Showing 96001 words to 99000 words out of 142577 words
Chapter 33 - WANI SALO BOOK COMPLETED by Sa'adatu Alkali D-Tsafe.txt
da sanyin gwiwa kai tsaye yanufi b'angaren su bedroom ya shige sannan ya
fad'a kan gado yana kuka mai cin rai yana furta,
"yazanyi yazanyi da raina, Allah ka ceceni ka kawomin d'auki Ummul har gobe ina sonki
aurenki ne kad'ai zai bani damar kula da amanar d'an uwana Ummul ina sonki ina son d'ana
Farouq bana son a rebamu".
Shiru yayi dan yaji motsi wanda ya tabbatar mashi da akwai mutum a d'akin da sauri ya
d'ago kai......
*Sadaukarwa GA Dr Umar Ibrahim Umar shuwa (Hamma Umar)*
*By*
*GARKUWAR FULANI*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
page 3β£3β£
*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*MOH ALLAH WUJI FURD'ATA, MOH ALLAH HOKKI B'URI MOH BABA HOKKI*
*Wannan shafi naku ne matan kirki masoyan kirki yan uwa a musulunce SADNAF tare da
SURBAJO tawa ina Al'fahari daku Allah ya sanya alkhairi a rayuwarku da yaranku Allah ya raya
mana yaranmu Yusuf namu ya auri ikram tamu muyi tuwona maina ν Ύν΄ν ½νΈ*
*Y*a d'ago kanshi idanun shi da suka canza kala zuwa jawur ya sauk'e sure akan fuskar
ya Adam,
dayake tsaye ya hard'e hannayen shi a kirjin shi yana kallon shi cikin tuhuma,
sai kuma ya tako a hankali jiki ba kwari yataho ya zauna kusa da shi,
hannun yasa ya dafa kafad'ar shi yazuba mai ido cikin tuhuma da tausayi yace,
"Usman me kake fad'a?".
hannu yasa ya goge k'ollar daketa bin fuskar shi cikin sanyi yace, "bakomai Adam".
"a a Usman kar muyi haka dakai dan Allah, kayi hakuri kad'auke ni matsayin Hamma
Umar abokin shawara, meyasa zaka b'oyemin damuwar ka?
nifa d'an uwanka ne kuma mai k'aunarka please ka fad'amin menene?".
Zame hannu Adam yayi daga jikin shi cikin kauda kai yace,
"Adam nacema bakomai".
ido cike da k'ollah yana gir-giza kai yace,
"naji Usman naji abinda kake fad'a fa,
kayi hakuri kamin bayani mana".
jajayen idanun shi ya zaro cikin gajiya da maganar yace,
"Adam tashi kabar gurin nan tunda nacema ba komai ai ba komai d'in ne".
sai da Adam ya mik'e tsaye sannan yace,
"gaskiya akwai damuwa Usman kadai b'oyemin ne amma hakan bazai sa nabarka cikin
damuwa ba dan haka zanje in fad'ama Abba abinda kunnena yajiye min".
Yana kaiwa nan ya juya yafuce,
shiko Usman ganin haka yabi bayan shi da sauri a palour ya sameshi yana shirin fita,
da sauri ya kamo hannun Adam d'in kan kujere ya jawoshi suka zauna murya can k'asa yace,
Adam please karka gayawa kowa maganar nan".
ido Adam ya rumtse wasu hawaye masu zafi suka zubo a fuskarshi ranshi cike da tausayi
Usman a hankali yace,
"Usman meyasa kake son b'oye min matsalar ka wacce kasan zan iya magan ceta".
shiru yayi cikin lumshe idanun shi murya can k'asa yace,
"Ina son Ummul Adam ina sonta ina son zama da ita da yaro na, bana son b'acin ranta
bana son suyi nesa dani nafi son na renesu da kaina nafi son na kula da jinin Hammana da
kaina bana son Farouq yayi agolanci bana kuma son rabashi da mahaifiyarshi bana son ya taso
kamar yadda nida Hamma na muka taso ba Uba uwar kuma bata kusa damu bana so Farouq
ya tashi a gida na kuma ace ba mahaifiya shi
bace ta reneshi,
kuma bana son b'acin ran Ummul ko abinda zai tayar mata da hankali gashi ta tsani aure
bata son a mata maganar aure sai tayi ta kuka kukanta na sani cikin k'unci sai in rink'a ganin na
gaza samawa iyalen Hammana farin ciki ne bana son b'acin ran ta ina jin ciwon biyu in tana
kuka, Adam kamin alkawarin zaka rik'e min wannan sirrin nawa muyita addu'a har muga
abinda Allah zaiyi mana da ikon shi a hankali farin cikin Ummul zai dawo".
