Showing 3001 words to 6000 words out of 189984 words
Chapter 2 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
yayi kwari dole ko wacce ta aje komai ta fara shirin tunkarar abinda ke gabanta, goggo kuwa kallon su kawai take babu wanda zai ce ga ainahin abinda ke boye cikin zuciyarta,saboda gaba dayansu tattalinsu ta shiga yi da ririta su,har zuwa lokacin haihuwar murja.
Kamar wancan lokacin yauma dukan su suna harabar dakin da murja ke yin lebou,sai dai a maimakon murja da maimuna, yau hanne ce da maimuna,dan duk da tsohon cikinta kasa zama ta yi a gida ta jira haihuwar.
To alhdlllh murja dai ta sauka lafiya kuma ta haifo santalelen yaron ta namiji me kama da goggo Rahma,dake murja ta danfi hanne wayo sai bata nuna tashin hankalin ta gaban surukanta da mijinta da kishiyarta harma da faccalarta ba,hannu biyu ta sa ta karbi yaronta tayi masa addu ,haka Alhaji Muhammad nurr shima bai nuna komai ba dama kuma babu komai a zuciyarsa ,yayiwa Allah godiya da ya bashi zuri'a yana kuma fatan su zama shiryayyu a cikin al'umma.
Yaro ya ci sunan mahaifin murja ,wato Musa ,suna kiranshi Affan.
Bayan wata daya da haihuwar murja ,hanne ta sake santalo yaronta namiji daga nan kuma kowacce ta fara kokarin boye abinda ke ranta,ta rungumi yaranta.
Daga nan kuma haihuwa ta buɗe a gidan ,murja ta sake samun namiji ya ci suna idris....
Maimuna ce dai har yanzu shuru tun daga haihuwar Bashir.
Bayan shekara hudu,
A yanzu ko wacce tana da yara uku,bayan idris murja ta kuma samun rufa i,hanne kuma ta samu jamilu,har yanzu dai kowacce ta ɓoye tashin hankalin ta na rashin samun RAIHAN,sai dai abin da sauki tunda ko wacce tana ganin yar uwarta bata samu ba,dan haka suke tunanin hada kai dan samowa kansu mafita , duk da cewa ba su bude wa junsan su sirrin juna ba, goggo ma dai yanzu hankalinta a kwance yake ,duk da cewa ita macece da baka isa gane gabanta ko bayanta ba.
Maimuna da mijinta Yahya suma sun rungumi kaddarar su ta rashin yara masu yawa,yanzu dama bata da matsala da goggo tunda dai ta haifa ko kuma ta ce arzikin Muhammad nuurr da ya taka na mijinta sau babu adadi ya sa ta samu sassauci
Ta bangaren Muhammad nurr kuwa tuni ya fauwalawa Allah komai,duk da cewa har yanzu bai cire ransa daga samun RAIHAN ba,dukiyar sa kuwa da yanzu fin rabi ta zama ta RAIHAN tuni take karuwa,kamfanunuwan RAIHAN da sheres dinta sai bunkasa suke ,su dai matansa na ganin ikon Allah,duk da cewa kullum zuciyarsu cike take da fargabar samun RAIHAN.
Yara tuni sun tasa sun zama samari,makaranta suke yi masu tsada na yayan manya kamar yadda suma suke ya'yan manya.
Kwatsam kuma sai idanun Alhaji nurr ya yi gamo da SOYAYYA,wadda bai taba fadawa cikin ta ba,bai ma san ya ake yinta ba,tunda duk matan shi ba aba shi damar zaba da kanshi ba.
A can yawon shi na zaga kamfanin RAIHAN,wanda ke cikin wani kauye dake can gabas da agadex,ya haɗu da Ramlatu ne a wajen kamfanin RAIHAN wanda take kai wa ma'aikatan cukyi suna siya su bata kudinta ta koma cikin kauyen su,ranar da ya fara ganin ta yace shima yana son cukui ta kawo masa da yawa zai siya,haka kuwa akayi ta kawo masa ya siya ya bata kudinta ,harma da kari ,saidai kuma tana irgawa ta cire masa kudinsa ta hade nata tayi gida ba tare da ko waiwaye ba.
