Showing 1 words to 3000 words out of 189984 words

Chapter 1 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

09 Nov 2024

16202

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*___________________________________






Labari ne da yake dauke da sabon salo,wanda nasan cewa ba ku taba cin karo da irin sa ba,ba zan ce muku komai game da wannan labari ba,ku dai kawai ku biyoni sannu dan jin me yake dauke dashi,me nazo muku da shi a wannan karon


Daga gwanar ku fatima y Adam me dauke da




Ƙudurar Allah da kuma kaddarata sanadin haske,yanzu kuma gani nan tafe cikin ɓoyayyar raihan,salon na daban ne faaa.....😄




Pg 1




,,,,,,,,,,,,,,,,,,Yola




..........Alhaji Muhammad nurr shahararren attajiri ne,wanda yayi shura a cikin kasar mu ta Najeriya,kai harma da wajen kasar, bafulatanin Yola ne,sai dai mahaifiyar shi cikakkiyar bakaniya ce wadda mahaifinsa ya aurota a yawon almajiranci ya kawo ta Yola,ya aureta ne a matsayin bazawarar da miji ya rasu ya barta da yaro guda daya me suna yahya,kasancewar shi me son yara yasa shi karbar Yahya a matsayin ɗa tamkar shi ya haife shi,mahaifiyar su me suna rahma su biyu ta haifa. mahaifinsa me suna Aliyu kuma shi kadai ya haifa kwaya daya tilo a duniya, sai dai ba zaka taba gane hakan ba saboda yadda ya rike dan matar sa Yahya tare da nasa dan tamkar duka shi ya haife su, Alh Muhammad nurr bashi da wani dan uwa na jini sai Yahya,sai dai malam Aliyu wanda suke kira da baffa yana da tarin yan uwa.haka mahaifiyarsu rahma tana da tarin yan uwa a can Kano.




Alhaji Muhammad nurr ya ta so cikin so da gata,tare da dimbin kulawa daga iyayen shi,ya samu karatun addini daga mahaifinsa kasancewarsa malamin addini,haka kuma ya samu ilmin boko me zurfi shima duk da taimakon jajircewar mahaifinsa,uba tamkar da dubu,saboda gaba ɗaya kusan dukkan komai ya same shi ne daga mahaifinsa,sakamakon mahaifiyarsu ,bata damu da wasu hakkoki na tarbiyya da suke wajibi akanta ba,saboda ita ɗin wata iriyar macece da baka taba iya gane mata ko gane inda ta fuskanta.


Yadda baffa Aliyu ya bawa Muhammad nurr tarbiya da ilmin boko da na addini haka ya jajirce ya bawa dan matar shi Yahaya wanda tsawon rayuwar Muhammad nurr bai taba sanin cewa ba uwar su daya uban su daya ba.


Sai dai kuma Yahya shi sam ba shi da ra'ayin karatun boko, shi yasa ya dinga wasa tun lokacin secondary wanda daga karshe ya sanar da mahaifinna su shifa ba zai iya wannan karatun ba,duk da baffa bai so hakan ba saboda ganin Muhammad nurr nashi karatun ya mika harma ya wuce yayan na shi,to amma babu yadda ya iya haka ya rabu da Yahya ,sai kawai ya kai shi kasuwa ya bude masa shagon Saida takalman roba irin wadanda Fulani suka fi amfani da shi a can babbar kasuwa.


Ai ko hakan ba karamin dadi ya yiwa Yahya ba,dan haka da kwarin sa ya fara zuwa kasuwa,sai kuma Allah ya sawa abun albarka.




Muhammad nuurr ya shahara ne ta hanyar jajircewar mahaifinsa,ta yadda ya tsaya tsayin daka ya samar da ilmi da tarbiyya ga tilon dan nasa,shi yasa shima yahya bai barshi haka ba ya bashi abin da ya nuna yana so wanda kuma yake samu sosai dan harma sun kuma bude wani shagon, wannan jajircewa ta baffa kuwa ba ƙaramin taimako yayiwa rayuwar nurr ba,saboda lokaci ɗaya ya samu nasarar rayuwa.