Juyowa Adam yayi cikin kuka ya rungumi d'an uwan nashi suka cigaba da kuka mai
cin rai har zuwa d'an wani lokaci,
a haka sunata kuka babu mai rarrashin wani haka suka gaji suka kai shiru,
a hankali Adam ya kwantar da kanshi akan cinyar Usman d'in murya na rawa yace, "Ya
Usman to haka zamuyi ta zama da wannan damuwar?
har sai yaushe farin cikin mu zai dawo?
shin fushi mukeyi da hukun cin mahaliccin mu kenan?
shin bazamu gane cewa wannan rubutaccen al'amari ne daga Allah ba ko so muke mu raunata
imanin mune haka zamu rayu kullum ba walwala, addu'ar da muke yiwa Hamma itace so mu
daure mu bar kuka,
ka auri Ummul ka reni Farouq da kanka tunda aure dai abin yine tunda da lafiyar ka?".
Cikin sanyi da rauni ido cike da k'ollah,
Usman ya shafa kanshi murya a raunane yace,
"A a Adam bazamu zauna cikin k'unci ba done wata rana zamuyi farin ciki ai ya rigada Allah
ya sama bayinshi mantuwa a ransu ba dan mantuwar da Allah ya sa mana ba da ciwon
mutuwar wani zai jawo na wani ba dan danganar da Allah ya samin ba da ciwon mutuwar
Hammana ya kasheni Adam kalli rubutaccen al'amari yau ni Usman mai hujejjiyar zuciya ina
raye nida kowa ke zatawa mutuwa amman bata d'aukeni ba sai ta d'auke Hamma na wanda
ba'a tuna maiba kuma ta hanyar da ba zato ba tsammani,
Adam zamuyi ta addu a Allah zai mana maganin damuwar mu nagode naji dadi da
samun d'an uwa mai rik'emin sirrina". Murmushi k'arfin hali Adam yayi sannan ya tashi
yakoma bedroom ya fad'a bandaki ya sakarma kanshi ruwa,
shiko Usman tashi yayi ya d'auko qura'an ya fara karatu cikin rauni da halarto da kushi'i tun
yana yi yana zubda k'ollah har yaji zuciyar shi ta fara sanyi a hankali yaji k'unshin ranshi na
gushewa,
Qura'ani kenan mai girma maganin hawan jini maganin ciwon suga maganin jutar daji maganin
Iblis da junnu da mugun bani Adam duk tsanani sauk'in shi nan cikin qura'ani sai dai in mutum
bai lizamceshi ba.
A parlour bak'in Kuwa Mustapha yanata aikin rarrashi a hankali ya taso yamatso kuda da
kujerar da Ummul ke zaune ya zama yayi a gaban ta ya tonk'oshe k'afafun shi a cikin sanyin
murya da tausasawa yace,
"Ummul narok'eki kiyi hakuri kiji tausayi na ki sassautawa zuciyarki Khairi na kinfi kowa
sanin yanda nake jinki a zuciya ta kukan ki yana k'onamin zuciya, kiyi hakuri kibani
dama indawo miki da farin cikin ki Ummul ina sonki wallahi ina miki son da bana yiwa
kaina Ummul rayuwa ta zata cikane kawai idan ina tare dake". Yanda yaga Ummul ta d'ago kanta cikin razana ta zuba mai manyan idanuwan ta da
suka canza kala zuwa jawur yasa yai shiru ya zuba mata nashi idanun.
Kalmar da Ummul taso fad'amai ta "bana sonka". ce ta kasa fito sakama kon tunawa da
tayi da yanda taita furtawa Hamman ta kalmar wadda gashi yanzu tazamo mata sana
diyyar b'acewar farin cikin ta a yanzu wanda bata tab'a yin nadamar wani abu a duniya kamar
shiba, wani irin abune yataso mata ya tokare mata zuciya dakyar ta samu ta fisgo wani irin
nannauyan ajin zuciya wanda ya fito da kuka mai k'una da zafi,
ido a rufe ta rab'a gefen Mustapha da sassarfa tayi cikin gida,
shiko Mustapha binta yayi da kallo harta fita sannan ya juya jiki babu k'arfi ya koma
yad'auki Umar Faruq daketa wasanshi ya rungume yanajin wani irin so da kaunar yaron
da mahaifiyar shi Ummul a ranshi sannan ya fito,
Ita kuwa Ummul da gudu tafad'a cinyar Ammi tasaki kuka mai k'arfi jikinta duk na
rawa,
a gigece Ammi take tabbayar ta,
"menene Mama na kiyi hakuri ki fad'amin mana meke faruwa?".
