Showing 12001 words to 15000 words out of 189984 words

Chapter 5 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

09 Nov 2024

16208

business account,burin sa ya yi aiki irin na mahaifin sa,to gashi yanzu daga dawowarsa ya fara aiki da sabon gidan rediyon da mahaifin sa ya gina musamman saboda shi,ɓangare biyu yake dauka,yana daukar bangaren binciken yan siyasa da zakulo manyan matsaltsalin da muke fama da su musamman akan siyasar manyan mu da yadda ake gudanar da ita,sai kuma ɓangaren nishaɗin masoya da yake gabatar wa a kowa ce ranar juma a da misalin karfe takwas na dare.


Duk da matsayin da yake kai bai hana shi gabatar da shirin ba,a cewar sa bai samu wanda zai iya gabatar da shirin yadda ya kamata ba.




Jajircewa da kamanta gaskiya yasa matsayin sa dagawa yaje har inda bai zata ba,sunan da mahaifinsa ya yi sai ya zamana ba komai ba ne akan yadda nasa ya yi,daukaka dai daga Allah ne to su dai Allah ya basu dan babu in da sunan AHMAD WAZIR CHIBADO bai kewaya ba.




Innawuro macece fasifaffiya sai dai tana da mutunci ga san kyauta,amma fa idan ta ce bata son abu sai dai ka bita da yadda take so,sai abin da ta faɗa ta kuma tsara ,saboda ya'yan ta suna matukar yi mata biyayya ,shi yasa hatta da jikokinta suke mata biyayya bata daukar wargi ko kadan,tana matukar son Ahmad
Wazir tamkar tayi masa numfashi haka shima yake sonta da son faranta mata,sosai yake mata biyayya kamar ita ce ta tsuguna ta haife shi,shi yasa ma gaba daya ya yi kaura zuwa sashen ta ,ko mai yake so tana yi masa,shi yasa shima yake faranta mata akan duk abinda take so.




Wannan ke nan.




Ahmad wazir chibado nutsutstsan matashi ne ,wanda yake cike da haiba da kwarjini irin na matasan samarin da suka san ciwon kansu, kyakkyawan bafulatani ne dogo me cike da kwanji irin na asalin barebari,kasancewar mahaifiyar su yar asalin meduguri ce babarbariyar Usul,miskili ne a ɗabi a da halayyar sa,amma a bangaren aikin sa yana kawar da wannan ɗabia tasa,amma duk da haka cikin zancan sa da yadda kalaman sa suke fita dallah_dallah zaka fahimci shi ɗin mutum ne kamamme mara son hayaniya,fatar shi ba fara ba ce ,sai dai tana da wata irin kala mai matukar kyau da ƙyalli ,wadda zamu iya kiranta da sama da ruwan tarwada,saboda ruwan tarwada ce amma kasancewar ta haɗu da hutu da gogewa yasa ta koma kala me tsada a cikin al'umma,bai da zafi ko saurin fushi amma yana da wahalar saukowa idan yayi mummunan fushi,yana da tausayi sosai shi yasa tun yanzu talakawa da kananan yara wadan da suka sanshi na kusa suke matuƙar kaunar shi da mutuntashi,hannun sa a bude yake ga duk wanda yayi katarin mikawa hannun,shirin da yake gabatarwa ya kara masa farin jini da daukaka a idanun matasa da kuma yanmata masu haukar sonsa da bai ma san da su ba.kadan ke nan daga dabiun AHMAD WAZIR CHIBADO,sai gaba zamu kara fahimtar wasu daga cikin halayyar sa.






A ɗan kure ya shiga office ,ko sauraron staff din shi dake ta miko gaisuwa baiyi ba,saboda yau yaso yayi abin da tun da ya fara aiki baiyi shi ba,wato latty, sai da ya ji shi a cikin lafiyayyan officer din shi me kama da fadar shugaban kasa,kana ya samu nutsuwa, cikin kan kanin lokaci ya fara karbar bakuncin manyan mutane yan siyasa da manyan yan kasuwa,duk wadan da suke son a saka musu talla,saboda duk wanda yayi dace Ahmad wazir chibado ya karbi tallan sa,to tamkar ya fara kasuwanci ko siyasa a Sa'a ne, wannan farinjinin nasa shi yake taka rawar gani a duniyar 'yan siyasa da 'yan kasuwa,wanda mutum ko ba yaso sai yabi abin da ya tallata ya kuma bi shi har inda yake,hakanne yasa yan siyasa da manyan 'yan kasuwa suke rubububin mika tallarsu ga tashar me farinjin yaro matashi wato AHMAD WAZIR CHIBADO.




