Showing 6001 words to 9000 words out of 189984 words
Chapter 3 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
roba ce saboda yanayin jikin abin, kuma zaki iya cire mata duk lokacin da kika so dan wanke ainahin halittarta,Dr yanzu a ina zamu samu sannan zuwa yaushe zamu samu? Kasan cewa fa ko da yaushe zan iya sauka indai Allah ya nufa,amma dan Allah indai banyi rai ba ina so ka ɗauke Abinda na haifa ka dan ƙawa iyayena indai ya kasance RAIHAN ce" kar ki damu insha Allahu ma zaki haihu lafiya, yanzu zanyi magana da Dr eka ko da abin bai ƙaraso yau ba ,zan yi kokari koda kin haihu na toshe hanyar ganin ki da ke da jariri har sai mun aiwatar da shirin mu"na gode Dr Allah ya saka da alheri Allah ya taimake ka kamar yadda kake son taimakon rayuwata, Allah kuma yasa abinda mu kayi ya zama Alkhairi a garemu baki daya"Amin Ya Allah,ya ce" yanzu bari naje na fara wancan shirin daga nan sai mu fara shirin yi miki c s,tunda naga lokacin da muka diba idan baki haihu ba ya kusa" daga nan ya bar dakin dan fara aiwatar da shirin su kamar yadda ya faɗa.
Hankalin Alh nurr ba ƙaramin ta shi yayi ba ganin har lokacin da aka diba ya cika ,Ramla bata haihu ba,hakan yana nufin dole sai anyi mata aiki ke nan,da kyar ya iya sa hannu aka shiga da Ramla dakin da za ayi mata cs.
Sai dai kuma lokacin da ake ƙoƙarin fara aikin Allah da ikon sa ya bawa Ramla dama da karfin nishin haifuwa, tana sun kuto babyn ta Dr Sabo yayi saurin ɗauka ba tare da ya bari kowa ya gani ba,hamdala yayi wa Ubangiji dan tabbas da anyi cs sai an samu wani ya iya gane abin data haifa ,amma dake Allah ya gama zartar da ikon sa na cewa za a haifi RAIHAN kuma zata yi doguwar rayuwa,sai ya bawa mahaifiyarta ikon haihuwa da kanta dan hakan ya zama kariya daga idanun da suke kokarin cutar da ita.
Nass ɗin da aka bawa wannan aiki tuni ta shiga baza idanu dan ganin abinda aka haifa,Dr kawo muga abinda aka samu? Ta faɗa tana murmushi kai ba zaka taba kawo cewa akwai wata mummunar manufa a ranta ba,da sauri Dr Sabo ya ce" wannan babyn namiji ne sai dai amma gaskiya ba shi da lafiya dan haka ku gyara uwar Ni kuma zan tafi da shi can dakin bincike" yana gama fadar haka ya fita ta wata kofa daban ba ta kofar da suke shigowa ba.
A hankali labarin haihuwar Ramla ya karade dangi, amma ganin yaro ya gagara har yau kwana ɗaya da haihuwa , saboda likita ya sanar da su cewa yaron bashi da lafiya dan haka babu mai ganin sa sai nan da kwana uku,dole kowa ya hakura da ganin baby,Amma dai da yawa hankulan su ya kwanta da sanin cewa Ramla namiji ta haifa.
Bayan kwana uku , babyn Ramla ta baiyana cikin kyakkyawar shiga ta fararen kayan sanyi,Masha Allah kowa yake fadi yau gaɗan buzaye kyau ya hadu da kyau ya bada kyau,tunda Alh nurr ya dauki babyn nan ya zuba masa ido yaji gaban sa na faduwa sai dai ba ya ce ga dalili ba,tabbas har mafarki an nuna masa cewa Ramla ta haifi RAIHAN,to sai dai kuma ga shi Ƙudura ta ubangiji ta sauya al'amarin,haka nan yaji zuciyar shi ta karaya ta kuma hakura da samun RAIHAN,amma kuma wani abun mamaki da shine jin duk wata SOYAYYA da yake yiwa RAIHAN ta juye ta rikida ta koma kan jaririn da Ramla ta haifa,wanda take yayi wa babyn huduba da Abdulrahim,haka goggo ta dauki babyn tana ta juyawa cike da so da kauna.
