Showing 84001 words to 87000 words out of 142577 words
Chapter 29 - WANI SALO BOOK COMPLETED by Sa'adatu Alkali D-Tsafe.txt
abu mara dadi ya samu dayanmu kamar ya samemu ne baki d'aya kamar yadda
mutuwar Hamma Umar ta ratsa zuk'atanmu baki d'aya nida kaina Aysha ban san adadin
addu'oin da bawan Allah nan ya samuba a cikin kwana biyun nan fatana Allah ya amsa
addu'oinku gareshi Usman Ammi da Ummul suna godiya a gareku Ummul kuma tana neman
addu'arku dan tun shekaran jiya bata da lafiya saka makon abun da ya zame mata sabo Ummu
na Allah ya baki lfyν Ύν΄ν ½νΈ*
*Abu na biyu ina baiwa masoya na hak'uri daga jiya da daddare zasuga suna magana bana
amsa musu to na canza number ne sakamon yawan da Jama,a sukamin duk ta inda na lek'a
kafafen yanar gizo-gizo sai naga sak'on ni bila adadin hakan yasa dole na canza number dan
samun sauk'i toh dan Allah duk wacce taga tayi mgn ba amsa toh na canza number ne ngd
matuka Allah bar zumunci da k'auna sisters bada ku na gajiba da bada amsa na gaji amman ku
kam ana mugun tare domin kun zamani na zamma ku na godewa Allah daya bani ku masoyana
tabbas jama'a rahamace Allah ne yamin wannan rahamar kuma ngdwa Allah na Alhamdulillah*
*Y*a rink'a juya kai yana b'ari kar-kar kamar mai farfad'iya wani irin zufa ya keto mai daga
tsakiyar kanshi har kan d'an babbar yatsar k'afarshi hatta cikin gashin kanshi sai d'igowa yake
tol-tol,
Hajjajo kuwa wacce tun ihun da Aliyu yayi ta fito amman ganin Abba a sume Aliyu a sume ga
Ummul jiki duk jini,
a take sai jijiyoyin ta suka sassake k'afafun ta suka kasa rik'e ta jiri ya rufeta cikin tashin hankali
ta fad'i k'asa dirsham hawaye na bin fuskarta ta kasa tashi sai yanzu ta mik'e da kyar ganin
halin da Usman ya shiga,
tana xuwa ta kamo hannun shi tana k'ok'arin zaunar dashi amman ina sai taji jikin shi kamar an
dasashi ganin haka cikin muryar kuka tace,
"Usmanu! Usmanu! Usmanu ! ka ambaci Allah shi zai kawo mana agaji Usmanu kar kabar
zuciyarka ta mance da Allah Usmanu wannan shine jarrabawarmu a wannan shekara a wannan
wata a wannan rana muyi rashi mai girma ban sani ba waya kashe mana Umar".
sai kuma ta k'ara rik'o hannun Usman d'in sannan cikin kuka ta kalli Adam dake yayyafawa
Abba da Aliyu ruwa,
a firgice Aliyu ya farfad'o cikin k'ara tare da rarumo Sadik dake gefen shi,
karan da Aliyu yayi ne yayi dai-dai da farfad'owar Abba a razane ya mik'e dai-dai lokacin kuma
sojojin dake harabar gidan suka shigo dan jin k'aran da Aliyu keyi,
suna shiga Usman suka kama suka rik'e sabida ganin yadda yake tsaye,
zau nar dashi suke k'ok'arin ya,
cikin hard'ewar harce ya janye hannayen shi gaban Abba yaje ya tsaya hannun Abba ya kamo
ya rik'e harce a nad'e maganarsa bata fita sosai kuma yadda bugun zuciyarshi tayi k'asa haka
muryarshi numfashi a cushe ya nuna Ummul dake zaune ta zama mutum mutumi sai ida nun ta
da sukayi jazir tamkar rushi sai lips nata da suka kumbura, a hankali yace,
"A..! Ab...! Abb!...