Kamar yanzun dai ,da ya samu bakuncin babba kuma shahararren ɗan kasuwa kuma ɗan siyasar da zai fara damawa acikin wannan shekarar ta dubu biyu da ashirin da uku,kamar yadda kuka sani ne duk wani dan siyasa ko ɗan kasuwa yana son a talla shi domin samun kaiwa ga cimma nasara a kan burin su da kuma kudirin su, shahararren ɗan kasuwa wanda a yanzu ya juya ya koma dan siyasa ,wato Alh Garba me fata,da kan shi ya tako ba sako ba wanda shi yanbarwa kan shi dalilin zuwa kafa da kafa.




Bayan ya samu ison shiga office din ,ya bar gerd din sa a wajen kofar kamar wasu status, sallama ya yi cikin kamilalliyar Muryar sa,wadda a cikin Muryar zaka fahimci tsananin dattijantaka da kamala, cikin girmamawa A Wazir ya amsa yana miƙewa tsaye dan girmamawa ga mutumin da ya yi sa a da mahaifin sa ba ,wai dan yana me kudi kuma dan siyasa ba,musabaha su kayi cikin mutunta juna, sannan A. WAZIR,ya nuna mishi wajen zama,duban shi ya yi bayan ya zauna tare da haɗe hannayen shi guri guda ,cikin kammammiyar muryarshi irin ta matasan da suka san ciwon kansu,ya ce"Alhaji Garba muna yi maka Barka da zuwa da kuma ban hakuri akan rashin ganawar mu da wuri sakamakon kasa amsa kira da nayi", Alh Garba ya gyara zaman babbar rigar shi tare da yin gyaran murya duk a lokaci guda, sannan ya ce" babu komai mune da godiya ai mun san yadda abin yake dole sai ana daga muku ƙafa,dan haka kar
Ka damu muna godiya abisa karramawa",jinjina kai A, Wazir ya yi daga nan suka hau kan ainahin abin da ya tara su,a wazir ya karbi tallan Alh Garba na siyasa,duk da cewa baya karbar talla sai yasa anyi masa bincike a bisa sahihancin abin da yake tallatawar,a cewar sa ba zai taba karbar tallan gurbataccen abu ba,saboda hakan zai iya ruguza duk wata kima ta su,amma a wannan gabar sai yake yiwa Alh Garba kyakkyawan zato saboda kowa yasan shi yasan halinsa da kuma nagartarsa,duk kuwa da cewa sanin zuciyar mutum sai Allah,kuma shi ma ba ya karba haka nan bane ,ya karba ne kafin yayi bincike da tabbacin zai samu kyakkyawan sakamako daga Alhaji Garba,sallama su kayi cikin mutunci daga nan Alhaji Garba ya bar office din cike da farinciki.




Yana shiga mota babban Aminin shi Alh Muhammad nuurr ya fara kira ya bashi albishir,saboda yana daya daga cikin masu karfafa masa gwiwa akan shugabancin jahar ta su,saboda yadda da aminci da kuma sanin halin Dattaku Da amana irin na Alh Garba,kai tsaye Alh Muhammad nuurr ya sanar da shi ya same shi a gida su tattauna batun.




********


Rahim lafiyar ka kuwa ka zauna ka haɗa tagumi kamar wanda uwarsa ta mutu,cewar jiddo ke nan(jikar ƙanwar Hajiya goggo da ta dauko ta tun shekarun baya)zame hannun shi ya yi,tare da kirkiro murmushi kan kyakkyawar fuskarsa har gefan kumatunshi daya tana lotsadawa,ya ce" babu komai kawai dai ina tunanin yaushe zan fara zuwa school ne kamar yadda Anty amarya ta faɗa"jiddo ta zauna gefan shi tana cewa kai ma dai dan uwa Rahim ai kasan zaka je school,me ye na wahalar da kanka da tunani? Ɗan yatsuna fuska ya yi sannan ya ce" tsoro nake ji kar Anty amarya ta hana Ni zuwa,bayan Ni kuma burina bai wuce nayi karatu ba,ko dan na zama ɗan jarida kamar A Wazir chibado"dariya jiddo ta yi kana ta ce" dalla ka share Ni nasan cewa Anty amarya zata Barka kayi karatu kamar yadda kowa na gidan nan ya yi"Allah yasa ya fada cike da alamun karaya,daga nan ya ware su ka ci gaba da hirar su.






