Showing 102001 words to 105000 words out of 189984 words

Chapter 35 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

09 Nov 2024

16209

son sani ba.




Wani kiran ya shigo,tambayar da wannan bawan Allah ya yi tayi matukar girgizasu,ya kashe kuma ba tare da ya fadi ko da sunansa ba.


Abinda yake tambaya shine ,ur exsellency munji a majiya me karfi cewa,dukiyarka da mulkin da kake kai duk ba naka bane,kana yin komai ne da bazar dukiyar amininka Alh Muhammad nuur shin gaskiya ne ko ba gaskiya ba?




Da sauri Raihan ta tari numfashin ur exsellency dake kokarin yin magana cikin wani irin sagewar gwiwa da zuciya,ta ce",malam ka sauka daga kan layi ba maganar dukiya ko pravency din ur exsellency aka ce ka tambaya ba, wannan abinda ya shafe shi shida ahlinsa ne dan haka bamu karbi wannan tambayar ba,daga haka ta ɗora da cewa duka duka a nan ne muka kawo karshen wannan tattaunawa tare da gwamnan yanzu wato Alhji Garba me fata,a cikin dandalinmu na siyasarmu a yau,Ni da nake gabatarwa Rahim Muhammad nuur Aliy .tare da abokin aikina,se ta bawa wazer damar magana ya dora da cewa AHMED WAZEER CHIBAƊO.




Tunda ya baro gidan tv ya fara nemo lambar amininshi sai dai bai samu ba,hakan yasa ya hakura da kudirin dole anjima yayi fitar sirri dan ganawa da amininnashi.




Ki biyo NI office wazer ya fadawa Raihan lokacin da yake wuceta dan hayewa lipter.




Ƙasa_ƙasa take ƙunƙuninta,haka ta bishi ta na faman cuna baki,akan idanun rabi komai ya faru duk da cewa bata ji abinda yace da Raihan ɗin ba,ji ta yi bazata iya jura ba hakan yasa ta bi bayansu ba tare da su sun lura da ita ba.




Har zata shiga sai kuma ta dakata,tasan halinsa sarai zai iya dizgata agaban yaronnan kuma tajawa secteriya wadda bata san ma ta shigo main office din wazer din ba,hakan yasa ta ɗan saka kanta ta kafar key ko zata iya ganin wani abu sai dai ina kofar ba irin ko wace kofa ce da ta sani ba,dan kofa ce me security babu ta yadda za ai na waje ya jiyo Muryar na ciki sai dai na ciki zai iya jiyo Muryar na waje,saboda tsoran kar ya fito ya same ta yasa ta hakura ta juya ranta a matukar ɓace.




Tana shiga office ɗinta ta samu suryy wanda hakan ba karamin dad'i ya yi mata ba,janta Surry ta yi acewarta Gara su tafi can gida saboda maganar da zasu yi bata nan ba ce.




Suna shiga office ɗin ya juyo yana hasketa da wannan idanun nashi masu kama da me jin bacci,kif_kifta nata idanun ta shiga yi saboda yadda nasa ya yi mata ƙarfi,bata san yaushe har ya ƙaraso gabanta ba ,sai din hucin numfashinsa ta yi a fuskarta ,dan firgita ta yi zata ja baya ,cikin wani zafin nama wanda yake tafe da wani irin salo yasa dogayen hannayensa ya tarota,sai ga fiskarta daf da tashi jikinsu na neman hadewa da na juna,waro manyan idanunta tayi zata yi magana sai me wani irin ɗumi da zaki zaki taji ya sauka saman harshenta,mukut ta haɗiye wani kakkauran miyau ba tare da ta shirya ba,bata iya tantance komai ba ta ji wazer ya ci gaba da juya harshensa cikin bakinta cikin wani irin salo da gwanancewa,komai na wazer da ban yake kamar yadda yake,shi kansa sumbar tasa ta dabance a kuma gurin mace ta daban a rayuwarshi.




RUBY.....