Kasuwanci shine a binda Muhammad nurr yayi karatu akan sa,kamar yadda dan uwansa Yahya shima ya fara suna akan harkar takalma,


Yahya ya jima baiyi aure ba dan daga karshe ma baffa ne ya samo masa matar ya aura masa,sai kuma a kayi da ce yaji yana sonta,


Ganin baffa shine ya zaɓawa Yahya mata sai kawai Hajiya goggo ta ji kishi akan Muhammad nuurr, dan haka ita ce wadda ta fara zaba masa matar aure me suna murja, wadda ta kasance yar kanwarta,bai iya jayayya da iyayen shi ba,dan haka ya karbi murja da hannu bibbiyu duk da cewa babu so ko daya aranshi.


Har zuwa tsawon wannan lokacin Yahya matar shi bata taba yin ko ɓatan wata ba,wanda daga baya Hajiya goggo ta so ya kara aure amma ya furje dole ta hakura ta kyale shi,shi kuma ba komai ne yasa ya ki amincewa ba sai dan tabbacin da likita ya ba shi akan cewa kwayoyin halittar shi na haihuwa ne basu da karfi shi yasa har yanzu bai samu haihuwa ba,amma ba wai ance ba zai haihu ba ne gaba daya.


Alhaji Muhammad nurr,tun tasowar shi da kuma mafarkan shi,yake fata da burin samun ya mace a cikin zuri'ar shi, wannan burin na shi yana daga cikin dalilin saurin karbar auren murja da ya yi ba tare da musu ko gardama ba.




Lokaci ɗaya Muhammad nurr ya samu daukaka ta ban mamaki da arziki me tarin yawa,hakan ya sa ya dinga dibar iyayen shi da yan uwan su,yana kaisu kasa me tsarki,kafin wani lokaci ya wadata yan uwan mahaifinsa da na mahaifiyar sa,


Ba tare da kowa ya sani ba Muhammad nuurr ya sayi hannun jari a wata kamfanin sarrafa takalman roba,sai dai kawai ya dankawa Yahya a matsayin kyautar sa ta musamman, wannan al'amari ya yiwa baffa dadi sosai haka Yahya shima ya dinga zuba godiya harda kuka.


A hankali harkoki su ka ci gaba da budewa Muhammad nurr,ya yi suna a kasashen waje da manyan jahohin Nigeria,sai dai kuma har lokacin murja bata taɓa ko da bari ba,bare ta haihu, hakan kuma ba ƙaramin tayar musu da hankali ya yi ba,duk da cewa ba wani dadewa auren yayi ba,tunda yanzu bai wuce shekara biyu ba.



A cikin wannan tsukinne aka kammala babban ginin gidan da aka yi shi wanda za mu iya kiran shi da estate ta wani bangaren,sai dai ba shi da yawan bangarori,bangare shida ne kawai aciki,bangaren Yahya ,sai bangaren iyayen su,da kuma nasa bangaren da yakasance me bangarori har hudu bayan nasa da ya zama na Biyar,ragowar kuma an yi sune dan fatan zuri'a a nan gaba.ganin haka yasa
Ba tare da sanin kowa ba , goggo rahma ta shiga nemawa Muhammad nurr wani auren,ba tayi dubi da zumuncin dake tsakanin ta da uwar murja ba,ita kawai mafitar danta take nema,acewarta koda murja ta haihu dole ne Muhammad nurr ya kuma yin wani auren saboda dukiyar sa ba ta zaman mace daya ba ce.




Daga murja har Muhammad ɗin da mahaifinsa,daga sama suka sami labarin,sai dai a wannan lokacin ma baiyi mata musu ba,ya amince tare da sa hannun mahaifinsa baffa Ali da kuma shakikin dan uwansa da ba shi da kamarsa.


Sai dai kuma daga ɓangaren murja da mahaifiyarta ansha artabu dan ba daban dukiyar da suke kwadayi ba,da tuni ko mai ya lalace,daga karshe dai dole suka hakura suna ji suna gani aka kawo amarya hanne,wadda ta kasance yar kawar goggo Rahma.




Daga nan, aka fara fafata kishi ,tsakanin murja da hanne,yayin da kuma a gefe ta ciki na ciki tsakanin goggo Rahma da surukarta da kuma yar uwarta,(to bari muje zuwa muga me zai faru).