Aliyu daya biyo bayanta ya zuba gwiwa a k'asa shima hawaye na bin fuskarsa ganin yadda
Ummul ke wani irin kuka kamar ranta zai fita ko ina jikinta rawa yake,
Nanne da ya sadiq suma da gudun suka shugo,
Nanne ma tuni jikinta yad'au rawa zuciyar ta na bugawa ganin yadda Ummul tafita
hayyacin ta dan kuka,
ya Sadiq d'in ne ya matsota ya dago kafad'arta ya janyota jikin shi,
aiko shima tuni zuciyar shi tayi rauni dan jin zafin jikinta da yanda jikinta ke rawa
cikin sassauta murya yace,
"Ummu na meya sameki ne?".
K'ara tusa kanta tayi a cikin cinyoyinta ta k'ara sakin kuka mai k'arfi,
Su Usman kuwa sai yanzu suka fito shi da Adam zasu shige part d'in Nanne,
a farfajiyar gidan sukaci karo da Mustapha wanda ke rik'e da Umar Farouq,
aiko yana ganin Abban shi Usman ya mik'o hannu shima Usman da murmushi yakai
hannu ya karb'e shi sannan ya mik'ama Mustapha hannu suka gaisa cikin sakin fuska
sannan suka gaisa da Adam yai musu sallama ya shafa kan Farouq tare da cewa,
"bye bye bobona".
Amman yajuya ya nufi motarshi cike da damuwa da kunar zuciya da jin zafin kukan da
Ummul take yi.
Su kuwa da sauri suka k'arasa bangaren Nanne jiki na rawa dan jiyo kukan Ummul da
sukayi
cikin k'unar rai da firgici Usman yake salati idanuwan shi sun rufe da kyar ya matsa
jikin gini ya jingina yana sauke numfashi da kyar,
ya Adam ne ya k'arasa gurin ya dafa kafad'ar ya Sadiq yace,
"meke faruwa ne? meya sameta?".
Kai kawai Sadiq ke juyawa dan haka Adam ya tsuguna ya d'auko Ummul daga jikin
Sadiq ya gyara zama ya kuma matsota jikin shi sannan yasa hannu ya kamo fuskarta
cikin rarrashi yace,
"k'anwata kiyi hakuri ki sanar damu damuwar ki,
kinga dukkan mu hankalin mu ya tashi, kinga yaronki yana kallonki kada kisa mufara
zargin kanmu da rashin cikawa Hamman mu al'kawarin rashi baki kulawa,
daure ki fad'a mana". sai kuma yasake sa hannu ya d'ago kanta yace,
"kallemu Ummul dukkanmu zamu iya jure duk wani abu dan mu samar maki farin ciki
ki daure ki fad'a mana koma menene?".
Cikin kukan ta sauke nan nauyar ajiyar zuciya sannan tasake cusa kanta jikin Ammi
murya na rawa tace,
"Ya Adam dan Allah ka hana Mustapha zuwa gidan nan,
wallahi bana sonshi, ba zan sake son kowaba bayan Hamma na bazan so kowaba bare ma
Mustapha wanda soyayyar sace tasa na kasa ganin soyayyar da Hamma na yake min na
tsani Mustapha dan shine sanadin bijirewa Abbana duk da bai zugani ba kuma ya nusar
dani da inbi zabin iyayena amman taurin kai da zuqar shaid'an tasa nak'i masoyi na auren
Hamma na ya isheni ni nagama aure bana son ganin shi bana son ganin fuskar
shi,bazan aure shiba bazan auri kowaba a barni da auren Hamma na dan Allah".
Kafin kowa yayi magana Usman dake tsaye jikin bango ya sauke ajiyar zuciya ya
mik'awa ya Sadiq dake kusa dashi Faruq sannan ya matsa kusa da ita ya tsugunna ya
kamo hannun Ummul itama d'ago kai tayi tana kallon shi cike da rauni da tsantsar
nadamar illar rashin bin umarnin iyaye tace,
"Ya Usman".
da sauri yasa yatsa akan lips d'inta dasu kayi jawur sabida kuka a hankali yace,
"Na sani Ummu na kiyi hakuri zamuyi duk yadda kike so amma saikin daina kukan nan
sai na dena ganin hawayen ki".
Kai ta d'agamai sannan yayi murmushi yace,
"Yawwa k'anwata Allah miki albarka".
dukkan su suka amsa da "Amin".
Mustapha kuwa yakasa zaune yakasa tsaye zuciyarshi takasa samun sukuni yanajin
bazai iya rayuwa inba Ummul haka nan yayita fama da tunani da damuwa kullum saiya
kira wayar