Har sun shiga mota,sai kuma ta fara kokarin fita,da sauri suryy ta riketa tana cewa ina kuma zaki Hajiya? Cikin bakin cikin da ya kasa barinta idanunta har wani ƙankancewa suke saboda bala'i ta ce",suryy bazan iya tafiya ba, wallahi bazan iya ba ya za ai na tafi banga fitowar wannan tsinannan yaron ba,anya kuwa suryy ba neman juna wazer yake da yaronnan ba? Da sauri sury ta toshe mata baki tana cewa ke wace irin macece ruby so kike aikin mu ya lalace? To tun wuri ki kama bakinki kuma komawarki bata da wani amfani maganar da za muyi nida ke yafi abinda kike shirin yi tunda duk maganar kusan daya ce.dakyar ta samu ta lallasheta suka ja motar suka tafi.






RAIHAN kuwa rasa inda zata yi da numfashinta ta yi saboda yadda yake sama da kasa yana gauraya da numfashin wazer da suke fitarwa a tare,dogayen hannayensa yasa ya tallafo kugunta a hankali ya ƙarasa hadeta da jikinsa ba tare da ya bar abinda yake yin ba.


Shi kansa mamakin kansa ya shiga yi, baisan wane irin maganaɗisu Raihan ke tare da shi ba,sam ji yake yana kasa sarrafa kansa da tunaninsa akanta,to meye hakan wai? Wace irin macece ita din da yake jin ta daban da sauran mata? Me yasa ko mai nata yake ganinsa na musamman,bai taba yin kiss da wata mace ba amma ji yake kamar ba za a taba samun ɗadin harshe da baki kamar na Raihan ba,ita din fa tabbas ta musamman ce...


Ƙarar wayarshi da baya fita sosai shine ya ƙwaci Raihan,duk da cewa shi a gareshi ba wani dalili ba ne hasalima ba zai dau wayar ba,a hankali ya ƙarasa kujerar shi cikin takunshi dake kara bada tabbacin cewa shi ɗin fa namijin gaske ne.zama ya yi fuskar nan ɗif kamar ba shi ya gama tsottse bakin yar mutane ba.


RAIHAN kuwa na samu ta kubuta sai ta fara lalubar hanyar gudu,gam taji kofar a rufe wanda yasa ta tsayawa tana kallon kofar ba tare da ta juyo ta kalli inda yake ba bare kuma ta tanka.


Yi ya yi kamar baisan dalilin tsayuwartata ba,Saida ya gama hada tarkacenshi sannan ya nufota,da sauri ta rintse idanunta a tunanin ta irin na dazun zai kuma maimaitawa,ji ta yi yasa key ya bude kofar kana a hankali ta ji muryarsa yana cewa idan kin gama tsayuwar ki same Ni a mota",da sauri ta bude idanunta alokaci daya kuma tana bin bayanshi da dan gudunta,babu abinda take a ranta sai mita,shi wai wannan mutumin baya jin damuwa akan wannan halaiyan nashi? tab gaskiya wannan matarshi zata gane kurenta,au ashe fa Nima matarsa ce, ta faɗa tana da dafe bakinta, dan tabe fuska ta yi kamar da wani take zancan ta kuma cewa ai Ni matar wucin gadi ce haka Abbie ya fada daga haka ta karawa sawunta mai dan kokarin taddashi........✍🏽


[12/21, 12:40] : *Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page36 ```






Wannan tambaya da mutumin nan ya yiwa ur exsellency ta yi matukar jawo hankalin mutane da sanya cece kuce a cikin jama'a .




A ranar dai ur exsellency bai samu ganawa da amininnashi ba kamar yadda yaso.sai dai ya kwana da wata irin damuwa da jin kunya wanda bai taba shiga irinsa ba,hatta da iyalansa kasa fita ko ina su kai.kowa ya yi jugum jugum cike da tunanin ta inda maganar ta fito.su iyalansa ma gani suke sharri ne tunda su kansu basu taba sanin ko mai akan hakan ba,babban dansa Yusuf ne kawai ya sani wanda yake rike da daya daga cikin comfanonin Raihan ɗin,sai kuma lauyansa.



_________




A bangaren rabi a kuwa suna zuwa gida,ko zama ba su yi ba rabi a ta ce", Surry gaya min abinda za ki gaya min saboda hankalina ya kwanta",


Ganin yadda rabi a ta birkice yasa sury jin shakkar sanar da ita wata magana yanzu hakan ya sa ta yi tunanin dabarar da za ta yi mata yanzu.


