Showing 186001 words to 189000 words out of 189984 words

Chapter 63 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

09 Nov 2024

16212

duniyarsa ta riga ta mallakeshi ba tare da boka ko malam ba.




Soyayya suke zubawa kamar babu gobe ,babu abinda suke kallo sai junansu,komai tare suke yi har girki tayata yake idan tace ya bari sai yace Raihan wannan koyarwa ce ta Ma'aiki ya kasance yana taya matansa aikace aikacen gida dan haka ki bari Nima na samu ladan", da haka yake kashe mata baki,tana wankewa yana mata dauraya ko yana yanka mata wani abu.




Raihan Sarkin tsafta kullum sai ta yiwa gidanta tsafta ta musamman wadda ko da zata yi kwana biyu bata taɓa shi ba ba zai canja ba, wannan horone ta samu daga maminta sam bata hori Raihan da san jiki da nuna gata da so mara amfani ba,kar dai ku manta tun tana namijinta a haka maminta take sa ta aiyuka da girke girke har Hajiya goggo ta yi ta fada akan ta maida Rahim namiji,shi yasa a yanzu mami take bacci har da minshari saboda tasan ta nunawa yarta karshen gata ta bata horon da sam ba zata bata kunya ba, wannan kenan.




Yau Litinin ranar da tai daidai da cikar Raihan da wazer sati daya da tarewa,kuma ita ce ranar da za a saurari shari'ar su Abba yahya da hamma Idris.




Tun sassafe mutane su kayi dandazon cika kotun sabida ma kar wani ya rasa wajen ganin idanun alkali da irin hukuncin da za a zartar musu.




A bangaren RAIHAN tunda ta tashi take shiri cikin sauri ta yi ta gama komai saboda zuwa cotu,duba agogo ta yi bayan ta gama shiryawa cikin wata exclusive atamfa me shegen kyau tayi daurin zara Buhari ,kamshinta kuwa tuni ya isarwa wazer dake baccinsa hankali kwance.




Fita ta yi daga dakin da ta shirya zuwa dakin da suka kwana,taku take tamkar wata dawisu kamshin kabbasa da na turarukan da take amfani da su kuwa babu magana fuskarnan sai sheki take tana glowing kamar ka kalli kanka a cikinta,turus ta yi ganinsa da tayi kwance dan a tunaninta tuni ya tashi saboda yau guduwa ta yi ta shirya ita kadai idan ba haka ba shiririta zasu yi ta yi wajen shirin har a tashi a Shari'ar,kugu ta rike tana cika baki da iska kafin ta tako cikin nutsuwa tazo daidai kansa ta zauna,hannunsa ta fara kamawa kafin ta shiga yi masa massege a hannun,ganin yaki motsawa sai kawai ta sauko kasan gadon tare da rankwafawa ta hade bakinta da nashi tana tsotsa,caraf ya cafke jin ya farka yasa ta fara kokarin zare bakinta amma ina hakan ya gagara dan ɗan gidan Ammi ya ce", bai san zancen ba", tarairayota yayi jikinshi ya ja duvet yana cewa yauwa yar albarka kamar kinsan bannkoshi ba", zaro ido ta yi kafin ta kwace bakinta cikin marairaice fuska ta hade hannayenta biyu alamun roko ta ce", pls hayatnur kaga fa na shirya kaima ka tashi ka shirya kar a gama Shari'a ",waya ce miki zan bari ki shiga cikin maza eye? Ya fada yana ci gaba da bata sumba da kisses ta ko ina ba tasamu damar amsa masa ba,ko nace bai bata dama ba ya shiga bata zazzafan kissess masu rikita kwanya dole yar gidan Abbie ta yi gum saima taimaka masa da ta shiga yi dan ya samu nutsuwa,yadda Raihan ke tafi da mijinta a shimfida abin ba acewa komai duk wani salo da ya koya mata sai ta fishi kwarewa duk abinda ta fuskanci yafi so shi take yi masa, daga nan labarin ya sauya wannan sirrinsune Raihan ta rufe min kofa dole na hakura na fito.




Sai da suka gama shiryawa Raihan ta daga kai ta dubi agogo take ta kwabe fuska tare da neman guri ta zauna dan tasan zancen zuwa kotu ta tashi daga aiki kamar yadda ya fada.




