Showing 3001 words to 6000 words out of 27623 words
Chapter 2 - Darajar Yayana Book 1 Complete by Halima Abdullahi K Mashi .txt
ya
nufi can harabar gidan, dan kada ya tashi wani
daga cikin iyalin sa. Yanzu ya fi shakkar yaran sa,
domin ya fahimta lallai in yayi wasa zai sha
mamaki dasu. Layin mujidat ya kira, ringing na
uku ta dauka Aliyu yace, na kirakine in gargadeki,
kiyihanzarin fita harkata, kuma ki nemi uban
cikinki, ni ba nine uban sa ba. Dama karuwa tana
da miji ne da har zata sami uban da? Ta soma
kuka, tana cewa kaine ubansa, kabidani ta lalama
in ba haka ba zaka ga yanda ake iskanci. Kana
kirana karuwa kai ya sunan ka? Gara ma kazo
cikin satin nan in ba haka ba za ka ganni a
Kaduna. Aliyu ya ce dole zan dawo tinda gurin
aiki nane, amma ki sani babuke, zai fi maki sauki
ki zubar da wanan cikin tunda baki tuna
ubansaba... Mujidat ta katse shi ina zaton baka
sanni ba ne shine yasa ka ce haka, amma zan
nuna maka kalata. Kuma bazan zubar da cikin
ba, wanan cikin shine ya zo min dai dai lokacin
da nake bukatar shi zai tai maka min sosai.
Wanan cikin shine zai hana rabuwar mu ni da
kai, kasani mun hadu har abada . Ta katse
wayar.
Ranar da zai koma tamkar inyi me don ta kai ci,
nasan dole sai sun hadu da yarinyar nan ga ciki.
Shi kanshi tunda akayi batun cikin ban sake ko
dariya ba, ya lura da hakan. Da zai tafi sai min
dadin baki yake gaskiya ni fa Abban kausar gara
min ace daga ni har kai muna da ciwon kan
jamau da batun cikin. Nan ya rike min hannu,
don Allah ki saki ranki ki aje maganar yarinyar
nan a gefe, ke kiji a rankima an
shafe babin ta a bayan kasa, kinji don Allah. Na
ce hum! Shi ke nan Allah ya saukeka lafiya. Ko da
ya sauka yana ta kokarin yawan kirana da
sauransu. Nakula sosai yana son shikam lallai sai
mun koma tamkar da, nima dai ina ta kokartawa
don ganin anyi hakan duk da ina tsoron mai zai
biyo baya kan batun yarinyar da cikinta.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu da yake zaune a bayan motar sa ya dubi
Ade wale da ke tuki ya ce masa kasan gidan da
Mujidat take? Ade wale ya ce a a sai dai gidan
yarta yasa ni inda ya taba kaita sai ko asibitin da
ta kwanta. Aliyu ya daga waya ya danna mata
kira, har ta katse bata daga ba. Ya shareta da
farko amma sai kuma ya tuna yana son kwarai su
tattauna abu mai mahman ci. Don haka sai ya
sake daga wayar da nufin kiranta, amma sai ga
kiranta ya shigo, cikin sauri ya daga. Ta ce kamar
kana jiran kira na? Aliyu ya ce ko daya ina dai
yunkurin kiranki ne. Tayi yar dariya. Ashe dai ka
damudani? Yace ke bankiraki don naji salon
zancekiba, inaxan same ki? Ta sake yin yar dariya
da ya tsana a yanzun, ka bari ni nasan indazan
sameka,tunda ka shigo garinnan nasami labarin
zuwanka, sanan ka manta nice na kiraka ba kai
ne ka kirani ba da har zaka ce bakakirani dan kaji
salobane. Ya katse ta, ki fada min inda xan same
ki yanzu nace,tasake yin yar shewa tare da fadin
ashe dai har yanzu kana tare dani, ni nasan
tunda ka shigo dole ka neme ni ko dan cikinka.
