Showing 78001 words to 81000 words out of 189984 words

Chapter 27 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

09 Nov 2024

16211

Raihan tayi da za ta iya fin ta Raihan din ma.........✍🏽


[12/21, 12:40]: *Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page26 ```






Dan numfasawa ya yi tare da kaucewa koridon da zai kai shi dakin aunty amarya, yana mai jin wani irin yanayi na tsananin tausayin lamra.




Duk wannan budurin da ake yi ,su mama murja da ya'yan su babu wanda ya sani ,saboda su a yanzu duk gaba daya hankalin su ya karkata akan yadda za su wawushe dukiyar da suke kira da tasu kuma hakkinsu.




CHIBADO's HAUSE........




Da kallo kawai Ammi ta bi Abbu ba tare da ta iya cewa komai akan bayanin da ya yi mata ba,tunani daya ne ya damu zuciyarta shine an hana yaron ta ya ji dadin rayuwa wanda kuma hakan yana da nasaba da auren zabinsa da aka hana shi yi.duk da cewa Abbu ya ce" zabin nashi aka ba shi yanzun amma hakan baisa ta ji gamsuwa ba,dan haka ta sha alwashin jin ta bakin wazir ɗin,kuma tasha alwashin indai dole aka kuma yi masa to kuwa ba zata yarda ba a karo na biyu a sake cusa masa Macen da ba ita ce zabin sa ba.




TSOHUWA........




Cikin fidda haki daga manyan kofofin hanci da bakinta,ta nuna dudu wanda ke durkushe a gabanta tamkar me sujjada,ta ce",jinin tsohuwa ya ce,dole sai an hada da makirci saboda hadarin da ke tattare da lamarin,mun kasa gano jinsi bare yare babu abin da muke gani sai duhu,saboda haka jini ba zai iya ganin komai ba,ya ce" sai mun hada da bincike ta hanyar mutane,yanzu dole ne mu bawa kanmu hutun zaman kogo saboda wannan dalili,kuma hakan shi zai bawa jini damar yin kyakkyawan bincike akan komai dake tunkaro mu",daga haka ta nuna su da wata doguwar sanda me kan maciji,cikin wani karamin lokaci hayaki me ban tsoro ya turnuke wajen baka ganin komai sai hayakin da ya zama tamkar gajimare acikin sa suka bace kowa ya san inda dare ya yi masa.
......


Haka nan aka ci gaba da biki,dama can babu ango ake yi,shi yasa ko da hakan ta faru ma babu abin da ya sauya,sai dai daga zuciyar amarya da kakarta harma da wadan da ba muyi zato ko tsammani ba sam babu zaman lafiya ko alkhairi a acikinta.




RAIHAN.............




Sosai ta dauki fushi da ko mai da kowa,wazir kuwa hatta da nombobin sa sai da ta yi delete dinsu,sai dai kuma duk abanza dan duk tana da su akanta,haka kuma tunanin abin da ya faru ya ki barin ƙwaƙwalwarta, sannan ta kasa sanin dalilin da yasa duk take jin hakan,dan tsaki ta yi tare da janyo wayarta ta ci gaba da aikin ta da ta mayar da shi gida a kwana biyun,sai dai tana yi tana kumbura fuska da kyarɓe baki tamkar wanda wazir din ke gabanta,kamar yadda Abbie bai sanar da goggo da aunty amarya ba haka itama babu wanda yasanar mata da halin da ake ciki,bakin rai ne dai ta ke ta yinsa tun ranar da abin ya faru,kuma har yanzu bata san cewa sace ta aka yi ba.




Bangaren Abba yahya ma bai sanar da inna maimuna komai ba,shiru ya yi da bakinsa tunda wannan sirrinsune na cikin gida,sai dai kuma a ransa ya kudurta taimakon ɗan uwannasa ta hanyar bincike a bangaren Alh Garba ur exsellency,dan ya lashi takobin cewa ba zai barshi ba duk ya bincika ya gano da sa hannunsa cikin wannan al'amari.


Niamey..........