Zama yayi kusa da ita yana cire mata tagumi tare da cewa bari na kunna miki kigani ", daukar remote control yayi ya kunna ƙatuwar plazima da ta kusan cinye rabin bangon.




A can bangaren kotu kuwa, anyankewa abba Yahya daurin rai da rai shida dansa,shi kuma Idris anyanke masa shekaru biyar tare da tara ta miliyan biyu ba tare da beli ba,inna maimuna kuma anyanke mata zaman kaso na shekara ashirin da biyar tare da tarar miliyan uku ba tare da beli ba.




Take kotu ta tashi jama a kowa ya yi shiri kamar yadda suka shirya,ana fitowa da su Abba yahya dan shiga mota ai sai jin saukar ruwan duwatsu su kayi akansu,duk yadda jam'i an tsaro suka so hanawa abin ya faskara barkonon tsohuwa da harbi kuwa babu abinda ya yi musu,inna maimuna ma da Idris sai da suka samu rabonsu,da dai jami'an tsaro suka ga suma abin yana shafarsu sai kawai suka bawa mutane waje suka ci gaba da jifan Abba yahya da Bashir,inna maimuna da Idris dai sun bari an shiga dasu mota,yadda su kayiwa Abba yahya da Bashir abin babu kyan gani tuni ido ɗaya ya cire na Abba yahya Bashir kuwa karaya fuskarsu ko ganuwa ba tayi saboda yadda ta ɓaci da jini faca faca ( dama ai abinda ka shuka shi zaka girba)




Rabi a kuwa tuni ta faki idon mama ta fita daga gidan dan zuwa gidan wazer isar da sakon zuciyarta?


To ko wazer zai karbeta ?😂




Fatima y adam..... ✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page70 ```




Kawar da kanta daga kallon ta yi lokacin da ya kunna saboda daidai lokacin da ake jifansu Abba yahya ne,shi dinma runtse idanunshi yayi cike da alhini da tausayin yadda karshensu yazo,kashewa yayi yana matsawa jikiinta Kamota ya yi tare da tara hannunshi akasan habarta saboda yadda hawayenta suka fara gudu, sorry my friend addu'a zaki musu Allah ya sassauta musu amma banda kuka", jinjina kai ta yi tana shigewa jikinshi,ehem Madam garama da baki je ba Kinga anjima sai muje gida muyiwa su Hajiya goggo jaje ko? Da sauri ta daga kanta cike da murna ta bashi kyakkyawar sumba a kuncinshi sannan ta sakeshi ta mike da sauri ta bar falon,Binta da kallo yayi kafin a hankali ya lumshe idanunsa da basa gajiya da kallonta.




Dakyar aka samu aka dakatar da jama'a sannan aka kwashe su ba tare da tunanin zuwa asibiti ba,kai tsaye gidan yarin aka nufa dasu wanda sai acanne aka basu gado a sashen asibitin gidan,ba dan a na zaton musu rayuwa ba.




Jama a suna kokarin fashewa sai ga tsohuwa me jini ƙatuwar mesarnan ta kawota cikin tsakiyar mutane dan su kara rage haushinsu,kai abun babu kyan gani gaba daya ta dagargaje amma dake Allah yana son nuna izna sai yabarta da ranta duk da yadda ta koma din yaci ace ta mutu inda ana dawowa ma to yaci ta mutu sau goma ta dawo,numfashin da take fitarwa shi kansa wani irin hucin zafi yake yi,gaba daya fatar jikinta ta kwaile gashi babu kafa babu hannuwa gaba daya mesar nan ta cinyesu,idanunta kuwa ras sai fuskar da ta yagalgale tayi wani irin rashin kyan kallo.




Har mutane zasu fara guduwa sai suka ji wata mata tana cewa wannan fa ita ce annamimiyar tsohuwa me jini da ake kaimata sassan jikin yayanku dan haka itama ku karasata ko kwa kara rage radadi ", aiko take mutane suka fara yi mata ruwan dutsuna wani dutsen ma yafi karfin hannuwansu amma haka suke dauka su jefa mata,tuni su Dady da Salim wakilan tashar Chibado FM suka fara kwasar labarai harma da sauran yan jaridu masu jiran kiris.