Kamo hannunta ta yi suka zauna, sannan ta ce", haba ruby me yasa kike son kidinga acting like wata mahaukaciya? Dole fa sai kina sarrafa tunanin ki akan wannan bukata taki,idan baki sawa kanki nutsuwa ba kina tunanin za mu samu mu nemi mafita akan matsalarki,"ganin kamar ta dan fara samun kan rubyn yasa ta yi saurin bude jakarta ta fiddo wasu kwalabe guda uku,mika mata ta yi tana cewa karbi wannan ki sha zaki samu nutsuwa ", zubawa kwalaben ido ruby ta yi ba tare da ta karba ba,karbi mana ruby ba sai na gaya miki ko menene ba ai",dubanta ta dauke daga kan kwalaben ta maida kan sury kana ta ce",sury kin san dai duk iskancina bana shan wadannan kayan ko?da sauri suryy ta amsa da cewa na sani amma ki sani cewa yanzu lokacin amfaninsu yazo a wajenki, wannan da kike gani su kadai ne zasu baki damar aiwatar da duk abinda kike son aiwatarwa akan wadda ta ke kokarin raba ki da farincikinki wadda ta raba tsakanin zuciyarki data wazeer,rabi'a dole ne ki koyi mu amala da waɗannan kayan domin sune zasu dinga doraki akan saiti koda bana kusa,kuma wannan da kike gani su zasu kawo miki nutsuwa yayin da kika fuskanci gaskiyar abinda nake son sanar dake,domin kuwa jinta ba tare da kin shirya ba babban hadari ne,dan haka Ni ba zan sanar da ke komai ba idan har baki sha Wadannan maganinba.




Tana gama fadar haka ta ajiye mata kwalaben kan cinyarta ta dauki jakarta ta rataya,idan kin canja shawara sai ki kirani ", binta da kallo ruby ta yi bata iya cewa komai ba har Surry ta fice,dawo da dubanta kan kwalaben ta yi tana jin zuciyarta na wani irin luguden fargaba akan labarin da sury take shirin bata, tabbas ya kamata tasan abinda tazo da shi.


Sai kuma tunaninta ya koma kan maganganun sury akan magungunan,kamar fa gaskiya take fada ,ta faɗa tana juya kwalba daya a hannunta,zan gwada amma fa idan har naji abinda ta faɗa ba haka bane to zan bari da zarar ta sanar da Ni abinda take son sanar dani din,har za ta fara sha sai kuma ta tuna ba lallai sury ta yadda cewa ta sha ba,dan haka zata bari zuwa safiya sai ta kirata ta zo tasha agabanta sannan ta sanar da ita labarin.




_________________


Lokacin da Raihan ta shiga falon Abbie samunsa ta yi shida Abba yahya da aunty amarya suna tattaunawa akan abinda ya farun,waya ce a hannunshi yana ta neman wayar ur exsellency ya kasa samunsa da alama dai kashewa ya yi ko kuma matsalar network,itama take sai jikinta ya yi sanyi abun ya kuma dawo mata,zama ta yi gefan Abbie tana musu sannu da gida, Abbie dan Allah kayi hakuri nasan damuwar ur exsellency damuwarka ce amma dan Allah kayi haƙuri,kaga bamu amsa tambayar ba duk da cewa mun san bata da wani tushe bare makama,ta yaya za a ce dukiyar ur exsellency ta ka ce ko ma taka ce su me ye ruwansu ba tsakaninku ne ba", Abba yahya ne ya dakatar da ita da cewa shike nan Rahim ta shi kaje ka huta Allah ya kiyaye gaba", Tom ta faɗa tana tashi jikinta a sanyaye idanunta akan Abbie da take ganin kamar fushi yake yi da ita,aunty amarya ce ta tashi taja hannunta suka fita,ita kanta aunty amarya mamaki da ne cike fal akanta da kuma tunanin hakan zata iya kasancewa,to amma me yasa bata sani ba ? Bata da wannan amsa hakan yasa ta ture tunanin taka Raihan dan bata abinci da rarrashinta saboda yadda taga dukiya damu da yanayin Abbien nata.