Cikin dare Rahim ya tashi da wani matsananciin ciwan mara,shi kadai yadinga birgima saman katon gadon sa.




Farkawar ta ke nan ,ta shiga bathroom,bayan fitowar ta ,sai ta kasa komawa ta kwanta ,duk da cewa bata jima da duba Rahim din ba,Anty amarya na kula da Rahim sosai ,saboda duk tashin da ta yi sai taje ɗakinsa ta duba shi ,sam bata sake a bangaren kula da sanyin idaniyarta,a hankali ta tura kofar dakin bayan ta saka safaya key dinta,,da wani irin hanzari ta karasa bakin gadon da Rahim ke kokarin faɗowa saboda juyin ciwon da yake yi,ɗago shi ta yi tana cewa lafiya Rahim me ya same ka haka? Dakyar ya yi mata nuni da cikin sa saitin mararsa,da gudu ta koma dakinta,ta dauko waya,hannun ta har rawa yake wajen danno lambar Dr Sabo,sai da kira wajen sau biyar sannan ya dauka a na shidan ,cikin alamun bacci yayi sallama,ba tare da ta tsaya gaisuwa da amsa sallamarsa ba,ta shiga koro masa bayani,tashi zaune ya yi yana ture matar shi dake bacci a jikin shi,ya ce" ok Amarya ki nutsu yanzu zanyi miki bayanin yadda zaki bashi taimako kafin gobe ku karaso asibiti"ok Dr Amma kasan fa Abbie shi yana gari ina tsoro ko wata matsalar ce,saboda nasan dole shi zai ce zai kawo shi ,tun da yanzu da asuba tayi zaka ga yazo ta dashi suje masallaci kaga kuwa dole sai yasan halin da ake ciki"calm down karki damu da wannan ko da tare kuka zo kin san ba zanyi abinda zai kawo matsala ba,zan bashi wasu bayanan daga baya ke sai nayi miki bayani,saboda Nima naga alamun ciwan kamar ya danganci sirrin mu"shike nan Dr Sabo"ta faɗa tana shafa kan Rahim da ya dan fara samun nutsuwa saboda ɗumin jikin uwa,kamar yadda yayi mata bayani haka ta yi masa ,cikin ikon Allah kuwa Rahim din ya samu bacci,a jikinta,jingina ta yi da makarin gadon tana sauke ajiyar zuciya,a duniya babu abinda yake saurin firgita Anty amarya da saka ta cikin mummunan damuwa kamar abinda zai taba Rahim ko wane iri ne.




Har asuba bata samu kara rintsawa ba,Rahim na jikinta tana tattalin lafiyar sa,a hankali ta janye shi taje ta dauro alwala,tana fitowa taji knock din Abbi yana kiran Rahim cikin taushin murya,da sauri ta fita tana cewa Abbien Rahim kayi hakuri ka tafi masallaci Rahim baya jin dadi tun jiya da dare"da sauri ya nufi dakin yana kiran subhanallah amma shine baki sanar dani ba,antyn Rahim?kar ka damu cikin dare ne kuma na kira Dr Sabo ya gwada min dabarun da zanyi masa kafin mu karasa asibiti shi yasa ma har ya samu yayi bacci" ajiyar zuciya Abbin ya yi tare da shafa kan Rahim din yana cewa shike nan bari naje kar na makara idan na dawo sai ku kimtsa muje muga likita" Tom shike nan sai ka dawo" fita yayi ya dan waigen Rahim din kamar ance masa idan ya dawo ba zai ganshi ba.