Ba tare da jin komai ba,baba buzu ya sanar da kakar Raihan komai bai boye mata komai ba,kallon shi kawai take ciki da tsantsar razani da mamaki wanda ya kasa boyuwa daga kan kyakkyawar fuskarta da har tsufa bai buya ba,shurunta da zurfin da ta yi a tunani ne yasa har sai da ya dan zungureta,yana cewa fatsima lafiya dai ko?cikin dan daburcewa ta ce",babu komai mamaki da tuajjibi shine ya hanani Magana,to yanzu ina ita Raihan ɗin?
Amma dai ba yanzu za a ba shi ita ba ko?


A'a ba yanzu ba sai komai ya lafa,duk da ba zamu tsaya muce har sai mun binciko komai ba,tun da ba mu san ranar da gaskiyar zata bayyana ba,wacce gaskiyar?
Hajiyar agades ta kuma tambaya da alamun mamaki shima cikin mamakin nata ya ce" a'a to haka zamu zauna ba za mu nemi sanin makiyan da suke son kashe mana jika ba?da sauri ta girgiza kanta tana Murmushin da na kasa gane ko na meye,ta ce",ba haka nake nufi ba, wannan ma aikamar ya zama dole ne,sai dai kawai mu yi fatan Allah ya kare mu baki daya,Amin ya amsa yana kokarin barin dakin,amma dai ya kamata nima na leka su ko?


Juyowa ya yi daga kokarin fita da yake yana duban ta cikin yanayin mamakinta,yau kuma ke kike cewa zaki gidan ramla bayan kuma ke ce me kin zuwa kamar wata Yar fari a gareki?shafa gashinta da ya kwanta ta yi tana cewa ,to yanzu na ce ina bukatar zuwa ,kuma idan na je ba yanzu zan dawo ba,dan sai na gano ɓoyayyiyar makiyan Raihan,daga haka ita ta bar shi a dakin tsaye yana jin jina lamarinnata da a yanzu yake daure mishi kai.






CHIBADO's HAUSE........




Anyi biki an gama lafiya,zuciyoyin wasu babu dadi sai dai dannewa kawai da suke yi,haka nan basa bari a gane cewa suna cikin damuwar,a babban sashen sa dake cikin gidan ya ce",zai zauna dan haka nan aka kai amarya rubyy,duk da cewa ba ta so zaman gidan ba ,amma sai ta danne saboda ta hakanne kawai zata gane abin da ake kulla mata a cewarta.




Katsaham aunty amarya taga hajiyar agades,bata kuma shan mamaki ba sai da ta ganta da uban kaya,tana kuma fada mata cewa tazo ne ta danyi musu kwana biyu ta debewa Rahim kadaici,ta faɗa alokacin da take duban RAIHAN da wani kallo da na kasa tantance manufarsa,ai ga guri nan sai ki ta zama", Raihan din ta faɗa tana barin dakin bakin da aka kai hajiyar,dariya hajiyar agades ta yi tare da cewa idan ma dai baka so zuwa na ba kai ka sani zama daram tunda gidan ɗiyata ne.






Tunda Ruby ta tare bata sa wazir a idonta ba,abin da ya kuma daga mata hankali ke nan ya kuma tunzura zuciyarta akan yarinyar da aka aura masa,duk da cewa ta ji dadin ganin ba tare suka tare ba,to amma ba hakan yana nufin ta sakankance ba ne,dole ne ta tashi tsaye ta yi yaki da duk wata mace da ke son rabata da soyayyar wazir.


Har kwana biyu babu wazir a bangarenta,kai ba ta ma da tabbacin ya dawo nan sashen ko bai dawo ba,haka ne ya sa ta kanas ta dauki waya ta kai kararsa gurin innawuro,tsaki innawuro ta yi tana balbaleta da masifa,yanzu ke rabi kullum ina nuna miki hanyar jan aji da kama kai amma ba zaki dinga ganewa ba,to wallahi indai wannan halin za ki ci gaba da yiwa wazirin gida to kuwa ba zaki taba samun SOYAYYAR sa ba,Gara tun wuri ki kama kanki kinemi hanyar da kika san zai so ki cikin sauki da saukakawa,ba kuma na ce ba zan mishi magana ba ne,zan yi mishi amma dole ki gyara dabi,arki ta san zama mace mara kamun kai",daga haka ta kashe wayarta ta bar rabi da sake baki tana bin wayar da kallo,zuciyarta kuma cike da sake sake,wai me tsohuwar nan take nufi da Ni ne?ta tambayi kanta tana kallon wayar kamar innawuro zata bata amsa ta ciki,numfashi ta sauke tare da ajiye wayar tana fadin idan ma da wata manufa azuciyar ki zan yi maganin kune, dan tuni na fahimci jikokin da kike so tsakani da Allah.




