Showing 1 words to 3000 words out of 27623 words
Chapter 1 - Darajar Yayana Book 1 Complete by Halima Abdullahi K Mashi .txt
Darajar Yayana3-01
Posted by ANaM Dorayi on 10:48 PM, 31-Mar-16
Under: DARAJAR 'YA'YANA
___________________NA
___________HALIMA K/MASHI
Gudu sosai Aliyu yake tamkar zaibar
gari,zuciyarsa ta karaya gani yakeyi lallai yana
dauke da ciwon har ya hangoshi kwance a rame
ga kuraje sunyi mashi caba caba a jiki.da sauri ya
ciro wayarshi ya kira layin likitan, Dr kana Asibiti
ne? Dr ya ce eh, amma yanzunnan zan fita.Aliyu
ya ce, don Allah ka jirani gani daf da
Asibitinka.Sama sama suka gaisa, Aliyu yace likita
ana yin gwaji yanxu a fitar da sakamako yanzu?
likita ya ce gwajin mene?Aliyu ya ce, (H.I.V)
,Likitan ya zaro ido yana kallon Aliyu ranka ya
dade kana zaton ciwon a tare da kaine?Aliyu ys
ce eh likitan ya ce, likitan yace za a iya, da kansa
yayi gwajin, ya daga ya nunawa Aliyu tare da
cewa yanzu dai ya nuna baka da ciwon sai dai ba
a gwajin farko ake tantancewaba.bayan wata uku
za ayi wani, sanan in an sake yin wani wata ukun
sai a sake gwadawa sau uku kenan,induk ya nuna
babu to babu din kenan saboda gwajin farko
yakan nuna babu kuma akwai.Aliyu ya lumshe
ido, kenan likita yanzu bani da tabbas kenan?
Likita yace gaskiya babu tabbas.ya dafa kafadar
Aliyu cikin murya ta son kwantar masa da hankali
ya ce, yallabai kadakadamu, ko da ya kasance
kana da ciwon domin akwai magunguna wadanda
masu ciwon suke sha duk karshen wata.sanan
zakaci abubuwan gina jiki don karin kuzari, su
magungunan suna yakine da kwayoyin cutar,
suna hana kwayar ta karya garkuwar mai dauke
da ciwon.Aliyu ya share zufar da ta keto masa ta
goshi, sanan ya ce to nagode likitan ya ce se
iyalanka ya kamata a gwadasu.Aliyu yakalli likitan
yace ana iya daukar ciwon ta hanyar mu'amulan
yau da kullum? kamar misalin ta hada kwanon
abinci ko yin hirar fatar baki ne?likitan ya ce a'a
Aliyu ya ce, to bana tsammanin suna da
ciwon,kafin likitan ya sake magana, ya ce na
gode likita, na barka lafiya.Da azama yafita ya
nufi gida.Nikam lokacin ina zaune bakin gado,
idanuna banda xafi ba abinda suke yi, saboda
kuka.hawayena sun daina zuba sun kafe. Nakosa
yaya ya dawo, addu'a ta Allah yasa yaya bashi
da ciwon, dama gidan bude yake dom haka
sallamar shi kurum naji abakin kofa,Zubur na
mike ina kallon shi, ya zauna bakin gado tare da
sunkuyar da kai na dafe goshina ta re da cewa
innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yaya kana da
ciwon ke nan? Shima da sauri ya mike tare da
kama hannuna Sadiya kinatsu mana,nasoma
kuka. Yaya ka cucemu, kila nima ina da ciwon,
shike nan ka mai da mana yara marayu? Ganin
yadda na rude yasa shi rumgumeni a jikinshi
tsam.Saurara mana nima fa ba cewa akayi ina
dashi ba. Na kalle shi me aka ce? Ya ce, sai anyi
gwaji uku sanan za'a tabbatar amma yanxu ma
ya nuna babu. Na sauke ajiyar zuciya, sanan na
ci gaba da gunjin kuka ina cewa. Duk lokacin da
bawa ya bar hanyar Allah tabbas sai ya fada da
nasani. Aliyu ya ce kiyi hakuri mana Sadiya,
nasan cewa ko da ta kasance ina dauke da ciwon
nan, wlh sam nasan baki dashi, domin lokacin da
na fada wanan kuskuren Allah ya sani ban rabeki
ba sai yanzu na tuna ta iya yuwuwa baki da hakki
ne shi yasa Allah yasa ban kusance ki ba.