Ko waccen su so take taga ta samu ciki,saboda shine damar farko ta samun mallake gidan,a wannan karon ba hankoron neman samun cikin kawai ake ba,harma da fatan samun jinsin da me gidan ke fata da buri,ko waccen su fatan ta ace yau ta samu diya mace,saboda duk wanda yasan Muhammad nurr yasan me yake bida yake fata da buri.




Ba komai ne yasa hankalin matan ya kuma ta shi da neman haihuwar mace ba,sai yadda suka ga duk wata babbar kadara da Alhaji Mohammed nurr ya mallaka ya daga ya rubuta sunan RAIHAN,da niyar mallaka mata su ,ba tare da yasan za a haifa masa RAIHAN ɗin ba,ba tare da yasan wacece zata haifa masa RAIHAN ɗin ba,hankalin su ya matukar ta shi da wannan danyan hukuncin da Alhaji Mohammed nurr ya yanke,dan magana har sai da ta kai gaban Baffan shi,duk da cewa da sanin shi yayi hakan, cikin nutsuwa malam Ali ya dubi dan na shi, kafin cikin muryarshi ta Dattako ta karade falon,ya fara da bude taron da addu a , sannan ya dora maganar shi da cewa, Muhammad nurr kasan rigimar da ka haddasa cikin iyalanka a kan wannan hukunci da ka ke ta zartarwa kuwa? A hankali Alhaji nurr ya numfasa sannan cikin tsantsar ladabi ya dubi mahaifin nashi tare da cewa,kayi hakuri Baffa zuciyata ce ta kasa sarrafuwa akan soyayyar da take yiwa RAIHAN,shi yasa na yanke wannan hukunci" goggo Rahma ta yi zaraf ta ce" to kai kana da tabbacin za a haifa maka RAIHAN dinne da har kake kwasar dukiyarka kana rattaba sunayen ta a matsayin ka mallaka mata su?jin jina kansa yayi sannan ya ce" ban san gaibu ba,dan haka ban sani ba ko Allah ya ƙaddara min samun RAIHAN a duniya,abin da na sani kawai kullum duk sakan da mintuna zuwa awowi addu'a nake Allah ya bani RAIHAN" Baffan shi ya ce" RAIHAN kawai kake bukata ba ka neman Alkhairi? Nan ma jinjina kai yayi tare da cewa a'a Baffa ,na roki Allah idan RAIHAN ba Alkhairi ba ce Allah ya musanya min zuwan ta da Alkhairi,idan kuma hakan ba zai samu ba,to nafi bukatar Alkhairin" murja ta tunzura baki tare da cewa amma kuma kasan Allah zai iya yin duk yadda yaso akan RAIHAN ɗin,kake duk wannan a bun bayan kasan zata iya zuwa maka da akasin alheri idan ma an same tan,balle ma babu tabbacin samun nata" cewar hanne ke nan da sai yanzu ta tsoma baki cikin zancan.




Alh nurr ya girgiza kan shi sannan ya ce" nayi addu ar samun RAIHAN kuma addu a ta Alkhairi,shi yasa nake ji ajikina cewar zan samu RAIHAN,a kusa ko a nesa insha Allahu".




Goggo ta sa salati tana mai tafa hannayenta,kaifa nuru na fahimci kamar baka cikin tunanin ka,idan ba haka ba waye yake zance da gaibu" Baffa ne ya dakatar da ita daga banbamin da take yi,tare da duban Alhaji nurr ya ce" amma kasan abinda kayi ya haddasa fitina cikin iyalanka? Dan gyara zaman sa yayi kana ya bawa mahaifinshi amsa da cewa ey Baffa Amma Ni banga abin husuma a cikin wannan abun ba,tunda dai dukiya tawa ce kuma Ni nayi niyar bayar da ita ga RAIHAN, sannan kuma dukkan su duk wacce ta haifa min macen gurinta dukiyar zata koma idan kuma dukan su suka haifa to nayi alkawarin bada kyautar ga dayar kamar yadda na bawa ɗaya,dan haka ina ga maganar nan a barta kuma nayi alkawarin ko waccen su zan bata kyauta me tsoka tare da kadara wadda zata ji dadi harma su kawar da idanun su daga kan dukiyar RAIHAN".