Abba wai jinin Hamma nane a jikin Ummul Abba kace ta gaya ma inda ta barmin d'an uwana
Abba kalli matar nan wai cewa take d'an Uwana ya resu Abba wai Hamma fa suke cewa ya
rasu".
kife kai Abba yayi tamkar yaro ya rink'a kuka yana durk'ushe a gaban mahaifiyarshi,
Aliyu kuwa kuka yakeyi da shid'ewa Nenne ma kuka takeyi da tsananin k'una ya Sadik kuwa
kanshi ya rink'a murzawa yana kuka cur-cur Adam kuwa ruggumo Usman yayi yana kuka tankar
ranshi zai fita,
Umman Mustapha ma tuni kukan take,
ganin haka sojojin suka kama Abba suma kansu kuka suke dan tausayawa rayuwar wannan
family,
cikin hikima sukayi wa Abba bayani,
suka k'ara da cewa,
"yanzu haka gawarshi tana gidan sarki ya kamata kuje ayi mishi sutura".
Abba jikin shi sai rawa yake cikin kuka yace ,
"Mu tafi".
juyawa sukayi har zasu fita Adam yaga yadda Usman yake tafiya numbfashin sa na yankewa
ganin haka ya kamoshi da sauri a cikin kuka yace,
"Usman ka zauna a gida Abba kace Usman karya je".
Abba ya bud'i baki zaiyi Magna kenan Usman d'in ya d'ago ida nunshi da suka koma tamkar
zasuyi aman wuta murya a nad'e yace,
"Gun Hamma na kuke cewa kar naje idan banje gunshi ba ina zan shiga a duniyar nan wai yau
ni kuke cewa kar naje gun d'an Uwana idan banjeba me zanyi".
daga jin Maganar Usman an san baya hayyacin sa,
haka yasa Adam ya rik'eshi suka shiga motocin sannan sojojin suyi gaba suko suka bisu a baya
dan an hana zirga-zirga a garin suma dan da sojojin ne,
Mustapha kuwa kai tsaye gida su Ammi ya nufa dan yasan gidan sun tab'a zuwa shida Hamma
Umar d'in.
Ammi kuwa tunda garin wannan ranar ya waye ta kasa yin komai gaba d'aya jikin ta a mace
yake,
a haka ta jawo radio ta kunna wanda yayi dai-dai da saka harbe-harben da yan BH sukayi a
garin na damaturu sannan mai bayanin yaci gaba da fad'in uguwannin da suka fara shiga da
kuma irin b'arnanr da sukayi,
jin an kira uguwarsu Hamma Umar ba k'aramin tashin hankali da firgici ya sawa Ammi ba a take
taji wani irin sanyi yana ratsata har cikin hanjin cikinta tsoro mai tsanani ya rufeta ido cike da
k'ollah tib ta kalli mahaigiyarta cikin muryar kuka tace,
"Inna ta uguwar su Farouq suka fara shiga Inna kinji sunfa kakkashe mutane".
Itama Inna gaba d'aya jikin ta rawa yake cikin hargitsi tace,
"Kira min wayar Umarun kira minshi maza Amina".
jiki na rawa tayi ta kiran Hamma Umar d'in amman tuni abinda Ammi bata saniba an kashe
mata d'anta,
ganin Umar baya d'aga woyar sai kukanta ya k'aru sai kuma ta rink'a kiran Usman ina shima
baya d'agawa hakan yasa hankalin ta ya tashi ta rink'a kiran mutanen gidan Abban amman duk
basa d'agawa haka yasa ta koma ta zauna dirsham kan taburma a gaban Innarta d'in ta zauna
kenan, Mustapha yayi sallama,
shi kuwa Mustapha ganin tana kuka sai yayi zaton taji batun rasuwar Umar d'in sai ya tsuguna
gefenta cikin kuka kamar yaro yace,
"Ammi kiyi hak'uri hak'ik'a munyi rashi mai zafi amman Hamma Umar yafi but'atar addu'armu a
kan kuka Addu'a zakiyi mishin Insha Allah muna zatama mai rahama Allah ya karb'i
shahadarsa".