Nakalleshi idanuna jajur, tayaya kake zaton
abinda ya shafeka bai shafeni ba? Naci gaba
kaifa mijinane nasunna, ina sonka koda kai baka
sona. Ya maza a ce abinda ya shafeka bai shafeni
ba. Yace haka ne kiyi hakuri Sadiya. Tsam!
namike nafada bandaki nayo alwala, zuwa nayi
na fara jero nafiloli don neman sauki a gurin
ubangijina. Can shima sai naga yayi tashi alwalar
yazo ya kama yin nafilar, a hankali nake jin
zuciyata tana sauka, danagaji sai na dauki
alkur'ani littafin da ke dauke da waraka na soma
karantawa. Munfi awa uku cikin wanan halin,
lokacin zuciyata tayi sanyi kalau.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Shi yasa kullum ina alfaharin kasancewata
musulma. Ina kara godewa ubangijin musullunci
da ya kageni cikin wanan addini ya saukar mana
da Alkur'ani don ya kasance waraka a
garemu.Aduk lokacin da na karanta alkur'ani ko
na saurareshi nakanji sauyin zuciya, ko cikin wata
i ciiin matsala nake.Na kammala nazo na kwanta
yanzu ina jin zan iya jure ko wacce iriin kaddara
da zata hau kaina. Hakanan zan rufawa mijina
asiri inshaAllahu, shima yazo ya kwanta dan nesa
dani muna fuskantar juna. Ya ce kiyi hakuri don
Allah kinji? Na ce, nayi hakuri, na yafe Abban
Kausar, ya wuce a gurina na matsa kusa da shi.
Ya ce baki jin tsoro na? Nace Abban Kausar mu
bar wanan maganar. Ya rumgumeni, yau she
rabom da na kwana hakarkarin mijina sai yau.
Munso mu makara dan haka shine ya jamu
sallah. Zan tafi kicin yace, dawo mu kwanta mu
huta anjima ma karya na dawo muka kwanta
Yadda nake jina yanzu ba zan juya masa baya ba.
Har sai sha daya muka karya, sanan ya shirya ya
nifi gidansu Iya ni kuma na shiga gyaran daki,
minti shabiyar da fitar sa sai gashi ya kira, na
daga tare da sallama. Cikin rudewa ya ce Sadiya
kinga yaran nan sun hadani da Iya ko? Kuka fa
na sameta tanayi please, kizo yanzun kitaimakeni
sam taki saurarena. Hankalina ya tashi. Akofar
gida na sameshi tsaye cikin damuwa nace
meyafaru? Ya ce wlh ban sanme yarannan suka
ce mata ba, na shigo na sameta cikin damuwa
natambayeta me ya faru? Tana kallo na sai kawai
ta fashe da kuka, wai naci amanar ta nasan dai
maganar bata wucea kan matsalarmu dakeba.
Ban san me zance mata ba, domin bani da yanda
zan wanke kaina. Laifi dai nayishi, don Allah shiga
ki bata hakuri, anjima zanxo da Usman neman
tuba gurinta. Cikin hanzari na shige gidan, kan
kujera na sameta cikin tashin hankali nazauna ina
fadin Iya menene? Abban kausar yayi min waya
wai inzo, ya ganki cikin damuwa. Sam idona ya
rufe ban lura da su Kausar ba, sai da naji
muryarta ta ce, wlh Mami ni banibace nafadaba,
Al'amin ne yace yasan yanzu kina can kina kuka,
shine Iya taji tace kukan me? Shine mukayi shiru,
ta ce mu fada nacemashi ni ba ruwana kin hana
mu fada, shine ta tsaremu ta ce, zata zanemu,
shine nace inmun fadamata kada ta fadamaki.