Ana sallamar su gida suka wuce,sai dai kuma suna komawa gidan Ramla ta ji zuciyarta taki gamsuwa da zaman gidan,dan haka kawai ta nemi alfarmar Alh nurr da ya barta ta je gida wanka,ya so ya hana ta to amma kuma baya jin akwai wata alfarma da Ramla zata nema a wajen sa in dai yana da ikon yi mata baiyi ba, goggo ma dai taso Ramlah ta zauna to itan ma bata tauye Ramlah ba,tunda sun san halinta da alkunya da bata bukata da bazata taba tambaya ba.
Maimuna ma taso ramla ta yi zamanta ,acewarta ita meye amfanin ta da har tana zaune gata ga goggo sai ramla din ta tafi gida wanka,to amma itama ganin ramla hankalinta ya fi karkata ga son zuwa gidan yasa suka bita da fatan alheri.
Da wannan hankalinta ya kuma kwanciya tasan ko a kasi aka samu innar ta ce a kusa da ita ,bayan suna Ramla ta wuce agades ita da goggo da tayi mata rakiya.
........Rayuwar Ramla agades.
Cikin taka tsantsan take rayuwarta a sirrance,duk da cewa Nan din iyayen ta ne Kuma marufar asirinta ,to Amma tayi yakinin cewa duk ta sake suka sani tabbas maganar zata iya yaɗuwa har tayi Yaɗon da zata Kai inda take tsoran zuuwanta,tun wankan sati Daya da ta bari goggo ta yi wa baby Bata Kuma bari Wani ya yi mata ba,tunda suka dawo agades tace wa innarta ai goggo ta koya mata wankan baby Kuma likita ya ce" lallai ta dinga yi mata da kanta saboda kiyaye wasu abubuwa Wanda ko ita Bai sanarwa ba.da wannan ta samu ta ke wa babyn ta wanka ba tare da anga rashin kunyarta ba,duk da cewa daga ita sai innarta ne a gidan.
Tunda suka dawo agades alhaji Muhammad nurr Baya sati Daya sai yazo yaga sanyin idaniyarsa,wata irin soyayya ce me zafi yakewa Rahim tamkar soyayyar RAIHAN,abun har mamaki yake bashi da Kuma Saka shi shakkun da baisan dalilinsa ba,duk lokacin da yaje ya dauki RAHIM ya tsira mashi idanu yakancewa,Ramla gani nake yi ba a taba haifar kyakykyawa kamar RAHIM ba,Wani lokacin idan na kalle shi sai na ga kamar mace saboda tsananin kyansa"a razane Ramla ta dube shi kafin cikin rawar Baki ta ce"Abban RAHIM lallai Ina tunanin ka fara zautuwa akan son RAIHAN idan ba haka ba ta ya RAHIM zai na juya Maka zuwa mace?murmushi yayi tare da cewa to Ina ga dai hakanne maganarki".
Tun daga lokacin ta Kuma daukar aniyar boye RAIHAN dinta,Dan ta tabbatar da cewa idan Bata dauki mataki ba wata rana Abbin ta zai iya ganin abun da suke boyewar wanda Kuma Hakan Yana dai_dai ne da rasa yar ta su GABA Daya.
A cikin tsananin taka tsantsan Ramla ta ci GABA da wanka har zuwa ranar da ta yi arba in,duk da cewa alhaji Muhammad nurr ya damu da dawowar su Amma hakan bai hana shi bari su zaga dangi ba,sai da su ka Kara sati ɗaya Sannan yazo ya tattara iyalan sa suka koma Yola,zuciyarsa cike da farinciki na zai kasance da RAHIM din shi a inuwa guda.
Wannan shine tushen labarin.muje zuwa yanzu din ma ba a fara komai ba,kamar dai yadda na gaya muku salon nasa na dabanne.