Cikin fushi ya ce, kar ki tsamma ci cewa haduwar
mu zata haifa maki da mai ido, ko kusa ganina
bazai farantamaki rai.... Ta katse shi da cewa, in
ji wa? Ai ko zaka kashe ni ganinka ya fiye mun
komai farin ciki ko kasan ina sonka fiye da
mahaifana? tayaya zan kasa farin cikinganinka?
cikinhaushi yace Amma kin yi asara tunda baza ki
fadin in da kike ba bari in koma gida Cikin sauri
tace ina Hotel din Hamada Daki na sahashida,ka
iso lfy masoyina Tsaki yaja sannan ya katse layin
sannan ya kalli direba muje Hotel din Hamada ko
cikin harabar hotel bai shiga ba Aliyu yace ya
tsaya ya sake kiran layin ta ta daga tare da fadin
bude ka shigo mai sona yace ke shashasha fito
ina can bakin gate sannan ya katse bai tsaya jin
me xata ce ba sanye da dogowar bakar jallabiya
da dan kwalinta sai takalmi baki mara tudu sam
yanxun baya ko son ganinta don haka ya daure
fuska tamkar baitaba dariya ba sam,yanxu baya
ko son ganinta don haka ya daure fuska tamkar
in ya bude baki xai fito da wuta don hada rai,
tana isowa saitinsa ta nufa don tasan gurin
xamansa yasauke gilashin tana kallonshi gabata
ya fadi amma sai ta dake saboda iya bariki tace
maigidana ina son in ganka cikin iri kamewar
gaskiya kada kace aikinka kafito mushiga ciki ya yi
mata kallon banxa tamkar yaga kashi sannan
yace shiga mota muje tace ina? tace. sai kinji?
Tace bari in dauko jakata yace (cikin tsawa ) in kin
koma ciki ni kuma zan fi cikin sauri ta zagaya ta
bude mota tana fadin gida zamu je kenan? ko
tanka ta bai yi ba yace Adewale sai da ya harba
motar kan titi sannan yace Oga. gida zamuje?
Aliyu yace babban asibitin garin nan zamuje ta
zaro idoda sauri tace yin me? ku tsaya in sauka
bazanbikuba ,tasoma lalube zata bude kofa Aliyu
yace bazan hanaki ki fita ba amma ki sani in ki
fado kan titin nan ba lallai ne ki rayu ba wanda
hakan ba zai dameniba yan uwanki ne za su yi
rashi,ta dan shiru tana tunanin me zatayi don
kuwa itakam bazata taba yarda a cire mata
cikinnanba Don tasan shi ne kadai abinda ya rage
mata wanda zata rike Aliyu da shi dole ya
saurare ta ta kalleshi nifa bana son ka kai ni a
cire min ciki ya dubeta. ina ruwana da cikinki
bashi ne matsalata ba ta sauke ajiyar zuciya tare
da jingina kanta a jikin kujerar mota ta tabbata
gaske ne ba abinda zai kaisu kenanba ta sake
kallon shi me zamu je yi ya dauki wayarshi yana
naiman wani layi ya karata a kunne tare da fadin
in mun je kyaji,Suna shiga dakin ganin likitan
wanda ya riga ya shaida masa yana tafe, ya
baiwa likitan hannu suka gaisa. 'Yan sanda sukan
saba da likitoci sbd yanayin ayyukansu, don haka
Aliyu yasan likitoci da dama a Asibitoci daban
daban. Ya nuna Mujidat gata nan, Mujidat ta
soma zare ido, sai dai ganin Likitan ya dauko
kayan gwajin (H.I.V), sai ta kwantar da hankalinta
dan tasan bata da shi din amma Likitan ya ba da
lokaci wata uku nan gaba su dawon a sake
gwadawa, ya umarta shima a gwada shi.