Ita kam Ammi tunda taga Mustapha jikin ta ya rink'a b'ari kar-kar ta kasa tashi amman jin ya
ambaci Hamma Umar yasa ta mik'e da sauri cikin razani a kid'ime zanin ta ta rink'a d'aurawa
tana kuncewa tana sake d'aurawa sai karkarwa takeyi ganin haka cikin kuka Inna ta kamota ta
rik'e tana cewa, "Innalillahi WA innailaihi rajiun".
haka ta rink'a maimatawa har akayi sa'a itama Ammi cikin kukan daya kufce mata ta rink'a
cewa,
"LA haulawala k'uwta illabillahi aliyul azim hasbunallahuwani'imam wakil Allahu Akbar Allah
Akbar innalillahiwa Inna ilaihirajiun Allah mai girma yau kuma da k'unar dana wayi gari kenan
Mustapha yau kuma Boko Haram sun yanke min naman jikina kenan Mustapha ina Usman
Mustapha Usman yana cikin wanne irin hali?". sai kuma ta kife kanta kan ciyar Innarta ta saki wani irin kuka mai cike da k'unci a zuciya,
itama Inna sai kuka shima Mustapha ya kasa barin kukan,
a haka Uncle ya shigo ya samesu wanda dama Abba ne ya kirashi ya gaya mishi,
abin tausayi shima Uncle sai yasa yar uwarshi a gaba suna kuka tamkar yara Ammi kam kuka
take har numfashin ta na tafiya,
a hakan Uncle ya daukosu ya kawosu gidan Abban sannan shida Mustapha kuma da sauran
abokan Hamma Umar dana ya Usman da abokan Adam Sadik da abokan Abba duk suka
d'ugguma damaturun,
suko Inna da Ammi suka wuce cikin gidan.
A damaturu kuwa suna isa suka samu ana shirin yiwa mamacin wonka suna shiga Usman ya
wuce kai tsaye inda yaga an mik'e gawar a shimfid'e ta a k'asa Adam ma da Abba da Sadik da
Aliyu gaba d'aya sai sukasa gawar a tsakiyan su,
shiko Usman hannu yasa ya d'ago gawar fuskar ya tsurawa ido cikin wani irin yanayi mafi rauni
da muni ya rink'a kallon wuyanshi da aka yanka, ruggume gawar yayi da k'arfi,
a hankali ya rink'a juya kanshi yana wani irin numfashi Adam kuwa kuka yake kukan tausayin
Usman Sadik ma kukan yake Aliyu Kuwa a k'asa ya kife kanshi yana kuka,
Shiko Usman cikin hard'ewar murya da juya kai yace,
"Sun cuceni sun cuci rayuwata sun rabani da mutun mafi soyuwa a gareni ina ma ina wurin in
fanshi ran Hamma na da nawa ran Ammi sun cuceki sun kashe miki lafiyayyen d'anki suka bar
miki ni wanda zama danima larurace".
sai kuma ya kalli Abba cikin wani yanayi da yafi kama da wanda baya hayyacin sa yace,
"Ashe duk hirar da nike da Hamma na watsiyace ashe yana barmin abinda har in mutu bazan
manta bane Abba Adam Sadik Aliyu ko jiya da dere Hamma na yace ince ku gafarceshi fad'an
da yayi a kan Ummul".
sai kuma ya ruggume gawar ya fara magana kamar zai bashi amsa cikin bushewar zuciya yace,
"Hamma na ba jiya nake cema in na mutu zaka zama gatana na ko?".
sai ya kuma kallin fuskar Hamman nashi yace,
"Hamma na ka tuna kace min zaka zama gatana bazaka zubdamin hawaye ba zaka min wonka
kamin sutura sannan zaka dauwama dimun wa da'imun kana min addu'a har sai randa kabar
numfashi,
to Hamma na Insha Allah zanyi maka wannan gatan har zuwa lokacin da nima zan biyo bayan
ka".
sai kuma ya kalli Adam yace,
"Adam taya ni in yiwa Hamma na wonkan k'arshe a duniya".