Tun daga wannan rana Muhammad nurr ya rikice da neman Ramlatu da SOYAYYAr ta ,bai kasa a gwiwa ba har sai da ya samu soyayya daga Ramlatu,har kauyen su ta kai nurr wajen mahaifinta cikakken buzu me matuƙar kirki da dattijon taka ,haka mahaifiyarta mace me kirki da sanin ya kamata wadda kusan duk ɗabi unsu ne hakan,su biyu kacal iyayen su suka haifa daga yayan ta sai ita,wanda shi yanzu yana can cikin garin yamai da matar shi, da ɗan shi guda daya yana aikin gadi a wani gidan babban mutum me suna Alhaji Abubakar matawalle,iyayen Ramla sun yaba da Muhammad nurr,dan haka kai tsaye Baba buzu ya sa yayan Ramla ya bincika mishi asalin Alhaji Muhammad nurr.
Tabbas ba ƙaramin tsoro ne ya kama Baba buzu ba,lokacin da ya samu labarin waye Alhaji Muhammad nurr,dan haka ya ce shi sam ba zai ba shi yar sa ba,ba kuma wai dan bai yadda da tarbiyyar sa ba ne ,a'a kawai saboda yana tsoran sharrin kudi da tsoran kai kan su inda Allah bai kai su ba,hankalin Alhaji muhammad nurr ba ƙaramin ta shi yayi ba,ko a gida sai da suka fuskanci cewa yana cikin tsananin tashin hankali,daga abun ya gagare shi ,sai kawai ya sanar da Baffa,kai tsaye Baffa ya ce" da sai musu tiket su tafi can agades ɗin.
Cikin ikon Allah Baffa ya shawo kan mahaifin Ramla har ya amince da batun auren,daga nan ba su dawo ba sai da Baffa ya bada sadakin Ramlatu,aka tsaida Ranar daurin Aure.
Baffa ne da kansa ya tara su murja ya sanar da su maganar auren ,take fa suka shiga tashin hankali harma da koke_koke,ita dai goggo tasa albarka bayan hakan babu wani abu da ya biyo baya,saima shirye shiryen bikin da ta shiga yi gadan gadan,a cewar ta dole itama ta farantawa nurr kamar yadda ya faranta mata ya auri zabinta ba tare da musu ko gardama ba.
Duk yadda su Hanne suka so a fasa auren nan saboda shige shigen bokaye da su kayi hakan bata samu ba, Allah ya rubuta cewa Ramla matar muhammad nurr ce
Tofa makaranta ya kuka ji abin ,muje zuwa muji shin za a samu RAIHAN ko dai mafarkin Muhammad nurr ba zai tabbata ba,
Idan an same ta wace cakwakiya za a tafka,
A cikin matan Alh muhammad nurr guda uku wace zata haifa masa sanyin idaniyar sa RAIHAN?
Hmmmm wasan da har yanzu bai soma ba ku dai ku biyo NI. Asannu dan jin salon da wannan labari yake dauke dashi.
Fatima y Adam✍🏽
Typing
💕*BOYAYYIYAR
*FATIMA Y. ADAM*💕
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page2 ```
An ɗaura aure ankawo amarya Ramlatu, cikin gidan ta a matsayin mata ta uku ga Alhaji Muhammad nurr.
Hannu biyu goggo ta karbi surukarta fuskarta cike da farincikin samun kyakkyawar buzuwa cikin ahalinta,Baffa da Abba yahya ma cike da soyayya suka karbi Ramla,sai dai a ɓangaren su Hanne a bin ba haka yake ba,dan kiri_kiri suka nuna rashin amincewarsu a kan amanar Ramla da aka ba su,to shi dai ango ba ta su yake ba ,dan haka cike da farinciki ya haɗa kan su ya yi musu nasiha daga nan ya ja matar sa suka wuce sashen sa.
Ramla macece mai tsananin hakuri da kawar da kai,shi yasa taci ribar zaman gidan aure, saboda duk irin cin kashin da su murja suke mata bata taɓa daga kai ta kalle su ba,bare a kai ga tankawa,da wannan suka gaji su ka rabu da ita ,harma da ganin shekaru kusan biyu ko batan wata bata taɓa yi ba,sai suke ganin kamar bin malaman da suke ne ya ba su wannan nasarar,dan haka suka kwantar da hankulan su acewar su sun dinke bakin matsalar su,sai kuma hankoron neman yadda za suyi dukiyar RAIHAN ta zama ta ya'yan su, wannan ke nan.