Sakamakon dai duk daya ne, babu, Aliyu
zuciyarshi yanzun ta nutsu d cewa bashi da
(H.I.V) ya yi wa liktan godiya sannan suka yi
sallama. Suna fitowa ya shiga motarshi. Direba
zai tada kenan tazo ta bude zata shiga. Aliyu ya
ce, (cikin tsawa) 'karki shigo min mota, sannan
banida buqatar sake ganinki a rayuwata.' Ta ce,
'Labari kake yi'. Ta dafa cikinta, 'in kai danka
ina? Kai ba ka san bala'ina ba ko? Za ka sha
mamakin abinda da zai biyo baya in har ka ki
tsayawa mu sasanta, Mujidat kawai ka sani
amma ba ka san halinta ba. ya daka ma Adewale
tsawa, 'Muje mana, 'Take ya figi mota suka yi
gaba in da har Mujidat ta ku san faduwa, kofar
motar ta rufe gam! Suka bar ta a nan. Ta bi
motar da kallo cikin kunan rai, a fili ta ce
'Wannan bai sanni ba, bai san yana cin
albarkacin so bane? Amma zai san ya kirama
kanshi ruwa.' ta nufi titi don hawa acaba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tun lokacin d muka samu sabani d Yaya
Aliyu,kusan ko yaushe dakin yarana ni ke kwana
don samun sauqin wasu abubuwan, ko na ce
tunane tunane. Yau ma niyyata kenan inna gama
can zani cikinsu in kwanta, zan fita dakin kenan
wayata ta soma ruri. Na koma kan gado na
kwanta sannan na daga tare da yina sallama. Ya
Aliyu ya amsa,sannan ya ce 'My choice
Alhamdulillah.'Na ce, 'Shin ne abin godiya. Ya ce,
'Ina mana murna gaske yarinyar nan ba ta da
(H.I.V). Na lumshe ido cikin jin dadi,amma sai na
tuno d cikinta, na ce 'To cikin fa? Ya ce, 'Ina
ruwana d cikinta, ban bi ta kanshi ba, don ba
matsalata ba ce,' Nace, 'Matsalarka ce, tunda
kwanka ne. Babu yadda za'a yi mace ita daya ta
dauki ciki. 'Raina ya soma zafi, ya ce 'Ni kadai
nayi hulda d ita?? cikin bacin rai na ce 'Amma kai
ka ajeta a gida.' Kuka ya subuce min, sai na
kashewayar nayi jifa da ita na ci gaba da kuka.
Inaji yana ta sake kira amma na qi dagawa, inna
tuno wai Aliyu shi ne ya yi ma wata ciki, abin nan
yana soya min rai. Duk ranar d aka kawo mana
dan me zai fada ma duniya? Mezai fada ma
zuri'arshi? Musamman yaranshi masu wayon
tsiya? Banji bude kofa ba, sai dai muryar kausar
naji tana cewa, 'Momi wanene? Da sauri na share
hawayena ta ce, 'Momi Abbanmu ba ya ce kun
daina fada ba? 'Na ce, 'Jeki dauko min magani,
kaina ke ciwo na kasa tashi ne. Da gudu ta fita,
saiga ta da shi har da ruwa. Ina sha ne naji
sakonni suna ta shigowa cikin wayata,na bata
kofin na ce 'Kije ku kwanta, kiyi muku addu'a zan
yi waya da Abbanku. Ta ce, 'Momi kin fasa yi
mana tarihin d ki ka ce za ki yi mana na rayuwar
Manzon Allah? Na ce,'kin ga kaina na ciwo,sai
gobe.
My choice ki bari mu sake daidaita kanmu, ki bari
mu saita rayuwarmu, ki amince da ban hakurina.
Tsaki naja sannan na duba dayan sakon.
Kin yi alkawarin cewa kin yafe min, kamata yayi
ki mance kmai,ina sonki my choice, kece
rayuwata.
Na sake jan tsaki a fili na ce, 'Kamar gaske. Wani
sakon ya sake shigowa.
Don darajar Allah da girmansa d darajar lokacind
muka kasance a baya, d martabar soyayyarmu,ki
amice da ban haqurina. Amicewarki kurum shine
daga wayata , xan kira ki yanxun . Dagawarki
itace zata tabbatar min cewa kin hkr.