Ajiyar zuciya Anty amarya ta sauke ,kafin ta kabbara sallah,sai da ta idar sannan ta tashi Rahim din ,ta raka shi ya dauro alwala,bayan yayi Sallah ya koma jikinta ya lafe yana sauke ajiyar zuciya,shafa kanshi ta yi cikin taushin murya ta ce" Sweet ya cikin ya rage maka ciwon? Ɗaga kanshi yayi kafin ya bude baki a hankali ya ce" Anty ya daina amma ba duka ba" ok my boy kar ka damu yanzu Abbin ka zai dawo muje Dr Sabo ya duba ka"jinjina kai ya yi yana mai lumshe idanun sa.


Yau ko zaman da ya saba yi a masallaci bai yi ba,Baffa da Abba yahya ne suka lura da dakuwar shi har suka takbaye ko lafiya,Rahim ne ya ke ciwon ciki tun daren jiya, subhanalla cewar Baffa shima da damuwa ta kwanta saman kyakkyawar fuskarsa, Abba yahya ya ce",ya kamata muje Asibitin a duba shi ciwon yaro kamar Rahim ba shi da dad'i", ganin yadda suka shiga damuwa yasa abbie ya ce kar ku damu ya yi sauki yanzu zamu je idan da wata damuwa sai na sanar da ku",to Allah ya bashi lafiya Baffa da Abba suka hada baki wajen fada,daga nan ya shige bangaren aunty amarya da damuwar rashin lafiyar Rahim din,kai tsaye dakin Rahim din ta wuce, ya same su Rahim kwance jikin Anty amarya,da alamun san komawa bacci a tare da shi,zama yayi gefan su yana shafa kan Rahim din cikin wata irin soyayya da kauna ,ya ce" Rahim ya jikin naka? Jin Muryar Abbien shi yasa shi saurin bude ido,take fuskarshi ta yalwata da murmushi ,a hankali ya zame daga jikin Anty amarya ya koma jikin Abbin shi ya lafe, sannan ya ce" Abbie Barka da safiya? Barka dai my Love yajikin naka? Alhamdulillah Abbie da sauki" zuba musu ido Anty amarya ta yi zuciyarta cike da sake saken da kullum suke saka ta neman zaucewa,hannu yasa yaja dogon hancin ta yana cewa ya dai da tunani haka,antyn Rahim? murmushi ta kirkiro saman fuskarta tare da cewa kawai ina kallon wata ƙauna ne tsakanin ɗa da uba" dariya Abbie yayi cike da farincikin kasancewar Rahim a tsatson sa,ya ce" tashi ku shirya mu wuce asibitin kin san bana wasa da lafiyar Rahim".




Lokacin da Abba yahya ya ke sanarwa da inna maimuna rudewa ta yi Sosai,sai da ya kwantar mata da hankali ya nuna mata cewa ba wani abu ne babba ba,duk da haka dai bata gamsu ba, ta hakura ne dan ba yadda ta iya.




Abba yahyan ma hali yake, dan suna matukar son Rahim kamar su suka haife shi.




Fateema y Adam..........✍🏽
*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page5 ```




Ɗan jim Dr Sabo ya yi bayan ya gama bincike harma da scainin akan ciwan cikin Rahim din,wanda bayan ya gama binciken ya tabbatar da cewa ba ciwan ciki bane,tsananin ciwan mara ne ya kamu da shi a sakamakon magungunan da Anty amarya take bashi na hana yin jinin al'ada,duban ta yayi fuskarshi cike da tuhuma da tambayoyi na me yasa ta yi hakan bayan tun tuni ya ce ta daina bashi sakamakon binciken sa da ya nuna masa cewa hakan zai iya zama babbar illa a tare da lafiyar mahaifar RAIHAN ɗin,likita kayi shuru baka ce komai ba ina fata dai ba wata babbar matsala ba ce"Alhaji Muhammad nurr ya tambaya fuskar shi na nuna tsananin damuwa da fargabar da ya samu kanshi a cikinta. da sauri Dr Sabo ya daidaita kanshi cikin jawo jarumta,ya ce" a'a Alh kar ka damu ba wata matsala ba ce,ɗan ciwan ciki ne kawai wanda ya yi shi sakamakon yawan cin kayan zaƙi da yake,amma ga magunguna na rubuta insha Allah ba wata matsala sai dai a kiyaye da irin zakin da zai dinga sha"ajiyar zuciya Abbie ya yi tare da duban Anty amarya da tayi tsumu_tsumu zuciyarta cike da fargaba dan tasan ma anar kallon da Dr Sabo ya yi mata,ya ce" kinji dai antyn Rahim sai ki dinga kulawa tun da ke ce kike tare da shi ko da yaushe idan kuma ba zaki iya kiyayewa da kulawa min da lafiyar Rahim ba,sai na dauke shi na ta fi da shi can kalfoniya ,idan yana kusa da Ni sai na fi samun nutsuwa,tun da ke nayi nayi ki bini can din kin ƙi"ya karashe maganar idanun sa akan Rahim dake lafe a jikin sa.