A bangaren maimuna kuwa sosai take kaunar ramla,dan sai da Abba yahya ya zauna da ita yaja mata kunne ya yi mata nasiha a lokacin da aka kawo ramla,to dake dama ita don ba mai tashin hankali ba ce sai ta karbi nasihun mijinnata da hannu bibbiyu, wannan yana daga cikin abin da yasa su murja kuma tsanar ramla,dan acewar su ba komai suke kullawa ita da maimuna ba sai munafunci.
A bangaren goggo ma sam bata da matsala da Ramla ,saboda tana yi mata tsananin biyayya,shi yasa bata taɓa tsangwamarta ba,duk da cewa goggo tana da fada da rashin hakuri a wasu lokutan,amma bata taɓa yiwa Ramla ba,haka Baffa tsakanin sa da ita girmamawa ce,ta ɗauke shi tamkar mahaifinta, Abba yahya ma bashi da wata damuwa da ita tsakanin su girmama ce da mutunta juna.
Haka wajen mijinta ta samu kyakkyawar shaidar zama mata ta gari yar aljanna, Alhaji Muhammad nurr yana matukar son Ramla da girmama duk wani abu da yazo daga gareta....
A bangaren burin Alhaji Muhammad nurr kuwa babu abinda ya ragu, sai ma karuwa da yayi , a kullum mutane kallon mahaukaci suke masa akan wannan gaibun burin nasa,dan a halin yanzu duk wasu kamfanunuwa da gidajen mai da shaguna sun koma sunan RAIHAN,duk abinda ka ga Ba a maida shi sunan RAIHAN ba to shine nasa ,amma kafin ka je kamfanin da ba sunan RAIHAN ba guda daya sai ka je wanda sunan ta yake kusan guda biyar, wannan al'amari shine yake kuma tunzura zuciyar matan sa,kai harma da ƴaƴan sa da suka fara zama samari,hudubar iyayen su na tasiri a zukatan su.
**********
A hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya ta yadda wasu ke so da kuma sabanin yadda wasu ke so,yau shekarar Ramla uku cur a gidan Alhaji Muhammad nurr,wanda yayi daidai da bayyanar cikin da wbabu wanda yasan da shi harma ita kanta mai cikin,tashin hankali wanda ba a saka masa rana shi ne ya baiyana kan fuskoki da zukatan matan Alhaji Muhammad nurr,lokacin da Alhaji Mohammed nurr ya kai ta a sibiti Dan a duba lafiyar cikin da me cikin,a nan aka tabbatar masa da cewa ciki dai ya kai wata shida harma yana shirin shiga na bakwai,al'amarin da ya kuma gigita su murja ke nan,take suka shiga fadi ta shin neman salwantar da cikin,a bangaren goggo da Baffa kuwa kai harma da maimuna da Abba yahya wata kulawa ta musamman suka shiga bawa Ramla, uban gayya kuwa ai ba a magana ,ji yake tamkar ba a taba haifa masa ɗa ba,ji yake da abinda Ramla zata haifa ko da kuwa ɗa namiji ne,duk da cewa a zuciyar shi da jikin shi ji yake kamar lokacin zuwan RAIHAN ne yayi.
Ramla tana sane da burin mijinta akan samun RAIHAN sai dai a kullum nuna masa take yi,ya nemi zabin Allah a dukkan ya'yan da za a haifa masa,bata taɓa kwallafa rai akan haihuwar mace ba,sai dai kuma tana taya mijinta fata da neman zabin Allah akan samun RAIHAN,ko ga ita ko ga abokan zamanta,bata taɓa kwaɗayin dukiyar da ta kasance ta abinda har yau ba asame shi ba.
Duk irin abinda su murja suke dan ciki ya zube ,abun ya ci tura dan kuwa ciki dai ya kai lokacin haihuwa ba tare da wata matsala ta faru da shi ba.