Na ajiye wayar tare da yin rigingine na
kumaruntse idona, matsalata ina da rauni da
sanyin zuciya, bugu da kari ina son mijina.Bana
jure in wulakantahi, tausayinshi na daga cikin
abinda ke sa in kauda kai ga abubuwan da yake
min...ringing din wayarsane ya dawo dani
tunanina. Na dauki wayar tare da yin sallama
cikin makoshi , yace"ngd da daga wayata, yanxun
na yarda kin yafe min.Inason mu koma kamar
da, yanxun ki fada min abinda kikeson muyi.
Nace kamar me? Yace wlh bana son bacin ranki
ne, shine nake son ki tsara mana yanda zamu
shimfida sabuwar rayuwa, wadda baza ta katse
ba."Nace kamar gaske, kila sai kasa na soma
farin ciki daga baya ka canza min. Allah sarki
Sadiya sarkin son soyayya, sai gani ina 'yar
dariya, nace duk lkcn da ka so. Shima yayi 'yar
dariya.Inzo gobe? Nace koh yanxu ma ka zo.
Yace insha Allahu ranar jumma'a xan taho, roko
nike ma Allah yasa suyi min transfer zuwa
arewa.Nace amin yace ina yarana? Nace suna
dakinsu sunyi bacci. Yace, to bari in amsa waya
xan sake kiranki.Ba'a fi minti dayaba ya sake
kirana yace zan fita barayi ne a cikin wani kauye,
shi ne aka kira ni yanxun. Nace Allah ya tsare.
Nayi birgima a kan gado, zuciyata fes. Wata
zuciyar tace lallai ke dai sakara ce, duk irin
abinda mutumin nan ya kunsa miki shinecikin
mintin da bai kai 10 ba har kin manta?Nadan yi
tsai ina son inyi tunani, tabbas xuciyata
shagalalliya ce ma'abociyar son a sota, da zaran
abin son ta ya fuskance ta sai ta bude da yawa
ta shiga cikin farinciki.Idan abin sonta ya juya
mata baya sai ta shiga kunci ta tsuke , ta dinga
zafi. Nayi murmushi tare da rungume filo, a fili
na furta.Allah kakauda shedan tsakanina da
mijina. kullum yanxn ina cikin farinciki sbd xan
kira yaya a lkcn dana so, kuma shima yana
kirana, sannn ga hirar kwantar da hankali tare da
ban baki da yake min kullum.Tun ranar Alhamis
naje gidan kitso na kuma biya gurin mai zana
fulawr dayis tayi mana har da Kausar da Mama.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tun safiya Jumua'a na hana kaina sakat da
ayyuka. Funkasau na kwaba sai kuma farar
shinkafa, nayi kunun zaki na sayo fura.Duk
abinda nasan yanaso haka na tanade shi, a
wayarmu ta karshe baifi saura minti hamsin ya
isoba don haka na feshe yara nima na saka kayan
da bai sanni dasu ba, a sunan Aisha na dinka su,
atamfa ce blue mai ratsin yellow. Ina jin
kwankwasa gida nace su Kausar Abbanku,
maimakon su biyo ni kamar yanda da can
mukeyi, sai naga duk sun tsaya.Kausar ma hade
rai tayi, na kamo hannunta,kuzo muje mu taro
shi. Biyo ni sukayi , na bude gida jan gwarzo na
yau cikin kakinsa yake, ya aje jaka muka rungume
juna cikin murna da doki.Muka kalli yaranmu
lamarin ya zame musu tamkar sabon abu.Kausar
ma rufe fuska tayia lamun kunya.Al'ameen ne
ma naga yana tadariya. Muka kalli juna ni dashi ,
ya sakeni yaje ya rungumi Kausar, sannan
Al'ameen da ya aje shi ne ya dauki Maama ni
kuma na kwashi kayansa muka nufi ciki.Tamkar
da ya basu leda dauke da kayan ciye ciye tasu
tsarabar, nan muka barsu faloya shiga wanka,
kamar da nice na taimaka masa yayi wanka.Tsaf
ya shirya muka fito gurin cin abinci, yanda yaran
suka ganmu har sun soma sakin jiki, abinci kam
ya rasa da wanne xai soma.Ya kamo hannuna
yana yabon lallena, kausar dake can gefe tace
Abba nima kaga nawa, harda Mama akayi mana .