Baffa ya danja numfashi kafin ya ce" shi ke nan na gamsu da hujjojinka , Allah kuma ya baka abinda kake so ,ya kuma zama me alheri a gareka damu baki daya" Amin suka amsa gaba ɗaya,sai dai goggo sam bata gamsu da Wannan lamari ba,dan aganin ta duk wadda ta haifa masa mace ko kuma suka haifa gaba ɗaya ,to tabbas ita ce zata kwana a ciki,ya ma za ayi ita da haifar dan su da mora ai hakan ma ba abu ne mai yuwuwa ba,amma dai bata ce komai ba dan wannan lamari yana bukatar dogon tunani.




Tun daga wannan rana ko wacce ta shiga fafutuka ta neman haihuwa ,haihuwarma ta ya mace,yayin da goggo take gefe ɗaya tana kallon kowaccen su,tana kuma fatan ace basu samu abin da suke neman ba,kai ita fa a yanzu bata ki a ce Muhammad nurr ya ki samun haihuwa ba,don kuwa rashin samun haihuwar tasa shine alheri a gareta,tasan cewa idan ya mutu bai haihu ba,dole ita ce mai gadon sa,(Hajiya goggo an san gawar fari ke nan).






Kwatsam abin farinciki ya samu a gidan Alhaji Muhammad nurr, sakamakon cikin da aka wayi gari hanne na da shi,kar ku so kuga yadda Alhaji nurr yayi FARINCIKI,sai dai kuma daga ɓangaren goggo da murja abin ba haka yake ba,murja dai har cuta ta yi saboda tsananin tashin hankali,daga nan sai suka samu damar hade kai ita da goggo barakar da ta shiga tsakanin su suka dinke ta,suka shiga fafutukar zubda cikin,sai dai kuma zakaran da Allah ya nufa da cara dole sai yayi,lafiya ƙalau hanne ta raini cikin ta,har zuwa ranar haife shi.


To a lokacin ashe itama maimunan Yahya tana dauke da mata cikin wanda hakan ya kara haifar da fariincikinazan tamkar zasu ci kasa.


Baffa dai da Alhaji nurr sunturi suke a raseption,tare da adu ar fatan sauka lafiya ga hanne, goggo da murja kuwa ba wannan fatan su ke yi ba,dan ba su ki a ce daga uwar har dan sun mace ba,kamar daga sama suka tsinkayo kukan jariri tamkar zai tsinka musu dodon kunne,kafin ka ce me sun shiga rige rigen fadawa dakin tsakanin goggo da murja,saboda basa jin zasu iya tsayawa har likita ya fito ya sanar da su abin da aka haifa,ita dai maimuna kallon su kawai take tana mamakin yadda suka.kasa boye damuwarsa akan haihuwar hanne, sai dai kuma ba su kai ga samun nasarar shiga dakin ba,wata nass ta dakatar da su,ba dan ran su yaso ba suka hakura sai dai kana kallon su zaka tabbatar da cewa suna cikin tashin hankali da fargaba me tsanani.




Sai da suka kwashe tsawon mintuna talatin sannan aka fito da babyn nannaɗe cikin farin shawel me tsananin taushi da kyau,da sauri goggo ta tari nas ɗin da tambayar me aka samu? Mika musu babyn ta yi fuskarta dauke da murmushi ta na cewa meye tukyici na? Murja taja dogon tsaki tana hararar nas ɗin, Baffa ne ya ce" me muka samu tukun daga nan sai a tafi batun tukyici"dariya tayi sannan ta ce" ina taya ku murna an samu baby boy,me kama da maman shi" wata irin guda goggo ta saki tare da cewa alhdlllh anyi min miji lallai kin cancanci tukuici dan haka ungo nan"ta faɗa tana mika mata sabbin yan dubu guda biyar, cikin sauri nas ta sa hannu ta karba tana zuba Godiya,sosai Alh nurr yay farinciki tare da nuna godiyar shi ga Allah,Yahaya ne ya karbi dan ya yi mishi addu'a ,daga nan ya mikawa Baffa Shima ya jima yana masa addu'a,sai kuma ubangaiya shima dai addu'a'in ya yi masa tare da fatan zamowar shi shiryayye.




Murja kuwa zamu iya cewa tasa mu sassauci ,duk da cewa ba wai tayi farinciki ba ne,tunda dai a ganin ta ita bata haihu ba,sai dai a ranta tana jin cewa itama tana kusa dan bata fidda rai da samu ba.