Adam yana kuka da majina suka kamo gawar suka matso inda aka tanadi abubuwan buk'ata
dan yin wonkan gawar,
Abba kam da Sadik zama sukayi suna ganin duk ta inda aka juya kan Hamma Umar sai yayi
lagwas shiko Aliyu kuwa kuka yake da zafin rabuwa da d'an uwa,
shiko Usman nad'e k'afafun wondonshi yayi cikin bushewar zuciya ya rink'a wonke wuyan nashi
da sauran wuraren da jinin ya taba sannan yayi mishi wonka yadda addinin musulunci ya
tanadar,
bayan sun gama ya shiryashi tsab cikin likkafanin shi aka kawo makara motor da babu taya
motar da ta zame mana dole shigarta bayan an sashi a cikine aka fitar dashi akayi mishi sallah
bisa koyarwar annabi sannan aka d'auki Hamma Umar aka nufi gidanshi na gaskiya da shi,
inda Usman da Adam su suka sashi a makoncin sa,
Allah Akbar ko wanne d'an adam k'arshen sa kenan,
an gama binne shi ne ya Usman ya d'aga hannu yayi ta karanto addu'oi bayan sun gama ne
aka fara juya baya ana tafiya,
a dai-dai lokacin ne Usman yaji wani irin suka da zogi a kahon zuciyarshi wanda ya fara ganin
duniyar tana juya mai,
da kyar yake d'aga k'afafun shi har suka fita cikin mak'abartan suka shishishiga motocin su suka
nufi Potiskum.
A gida kuwa Ammi da Inna suna shiga suka samu Anty Halima da matar Daddy da sauran yan
uwansu duk sun taru suna zaune a barandar Nenne,
Ammi na shiga Nenne ta ruggumota suka had'a kai wuri d'aya suna wani irin kuka,
Halima kuwa da Anty Shuwa gefen Ummul suke zaune wacce tunda tazo batayi magana ba sai
idonta da yake a zazzare,
cikin kuka Halima tace,
"Allah sarki Ammi wayyo ya Usman Ummul tashi ki cire rigar nan Ummu kar kiyi Ammi taga
wannan jinin zai iya kawar mata da hankalin ta".
shiru bata kula Halima ba sai kallon Nenne da Ammi take Hajjajo da Inna ma kuka suke kamar
zasu shid'e,
Ammi kuwa da Nenne sunyi kuka har idanu su sun rufe,
sai can Ammin ta kalli Ummul dake gefensu tana ta zaro ido tamkar idanun zasu firfito,
a hankali Ammin ta kalli Ummul d'in da k'aton cikin ta wanda jikin ta duk Jini,
kife kai tayi ta kuma sakin kuka,
amman Ummul sai kallonta takeyi kamar bata santaba ganin haka cikin kuka Ammin tace,
"Nenne kuka rahama ne kuka wani sauk'ine a garemu kusa min Ummul tayi kuka inba haka ba
zai zauna a zuciyarta ku samin yarinyar nan tayi Kuka Ummul ki zubda k'ollah".
amman ina Ummul Allah bai bata damar kukaba,
har Allah yasa su Abba da Usman dasu Adam Sadik da Aliyu suka dawo,
suna shigo wo gidan Usman yazo ya kife kanshi a jikin Ammin shi yana magagi harce a nad'e
yace,
"Ammi sun kashe miki lafiyayye sun bar miki nakasheshshe wanda rayuwarsa bata da tabbas
Ammi zan kai kararsu".
cikin kuka ta ruggumeshi tace,
"Usman ya zamuyi da *RUBUTACCEN AL, AMARI* wanda Allah ya tsara mana Usman ina
zaka kai kararsu waya gansu".
harce na k'ara nad'ewa yace,
"Allah Ammi Allah ya gansu kuma zan kai k'ararsu gun adalin sarki Allah zan had'asu da Allah
ya bimin hak'kin jinin yan uwana musulmai Allah zaiyi mana hisabi dasu zubarmin da jinin
Hamma na da sukayi Ammi babu kotu ko lauya ko alkali da zaiyi wannan shariyar sai Allah dan
haka zan dawwama ina kai kararsu gun Allah zasuga saka makon aiyu kansu a ranar da
gabbansu zasuyi bayanin rayukan da suka kashe Allah ya isar mana ana cutar damu musulmai
a k'asarnan ana kashemu tankar kiyashi Allah ya isa! Allah ya isa! Allah ya isa jinin d'an
uwana".
gaba d'aya sai gidan ya kuma cika da tasbihai dan samun sanyin zuk'atansu ita kuwa Ummul
sai binsu take da kallo,
Aliyu ne wanda tunda suka shigo yake kuka sai yanzu Sadik ya kamo hannunshi suka k'araso
cikin gidan suna shiga Aliyun ya fad'a jikin Ummul d'in yana kuka mai tarin k'una shi kuwa Sadik
cikin rawan murya yace,
"Ammi mun kai Hamma Umar gidanshi yanzu addu'arki yafi buk'ata".
daga wannan kalmar Ummul bata kuma sanin inda takeba ko a wanne halin takeba,
ta sume cit suma mafi munu domin harda k'ok'olwarta tayi sanyi,
daga nan aka kwasheta akayi asibiti da ita Dr Bashir shike duba lfyar ta,
yayin da Usman Kuwa yake ganin suma hutune a wannan halin da yake ciki ba kuka ba suma
sai tarin k'unan zuciya ga fargabar halin da Ummul take ciki.