Typing
Fatima y Adam ✍🏽
Typing
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page3 ```
Da fargabar abun da zai iya faruwa Ramla ta koma Yola,sai dai ta yi kwanaki biyu ta samu nutsuwa ganin babu abinda ya faru,kamar yadda take taka tsantsan a can agades haka Nan ma take yi Harma fiye da can din,kullum goggo sai ta sa an dauko mata RAHIM tun Ramla na fargabar hakan har ta hakura ta Maida hankalinta kan mijinta da alamuran da suka shafi rayuwarsu.
Kwanci ta shi yanzu gashi RAHIM yana da shekara biyu har da watanni takwas,tuni Ramla wadda yaran gidan suke kira da anty amarya ta yaye shi daga Shan mama,su mama murja tuni suka dauke hankalinsu daga kan lamuran anty amarya duk da cewa suna sane da irin mugun son da alhaji Muhammad nurr yake wa tilon ɗan da ya fito daga tsatson Ramla anty amarya,sai dai yanzu ba wannan ne a gaban su ba, abinda ke gaban su kawai shine yadda za ayi dukiyar RAIHAN ta dawo ta 'ya'yan su da su kansu.
Bayan shekara biyu da haihuwar RAHIM,a yanzu fa komai nema yake ya kuncewa,anty amarya saboda yanzu saura shekara uku abin da take sawa RAIHAN ya daina amfani saboda girma da zai fara zuwa mata,take ta fara neman hanyar ci gaba da ɓoyan RAIHAN dinta har zuwa lokacin da ta tabbatar da cewa babu wani me neman rayuwar 'yarta.babu bata lokaci ta nemi Dr Sabo,ya jima yana nazari kafin ya dan numfasa kana ya ce" Amarya wannan ba wani abun tada hankali ba ne,kawai da zarar RAIHAN ta cika shekara goma za a canja mata kayan da take sawa ya kasance duk kayan da zata saka su kasance masu girma da boye halitta ,saboda na tabbatar da cewa nan da shekara goma alamun girma zasu iya bayyana a jikinta ,idan mu kayi amfani da wannan kayan hakan zai taimaka mana wajen ɓoye halittar ta,idan kuma kan lokacin Allah ya bamu nasarar gane makiyan ta shike nan kin ga mun samu sauki,fatan mu dai Allah ya kaimu da ran mu da lafiyar mu" ajiyar zuciya Anty amarya ta sauke tare da cewa shike nan Dr Sabo na gode sosai da gudunmawarka a garemu kuma insha Allah zan kiyaye da duk abinda ka zana min fatan dai Allah yasa mu ga girman da rai da lafiya"daga nan su kayi sallama ta tuko motar su ka dawo gida.
Shekarar RAHIM hudu aka saka shi a makaranta me shegen tsada,Ta ya'yan manya,sai kuma su mama murja da suka fara shiga tashin hankali akan yadda komai na RAHIM ya sha banban da na nasu yaran,(a ganin su fa amma)dan hatta da Hajiya goggo kaunar da take wa RAHIM ta musamman ce,duk da cewa tana jin haushin yadda anty amarya take nuna mata rashin yadda akan RAHIM din tunda bata barin sa ko da wasa ya kwana a bangaren Hajiya goggo,bata san dalilin anty amaryar da yin wannan taka tsantsan din da RAHIM ba,ko wasa ba ta barinsa yi cikin yan uwansa yara,ko da yaushe yana kusa da ita a takure.
A haka ya fara zuwa makaranta,to makarantar ma ta ce ita ce zata dinga kaishi tana dauko shi,sam Alhaji nurr bai damu da hakan ba sai ma mota da ya siya musamman dan kai RAHIM din makaranta,hakan ba karamin farinciki ya saka anty amarya ba,sai dai kuma hakan tamkar ƙarawa su momy Hanne da yaran su ƙiyayyar RAHIM tayi,dan su momy sun dade da koyawa 'ya'yan su ƙiyayyar anty amarya da tilon yaronta.
Irin yadda anty amarya take takura RAHIM abin har yaso yayi yawa,saboda bashi da dama ya sake cikin yara yan uwansa ,sai kuma wani babban al'amari da yake son daga mata hankali wato yadda RAHIM bashi da aiki sai wasa da mata da duk wani abu da ya danganci mace, tasha kwace ribom a hannun sa,wanda take rasa a ina yake samu,saboda ta hana shi wasa da yaran anguwa da na ajin su,abin da bata sani ba shine RAHIM yana da wata kawa yar ajin su kuma makotan su,duk lokacin da yaga abin da ya burge shi nata kai tsaye yake cewa ta bashi,shakuwar da su kayi da ilham me yawa ce,kuma kullum gaba take yi.