A ɓangaren hanne kuwa ,bayan farkawar ta daga doguwar sumar da ta tafi bayan haihuwarta,sai ta nemi da a nuna mata abinda ta haifa,da sauri murja ta mika mata babyn bakinta kamar gonar auduga tana cewa gashi nan,mun samu baby boy me kama dake sak ,sai dai fatan Allah ya raya bisa sunna" take hannun hanne ya fara karkarwa harma tana neman yarda babyn sai da murjar tayi saurin tare shi tana jan a uziya,gani kawai su kayi hanne ta sa kuka kamar wadda aka ce mata uwarta da ubanta sun mutu, goggo ta kama baki tare da cewa yau nake ganin ikon Allah,yanzu ke hanne ba zaki yi murna da samun lafiyar ki ba,Ni dai kam na dade banga abin mamaki da takaici ba irin wannan,yanzu har munzo zamanin da aka daina murnar haifa da namiji? Baffa ne yayi saurin dakatar da goggo da cewa me yasa kike haka ne goggon nuru? Haka ta ce miki ba kukan farinciki take yi ba? Murja ta yi tsalam ta ce" yo Baffa ai abin a bayyane yake"harara Alhaji Mahammad nurr ya watsa mata,wanda hakan yasa ta ja baki ta tsuke ranta fes,maimuna kuwa karasawa ta yi wajen hanne tana bata baki cikin kyakkyawan malami, daidai lokacin ne mahaifiyar hanne da yan uwanta suka ƙaraso ,hakan yasa akabar maganar kowa ya shiga san Barka da yiwa juna Barka.




Cikin kuka Hanne ta dubi mahaifiyar ta da Yar uwarta tani, ta ce" inna dole nayi kuka,saboda Muhammad nurr bai barwa ya'yansa maza abun dagawa a faɗa a duniya ba,ya tattara komai da yake da muhimmi duk wata babbar kadararsa ya rattaba sunan gaibu ya bawa yarinyar da bata zo duniya ba,ba kuma a san ran zuwan nata ba,yaya tani ta kama baki cikin al'ajabi ta ce" yanzu kina nufin duk yawan dukiyar Alhaji nurr ya kwashe ya baiwa yar da babu batun samunta a duniya? Jinjina kai ta yi tana sharbar hawaye,inna ta ce Ey gaskiya dole ki yi kuka tunda a yanzu ko da yaushe za a iya cewa abokiyar zaman ki na ɗauke da ciki wannan kadan daga ikon Allah" amma kiyi hakuri mu bari zuwa nan gaba kadan tun da har yanzu ba a samu RAIHAN ɗin ba,amma nayi miki alkawarin cewa indai bake kika haifi RAIHAN ba to babu wata mace da ta isa ta haifawa nurr ita,da wannan alwashin na mahaifiyarta ta samu salama a zuciyarta.






Anyi suna lafiya an sa wa yaro suna Aliyu sunan Baffa ke nan,daga nan rayuwa ta ci gaba da turawa ,burika na daduwa a zukatan marasa godiya ga Allah.




Maimuna ta sauka itama ta samu namiji,kowa ya yi murna da samun karuwar da aka fara yi a zuriar ta su,yaro ya ci sunan baban maimuna wato Bashir,daga nan maimuna ta ci gaba da raunon danta cikin kwanciyar hankali,tunda dama ita babu wannan burin na son samun raihan, wannan ba hurumin ta ba ne,kai ita gani take ko da ace tana daga cikin matan Muhammad nuurr to kuwa babu abinda zai sa ta yi kokuwar neman duniya ta hanyar samun raihan.


Bayan shekara daya da haihuwar Aliyu, da Bashir murja ta samu nata cikin itama,wayyo farincikin ba mai faduwa ba ne,babu wanda ya sani daga ita sai mahaifiyarta a cewar ta kar mahassada su ga bayanta ita da abinda ke cikin nata,to ashe itama hanne alokacin ta kuma samun wani cikin ,itama sai tayi shuru saboda irin tunanin murja,haka nan kowaccen su ta shiga ɓoye cikinta da ririta abinta tare da babban fata akan dacewa da samun RAIHAN.




A lokacin da cikin da ake boyewa ya baiyyana ,dukan su sai da suka shiga shock na ganin junan su,sai dai tunda ciki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login