A ranar innawuro sai da ta kasa ta tsare ta samu hanyar ganin wazir, duk da cewa ranta cike yake da takaicin rabi a din,amma haka ta daure ta yi wa wazir tass,daga bisani ta dawo nasiha da tuni akan hakkin da ya rataya akansa,wanda shine ya dan yi tasiri a zuciyarshi har yake jin zai iya hakura ya sauke duk hakkin rabi da ke kansa amma banda soyayyar sa.




Misalin karfe goma sha daya na daren ranar ,ya nufi bangaren rabi ,cikin kamalar shi da kyakkyawar shigar shi ta pijamas na kamfanin eshar, sai kamshin mayataccen turaren sa hemo arara ud,a hankali yake takawa kafafunsa na nutsewa cikin tattausan Grass Capet din da yayiwa corridon kawanya,ba tare da yasan wane daki rabi a take ciki ba,daga cikin jerin dakunan dake wajen kamar na hotel zuciyar shi dai kawai ta canka mishi wanda zai shiga,sai kuma ya yi sa,a a nan din rubby take,zumbur ta mike daga wayar da take yi,jikinta har rawa yake saboda shigowar sa babu zato ko tsammani,duk da cewa kuwa ya yi sallama to amma sam bata ji ba saboda nisan da ta yi a wayarta,wanda ga dukkan alamu tana bata farinciki.




Cikin rawar baki ta ce" da shi sannu da shigowa Hamma wazir,yauwa ya amsa a saman leban shi da yanayinshi na kamewa,kallon da take yi mishi ne yasa ta fahimci ya amsa,kiyi alwala kizo nan,ya kuma fada yana dan zama saman resttin chare guda daya dake dakin ba musu ta shige toilet din sai dai kuma zuciyarta bugu take a maimakon tayi farinciki,sam bata yi tsammanin zuwan sa a wannan lokaci ba,kai ba ta mayi tunanin cewa innawuro zata mishi magana ba,haka nan ta yi alwala ta fito jikin ta babu kwari.




Bayan sun idar da sallah ya kama kanta ya yi mata addu'a Sannan ya yi mata yan tambayoyi akan addinin ta,wasu ta amsa wasu kuwa sai inda inda da zare ido,rabuwa ya yi da ita kawai ya shayar da ita madara,daga nan ya umarce ta da hawa saman gadon ta.




Komai nashi a nutse yake yin sa kuma amutunce,wanda hakan yasa tuni rabi a ta manta da yar faragabar da ke zuciyarta,ta manta da wa take ta shiga maida masa martani da wani zazzafan salo da nuna zalama da doki a gare ta.




Duk da cewa wazir yana injoyin abun amma Saida hakan ya haifar masa da mamaki,me ya kai budurwa yar Fulani yin irin wannan zumudin a darenta na farko?,bai bari tunanin ya yi tsawo ba ya kau da shi tare da yin addu'ar kusantuwa da iyali.




Cak ya tsaya da yin komai,hatta tunanin shi tsayawa ya yi,runtse idanun sa ya yi da ya ji suna masa wani yaji yaji,haka makoshin sa lokaci daya ya bushe,wani irin takaici da bakin ciki ya gauraye dan ragowar fariincikinshi,a hankali ya ture ta da ga jikinshi ya tashi cikin nutsuwa kayan shi ya maida ya ɗaure ,kana ya tashi daga gadon kai tsaye ya nufi kofa,zuba mishi ido rabi a ta yi tana mai kasa cewa komai,domin jin kwarjinin shi ta yi ya hana ta yi mishi karya,tana kallo ya fita daga dakin ba tare da ta iya kwakkwaran motsi ba,sai da ya fita ta saka kuka tana jin nadamar abin da ta aikata ,wata kila da yanzu ta samu soyayyar wazir ta silar mutumcinta.