Kafin kace me tuni an dagargaje kan tsohuwa yayi kwatsa_kwatsa a gurin tamkar an saka shi a turmi an daka,(kai Allah Ubangiji kasa mu dace ka shirya mu kasa muyi kyakkyawan karshe Amin ya rabbil alamin 🙏)a hankali mesar nan ta juya ta silale tabar cikin mutanen bayan ta tabbata tsohuwa tayi irin mutuwar da take ganin ita ce ta dace da ita(wannan mesar daya daga cikin jinnun da tsohuwa ta cutar ne ta hanyar korarsu daga tsibirinsu ta gaje shi ita da mukarrabanta ne,ba iya mutane kadai mutanen nan suka dau hakki ba harda jinsin da ba namu ba bayin Allah da ba ruwansu da kowa rauhanai).






Wannan abu da ya faru tuni ya kuma baza garin baki daya har da wasu garuruwan ma abinka da social media,sosai mutane suka ji tsoron Allah akan abinda ya farun dan kuwa abu ne da bai taba faruwa ba ko a labari shi yasa ya zama izna da tsoratarwa ga masu son zuciya masu ragowar imani wadanda basu riga sunyi zurfi ba kuma wadanda suke da rabon shiryuwa,to Allah ya kara shirya mu damu da zuriarmu baki ɗaya.




___________




Yana nan zaune tunda RAIHAN ta gudu, laptop ce kawai a gabanshi yana posting din wani labari akan shafinsu na tree full y truest,danjar dake nuna cewa da bako a waje ce ta kama haskawa, ɗan dafe goshinsa yayi tare da juyawa yana kallon kofar kafin ya janyo remote din security cord din kofar ya latsa saiga shi wanda ke wajen ya samu damar shigowa ,bai damu da sanin ko waye ba dan ya riga da yasan cewa dole yanzu zasu dinga baki a kai akai.




Rabi a da take ta kallonsa tare da gidan gaba ɗaya ta fara takowa tana ji kamar ta rungumeshi tayi ta kuka a jikinshi,wani irin kyau taga yayi na musamman kalarnan tashi me kyau ta kuma haskawa yayi yar kiba wadda tasashi yin dan tumbin da ya yi matukar yi masa kyau, lafiyayyan gemunannashi sai kyalli yake tare da dan siririn sajenshi da Raihan bata gajiya da gyara masashi,ji yayi gaba daya ya takura saboda alamun ido da yaji a jikinshi,hakan yasashi dan Dagowa fuskarnan a kame wato dai asalin kamammen wazer miskilin nan dan gidan Ammi jikan innawuro ba wai wazer mijin Raihan bawan Raihan ba.




Ai tuni rabi a ta zame kasa kafafunta har rawa suke yi bakinta kuwa tuni ya shiga karkarwa.




Meye ya kawoki ?




Haɗe hannunta ta yi bakinta na rawa idanunta na zubar hawaye ta ce", dan Allah dan kaunarka da Ma'aiki dan girman zatin Allah hamma wazer ka dubeni ka maida Ni dakina wallahi na yi karatun ta nutsu na sauya halina zan gyara duka kuskurena dan Allah ka maidani kaji",


Dama kina da daki a nanne?


A'a amma ko canne gida zan cigaba da zama",




To bani da wannan ikon",




Kuka ta saka tana ci gaba da yi masa magiya.




Rabi'a",


Ya kira sunanta wanda yayi daidai da fara takun RAIHAN daga saukowa downstairs,




Duk da yadda sunan ya daki zuciya da ƙwaƙwalwarta hakan bai hanata ci gaba da takunta cikin nutsuwa da burgewa ba,




Wata halitta ce ta musamman a gareshi me tsananin ado da kawatarwa, ɓoyayyiyar Raihan ce hakan yasa duk sanda ta yi ado da wani abu sabo na mata sai ta kusa zaunta bawan Allah dan Ammi da Abbu,shi kam zai iya cewa bai taba sanin da akwai halittar da kananun kaya suke yiwa kyau fiye da kowace mace a duniya ba sai yanzu da RAIHAN dinshi ta sako,me yasa kome ta saka sai yaji kamar ba a taba saka irinshi a duniya ba?