Yadda Baffa da Abba yahya suke kaunar Rahim abun har mamaki yake bawa mutanen gidan haka ta bangaren inna maimuna wadda suke dinke ita da aunty amarya tamkar wasu yaya da kanwa,dan duk yadda aunty amarya ta kai ga boyon Raihan bata iya yiwa inna maimuna shamaki da ita.
Kwanci ta shi gashi yau saboda tsananin kokari irin na RAHIM har an yi masa tsallake an kai shi primary one,daga free nursery,a kuma shekarar ne ya cika shekara biyar.
Wani irin sihirtacce kyau ne da rahim me sanyi ,wanda saboda yawan tanka musu shi da ake yasa Abbin sa sa manyan malamai dinga yi masa addu'a da karatun Alqur'ani,haka Hajiya goggo ta shiga bashi rubutuka da tofi na kariya da tsari,Anty amarya dama bata tsaya ba itama tsaye take kan tarbiyyar yarta da kuma yawan addu o i ,wanda take mata da wanda take koya mata.
A cikin islamiyar da Rahim yake zuwa ma duk yawancin kawayen sa mata ne,to amma saboda yana tsoran fadar antyn shi sam baya bari ta sani.
Hajiya goggo ta so sanar da Abbin irin takurar da antyn Rahim ke yi masa ,saboda shi bai san komai ba tunda ba yawan zama yake yi a kasar ba,wani lokacin ma saboda Rahim din yake takura kansa ya yanke wasu abubuwan ya dawo ya danyi kwana biyu ya koma,sai kuma ta bari saboda bata son manufar ramla akan hakan ba.
A yanzu gaba daya yaran tun daga kan Affan da bashir har zuwa kan jamilu Abbin su ya tura su karatu,dan haka yanzu babu kowa a gidan sai Rahim.ganin haka ya sa Hajiya goggo dauko jikar, kanwarta me suna jiddo,saboda ta dinga jin motsin yara a gidan tunda Rahim ya zama ɗan kurkuku,sam dauko yarinyar nan baiwa Anty amarya dadi ba saboda kusan sa'ar Rahim ce,dole zasu dinga wasa tare wanda ita kuma haka ne bata so, wannan dalilin yasa ta gwammace Rahim ya koma makaranta da yini,dan haka ta cire shi daga islamiyar da yake zuwa ya koma yini a makaranta,hakan sai yayi wa Rahim dadi saboda kawar sa ilham ma ta yini take yi,sharudda kuwa malaman makaranta sun sha shi ,sai dai kawai sun ji ta ne,dan babu yadda za ayi su hana yaro walwala cikin yan uwansa yara,tun da antyn su ta fahimci irin rayuwar da Rahim yake yi a gida ke nan,shike nan ta bashi damar wata yawa a makaranta,hakan ya mishi dadi kuwa har sai ya zama na yafi son zaman makaranta akan na gidan su,kasancewar yana da matukar kokari kamar wani aljan sai hakan ya da da jawo masa farin jini wajen malamai harma da daliban da suka girme masa,a hankali aka dinga yi masa tsallaken aji saboda basirar sa ta girmi ajinsa.
Shekara
Goma daidai wanda yayi daidai da fara zuwan shi makarantar gaba da primary,a lokacin ne Abbin shi ya haɗa masa kwarya kwaryar walima ta cika shekaru goma da kuma murnar kammala primary school,a lokacin ne hankalin Anty amarya ya kuma dagawa saboda yadda taga duk taron kawayen Rahim mata ne,mazan ba su da wani yawa, hankalin ta ya matukar tashi saboda gani take kamar yin mu'amalarsa da mata ita zai sa ya tona asirin da take ta ɓoye wa saboda shi,tana matukar son RAIHAN bata jin akwai wani abu da take wa son da take wa RAIHAN,shi yasa take matukar tsoran rasa ta,har hakan yana neman taba mata ƙwaƙwalwa saboda matsawa kanta da tunani,yanzu kam tafara tunanin ko dai bodin school zata maida RAIHAN din , to amma da tayi shawara da Dr Sabo sai ya nuna mata cewa ta bari zuwa lokacin da zata gama jiniyo su ga abinda Allah zai yi,idan har lokacin ba su gane komai ba kawai sai su Kaita bodin school ɗin,da wannan ta samu ta hakura ,sai dai kuma ta kara kaimi da tsaurara matakan tsaronta akan RAIHAN din.