_____________




Shi kuwa wazir dama babu wanda ya yi masa maganar tunda babu wannan fuskar,ko abban rabi a baiyi masa hirar ba,amma dai kowa ya ga tattaunawar tunda live aka nuna haka sun tattauna maganar a tsakaninsu.






_________


Take sauran gidajen jaridu suka fara yada karya da gaskiya, wasu har cewa suke ur exsellency ya amsa tambayar nan.




Hankalin Abbie ba karamin tashi yayi ba da ganin wannan abu,take zuciyarshi ta tafi tunani da nemo ta inda maganar nan ta fita,so yake ya fita ya hadu da ur exsellency amma hakan ya gagara domin tun jiya da abin ya faru kofar gidansa cike yake da manema labarai yan jarida da sauran yan bani na iya,kowa so yake ya ji ta bakinsa.


RAIHAN kuwa da kyar ta samu hanyar fita saboda yadda kofar gidannasu ya koma.




Mama murja da momi Hanne basu san lokacin da wannan masifar ta sa suka kuma hadewa ba,tuni suka manta da komai,ko wacce ta manta da zargin da takewa yar uwarta sun koma jajen ashe abinda suke yi wa ma baya kusa da su,tunaninsu ya fara juyawa ta yadda zasu karbi komai daga hannun ur exsellency,burinsu da damuwarsu ta kuma yawa saboda yawan dukiyar da suke hangowa ta wuce misali.




____________




*Ogan suryy*


Wani irin duka ya kaiwa teburin gabansa idanunsa har shudi suke saboda tsananin ɓacin rai da damuwa,yaransa gaba daya sunkuyar da kawunansu su kayi umarninsa kawai suke jira.




Hannu yasa ya kuma gyara fuskar da yasa kafin ya fara magana cikin wata irin murya wadda kana ji kasan cewa mamallakinta yana cikin damuwa me tsanani ya ce", duk wannan bulayin da nake yi ashe na banza ne,idan haka ne kuwa tabbas ya jawa amininshi dan ko da zan yawo tsirara saina gabayan duk wani wanda yasan da dukiyar nan ko kuma take hannunsa wallahi babu wanda zan kyale dole na samu abinda zuciyata ke muradi kudi nake so ko ta wace hanya dan haka zan kwato dukiya ko ta wace hanyaaaa.ya fada da wani irin ƙaraji wanda ke bayyana kwadayinsa da burinsa akan bukatar tasa.






Sintiri take tana kaiwa tana kawowa idan ta yi kamar zata zauna sai ta kasa ji take kamar ta aikata komai ya wuce burinta ya tabbata,me yasa sai a lokacin da take ganin komai nata ya kusa kammala sannan wannan mummunan labarin ya baiyana? zuciyarta da idaniyarta babu abinda ta jima tana son gani sai mushen Raihan da ubanta,to sai kuma ga wani mummunan labarin da yake ta yawo yake zagaye jahar tasu,hakan fa yana nufin sai ta karo makaman yaki,hakan yana nufin ta samu kishiya akan burinta domin ta tabbatar da cewa shi kansa ur exsellency ɗin da nasa target din,babu wanda zai yadda yaga samu da rashi,yasan cewa ur exsellency likimo yayiwa amininsa ta yadda sai ya gama yadda dashi zai yi masa me gaba daya,to amma ita ta yaya za ta yi ta karbi dukiyar daga hannun ur exsellency? Karbar dukiyar nan a hannunsa fa tamkar yankan tiikintin mutuwa ne saboda wahalarsa.




Duk wanda zai karbi wannan dukiya to sai ya taka matakai masu tarin yawa kafin ya cimma gaci.




Wani irin numfashi ta aje me tsananin zafi da huci,tana mai birkita gashinta kanta idanunta kuwa tamkar garwashi saboda ja.


Lissafo dan abinda ƙwaƙwalwarta ta hasasho mata ta fara yi.




Dole fa sai nasan wasu sirrika akan dukiyar,ta wace hanya ke nan?


Dole sai ta samu kusanci da ur exsellency,ta wace hanya ke nan?


Dole sai na san adadin campanin nasan ma'aikatan da suke aiki a karkashin Company's,to ta yaya?