Yace , iye! 'Yan gata kunyi kyau yarana, nayi kasa
da murya ina cewa Kausar fa hankalinta yana
kanmu. Yace, duk zatonta yau ma rigimar
zamuyi? Nace wannan ya zama tarihi. Muka sa
dariya, daya kammala ya mike.Dauko hijabinki
kuzo mu fita. Yara suka hau tsalle muna gaba ni
da yaya, su kam suna baya.Gidan iya muka soma
zuwa, muka bata tsarabarta. Sai gidan Usman
nan ne ma muka dan dade.Sun kama hirar siyasa
ni kuma muka kulle da Anty Abida cikin daki,
shawarwari tayi ta bani kan cewa kada in sake
inyi fushi ko in dauki gaba da mijina don yana
bin mata.Yin haka zaisa ya kara zakewa.tace kin
ba shi dama kenan, amma in kika jawo shi kika
ninka abinda kike masa ada, kika hada da addu'a
sai kiga komai ya daidata. Nace bakisan wani
abuba Anty, yanzun yarinyar tana da ciki, ko
Usman bai fadawaba, abinda ke batamin rai
kenan, kuma tasha alwashin sai ta haife dan
cikinta ta kawo shi.Anty Abida tayi salati tare da
rike baki tace lallai akwai matsala. Nace nayi nayi
ya tsayamuyi shawara ni da shi amma yaki yace
in bar zancen. Tace shikenan tunda baya son
zancen ki kyale shi, Allah ya rufa asiri, nace amin.
Daga nan yayi ta yawo damu supermarket da
stores kalakala. Mun kwaso kayan ciye,ne da
suturu da takalma, ni kama har da mayafai da
jaka. Gsky ranar ya kashe mana kudi, haka muka
shigo gida nikiniki da kaya, yarana nadade sosai
bangan su cikin farin ciki kamar yau ba. Lallai
rashin jituwar iyaye ba karamin shafar rayuwar
yara takeyiba. Don Allah iyaye in wata matsala ta
gifto muku ku daina sa'insa gaban 'ya'yanku, don
gudun lalacewar tarbiyyarsu, tare da jefa rayuwar
su cikin rudani,Tun daga ranar dayace min yana
tafe nayi ta hada abubuwana ina sha , yanxun
ma zumata na samu na kada kwaina na hada na
shanye.Sabon wanka nayi na saka sabuwar rigar
baccin daya zaba in a fitar da mukayi, yanxun na
kama gashina shi kam yana falo yana kallon
labarai a tashar Aljazeera,Yara tuni sunyi bacci,
ban fito ba nima sai nabi kan gadona na fada
tsakiyar gadon nayi kwanciyata.Da zai yiwu in
bada labarin daran ranar kila da nan zan kare,
domin ya shiga sahun tarihin da ba zai gogu ba a
zukatanmu.A cewar yaya, daran ya dara na
farkonmu.Da safe mun tashi tamkar sabon aure,
cikin kwalliya muke aiki tare dashi a kicin.
kwanaki biyun da Yaya ya yi sai da na rubuta su
cikin dan kundin adana mahimman sirrikana. Da
zai tafi har kuka nayi. Allah sarki rayuwa,mun
koma tamkar da har mun fi da kyau,rayuwar
aure d zaman lafiya gami d soyayya akwai dadi.
Tuni Aliyu ya mantar da ni abinda ya faru a baya.