Shine muka fada mata cewa kullum Abban mu in
ya dawo sai ya sa ki kuka, yayi ta zaginki. Na
kama musu kunnuwa, muryar Iya naji ta ce sakar
musu kunne, in ba ke ma kinaso inyi fushi dake
bane. Ni na san cewa wanan ramar taki akwai
bakin ciki a cikinta. Wato dama gadanga cin
amanar da aka bashi yakeyi? Shine ke kika zabi ki
zauna ki hadiye bakin cikin da namiji kina kan
kanuwarki. Sai yanzune kike cikin shekara ashirin
da biyar, amma kika juri wulakanci. To ki sani ni
ba xan yarda ba, ai kodanace in matsala ta taso
kada ki nemeni ban ce haka dan kicutu ba, na
furtane dan in tabbatar kina sonshi badole
nayimakiba. Da naga ta nunfasa sai na ce Iya
yaran nan karya suke yi, dan sabanine
mukasamu kwanan baya, kuma mun sulhunta,
dan Allah Iya kada kiyi fushi da yaya, ko mai ya
wuce. Ta ce yaro da wuya yayi karya. Daidai
lokacin yaya yasake shigowa,Iya ta dube shi Aliyu
ina son ka sani,Sadiya bazata koma gidan ka ba,
dan ba zan yardaba ace har yayanku sun san
cewa kana cutar uwarsu ba. Shi yasa tun farko na
ki batun auran, don nasan halinka. Hankalin yaya
Aliyu yasake tashi, ya curo wayarsa ya kirawo
Usman, ya ce dan Allah Usman kazo gidan Iya
yanzunnan. Ba tare da ya jira Usman me zai ce
ba, ya kashe wayar shi. Sadiya ta tsurawa su
Kausat ido sam bata so suka fada wa Iya wanan
maganarba.badon kar a rabata da mijinta ba, sai
dan bata son Iya tashiga damuwa, musanman
yanzu da ya kasance Iya batada koshin lfy. Iya ta
ce, kun tsaresu da ido ne don sun fadi gaskiya?
Na ce Iya yaran nan fa karya suke yi. Aliyu ya ce
ba karya bane Iya, sai dai sunfada maki a daidai
lokacin da muka shirya na san in Usman yazo zai
gamsar da ke. Wasa wasa har Usman ya shigo Iya
ba ta daina fada ba shi ma shiru ya zauna yayi
har sai da iya ta numfasa, sanan ya shiga bata
hakuri tare da lallashinta. Ya tabbatar mata da
cewa an daidaita, ta ce ina son jin wacce matsala
ce ta taso har yarinya ta kode haka? Sanan in san
wake da matsala? Muka kalli juna ni da yaya,
Usman yace zai fi kyau Iya abin da ya wuce ya
wuce muyi adu'ar Allah ya kare gaba. Ta ce sam
sai fa ta ji menene ya haifar da rashin jituwar
saboda gudun sake faruwar abin nan gaba dan ta
san wane irin mataki zata dauka. Inko ba'afada
minba to sai dai ya rubuta takardar sakin Sadiya
ya bani. Kai Usman ai kasan ko mai, badan son
raina akai auran nanba sabo da gudun haka, don
haka yanzun ma bata baciba ya bar min 'yata.