Shaya ya sakarwa kansa ko zai samu salama daga radadin da zuciyarsa ke yi,duk irin yadda ya kama mutuncin sa amma Saida Allah ya jarabce shi da auren mazinaciya,shi din mutum ne me tsananin kyankyami shi yasa yake matukar kyamar zina harma da me yinta,shi ko tarin abokai irin makusantan nan baida saboda kar ya yi mu'amala da mazinaci,sai gashi yau ya kusanci mazinaciya,duk da cewa ba son rabi ya ke ba amma dole ne ya ji ta kaici da kishi akan ta,ko dan matsayin da ta taka na amsa sunan 'yar uwarsa,duk da yasan cewa matan yanzu basu da tabbas amma yana da yakinin cewa ba duka ne iri daya ba,akwai na banza akwai na gari shi yasa bai taba sako rabi a jerin wadan nan matan ba sai kuma gashi ta baka mamaki,sai kawai ya ji zuciyar shi na rawa akan ko wace irin mace.




Tsaf ya fito cikin shirin sa na office,as usual cikin ash din cot wadda ta yi matukar amsar fatarsa me matukar sheƙi,sumar nan tasa kamar me saboda sheƙi da kwanciya.


Da sauri rabi a da zuwa yanzu ta samu nutsuwar yi masa magana,ta tare shi da gaisuwa sai dai ta kasa haɗa ido da shi kamar yadda ta saba yi masa,sai dai shi da ya kafe ta da idanunsa masu matukar tasiri da hukunta me lefi cikin sauki.hakan ya sa ta shiga kame kame duk abin da ta haɗa dan fada masa take suka tarwatse ko mai ya kama hanyar sa,hakuri kawai ta samu kanta da iya furtawa,bai ce mata komai ba sai gewaye ta da ya yi ya fita cikin kamewarsa,


Yana fitowa ya samu Samir securityn sa yana zaman jira,da sauri ya bude masa mota ya shiga, shi kuma ya shiga driver sit yaja motar da gudu suka fice daga tan kamemen gate din.






Cikin nutsuwa ya lalubo lamban wayar Raihan,saida ta yi ringing wajen sau biyar sannan yaji sassanyan muryarta me cike da wani salon shagwabar da yake halittarta,lumshe idanunsa ya yi yana mai sakin wata sirrintaccenyar a jiyar zuciya,ina kwana ta faɗa tana tura baki ba dan ta so ba,sai dan kawai raina na gaba da ita ba tarbiyyar ta ba ce,lafiya ya amsa shima a takaice ,kafin ya ɗora da cewa ki fito office muna wajen gate",zaro ido ta yi tana kallon wayar da ya katse mata ,kan bala amma wannan mutumin ya raina min wayo",dole ta ta shi ta fito dama a shirye take tsaf.




Hajiyar agades da ke tsaye tana sauraron ta,ta ce"mutum dai ya dinga kiyaye harshen sa dan kar ya je ya aikata zunubi ba tare da ya sani ba",wai me matar nan ke nufi ne?tunda ta dawo gidan nan take min wasu maganganu marasa kai",ta faɗa lokacin da ta samu aunty amarya a falo dan yi mata sallama,kafin aunty amarya ta bata amsa Abbie da yake shigowa ya riga ta amsa wa Raihan da cewa,wasa ne take miki tare da nasihar zaman Duniya irin nasu na manya da suka ga jiya suka ga yau".




Tura baki ta yi ta fice daga falon tana daga musu hannu.




Bude motar ta yi ta shiga tana faman ciccin magani, acewarta ta gaida shi dan haka ba za ta kara gaida shi ba.