Kuma ko na tuna bana jin haushi,don na dauke
shi matsayin jarabta. Sai dai fa duk lokacin da na
tuna cewa wata tana can dauke d cikinsa ina
tsorata da abinda zai biyo baya. Kwatsam sai ga
shi anyo ma Yaya transfer zuwa Abuja.mun yi
murna don ganin Abuja ni ke tamkar kaduna,
tunda ya koma nan ba ya jimawa bai zo ba. Wata
rana har can Abujar ya kan tafi da mu muyi
hutun karshen mako. Rayuwa dai ta jin dadi
muna ciki. Kwatsam wani yammacin ranar Talata
ina tsakar gida ina kwashe shanyar kayan
makarantar yara da na wanke. A jikina ina sanye
da doguwar riga mai hade da hula blue da ratsin
fari,sai naji ana buga min gida, na nufi kofar ina
tambayr kaina ko wa ye?? Ina budewa muka
hada ido da ita, gabana yayi mummunar faduwa.
Ina zaton ko cikin duhu na ganta zan gane ta,
bare a haske,domin na sha ganin hotunanta cikin
facebook, tana sanye d doguwar riga ja hade d
mayafinta. Sannan tana janye d akwatinta, ga
wata ta rataya a kafada. Na dake na sake
dubanta. 'Malama daga ina? Kuma wa ki ke
nema? Ta ce, 'Nan ne gidan Aliyu Tukur jami'in
dan sanda? Na ce, eh nan ne. 'Sai naga ta turo
kai, na ce 'Ba ki minbayani ba kina kokarin shige
min gida. Tayi min wani kallo sama da kasa, 'Ni
bakuwarshi ce, Allah yasa yana gari? Na maida
kofar na rufe,tare d cewa 'Bayanan yana Abuja,
lafiya? Ta nufi ciki. Zo ki nuna min inda zan
zauna, a gajiye nike, don na wahala kafin na
gano gidan. Falo na sauketa duk da tafasar da
zuciyata ke yi, amma na danne har ruwa na
bata. Sannan na zauna na kalle ta. 'Baiwar Allah
daga ina ki ka zo neman Maigidana? Ta gyara
zama 'Ciki ya yimin,ta fada a gadarance ba tare
d jin wani nauyi ko shakka ba, ni kuwa duk da
cewa nasan batun sai da gabana ya fadi da jin
furucinta. nace, 'Ciki? Ta ce 'Eh, shi ne don
wulaqanci ya ci moriyar ganga zai yada
kwauronta? Bai isa ba. Sai yasan ya taba annoba.
Raina ya soma daukan zafi a gurin,na daga waya
na kira shi,ringing din farko ya daga tamkar yana
zaman jiran kirana ne. Ya ce,'Ya ya dai my
choice? Don in nuna ma Mujidat ban damu ba,
na ce 'Sweety kayi baquwane,da sauri ya ce,
Daga ina? Na kalleta tamkar ban san ds batunta
da shiba, na ce ya ce daga ina? Ta miqo hannu
'Ba ni wayar. 'Nayi 'Yar dariya. Ke ba ki d wayar
ne? Fadi kawai daga inda kike in sanar dashi.
Cikin son ta tura min haushi ta ce, fada masa
wadda yayi ma ciki ce. Kalmar tana dukan kirjina
in ta furta, amma na dake na ce 'Wai wadda ka
yi ma ciki ce. Na karasa zance da dariyar bakin
ciki. Da sauri ya ce, 'Mujidat? Subhnllhi! Lallai
wannan 'yar iskar tana son jaza min bala'i ne. Ta
ya ya ta gano gidana? Na tabe baki tare da cewa,
'Oho' ya ce, 'Kai wannan akwai 'Yar iskar yarinya.
Sadiya don Allah kiyi hakuri kinji? Zan taho yau
din nan kmai dare, amma yanzun ya ya za'a yi?
Na ce, kaika san yanda za ka yi da ita. 'Ya dan yi
shiru yana nazari, duk a rude yake,ya ce, 'Sadiya.
Na ce, 'Na'am, 'Ya ce, 'Kuna tare ne yanzun
haka? Na ce,'Eh. Ya ce, shiga daki muyi magana.
Na ce, To. Na miqe na nufi daki. Na shige Toilet
na