Aliyu ya ce Usman fada ma Iya komai duk
hukuncin datayanke a kaina na cancanceshi. Nayi
saurin kallon Usman, ko da wasa bazan bari Iya
tasan ainihin abin da ya faru ba duk da na san
Aliyu dan ta ne amma bazanso tajiba. Muryar
Usman ce ta katseni, wato ainihin abin da ya
faru....Nayu zaraf na katse shi gaskiya Iya ainihin
abin da ya faru laifinane.Na kalli su Kausar kufita
waje. Suka fita nasun kuyar da kai ina tunanin
wane laifi zan dorawa kai na? Dama na ce ne
bana so in sake hai huwa, yara uku sun isheni,
shi ne yaya ya dauki gaba dani. Dakin yayi tsit,
na fada haka ne dan nasan babu abun da iya
take so kamar taga yayan ta suna haihuwa, na
saci kallon ta ni ta ke kallo cikin bacin rai. Ta
soma sabon kuka yanzu Sadiya ke ce baki son hai
huwa? In baki haihuba me zakiyi? Wasu ma son
haihuwar suke da kudi amma ba su samu ba, sai
ke ishashshiya. Na soma hawaye don tausayin
kaina, nazama kyandir in kona kaina don in haska
shi, na ce Iya ki yafe min, domin shi ma yaya
tuni ya yafe min. Na kalli Usman a gabanka aka
yi komai ko? Usman ya lumshe ido, zuciyar shi
cike da mamaki bai taba ganin irin Sadiya ba. Duk
irin cutar da mijinta yayi mata amma ta yarda ta
shafawa kanta kashi, don kurum ta wanke shi. Na
danyi dim dan tsoron kada Usman yatona dan
naga yayi shiru, na ce yaya Usman kuba Iya
hakuri. Iya ce ta daka min tsawa da cewa, kada
ki damu mutane, kuma ina son ki sani wanan ya
zama na karshe, in na sake jin wani laifi
makamancin wanan zaki ga matakin da zan
dauka. Ta kalli yaya Aliyu cikin taushin murya kayi
hakuri Aliyu, inshaAllahu bazata sake kwatanta
haka ba. Yaya Aliyu dai ya kasa koda daga kai,
jikinsa kuma ya mutu.Zan mike ta ce ke zauna
ban gama da ke ba,nakoma na zauna. Ya aliyu
ya zuba min ido, sanan ya kalli Iya. Iya kada ki
damu, ko mai ya wuce ta shi mu tafi. Iya ta ce
kuje zatazo yanzun, suna fita Iya tace, na san
cewa abin da kika fada ba shi bane ainihin
matsalar ku ba, kilama kin fada ne dan ki wanke
shi. Amna in haka ne da gaske ina mai yi maki
nasiha ki jitsoron Allah, ki bi abin da mijinkike so,
duk mutum na kwarai ba zai ki yin murna da
kyautar da Allah yayi mashi ba. Koma menene
zan ci gaba da yi maku adu'a, tashi kije. Na mike
zaraf ta re da cewa, to Iya nagode, insha Allahu
bazaki sake jin kan mu ba. Ta ce kuma kar inji kin
daki yaran nan, gashi a ban za kin sa suna jin
haushin mahaifin su, har suna fadin basu son
yadawo. Na ce bazan masu komaiba. nakirasu
muka fita.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Usman ya kalli Aliyu bayan sunfita ya ce aboki in
har ka sake cin zarafin matarka hakika Allah
bazai kyalekaba. Dubi yanda ta dorawa kanta laifi
don ta wanke ka. Aliyu ya ce, nikaina baka ga na
kasa maganaba? Lallai Allah ya taimakeni Sadiya
ta taimakeni, wlh kaji na rantse maka yau da Iya
ta ji ko mai na kade, ba zankara kima a
Idontaba. Sannan sai ta raba ni da matata.
Usman ya ce, to sai kayi mata adalci tunda abin
yazo da sauki. Da muka fito duk suka nufo gun
mu Usman ya ce Sadiya Allah ya shi maki
albarka,da'a ce mata da yawa suna da hali irin
naki, na tabbata da aure da yawa ba zai mutuba.
Nakalli Aliyu, shima ni yake kallo. Ya ce my choice
na gode, ina sake rokonki afuwa ki yafe min. Na
ce ya wuce. Na tasa yarana muka tafi gida
nazaunar dasu,Kausar nace yanzu kun kyauta
kenan da kuka sa Iya kuka? Kausar ta ce Momy
Al'amin ne. Na ce to kar ku sake, Al'amin ya ce,
momy ba zan sake ba.
Ko daran ranar Aliyu banda hakuri babu abinda
yake bani, duk ba wannan ce matsalata ba, ya ya
za'a kare da batun (H.I.V) da kuma batun
yarinyar nan? Don haka na waiwayo na dube shi
daga inda nike kwance, shima rigingine yake
idanunsa suna kallon sama. Tsakaninmu mutum
guda zai iya kwanciya tsakaninmu, na ce ' Yaya!