Wata irin zabura ta yi zuciyarta na cewa ki nemi wanda yayi test din tambayar nan,dan shine zai share miki duk wata tantance,to ta yaya?


Sam bata yi tunanin neman abokin cin mushenta ba saboda ganinta babu wani abu da zai iya tunda har ita yake neman gagararta.


Ji ta yi kanta ya fara juyawa kawai sai ta lalubo kwalbarta ta tuttula a bakinta domin hakan shi ne mafita akan zarewar da take son yi.






Kokarin fita take yi hamma idi da ya kawota yayi saurin rike hannunta ,fuskarshi cike da damuwa ya ce", RAHIM ka kwantar da hankalinka Abbie da ba fushi yake da kai ba kamar yadda kake zato,kawai dai abunne yake damunshi kuma har yanzu bai samu hanyar ganawa da ur exsellency ba kin ga dale ya damu,nasan tunanin shi bai wuce yadda ur exsellency zai dau maganar ba wata ƙil ma yayi zaton Abbie ne ya fitar da maganar tunda yasan shi kadai yasan abinda suka binne a tsakaninsu", zame hannunta ta yi tana share kwallar damuwar da suka fara sakko mata,bata iya cewa komai ba ta sa hannu ta bude kofar ta fita.binta yayi da kallo zuciyarsa cike da tausayin kanin nashi.




Tun daga saman office dinsa yake hangota,tun daga yanayin tafiyarta ya ganewa cewa tana cikin damuwa,sai kuma yaga tana share fuska.




Neman layinta ya fara yi bayan ya dawo cikin office din, ringing daya ta dauka miryarta a sanyaye ta yi masa sallama,cikin dakiyarshi ya amsa mata kana ya dora da bata umarnin zuwa office dinsa.dan bin wayar da kallo ta yi kafin ta canja akalar ta zuwa inda Lipter take.




A can bangaren ur exsellency kuwa,shiga yayi ta badda kama ya nufi gidan amininshi,dakyar ya samu hanyar shiga saboda har yau din yan jarida ba su bar zuwa kofar gidan Alh Muhammad nuur ba.




Abbie yana ganinshi ya gane shi,kai tsaye suka nufi can karamin falonsa da yafi ganawar sirri a cikinsa,dukkansu duban juna su kayi na tsawon wasu sakanni kafin suja numfashi a tare, Abbie ne ya fara magana da cewa bansan abinda zance da kai ba wallahi kunyar haɗa ido nake da kai, sannan bansan ta ina zan kare kaina daga irin zargin da nasan cewa zaka yi min ba",amma da fari ina mai baka hakuri tare da kara jaddada maka amanar dake tsakaninmu wall........da sauri ur exsellency ya katseshi ta hanyar dakatar da shi da cewa yi shiru dan Allah Nura,ranshi a ɓace ya ci gaba da cewa ban taba tunanin za yi irin wannan tunanin akaina ba,karfa ka manta cewa bani ne na nemi ka dinga tara dukiyar Raihan a hannuna ba, sannan bani ne na baka shawarar na riketa na dinga juyawa ba,sai dai nasan na baka shawara akan cewa ka dinga juya mata a maimakon ajiyar da kake yi kamar yadda kake ajewa sauran yaranka,domin ba a san me gobe za ta yi ba kuma ba mu san irin albarkar da zasu yi ba,daga Ni har kai bamu san gaibu ba dan haka ba musan zaka samu Raihan ba,har daga karshe Allah ya baka ita ba tare da kasancewa itan ba ce,to yanzu duk a nan me ye laifinka ko laifina da har zaka yi tunanin zan zargeka akan wannan abu? Wallahi Nura ban taba tunanin cewa zaka yi min ko abinda bai kai wannan ba bare kuma wannan,dan haka ka kwantar da hankalinka,Ni yanzu tashin hankalina daya ne", zuba masa ido abbie yayi yana jiran abinda zaice gefe daya kuma na zuciyarshi suna kara kauna da ganin kimar amininnashi.




Ur exsellency ya ce", Raihan ita ce tashin hankali na,nasan cewa tunda har aka san cewa dukiyarta na hannuna to kuwa tabbas a na gab da fasa kwan cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login