Wata ranar juma a ,da asuba Ramla ta tashi da azababbiyar nakuda,cikin sauri Alhaji nurr ya taso goggo suka nufi asibiti.
Tunda suka je ake abu daya haihuwa taki zuwa,har ta kai ga cewa Ramla ta jigata ko da hannunta bata iya dagawa,tana yi tana tsayawa har zuwa lokacin tafiya masallaci,Baffa da Abba yahya da Alhaji nurr suka tafi masallaci suka bar murja da hanne sai kuma noss ɗin dake kula da Ramla.
Kamar daga sama Ramla ta fara jiyo maganganu ta bayan window dakin da take labou,wani irin gumin tashin hankali da wahala ne ya fara tsatstsafo mata,yayin da a wani gefe ta yi tsam da ranta tana son gano Muryar da ke son halaka abinda take shirin haifa ɗin.
Ina so ki tsaya agurin, ko da aiki za ayi mata nasan cewa kina gurin dan haka ,da kin tabbatar da cewa mace ta haifa ,ki san yadda zaki ki kashe ta,idan kika ga uwar zata kawo miki matsala ki hada har ita,Ni kuma zan cika miki ragowar kudin ki ,idan kuma namiji ta haifa ki rabu da su kuma na bar miki kuɗin da na baki duniya da lahira,"Muryar noss ɗin ta ɗora da cewa kar ki damu zan yi miki abinda kike so ba tare da an samu wata matsala ba,yauwa maza ki tafi kisa dukan idanun ki a dukan motsin su" daga haka Ramla ta ji ɗif, alamun sun bar wajen dan sun kawo karshen maganar su.
Duk da yadda take jin jiki amma saida tayi kokarin tashi ta ɗaga labulen window,wai ko Allah zai sa ta ga fuskar matar da take son raba ta da rayuwarta,sai dai ina kafin tayi wannan zafin naman tuni matar tabar shiyar gaba ɗaya,komawa tayi ragwaf zuciyarta na mai dukan tara_tara,take ta fara addu'a akan Allah ya bata ɗa namiji abinda bata taɓa yi ba arayuwata zabar jinsin da take so Allah ya bata, cikin kankanin lokaci naƙuda ta dawo sabuwa,a daidai lokacin kuma likita ya shigo dakin shi da wannan nass ɗin ,da sauri ya ƙaraso inda take yana balbale nass ɗin da faɗa,ai Ramla bata san sanda ta kamo hannun likitan ba,wanda ya kasance likitan su na family, cikin azabar da take ji ta ce" dan Allah likita Ina son magana da kai"shi kadai ya ji abinda ta ce,duban nass ɗin yayi ya ce" je ki wajen Dr alasan ki karbo min sako" dan jim ta yi saboda tasan wajen Dr alasan ɗin a kwai nisa ,ita kuma awannan lukacin bata son abinda zaiyi nisa da ita daga dakin nan,amma babu yadda ta iya haka ta tafi ba dan ranta ya so ba,likita duba ka tabbatar babu kowa a ta waje da window dakin nan,maganar da zanyi da kai tana da matukar muhimmanci" cewar Ramla ke nan tana mai cije labbanta wanda har sun fara fitar da jini,baiyi mata musu ba ya je ya duba ko ina ya tabbatar babu kowa,kana ya zo ya sanar da ita.