Har tsawon kwana uku Ummu bata farfad'o ba hakan yasa yan uwa cikin wani sabon tashin
hankali ganin haka Dr Bashir ya bada shawaran a fiddata woje,
haka kuwa akayi cikin kwanaki aka shirya fita da ita k'ark'ashin d'aukar nauyin gwamnatin jihar
tasu aka fidda ita,
Egypt inda aka kai tsaye suka wuce Magrib Medical Center Cairo,
ita da Ammin Hamma Umar sai ya Adam tare da jagorancin Dr Bashir,
koda suka je Ummul saida tayi kwana 8 a sume sannan ta farfad'o koda ta farfad'o d'in kuma
bata magana sai kallon mutane kawai,
duk bincike anyi da magani amman ba magana a haka aka sallamesu dan doctors sunce a
koda yaushe zata iya magana,
an sallamesu da sharadin watan haihuwar ta na tsayuwa su dawo dan bugun zuciyarta yayi
k'asa sosai bazata iya haihuwa da kantan ba,
a haka suka dawo gida dan hankalin mutanen gida ya konta.
randa Hamma Umar ya cika sati uku da rasuwa a ranar suka dawo,
suna dawowa koma yazo yanawa Ummul magana amman ba amsa,
bata ko d'ago kanta ta kalli kowa sai in Ammi ce tayi magana,
haka gaba d'aya farin cikin su ya koma ciki.
A daren ranar ne bayan duk an shiga an konta Ammi na zaune da Usman a gefen Ummul da ta
konta tana kallon su ba magana,
Usman ne ya kalli Ammin cikin rauni yace,
"Ammi cikin kam baida matsala ko? ".
Ammin ta bud'e baki kenan zatayi magana Ummul tayi wani irin gigitaccen......
*By*
*GARKUWAR FULANI*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 3β£1β£
*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*MOH ALLAH WUJI FURD'ATA*
*DEDDE Na Ummu uwata ta kaina mahaifiyata abin k'aunata abin Al'faharina yau kuma kirarinki
da kikemin na yarintata na tuno lallai bani da tamkarku kida Abba na domin a yau Kirarin da
kikemin zai iya kasan cewa a horkon ko wani shafina na littafaina inada kike cemin*
*KIN KINI KAN KAD'A DAMONI NA DAMONI GID'D'O MO FINA LARA GAID'O MO FINA
SUKOYO LADDE ALLAH YAMAD'UM! KI D'OIDI YALETE! KI B'IB'B'E SAMMMETE! B'ENDUKI
YAMETE! YORIKI TENETE! DAMONI NA DAMONI GID'D'O MO FINA LARAMO GAID'OMO
FINA SUKOYO LADDE ALLAH YAMAD'UM ALLAH WANNE BARKA BOD'D'I DEDDE Allah
fintine ba seto arana*
*wata kalmar sai a bakin Fulani*
*Wani Abu sai Uwa da Uba wannan kirarin duk ni kadai Aisha Aliyu garkuwa mahaifiyata da
mahaifina kemin da sanya min albarka tun ina karama har zuwa yau Ya Allah ka sakawa
iyayena da mafi kyawun sakamako ya Allah ka yiwa iyayena jagoranci har cikin jannatul firdausi
DEDDE NA DA ABBAN ina sonku fiye da kowo har kaina Allah ya barmin kuν ½νΈν ½νΈ*
*T*ayi wani irin firgitaccen zabura cikin tsananin
razana ta yunkura da karfi zata tashi tana wani irin gurnani,
ganin haka cikin karfin hali da firgici Ammi da ya Usman sukai saurin rik'ota suna mata
addu'a,
ita kuwa gaba d'aya jikinta rawa yake kar-kar hatta d'an cikin ta sai motsi yake