Gaban Anty amarya yayi mummunan faduwa ,cikin sauri ta ce" a'a Abbie wallahi zan kula sosai ,insha Allah ba zaka samu damuwa akan haka ba"jinjina kai ya yi yana mai mamakin yadda bata son su zauna kusa da shi ita da Rahim ko kuma shi Rahim din yayi nesa da ita,baya son zurfafa bincike akan abin da yake ganin ba shi da wata hujja ko makama ,dan a ganin shi har yanzu Anty amarya bata waye ba,kasancewar rayuwar da tayi me tsawo har girmanta a cikin jeji,duk kuwa da cewa yanzu tayi ilimi kuma tayi cuɗanya da manyan mutane matan abokanan sa,da kawayen ta yan makaranta.




Maganar Dr Sabo ce ta dawo da shi duniyar mutane,Dr Sabo ya ci gaba da cewa shike nan, Alh zaku iya tafiya"musabaha su kayi da juna kana suka bar office din ,zuciyar Anty amarya cike da tunanin matsalar da Dr Sabo ya gani tare da RAIHAN.


Suna fitowa wayar Abba yahya ta kuma shigowa wayar sa ,dan tun zuwan su asibitin yake kira dan jin halin halin da ake ciki, wannan kauna da Abba yahya da matarshi suke nunawa Rahim na daya daga cikin abin da yake kara musu zumunci da kaunar juna,ɗaga wayar ya yi ya kwantar masa da hankali,ya ƙara da cewa ga su nan ma zuwa gidan yanzu,da wannan ne duka suka samu nustuwa har su goggo Rahman da Baffa.




Har bayan kwana biyu lokacin Abbie ya dawo ɓangaren Anty amarya,bata ji komai daga Dr Sabo ba,hakan kuwa ba karamin tayar mata da hankali ya yi ba,ji tayi ta ƙagu Abbie ya bar ƙasar,zaman shi a wata ƙasar shine kwanciyar hankalin ta,duk irin son da takewa mijin nata sam bata son ya ce zai zo kasar ,saboda gudun samun matsala akan sirrinta,da kyar ta iya daidai ta kanta ta dawo da walwalarta,har zuwa ranar da ya bar ƙasar,ranar kuwa daga filin jirgi asibiti ta wuce kasancewar a dakin ta ya tafi ita ce ta kaishi filin jirgi ita da Rahim.


Zugum ta yi tana duban Dr Sabo,idanun ta cike taf da hawayen tashin hankali,Dr Sabo ya ci gaba da cewa ,gaskiya amarya idan ba muyi gaggawar samun mafita ba,zamu cutar da rayuwar RAIHAN,karshe ma muyi abinda zai iya sanadin rayuwar da muke yin komai saboda ita"cikin kuka Anty amarya ta ce" dan Allah Dr Sabo ka taimaka min kamar yadda ka saba idan na rasa RAIHAN nima mutuwa zanyi"amarya yanzu fa duk wata dabarar mu ta kare,abu daya ne ya rage mana shine sanar da RAIHAN ita din ko wacece,tun da ko ba mu sanar da ita ba dole ne ta sani,saboda kullum girma take yi matakan budurci na hawa kanta,yanzu wannan abin da ya faru ina tabbatar miki da cewa shine matakin farko da RAIHAN zata gama tabbatar da jinsin ta,saboda watan da zai zo dole sai ta yi al'ada,kuma RAIHAN ba jahila ba ce,da ilmin ta,dan ko a yanzu na tabbatar hakuri kawai take take kawar da kai amma tabbas zuciyarta na cike da tunani da rudani iri_iri wanda kuma idan ba muyi hanzarin kawar mata da wannan tunani ba shima zai iya zama babbar illa ga lafiyar ta"ajiyar zuciya Anty amarya tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login