Har suka fara tafiya babu wanda ya tanka,ita ce ma take jin haushin shurun nashi ,ga kuma haushinsa akan auren da ya yi ba tare da saninta ba sai hakan ya kuma tunzura zuciyar ta,gani ta yi ya kuma yin wani kyau sai take ganin duk dan ya yi aure ne,ji ta yi kwalla ta cika idanunta har tana shirin zubowa,zuciyar ta kuwa ita kadai tasan halin da take ciki,idan baya kusa da ita tunaninta ya kan sassauta,yayin da tiririn zuciyarta da yadda abin ya ke toshe numfashinta duk yake bata mamaki a duk lokacin da ta tunashi da aurensa da kuma yawan matan dake sonshi,shi yasa ta dauki niyyar bashi iska na yanke haduwarsu ko ta samu ta manta da abinda yake damunta wanda satan hakan a bu ne mai matukar wuya,manta cewa wazir yana da aure.




Duk wani motsinta da tunanunta ta yi ne tare da bugawar zuciyarshi,ko me nata akan idanunshi da zuciyarshi ne,yana da yakinin cewa ko motsi Raihan ta yi sai ya ga ne abin da take nufi bare kuma damuwarta,tsaf ya fahimci dalilin fushinta akansa,wanda dama can faruwar hakan yake tsoro shi yasa ya yi kokarin kaucewa hakan.




Karasowarsu ma bata sani ba tana can tana fama da numfashinta da take ta kokawa da shi,jin sassanyan tafin hannunsa saman nata hannun shi yasa ta juyowa ta dube shi cikin yanayin karaya da sarewa..........jan hannun ta ya yi suka fita daga motar,


Mai makon ya rabu da ita ta tafi office dinta kamar yadda ta saba sai kawai ya cigaba da tafiya da ita zuwa office dinsa binsa kawai take cikin bunjuma bunjuman kayanta na maza...................✍🏽
[12/21, 12:40]: *Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page27 ```




Ganin inda suka nufa yasa ta ɗan dakilewa amma kallon da ya sakar mata shi yasa ta binshi ba tare da ta shiryawa hakan ba.hannu kawai yake dagawa ma'aikatansa da suke ta miko gaisuwa harma da masu yi masa Allah ya sanya alkhairi sakamakon rashin haduwa da shi ranar daurin auren.




Suna zuwa kofar office din sakateria tazo ta bude masa tana faman zabga masa sannu da zuwa cikin rawar jiki,duk halin da Raihan ke ciki hakan bai hanata zabgawa sakataria harara ba,suna shiga sakataria ta rike baki cikin alhini da mamaki ta ce,"anya kuwa wannan Rahim ɗin ba dan daudu ba ne? Cikin sauri ta rufe bakinta tana mai leka hanya dan samun tabbacin babu wanda yaji ta.




Suna shiga tacigaba da kokarin kwace hannunta,hakan bai samu ba saima janyo ta da ya yi gaba dayanta suna fuskantar juna,me ta yi miki kike harararta?taji tambayar kamar daga sama,tura baki ta yi tana mai kauda fuskar da ta fahimci so yake ya saka shu'uman idanunsa a ciki. dallin bakinta ya yi yana cewa zan yi maganin bakin nan",a hankali ya kuma matsawa daf da ita kamar wanda ake ja,wanda shi kansa bai san ya akayi ya samu kan shi da hade jikin shi da nata ba yana cewa me yasa kike haka? Me a kayi miki?ya fada yana kokarin cusa fuskarsa cikin wuyanta dake fidda wani Ni imtaccen kamshi,kokarin ture shi ta fara yi idanunta na cika da kwalla,dakyar ta iya buɗe baki ta ce",hamma me ye hakan bana so babu kyau",a hankali ya ɗago kanshi ya dan zuba mata ido kafin kuma ya saketa yana nufar wajen zamansa,kije ki yi aikin ki amma nan da awa biyu ki dawo za mu tafi",ya fada tamkar ba shi ya gama shin shine ta ba yanzu fuskar nan a kame kamar koda yaushe. cikin sanyin jiki ta fita daga office din wanda har ta fita tana jin yadda idanunsa suke kanta duk da cewa idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login