammi tasha rarrashi wonka kuwa sai Usman ya zauna gabanta yayi ta lallashi wani
lokacin ya kife kai yayi ta kuka kafin ta yarda Nenne ko Ammi su mata wonka abu kamar wasa a
zahiri Ummul ta zama tamkar zaucecciya komai sai an sata kuma tun randa Hamma Umar ya
rasu har yau Ummul Allah bai bata bakin manana ba kullum kuma in dere yayi toh tashin
hankali ya tashi kab zuriyar tasu basu da konciyar hankali da zaran an shiga za'a konta sai
Ummul tayi ta firgice-firgice tana razana tana son guduwa sai ta rink'a b'uya ko tana k'ok'arin
shiga duk inda taga luggu,
Usman kuwa haka zai zauna yayi ta kuka yana ga ya kasa tallafawa iyalan d'an uwan nashi a
haka ciwon zuciyarshi ya tashi.
Yau Jumma'a da yamma,
ya Usman ne zaune gefan Nanne ya Adam yana tsaye Aliyu kuwa yana durk'ushe gaban
Ummul sai kuka yakeyi duk sun zubawa Ammi da take bawa Ummul ruwan zam-zam da
aka tofawa addu'oi wanda yanzu shine ruwan shanta,
domin samun sauki da sassaucin kuncin zuciya,
d'an ture hannun Ammi tayi sai kuma ta rink'a binsu da kallo d'aya bayan d'aya kai ta
sunkuyar tana kallon k'aton cikin ta da d'an yaketa wintsil-wuntsul a hankali ta mik'awa Aliyu
dake zaune yasata gaba yana kuka,
hannu alamar ya d'agata da sauri fuskarshi cike da mamaki yace,
"In d'agaki?".
dakai tamai alamar eh, aiko cikin jin dadi yamike yasa hannu ya d'agota ta mike
sannan yasa hannu yana gyara mata d'aurin zaninta yana mai zubda k'ollah,
Ya Usman kuwa cikin saurin ya je bayanta ganin tana tangad'i kamar zata fad'i,
cikin k'arfin hali tafara takawa wanda hakan yasa dukkansu dake d'akin jin dadi kasan
cewar tun dawowarsu basuga hakan daga garetaba,
a hankali suke tafiya Aliyu na rik'e da hannunta har suka fita daga d'akin,
da hannu taiwa Aliyu nuni da hanyar inda Hamma Umar ke zama dan duba marasa
lafiya dake zuwa gida,
haka sukaita tafiya sanayi a hankali har suka isa gurin,
d'an juyowa tayi ta yafito ya Sadiq da suketa binsu a baya tunda suka fito ta nunamai
carpet dake jingine agun da hannun ta,
shiko jiki na rawa yace, "in shimfid'a?".
Kai ta kad'a, aiko ya shimfida nan da nan, kwace hannunta tayi dagana Aliyu ta juya
kamar tana neman wani abu, Ya Usman dake tsaye a bayanta kamar body guard' yace,
"me kike so?".
itako Ummul Ammi ta nuna da hannu takuma nuna mata carpet da aka shimfid'a,
cikin sanyin jiki Ammi ta zauna kan carpet d'in, Ummul tasa hannu ta rik'o hannun Aliyu
shiko yasa daya hannun yakuma rik'ota ya taimaka mata ta zauna sannan ta matsa
kad'an ta jingina bayanta da jikin Ammi, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta lumshe ido
sannan ta kalli Ya Usman daya zuba mata ido tamai nuni da ya zauna. zama yayi sannan taiwa Ya sadiq nuni shima ya zauna, ta kalli Aliyu tamai alama da
hannunta daya yazo yazauna kusa da ita haka taiwa kowa nuni suka zauna harda
Hajjajo,
Ya Adam yasa tafin hannunsa ya goge hawayansa a dai dai lokacin da Ummul taimai
nuni daya zauna shima,
Haka suka zauna agun itako Ummul tanata kallon su da dai-dai kamar bata tab'a
ganin suba saida aka kira magrib sannan suka koma cikin gida.
Kwanci tashi cikin Ummul ya isa haihuwa dan haka aka shirya komawa kasar egypt da
taimakon adalin gwamnan gwamnoni, gwamna daya d'au rayuwar talakawan jahar shi
da muhimmanci gwamnan jahar yobe.