Bai amsa ba, na daga murya 'Yaya' shru, da
alamu tunaninsaya tsawaita. Don haka na mike
na kunna fitilar dakin,haske ya mamaye ko
ina,na tsura mashi ido cikin faduwar gaba.
Nagirgiza da ganin hawaye suna gudu layi bibbiyu
daga idananun Yaya daya yamiko zuwa kumatu.
Yayin da dayan ya bi gefen ido. A fili nafurta'Inna
lillahi wa inna ilaihir raji'un! Yaya! Na kira shi tare
d zama kusa dashi na kwantar d kaina a kirjinshi,
kunnuwana suna jiyo yanda yake ta kokawa d
kukanshi a kirjin. Ina zaton yana kokowar danne
kukan ne, yayinda shi kuma kukan ke ta yunkurin
fitowa. Da sauri na dora tafin hannuna a kirjinshi
ina ta shafa kirjin, wai nufina in taya shi lallashin
kukan. Bakina ya soma fadin 'Haba Yayana, me
kuma ya faru? Tuni na yafe abinda kayimin,
namaka alkawarin rayuwar da tafi wadda muka yi
baya dadi. Sai naji hannunsa a gadon bayana, ya
damki rigata d dan karfi alamun har yanxu yna
ckin cikin kunci, muryarshi sarke cikin rawa irinta
mai kukan baqin ciki. Ya ce, Sadiya ba anan
matsalar take ba, Sadiya baqin cikina ciwon in ya
kasance ina da ciwo...'' kasa karasawa yyi don
kukan da ke son subuce masa. Nace Yaya ko
kana da ciwon nan zan zauna d kai,ko banidashi
zan yarda ka sa min. Nima kukan ne ya kufce
min,cikin kukan na ce 'Yaya zan zaunada kai haka
ina sonka.'' Sosai ya rungumeni tsam ''Sadiya ba
zan cuce ki ba, bayan Allahya tsare ki,nikuma
nine nacuci kaina, domin duk wanda ya bar
dokar Ubangijinshi ya dauki son zuciyarshi, ya
saki koyarwar Abul Kasim, Manzonmu mai tsira
da aminci, ya bi ta Yahudu d Nasara to bako
shakka karshenshi nadama da kuma danasani,
lokacin da ba su da amfani. Sadiya lokacin da
shaidaniyar yarinyar ta ziyarce ni da ban bi son
shaidaniyar zuciyata ba duk da haka bata faruba.
Ba ina kukan ciwon da kila zai zama ina da shi
bane, ba ina kukan ci gaba da rayuwata ba ne
ina kukan yanda zan bar ki da wahalar jinyata da
dawainiyar yarana. Sannan kukan abinda da zan
tarar a cikin kabarina ban san me zan gaya wa
Ubangijinaba, Yayi shru cikin shassheka, nima
kukana ya qaru. Nace, Yaya inshaAllahu
bakadashi, ka ci gaba da neman gafarar
Ubangijinka, Allah mai amsar tuban bayinshi
ne.Ya yunkura ya tada mu zaune ya dago fuskata
muna kallon juna ido cikin ido,ya ce 'Sadiya ban
makara ba ko? Na girgiza kai, Baka makara ba
Yaya. Ka daina tunanin cewa zaka mutu ka bar
ni,insha Allahu kai ne wakilin gawata,kai zaka
fara binne ni Yaya. Ya rungume ni tsam a kirjinsa
tamkar ya buda kirjin ya saka ni. 'Ina sonki
Sadiya,ina son yarana,ina son iya. Amma haka
nan in ta kasance zan barku...... Wayarshi ta
katse maganarsa, tamkar kada ya dauka don ji
yake komai ma ya tsara shi rayuwarshi ta kare.