Cikin irin azabar da take sha ta dube shi,kana ta fara magana a hankali,ta ce" likita don Allah ka taimake Ni ba danni ba ,dan Allah da kuma halaccin Alhaji nurr a gareka"ina jin ki fadi abin da kike so indai bai fi karfina ba kuma bai sabawa Allah ba zanyi miki shi ko dan halaccin mijinki a gareni kamar yadda kika faɗa",Dr so ake a kashe ni nida abinda zan haifa indai ya kasance mace ne"cikin razana da mamakin maganar ta ya ce" kamar ya? A gurguje kuma yadda zai fahimta ta sanar da shi abin da kunnuwanta suka jiye mata,numfashi yaja me cike da takaici ,duk da cewa yasan komai akan batun RAIHAN da kadarorinta amma bai taba tunanin cewa za a iya kashe rai a kan hakan ba' ya ce" to amma Ramlah me zai hana mu sanar da Alhaji Mohammed nurr tunda kince baki san matar ba likitar ma baki gane ta ba,bare mu neme ta a binciko matar,wanda nasan tabbas daya daga cikin kishiyoyin ki ne" girgiza kanta ta yi idanun ta na zubda hawaye ta ce" Dr alasan kar mu sanar da Alhaji sanar da shi ɗin yana nufin abubuwa da yawa ,da ace ma na gane ko su waye shi ne za mu sanar da shi,to amma yanzu hakan ba ƙaramin hatsari ne a tare da mu b.... Maganar ta tsaya saboda wata irin murdawa da marar ta tayi, subhanallah sannu yanzu muyi kokarin cire abinda yake cikin ki idan yaso sai muyi abinda ya da ce"da sauri ta dakatar da shi da cewa a'a Dr dole a cikin wannan lokaci nake son ka samar min mafita,duk da cewa bani da tabbacin macen zan haifa amma ya kamata na samu mafita" yanzu me ya kamata muyi ke nan? Ya faɗa cike da ɗan zurfafa tunani,Muryar Lamra ta katse shi da cewa, idan na haifi mace ka dauke min ita ka yi nesa da ita na baka amana har zuwa lokacin da zan nemeta",a'a Ramla ba za ayi haka ba mu dai nemi wata mafitar,amma raba ki da abinda kika haifa ba shi zai kawo maslaha ba,dole abinda kika haifa ya ji duminki ki kuma shayar da shi a matsayin ki na uwa ya rayu dake cikin farinciki"to likita ya kake so nayi? Ta faɗa cikin rishin kuka da karaya harma da sallamawa.
Idan kika haifi mace zamu ce namiji kika haifa a haka zata yi rayuwa a matsayin namiji ba mace ba, wannan shine kawai dabarar mu dan tseratar da rayuwar RAIHAN"zuba mishi ido Ramla ta yi kafin ta ce" ta yaya za ayi haka? Bayan kasan cewa halitta zata nuna kuma Ni ban isa hana mutane daukar RAIHAN ba, bare na ɓoye ta na hana daukarta,ban isa kuma na ɓoye halittar ta ta ɗiya mace ba"Dr Sabo ya yi dan jim kafin ya numfasa da cewa na sani ba wani lokaci hakan zai dauka ba,za muyi haka ne kawai na iya lokacin da zamu gano wannan mata wanda kuma a yanzu na tabbata cewa ba ita ka dai ce ba,zata iya yiwuwa a kwai wasu a can ta gefe waɗan da ba su bayyana kan su ba" duk da haka Dr Sabo dole a kwai kalubale a cikin wannan shirin" wajen minti ɗaya Dr ya dauka yana dogon tunani kafin ya dubi Ramla ya ce" Ramla akwai mafita akan ɓoye halittar matantaka sai dai ban sani ba ko zaki yadda da hakan? Cike da mamaki Ramla ta ce" ta yaya ne za a iya ɓoye halittar Mutum ba tare da wani ya gane ba? Amsa ya bata da cewa Ramla kin san cewa komai ya samu ci gaba a duniyar nan,barin ma a kasashen mu na waje,a kwai wani Dr eka a kasar Kuwait ya taba sanar da ni cewa an kirkiri wani abu mai siffar jikin namiji wanda manna shi kawai ake kuma na yara jarirai,sai dai kuma su sunyi abun ne ba da wata manufa ba sai dan wata cuta da ta bayyana a ƙasar ta lalacewar gaban yara maza to sai suka kirkiri abin saboda shi ake saka musu dan daidaita gaban na su da yi masa kariya daga daukar cutar harya warke sannan a cire musu,to ina ga muma zamu iya amfani da wannan abun mu siyo shi mu sakawa RAIHAN iya na lokacin da zata fara wayo wanda babu mai iya ganin tsiraicinta saike mahaifiyarta". numfashin wahala Ramla ta ja sannan ta ce" amma Dr Sabo kana ganin ba mu ɓata a cikin wannan lamari ba? Bamu ɓata ba,Ramla saboda kariya ce muka nemarwa abinda zaki haifa indai ya kasance mace"shi fa abin roba ne manna mata kawai zaki yi amma babu wanda zai gane cewa