Anyi tafiyar ne da Ammi, Abba da ya Usman sabida yanada buk'atar ganin likita akan
yawan aman jinin da yake kowane lokaci, isar su da kwanaki uku
aka gama bincike kan zuciyar Usman inda cikin ikon Allah doctor ya shaida musu za'a cire
na'urar dake tallafa zuciyar Usman domin sanadin wani tsoro da tsinkewar zuciya daya samu
yasa zuciyar ta harba cikin tsoron to daga nan yanzu ita da kanta take aikin harba jinin kuma in
anbar na'urar zata iya maida zuciyar ta cushe dan haka cirewa za'ayi, abin ba k'aramin Al'ajabi ya bawa Ammi da Abba da Adam ba haka Abba da Ammi suka sa'a
hannun,
ita kuwa Ummul bayan magun guna da allurai da likitoci keta bata ne akai shirin shiga
yimata aiki saboda babu halin haihuwa dakanta sakamakon sanyin da zuciyar ta tayi
dan bugun zuciyarta tayi k'asa sosai haka yasa rana d'aya za'ayiwa Usman da Ummul aiki
Abba kam da Ammi da Adam sai Addu'oi sukeyi Abba ya kira Daddy da Uncle dinsu Usman da
sukaje saudi ya shaida musu su tayasu da Addu'a.
K'arfe 8:00 dai-dai babban likitan da zai jagoranci aikin yakira Abba da Adam a office
din shi,
bayan yad'anyi rubuce rubucen shi ya d'ago kanshi ya sauke farin glass dinshi kasan
hancin shi yace,
"Alh Hassan, zamu shiga aiki da yaranka muna kuma bukatar addu'ar ku kasancewar ita
yarinyar aiki zamu me cike da hatsari domin kuwa bamuda tabbacin zuciyarta zata tsaya
yanda muke bukata har mu gama aikin".
Abba yai ajiyar zuciya yace,
"to Allah ya bada sa'a". Likitan ya mik'o musu form da zasu saka hannu dan yin aikin,
Abba yasa hannu ya janyo takardar ya juya ya kalli Adam da ya sunkuyar da kai k'asa
ya dafa kafad'ar shi yace,
"Adamu kadaure kasa hannu aima k'anwarka aiki ni zansa hannu akan aikin Usman".
a razane ya Adam ya d'ago yana kallon Abba da takardar,
a hankali Abba yasake d'agamai kai da lumshe ido cikin sanyi Adam yasa hannu ya janyo
takardar yad'auki biron sannan ya d'ago kai ya kalli likitan daya zubamai ido yana
kallonshi, cikin tausayawa likitan yace, "Insha Allah zamuyi aiki cikin nasara".
shi kam Adam ido cike da k'ollah yasa hannu tsoro tab zuciyarshi yana jin tausayin Usman a
ranshi yana jin tsoron kar wani abu ya faru da su kuma a zuriyar tasu,
hannu na rawa Adam yasa hannu a takardar yana zubar da kwallah, likitan yasa hannu
yaja takardar yace, "good, be prayerful".
da haka yatashi yafita sukabi bayanshi jiki ba kwari, karfe 9:00 dai-dai aka shiga da
Ummul d'akin tiyata ya Usman kuwa aka shiga dashi d'akin dashen zuciya,
akabar Abba da Ammi ,
tsaye suna karanto kowacce irin addu a da suka iya zuk'atan su cike da zulumi.
Har k'arfe 11:30 suna ta zirga-zirga bawanda yake magana kowanne da irin tuna ninda
yake a ranshi, bude k'ofar dakin da akema Ummul aiki ya tattaro hankalinsu, ya Adam
ya dafe kirjin shi da hannu yabi bayan likitan daya wucesu yanufi office d'inshi,
a lokacin kuma aka fito da ya Usman shi an gama aikin nashi,
Adam kuwa a office d'in doctor saida ya zauna a kujerar shi sannan yad'anyi murmushi
yace,
"congratulation". Allah yayi ikon shi da taimakon y'an uwana likitoci anciro baby boy,
yaro yana cikin koshin lafiya sannan insha Allah itama zata farka babu wata matsala".
cikin jin sauk'in razanar Adam ya dago rinannun idanunshi dasukai jawur yace,
"Alhamdullah Masha Allah".
Sanna ya mike ya fito ya nufi d'akin da yaga Abban na shiga wanda ya haggo ana shigar da
Usman,
suna shiga kuma sai ga ita Ummul an shigo da ita haka aka kontar dasu d'aki d'aya gadon
Usman na gefen na Ummul Ammi kuwa waje ta fita ruggume da yaron tana kukan abubuwa da
dama kukan tuno d'anta kukan fargabar halin da Ummul da Usman ke ciki kukan tausayin yaro
maraya tun yana ciki an kashe mai uba haka tayita kuka gwanin ban tausayi.
Bayan awanni shida Ummul na kwance kan gadon hutu na asibitin, shiko Usman
yana kwance kan d'ayan