Ni ce na dauko wayar na mika masa, Adewalene
direbansa na can, tamkar kada ya daga na
ce'Yaya ka amsa mana.' A kasalance ya yi
sallama,Ade ya amsa sannan ya ce, 'Oga dama
madam ce a Asibiti ba lafiya,shine take tasa aka
dauki lambata a ka kira ni. Me? Naji Aliyu ya
furta da karfi, 'Mujidat ba ta da lafiya?? Nima
gabana ya yi wata mummunar faduwa,tamkar ni
ce na daga wayar. Idanuna waje ni ke tambayr
me ya same ta? Aliyu ma da ya rasa me zai fada
sai ya maimaita tambayar da nayi. 'Adewale
meyasame ta? A can bangaren Adewale ya amsa
da cewa, shi fa bai sani ba,amma ga ta bari ya
bata. Aliyu cikin daga murya ya ce,kada ka
bata,bana son jin muryarta,macuciya. Na yi
saurin fadin 'Yaya a bata wayar mu ji daga
bakinta, da gaske tana da ciwon? Shiru Yaya yayi
yana kallona,hankali tashe bayn ya katse wayar.
Na ce Yaya don Alla ka kira a bata mu ji, ba don
son ranshi ya kira ba,sai don na nace da cewa ya
yi hakan.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
A handsfree ya saka ta, Ade ya daga ya ce
bata,murya can kasa ta ce 'Hello' ya katseta da
cewa,'Kiran ubanme kikace amin? Na fada miki
bani bake, kuma ina Allah ya isa da sanin da na
yi miki,macuciya.Dama kin san cewa kina da
(H.I.V) shi ne ki ka like min sabida ki cutar da ni
da Iyalina? Wani kara ta saki mai karfi tana fadin
'A'a, a'a ni ba ni d (H.I.V) sai dai in kai ne kasa
min. Muka kalli juna ni da shi, ya ce 'Yanzun
wane ciwo ki keyi dazakice baki da (H.I.V)? Tace,
'Ina dauke da cikinka ne yana wahalar da
ni,amma bani da (H.I.V)....' Ya katseta da karfi
Cikin tsawa cikin masifa take fadin 'Kada ka sake
zagin ubana,wannan cikin naka ne ban taba
yarda na bi wani ba tare da abin karyar cuta ko
ciki ba sai kai daya danike So. In ma (H.I.V) ne
kaika samin kamar yanda ka sa min wannan
cikin,kuma ina sonka sani ba zan taba cire shi
ba,zan haifi dan soyayya,zan zo har garinku gurin
danginka don su san kana da da' ko 'ya da ni.
Haka nan masoyiyarka da ka yi min wulaqanci
sabida ita,ita ma ya dace mu san juna. Duk da
tsawar da yake daka mata bata yi shuruba,sai
data kai aya. Ni kam baqin ciki ya hana ni
magana,sai hawaye. Na mike zan fita,ya riko min
hannu tare da finciko ni na fado jikinshi,ya kashe
wayar yana fadin. 'Haba Sadiya, ina ce murna
zamu yi tunda ba ciwon gare ta ba? Na mishi
wani kallo tamkar in hau shi da duka,cikin zafin
rai na ce 'Ba gara ciwon ba da cikin da ka yi
mata? Yanzun me ka shirya fadawa danginka in
ta zo musu da da'? Ya ce, ki barta bata ma isa ba
ne,taje can ta nemi Uban cikinta. Ya tausasa
murya. 'Na rantse miki bazan karbi cikinba,
kibarta zan nemi transfer in bar garin ba
shienanba. Yayi ta lallashina ina kuka, ya yi ta
tsara min zantuka har nayi shiru,amma sam naki
magana, ga ciwon kai tamkar zai rabe. Ya jawo ni
jikinshi 'Ba kincekin yafe min ba? Na dafe kaina
tare da fadin 'Wash Allah na.. A rude ya
tambayeta ''kan ki na ciwo ne? Na daga kai
alamun 'Eh''ya kawo min panadol ya ba ni na
sha. Haka ya yi ta ririta ni da lallashi tare da
maganganun kwantar da hankali har bacci
yadaukeni. Shi kuma ya mike ya shiga sintirin kai
kawo dakin, daga bisa niya dau ki wayar shi