Kasa ci gaba da jurar zama yayi dan haka ya mike tsaye idanunshi na cigaba da karade lungu da sako na jikiinta da kallo,sanye take cikin wata karamar riga me haɗe da bra hannunta dogone amma kalarshi kalar fatar jikiinta ne hakan yasa baza ka tantance ba har sai ka taba,jikin rigar kuwa dack brown ne wato copy,sai wandon da ya kasance kalar jikiinta shima amma Dan gajere ne kuma ya kamata dan haka sai tayi kamar bata saka komai ba,gashinta kuwa wani irin ado tayi masa daga gaban goshin sai yayi wani irin kwanciya tsagar ta fito rada rada,sai ta raba shi biyu tayi masa two baby's ta kuma kitseshi daga karshen jelar ta saka masa karamin rebom baby pink,sai ta zama kamar irin yaran Larabawannan masu waka,lip balm ta saka shima baby Pink,Masha Allah tubarakallah karshen kyau matar Ahmad wazer tayi shi.




Jiran karasowarta yake amma sai yaga kamar ma komawa baya take yi,sai kawai ya shiga takawa dan tarota,falon kuwa tuni kamshinta da nasa ya zauna a ciki daram ga kuma wanda ake yi na turaren wuta wanda shima ya zauna Kamar a lokacin ake yinsa,fuskarta babu yabo babu fallasa suka hade da wazer da yaje tarota,basarwa ta yi cikin wani aji da bata taba sanin tana da shi ba ta bude baki tare da cewa hayatnur wac....bai bata damar karasawa ba ya haɗe bakinsu guri daya ya shiga maida mugun yawuun da ta tsinka masashi yake tafiya babu doka bare oda,


Zaro ido ta yi tana son nuna mishi akwai baki fa a falon,amma ina shi tuni yayi nisa dan har ga Allah ya manta da wata Rabia a gurin,sosai raihan din ta tafi da imaninshi ta riga ta gama tashin kansa tuni komai ya kwance masa",




Rabi a kuwa sunkuyar da kanta ta yi tana share hawayenta,bata taɓa tunanin wazer zai iya yiwa mace irin wannan soyayyar ba sai gashi ta ji ta kuma gani da idanunta,duk da cewa zuciyarta ta karaya amma sai taji ta kasa tafiya wata zuciyar ta ce ki kama kafa da Raihan ɗin wata kila ya amince,take ta ɗan samu kwarin gwiwa da wannan shawarar da zuciyarta ta bata.




Dakyar RAIHAN ta dakatar da babynnata daga kokarin zarcewa da yake dan har ya fara cusa hannunsa cikin rigarta yana ƙoƙarin yi mata aika aika gaban idon baƙi.




Tsaf ya haɗe fuskarnan ya kuma dinketa tamkar bashi ya gama tsotse Raihan ɗin gabanta ba,sai da suka dawo cikin falon sosai sannan ta tabbatar da rabi an ce ba wai jin kunne ta yi ba,fuskarta ta saki cikin murmushin karfin hali ta ce", aunty rabi a ce sannu da zuwa",




Sai a lokacin rabi a ta kuma samun kwarin gwiwa,dan haka ta dan muskuta tana cewa nice Raihan ya gida da amarci?wazer ta kalla tana dan kashe masa ido ɗaya tare da langabar da kai wai ya bawa Rabia amsa ita kunya take ji", bai kalli rabi ar ba sai dai hankalinshi gaba daya yana kan Raihan fuskarnan tashi babu fara a ko digo dan baiyarda wata mace taga fara arshi ba bayan RAIHAN.