A hankali RAHIM (RAIHAN) ya fara fuskantar wasu abubuwa a tare da shi ,dole fa Rahim a matsayin shi na mace kuma musulmi wanda yake zuwa makarantar islamiya yana sanin addini yasan Meye jinsi,haka dole ne idan yana wayo yana shiga cikin mutane yasan komai dangane da banbancin jinsin mace da namiji, wannan dalilin ne yasa take kokarin nesanta shi da mutane ba iya mata ba har ma mazan,abu daya ta manta cewa Rahim yana zuwa islamiya kuma haziki ne shi din wajen karatu,da maida hankali akan duk wani abu mai muhimmanci.
Mamaki ne ya fara shiga kwakwalwarsa sai kuma tunanin sa ya fara kai kawo,ya za ayi yana matsayin namiji halittun jikin sa su dinga kamanceceniya da na mata,wayo da ilimin addini da ya ratsashi ne ya sa shi fara wannan tunanin.
Da fari so ya yi ya tambayi inna maimuna sai kuma ya fasa sakamakon tuna huɗubar Aunty da Ali da yaushe take gaya mishi duk abin da ya same shi ko ya kulle masa kai kar ya sake ya tunkari kowa sai ita,sam aunty bata ba shi damar fedewa wani samuwar shi ba bayan ita wannan ne yasa ya fasa tunkarar innar Bashir da maganar.
Wata ranar Litinin Anty amarya ta shiga makarantar su Rahim dan dauko shi,tana zuwa ta tarar da shi tsakiyar kawayen shi su ilham,yana ganin antyn na shi duk sai ya ruɗe yasan zata yi masa fada sosai tunda ta hana shi shiga cikin mutane irin haka,cikin sanyin jiki ya karaso bakin motar ya buɗe ya shiga yana yin ƙasa da kansa saboda mugun kallon da ya ga antyn na auna masa,ƙwafa tayi bayan ya shigo ya rufe motar,da gudu taja motar ranta a matukar ɓace,suna zuwa gida ko kallon shi ba ta yi ba ta wuce warta bedroom dinta,idanun sa ne suka kawo ruwa yana jin rashin daɗin kinjin maganar antyn da yake, sai dai kuma baya jin zai iya ci gaba da takurawa kansa ta hanyar hana rayuwarsa sakewa a cikin mutane akan dalilin da baisan shi ba,dakin sa ya nufa ya cire kayan sa kana ya shiga bathroom dan kimtsa jikinsa,tsayawa yayi jikin madubin da yayiwa bangon kawanya yana mai kallon kanshi,to Me yasa Ni nakasance a haka? Taba gashin kansa yayi wanda kullum ake cikin aske shi ,dan yau baifi kwana biyar da yi masa askin ba amma gashi har ya fara fitowa,me yasa komai nashi yake kama da na mata? Ya kuma yi wa kanshi tambayar da baisan amsar ta ba,da sanyin jiki yayi wanka tare da daura alwalar magriba,yana fitowa yayi saurin kimtsa wa cikin kayan sanyin shi na ko yaushe masu dan kauri da ɓoye halitta,fita yayi kai tsaye ya nufi dininng room da sauri saude me aiki ta zo ta fara zuba mishi abinci.
Abincin yake ci amma gaba daya hankalin shi na kan kofar bedroom din auntyn shi,haka dai cikin sanyin jiki ya gama cin abincin ,dai dai lokacin ne aka kira sallah magriba hakan ya sa shi miƙewa tare da ƙarasawa dinning sink ya kuskure bakin shi ,kana ya nufi ɗaki