Bari a akawo miki abin tabawa",


A'a ki barshi a koshe nake",




Kawai dai kice bazakici girkin yara ba", Raihan ta fada har yanzu da murmushi akan fuskarta,girgiza kai rabi a ta yi sananan ta yi gyaran murya tare da marairaice ta ta ce", Raihan ko zaki tayani bawa hamma wazer hakuri akan ya maida Ni dakina dan tuni na riga na tuba bazan kuma bari shedan ya yi min kida ba",


Ɗan jim Raihan tayi(kar ku manta Raihan bata san wazer ya saki rabi a ba)duk da cewa ita kadai tasan yadda zuciyarta ke kida to amma ba ta bari rabi a ta gane ba (ta koyi darasi tun lokacin da Rabia ta dinga yi mata wulakanci da karya akan wazer saboda nuna mata kishinta a fili da ta yi)


Rabia wannan maganar tsakaninku ce ba tawa ba ce, saboda aurenki ba a hannuna yake ba a hannunsa yake", ta karasa fada tana kokarin mikewa dan basu waje,kamar ya fahimci abinda take shirinyi dan haka ya yi saurin rike hannunta tare da girgiza mata kai alamar kar ta tafi", duban rabi a r ta yi sannan ta dubeshi ta bude baki zata yi magana ya janyota ta wado jikinshi yasa hannunshi yayi mata rumfa yadda ko hangota baka iya yi a cikin faffadan ƙirjinshi.


Zaki iya tafiya saboda ina da bukatar privency ",




Ya fada fuskarnan kai kace bai taba yin murmushi ba,nan ko idan ya samu guri da yar raihananshi harda su dariya.




Dan Allah hamma wazer kayi hakuri", ta kuma fada cike da nuna naci irin na mata marasa aji.


Kije zanzo gidan",


Ai tuni RAIHAN ta yi wata irin zabura zata tashi, take kuma ta tuna cewa har yanzu fa rabi'a matarshice,komawa ta yi ta kwantar da kanta yayin da ya shiga sara mata ƙirjinta kuwa tuni ya kasa jura ya fara yin sama da kasa tamkar numfashinta zai fizge,sosai take kokarin danne azababban kishin da Allah yayi mata mai tsananin zafi,to amma kamar hakan gagararta yake son yi.




Ita ko rabi'a cikin jin dadin maganarshi da bata yi zato ba ta mike tana cewa shike nan ina jiranka Allah ya kawoka," bai kulata ba bare ta sa ran samun amsa daga bakinshi.




Tana fita ya dago fuskar RAIHAN wadda yaji ta shiru ta daina mutsu_mutsun da take yi.




RAIHAN ",


RAIHAN",


Ya shiga kiran sunanta a dan ruden da ba a cika ganewa akan fuskarshi ba,a haka baza ka taba tunanin cewa a tsananin tashin hankali yake ba,amma shi kadai yasan irin gudun fanfalakin da zuciyar take yi saboda ganin idanun Raihan a kafe numfashinta kamar ya tsaya.


Kwantar da ita yayi ya nufi karamin Fringe dake falon ya dauki ruwa ya dawo,shafa mata yayi a fuskarta cikin kankanin lokaci taja wani irin dogon numfashi idanunta suna dai-daituwa akan fuskarshi.




Me ya faru?


Me ya same ki lokaci guda haka?


Babu ta fada tana tashi zaune tare da kawar da fuskarta,dan dube dube ta shiga yi wanda hakan yasa ya harbo jirginta,ey yasan Raihan tun can tana da kishi amma bai yi zaton abun ya kai ga haka ba,juyo da fuskarta saitinsa ya yi sannan ya haɗesu har karan hancinsu na gugar juna,a hankali kuma cikin nutsuwarnan tasa ya ce", me ne kike haka Raihan? Suma fa kikayi saboda kishi? To yanzu da ace ban saki rabi a ba ya za ayi ke nan? Da ace ƙaddara ta ratsa miki zama da kishiya yake nan? Pls Raihan ki sassauta saboda bamu san inda kaddararmu zata tsaya ba, bamu san abinda gobe zata yi ba,dan haka Kinga bamu da tabbacin zamu yi rayuwa iya mu biyu har abada,Ni a lissafina babu batun zama da mace biyu amma ban san ya gobe zata kasance ba,shi yasa ba zan miki alƙawarin zama dake ke daya ba duk son da nake miki kuwa,domin idan nayi haka tabbas na cutar dake."


Kuka take yi kasa kasa,tabbas maganganunsa haka suke kuma shine daidai akan duk namijin da yasan kansa ya kuma san ƙaddara yasan cewa tsarin rayuwarmu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login